🔱🔱ṨÄQÄŔ ṨÖ🔱🔱               ⚜️🗝️  ( _love cub_ ) 🗝️⚜️

EPISODE 1

by @asmau

🔱🔱ṨÄQÄŔ ṨÖ🔱🔱

              ⚜️🗝️  ( _love cub_ ) 🗝️⚜️


Mallakin :Queen Nasmerh

Marubuciyar 👇

1:Ayisherh

2:Mrs Bilal

3:Mrs Bilal continuation

4:Barrister Muhammad

5:Wani hanin ga Allah

6: Fayroz

7:Hajna


And now 8:SAQAR SO.


Praise be to Allah he who give me the opportunity to start this book, with the tittle (SAQAR SO) 💃🏻💃🏻💃🏻, YA ALLAH, YA RAHMAN, YA ZALJALALU WAL-IKRAM, YA KAREEM, YA MALEEK, YA AZEEZ, YA JABBAR, YA BAQIR, YA MUSAWWIR, YA JALAL, YA QUDDUS, YA ALLAH! YA ALLAH! YA ALLAH, Thank you for everything.


To My dear readers ❤️❤️❤️❤️

Many of you read my blogs, and have followed me through my different life experiences. In a sense, you have watched me grow up. Some of you readers have been there from the beginning – you’ve witnessed me through my career changes, mistakes, and ever-evolving perspectives. I want to take a moment and say ‘thank you’. I would have never had the courage to share my personal stories and vulnerabilities if it wasn’t for the strong love and support from my community. Every ‘like’, comment, WhatsApp, Twitter, Facebook , and second you spend reading my articles is appreciated. You are the reason I write.


If one of my articles can help one other person feel a little less alone, a little more understood and consider a perspective that could create positive change, then to me, that is success. I encourage you to join the conversation – talk about the topics that are considered to be too uncomfortable. Strive to be authentic, not perfect.  Share your vulnerability – that’s what enables humans to connect. And know that there is always someone listening – so be mindful of what you do put out there.


I’d like to sign off with a big thank you. Thank you for reading and for helping me grow as a writer. But most of all thank you for being a part of my journey…

With love,

Queen Nasmerh ❤️❤️❤️❤️❤️


بِسم الله الرحمن الرحيم

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai- in d Name of Allah the beneficent the most merciful.


Wannan littafi ƙirƙirarren labari ne, ban yi shi da niyyar cin zarafin kowa ba.


Na rubuta shi ne da dukkan nin zuciya ta ❤️❤️❤️❤️i write this with all my heart.


Masu karatu duk abunda kuka ji, kuka karanta kuyi haƙuri haka tsarin labarin yazo, kuma na riga na gama tsara komai, Allah yasa saƙon ya isa yadda nake so.

Bazan taɓa mantawa da soyayyar ku a gare ni ba GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION, ❤️❤️❤️har abada zan kasance me godiya a gare ku, nagode sosai.


Masoya na bazan manta da ku ba, Maimuna Abdullahi heroine (my moon❤️), Ni'ima Sulaiman Nimcy love (my beb and stubborn friend ❤️), ban manta dake ba Fateema Mhiss Flower (habeebty ❤️), Anup junyau and nana khadi (behties), Fauziya d Sulaiman (my aunty ❤️), Aisha bagudu (my sister ❤️), Rahama koise (loml), asli Smasher (hayatee❤️), Aisha (bali❤️) da sauran su, idan nace zan zayyano ku duka to tabbas zamu kwana, wannan shafi naku ne, sadaukar ce gare ku, i love so much ❤️❤️❤️❤️❤️❤️.WANNAN SHAFIN NAKU NE, DA SOYAYYAR TA A GARE KU🗝️🗝️🗝️❤️


EPISODE 1 - At work

°°°°💗°°°°


Daga cikin bathtub na ji motsi, amma bazan iya ganin wanda ke ciki ba kasancewar akwai ruwa wane cotton daya lulleɓe guri gaba ɗaya, tsayawa nayi na ƙarewa toilet ɗin kallo, babba ne sosai girman ɗakin wata ne, komai tsaf yake, komai na toilet ɗin fari ne, hatta cottons ɗin dake liƙe a window fari ne, da wanda ya lulluɓe bathtub ɗin, nafi minti 40 a toilet ɗin amma wanda ke wanka be fito ba, ballantana nasan wanene a ciki, fitowa nayi daga toilet ɗin, na dawo ɗaki, masha Allah, a ɗakin ma komai fari ne, sannan akwai mudubi ko ina a ɗakin, dan wardrobe ɗin kanta duka madubi ce, sannan ga dressing mirror, komai na ɗakin a tsare yake, carpet ɗin ƙasa na kalla itama fara ce, idan ka kalle ta bazaka ce an taɓa taka ta ba.


   Ina gurin ina kallon ikon Allah naji ƙarar buɗe toilet, da sauri na sauke ido na akan ƙafar wanda ke fitowa, wanda haka ya tabbatar min da macece, ƴan yatsun ta masu kyau ne sannan farace ita sosai, tun daga ƙafar ta nayo sama, hips ɗin ta sun fito sosai dan sun wuce ace musu coca cola shape, shape ɗin ya wuce misali, da alama zata ja hankalin mazan, dukiyar fulanin ta ma suna da girma amma ba sosai ba suma dai-dai, ba suyi yawa ba kuma ba suyi kaɗan ba, fuskar ta nake kallo, masu karatu wannan yarinya ta haɗu, sai dai mu ce tsarki ya tabbata ga ubangijin dukkan halitta, dan gaskiya gurin nan anyi halitta mai kyau, bakin ta bazaka ce mashi ƙarami ba, kuma ba zaka ce mishi babba ba, hancin ta dago ne sosai, idon ta dara-dara ne, ko yaushe a lumshe suke, amma idan ta gwale su zaka ƙara tabbatarwa ita ɗin mai kyau ce.


   Gaban dressing mirror ta nufa, inda ta shiga shafa wancan ta shafa wancan, tashi tayi cikin tafiya ta ƙasaita tana motsa ko ina na jikin ta, wardrobe ta nufa , buɗe shi tayi ta ɗauko wata arniyar doguwar riga ta atampha wanda sai ka rantse ƴan kanti ne, dan ba zaka ce ɗinka su aka yi ba, saka wa tayi inda ɗinkin yayi matuƙar karɓar jikin ta, turare ta fesa kala-kala masu ɗaukar hankali, dan ƙamshin zai iya ruɗa mutane, fuskar ta ba wata kwalliya, sai kwallin da ta shafa kawai, murmushi tayi lokacin da ta ƙarewa kanta kallo gaban madubi, masu karatu fararen haƙoron ta suka bayyana masu ɗauke da haƙoran makka, sannan daga tsakan haƙoran akwai ƴar tazara kamar wushirya wadda ta ƙarawa haƙoran nata kyau, dimple ɗin ta na side chicks ya bayyana, gashin kanta ta naɗe wanda sai yanzu na lura dashi, dogo ne ga laushi da santsi, naɗe shi tayi sannan ta kawo ɗan kwali ta ɗaura, da alama gwana ce, dan ɗaurin yayi matuƙar yi mata kyau, gyale ta ɗauka medium size ta saka, sannan ta saka flat shoes kasancewar ita doguwa ce bata buƙatar high heels, jaka ta rataya, tafi minti uku tsaye gaban mirror tana murmushi, sannan ta ɗauki wani cin gum dake kan dressing table ɗin ta, ɗaya ta ɓalla ta saka a baki, ta fara taunawa a hankali, cin gum ɗin na strawberry, haka yasa duk numfashin da zata fitar ya zama na strawberry.


     Tafiya take yi cikin isa da ƙasaita, har ta sauko daga upstairs, dan tasan zuwa yanzu kowa yana parlor, wata matace zaune akan kujera, ta sanya wata doguwar riga ta atampha tayi matuƙar yin kyau, zuwa tayi ta rungume matar, “good morning Ummie na"ta faɗa tana mata peck a goshi, murmushi ya bayyana a fuskar wadda ta kira da Ummie, “Leesha kin tashi lafiya? "Ummie ta faɗa, “lafiya ƙalau Ummie na, ina Ishtar da Zaina suke? ", murmushi Ummie tayi tace “Ishtar da Zaina suna ɗaki, wai sun gaji da jiran ki shine suka wuce ɗaki ", murmushi Leesha tayi tace “Ummie ki cewa Ishtar waya damu dan bata jira shi ba, ita kuma autar ki ki faɗa mata yau bata da chocolate "ta faɗa tana tafiya da alama fita zata yi, “Leesha ina zaki baki ci abinci ba" Ummie ta faɗa, “Ummie bana jin yunwa, zan nemi abun motsa baki a hanya "ta faɗa tana wucewa, Ummie ta girgiza kai tace “har yanzu kina nan yadda kike da rashin son abinci".


   A harabar gida kuwa, faɗa na sami tana yi “kai wani irin sakarai ne, tun yaushe na faɗa mata bada wannan zan fita ba, yau da farar mota zan fita ", “yi haƙuri Hajiya Leesha, itama farar an wanke ta ai" mutumin dake wanke mata mota ya faɗa, “to shikenan kira min Adamu "ta faɗa, da sauri Adamu ya taso, “gimbiyar mata Allah ya ƙara miki daraja" ya faɗa, “ya isa haka, ga mukullin mota muje "ta miƙa masa mukullin mota da alama drivern ta ne.


A gaban wata ma'aikata suka tsaya, ɗaga kaina sama nayi naga an rubuta ABEER GLOBAL COMPANY INTERPRICES, haɗe fuska tayi ta fito daga cikin mota, tafiya take yi kamar bata son taka ƙasa, amma haka bai hana gangar jikin ta motsawa ba, mutanen ma'aikatar sai kwasar gaisuwa suke yi, tafiya take yi har ta shiga ciki, wow masu karatu wajen bakomai bane idan aka haɗa da cikin, ko ina Ac ne, ga cc TV ta ko ina, cikin wani office ta shiga, babba ne gurin sosai, zama tayi kan kujera tare da aje jakar ta, files ta ɗauka ta fara signing, tana dubawa, knocking ƙofar aka fara yi, ɗago kanta tayi dake ƙasa tana kallon ƙofar, buɗewa aka yi, wata mata ta shigo sanye da gajeren skirt wanda ake kira da mini skirt, rigar ta fara ce, skirt ɗin kuma baƙi ne, kallon yarinyar tayi tace “Anita what's ur problem? "(Anita minene matsalar ki?), “u have a visitor" (kina da baƙo) Anita ta faɗa, Leesha tace “tell him that am busy right now, let's meet tomorrow by 1:30"(ki faɗa mishi ina aiki yanzu, mu haɗu gobe da misalin ƙarfe 1:30), “ohk ma "Anita ta faɗa tare da fita daga office ɗin.


  Anita tana fita ta sami mutumin tsaye yana jiran ta, matsowa yayi, da saurin shi ya ɗauka yau an dace, dan zuwan shi office ɗin nan yafi sau biyar amma be haɗu da Leesha ba, kullum sai ace mishi tana aiki, “u are ask to come back tomorrow by 1:30"(an umarce ka da ka dawo gobe da misalin ƙarfe 1:30)Anita ta faɗa tana juyawa zuwa gurin da aka aje ta, shi kuwa ranshi a ɓace ya juga, wani mutumi ya ce “Omar Faruk ka samu ganin hajiyar ", cikin takaice da haɗiye takaice yace “a'a baba, wai ita wannan yarinyar dama haka take da wulaƙanta mutane?", mutumin da ya kira da baba yace “a'a Omar, Leesha ta kasance mai mutunci, amma tabbas kam, tsawon shekarun da na ɗauka nan, na fahimci halin ta ɗaya da mahaifin ta Alhaji Abeer, mutum ne da baya so talaka ya raɓe sa, amma kuma suna da kyauta, da mutunci, zasu maka kyautar da har abada zaka daɗe kana jin daɗi, amma zasu maka wulaƙancin ds har ka mutu bazaka manta ba"baba mai gadi ya faɗa, Omar yace “to miye amfanin kyautar, bayan ba su daraja mutum ba ", baba mai gadi yace “su ko mai kuɗi idan suka ga dama wulaƙanta shi suke", Omar yace “ni bansan inda zan samu taimako ba, dole na haƙura na dawo, ƙanwata Farrah tana buƙatar taimako, amma ni na tsane mutane masu irin halin ta, har abada bazan so ta ba ", dariya baba mai gadi yayi yace “yau naga mutum mai ƙarfin hali, to kai wayace maka Leesha zata so ka, kai dai kawai kayi biyayya ka samu abunda kake so a wuce gurin dan mai so shike nema", gaɗa kai Omar yayi yace “to shikenan baba ni zan wuce sai gobe, in Allah ya yadda ".


To masoya na, ku biyo ni dan jin wannan ta ƙaddamar, shin gobe idan Omar ya dawo ko zai ga Leesha?.


Ku kasance dani a next episode.


Kuyi following account ɗina na Wattpad, ta link ɗin dake sama domin bibiyar labarai na ta reading list ɗina, Asmaunanalawalliman reading list.

Love u all my fans❤️.


ALQALAMINA YAFI KO WANE TAKOBI KAIFI.✍️💃💃💃💃💃