FreeArewaPen original
Ya Abin Yake?
- 1views
- 54chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
✍️ Welcome to the World of Nazeefah Sabo Nashe ✍️ If you love emotional stories, family drama, secrets, betrayal, destiny, and unforgettable plot twists, then you’re in the right place. 📚 My Published Novels: 🔥 ƘWARYAR WUTA (Now Available) ❤️ Me Zan Yi Da Ita? 🤔 Ya Abin Yak...
Sample · 2
_~ALƘALAMIN JIKAR NASHEYA ABIN YAKE ?LIttafin Nazeefah Nashe.***Paid bookFollow me on wattpadNazeefah381ELEGANT ONLINE WRITERS(Haɗin kai shine takenmu.)_2Free PageTuni hawaye ya b’alle daga idanun muneerah jin Abbu ya ce cikin zafin rai "Da izinin ubanta, kin ga sakina ki kiyayeni wallahi, ke Muneerah zo ki wuce kije kinji Allah yayi miki albarka.” Fuskar Ammi a ɗaure take jifa masa kallo mai cike da bala’i Ai kuwa Muneerah na fita ta sauke kwandon masifarta a kansa. “Na fa gaji da wannan rainin hankalin naka ba zaka dinga juyani kamar wata Ƴarka ba,ban maka dole ka zauna dani ba, haba ina dalili kayi ta sakin nawa mana sai me? Daɗin abin ba cusa maka ni aka yi ba, har ƙasar mu kaje ka yaudaro iyayena ka auro ni." tsaki yaja kawai ya fice yana jinta tana sake faɗar aikin banza, kuma wallahi ba wata shegiya da zan bari ta riƙe min ƴa, a barni idan ma kasheta zan yi na kasheta ai ta wace." Abbu girgiza kai kawai yayi yana mamakin Sakina da ko kaɗan bata jin nauyin furta masa duk maganar da tazo bakinta. A kullum kuma sai tayi wannan zancen na ba cusa masa ita aka yi ba wanda yasan gori ne kawai take wa Sadiya tunda itace aka yi musu auren haɗi. A zahiri ya ce "Ai fa, ko baki faɗa ba da zan iya nima da na sahhale miki, saboda na gaji da matsalolinki matsalar ɗaya ba zan iya ba, duk wannan hargagin a baki ya tsaya Allah ya riga ya jarrabeni da tarin ƙaunarki da ya riga ya zama jinin jikina, bana jin ma zan iya rayuwa babu ke, amma shi kaɗai ya san wahalar da take bashi wanda take rufe idonsa daga aikata adalci tsakaninta da kishiyarta duk da tarin haƙuri da biyayyar da Sadiya take masa amma sam baya mata so koda kashi ɗaya cikin goman da yake yiwa Sakina ya rasa irin wannan masifa ko fushi tayi dashi yana rasa sukuni har sai ta sauko yaga murmushinta sannan ya ke sakin ajiyar zuciya ta samun kwanciyar hankali. Bai sani ba ko don kasancewarta daga jinsin larabawa,shi yasa ya ke mata kallon tafi sauran mata?_________________________________Da sauƙi sosai a yanayin da ta samu jikin ƴar uwartata Muneerah ta sakar mata cute smile kafin cikin tsananin ladabi ta durƙusa ta gaida Mahmah, ita dai tana ganin mutuncin matar nan duk da ƙoƙarin cusa musu tsanarta da Ammi take. Sadiya ta shafa kan Muneerah kafin ta furta "ƴar albarka yau ba'a tafi Islamiyyar ba?" murmushi ta saki tana ajiye basket ɗin hannunta ta ce "Zuwa nayi na zauna kije gida ki huta kada su Humaid su buƙaceki don na jiyo rigimarsa ma da zan fito da na tambayi Saliha mai aiki sai ta ce wai Islamiyya ce ba zai je ba." Riƙe haɓa Mahmah tayi tace "Kiji min ja'irin yaro amma Humaid akwai ɗan kirki shikkenan bari naje na dawo bayan la'-sar sai na kwana da ita, kinga ai ba za'a barki ke kaɗai ba naga ma jikinnata da sauƙi ƴar nema ta sha allurai." Ta faɗa tana shafa gefen kuma...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.