UWAR MIJI KO KISHIYA?Free

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

UWAR MIJI KO KISHIYA?

  • 1views
  • 4chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Sunana Zainab Muhammad Umar wadda aka fi sani da (Indian Girl) Ni marubuciya ce mai ƙaunar marubuta da cigaban su domin alƙalami yafi takobi

More from @indiangirl20

Sample · 2

_*Bis-millahir-rahmanir-rahim*_         Duk dauriya irin tawa da ƙoƙarin ganin aman dake yunƙurin fitowa daga cikin ciki na bai fito ba hakan ya ci tura domin sai ta so min yake, ina jin tsoron fita bakin rariya domin gudun abin da zai je ya ya dawo tsakani na da uwar mijina Inna Salamatu da kuma kishiyata Hafsatu. A guje na miƙe nai tsakar gida sakamakon aman da ya taso min gadan-gadan, ban  tsaya ko ina ba sai bakin rariya na shiga kwararawa aman kamar wadda zan amayar da 'yan hanjin cikinna. Tun da na tsugguna ina faman kwarara aman Hafsatu ta fito ta ja ta tsaya jikin ɗakinta riƙe da ƙugu baki a sake cike da mamaki tana kallo na. Gaba ɗaya na galabaita sai da na ɗan dauki 'yan mintuna kamar biyar kafin na iya miƙe wa jiri yana ɗiba na, gabana ya yanke ya faɗi lokacin da na juyo nai arba da Hafsatu tana kallona cike da tsana sai girgije-girgije take da harare-harare. Da ƙyar na iya jan ƙafata na shiga daƙi na, buta na ɗauko na dawo bakin rariyar ta wanke baki na sannan na wanke wajen na juya domin koma wa daƙi. Tsawar da Hafsatu ta dakamin ce ta sa mai saurin tsayawa butar hannu na na ƙoƙarin faɗuwa. “Ke Zainabu! Meye haka? Me zan gani?”. Cikin kame-kame da in da-in da, Na ce“Am…Uhm…Dama…” “Dama uwar me? Nace dama uwar me munafuka? To wallahi! wallahi!! wallahi!!! Kin ji mai rantsuwar ɗan musulmi idan har abin da nake tunani ne a tare dake kin shiga uku a gidan nan wallahi!” Hafsatu ta faɗa cikin matsanancin ɓacin rai. Gabana ya buga da sauri; na dafe ƙirjina da hannuna ɗaya kafin na iya haɗa wasu 'yan kalmomi da zan faɗa cikin sanyin murya da tsoro, Na ce“Yaya Hafsatu ba fa abin da kike tunani ba ne kawai ɗan zazzaɓi ne nake yi”. Hafsatu Ta ce“Dalla can rufe min baki sha-sha-sha kawai ƙazama, bari Ahmadun ya dawo zaki sani ne!” Tana faɗar haka ta shige ɗakinta ta bar ni nan tsaye jiki duk a mace, da ƙyar na iya jan ƙafafuna nai cikin daƙi ƙirjina na lugudan bugu domin ban san wace masifa kuma zan faɗa ba dan ma Allah ya so ni Inna Salamatu ba ta nan yau da sai Allah ne ka ɗai zai cecen a gidan nan. Na faɗa kan gado na ina mai ƙare wa ɗakin kallo wasu zafafan hawaye na zubowa daga cikin kwarmin ido na zuwa kan dakalin kumatun fuskata, daƙi ne falle ɗaya wanda iya gado da kujera ɗaya ya iya ɗauka sai akwatina biyu babba da ƙasar wadda ke ɗauke da kayan sawata a ciki; Sai 'yan tarkacen kayan amfani na banbun ruwa ɗan madaidaici sai butoci biyu da 'yan kwanuka da tukwane biyu. Na sauke ido na ƙasa ina mai furta, “Duk da wannan halin ƙuntatar ta wajan zama da nake ciki bai isa ba sai an haɗa da wata jarabar duk kawai saboda kar na samu sukuni a rayuwata? Allah ga Zainabu Abu!” Na faɗa ina mai ɗaga hannuwa sama alamar roƙo sannan na sauke. A hankali na sauke idanuna akan lafaffen cikina wanda ba zaka taɓa tunanin ina cin a...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “UWAR MIJI KO KISHIYA?” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play