MATAR ARO..Free

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

MATAR ARO..

  • 1views
  • 2chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Arewabooks@cutiemeerat

More from @cutiemeera

Sample · Chapter 1

🌺MATAR ARO..🌺🥀      BYHAUWA'U OMAR   (Cutiemeerat)Page one…1      بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ.             Ba abin da kake ji sai kukan tsuntsayen dare da busar iskar dake karkarwa. A tsakiyar wannan dokar dajin, inda ko kura ba za ta sha'awar yawo ba, wata yarinya ce take takawa cikin sanɗa. Kanta ɗauke da wani katon tulu wanda ya riga ya addabi wuyanta, nauyinsa yana neman murkushe kasusuwan bayanta.Kowane taku daya da take yi, hawaye masu dumi suna rige-rige a kan fuskarta, suna ɗiga a kan kirajinta dake bugawa da sauri saboda tsoro. Ba takalmi a kafarta, haka take takawa a kan busassun ganye da ɓoyayyun kayoyi.Kwas!Ta taka wani busasshen icce, wanda ya soke karkashin kafarta har cikin jijiya. Yarinyar ta gimtse baki, idanuwanta suka firfito waje saboda azaba, amma ba ta da ikon sakin kukan da yake cin makogwaronta. Ta san idan ta tsaya, duhun dajin zai haɗiye ta, idan kuma ta koma gida ba ta cika tulun nan ba, abin da yake jiran ta ya fi duhun dajin nan ban tsoro.Ta saki wani nishi mai nauyi, tana jin dumin jinin dake fita daga kafarta yana gauraya da kura. Ta kalli sararin samaniya wanda hadari ya lullube, muryarta a rafe ta ce, "Ya Ubangiji, shin ni kadai ce ba ni da gurin fakewa a duniyar nan?Iskar dajin ta kara karfi, tana tura ta baya, yayin da take ci gaba da jan kafarta mai jini, tana fatan hantsi ya yi mata a cikin wannan dajin koda za ta ga hasken rayuwa..."Wai ashe kin dawo?" Muryar Maman-Yara ta fito, ba tare da ko digon tausayi ba. Ta fito tana gyara ɗaurin zanenta, idanunta suka sauka akan tulun ruwan. "Daga zuwa diban ruwa sai kace wacce aka kora yaƙi? Maza wuce ki hura wuta, ki ɗora ruwan zafi na wanka, sannan ki tabbatar kin share dukkan gidan nan kafin kowa ya farka."Yarinyar ta buɗe baki za ta yi magana, muryarta ta dashe. "Hajja... ƙafata...""Dalla rufewa mutane baki!" Hajja ta katse ta da wani hargitsi  mai cike da tsana. "Koda ƙafa ɗaya kike da ita, yau sai kin yi aikin gidan nan. Idan kuma kika kuskura kika zauna, to wallahi ba ke ba abinci har sai randa kika ga dama."Yarinyar ta runtse idanunta, ta juya tana dingishi ta nufi wurin icce. Tana ji a ranta cewa wannan rayuwar ta yi mata nauyi. Ta ji kamar ita ɗin wani tsumma ne da aka ara, wanda mai shi bai damu da ya yage ko ya ɓaci ba. "Ya Allah, idan har a gidanmu ni din 'Matar Aro' ce wadda ba ta da daraja, to a ina zan sami tawa madafar? Shin mutuwa ce kawai mafitata?"Ba ta gama wannan tunanin ba, Hajja ta fito da wani lallausan zanen gado (bedsheet) ta wurga  mata a kai. "Maza wanke wannan yanzu, kuma ki shanya shi ya bushe kafin azahar. Idan na dawo ban ga ya bushe ba, yau a waje zaki kwana wallhi shegiya dangin mayu!".....Cikin ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters2
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play