RAYUWAR HUSNAH

CHAPTER 1

by @milhaart

💫💫💫💫💫💫💫💫

 *RAYUWAR HUSNAH*

💫💫💫💫💫💫💫💫


 _(Ni da Yarima)_😭



 _(A Love & sympathetic Story)_

🥺🥺

By

Fadeelah Yakub

Milhat


Marubuciyar✍🏻

1)MATAR AURENAH

2)SAIRAH DA SARAH

3)DALIYAH DA DANIYAH

(Cigaban Sairah da Sarah)


      *AND NOW* 

 ```RAYUWAR HUSNAH``


 *RAYUWAR HUSNAH*_ ```Labarine Wanda ya kunshi Soyayya,tausayi, makirci da dai sauran su......``` 


 *Note* _```Bamu yarda wani ko wata su juya mana Labari ba, ba tare da izini ba

```

🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️


   M. W. A 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻``` 

***

_________________________


 Wannan labarin kirkirarren labarine , ban yi shi dan wata ko wani ba , idan labarin yazo dai dai da naka to akasi ne ban yarda wani ko wata ta sauyamin labari tako wani siga yin hakan babban kuskure ne 


```Ina goɗiƴa ga Allah daya bani iko da na fara littafin nan, yadda na fara lafiya Allah kasa na karasashi lafiya.

``` 

 _Wannan labarin sadaukar ga masoyana, Allah ya bar ƙauna_ 


 *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


 CHAPTER 1

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Nigeria, cikin Jahar Gombe a karamar Hukumar Yamaltu deba, garine mai tarin Albarka da kwanciyar hankali, anyi wani adalin sarki mai tarin dukiya, USMAN YUNUSA SANI d'an sarki jikan sarki, Yana matukar son jama'un sa sannan Yana mulki yadda yadda dace kowa Yana yabon kyawawan halayensa hakan yasa Babu kamar sa a yankin.


Kamar kullum zaune suke a fada dashi da fadawansa Hira suke Cikin nitsuwa kana ganin su kasan akwai kwanciyar hankali, sarki na zaune Akan gujerar sa yayin da fadawansa na tsaye a kansa sauran manyan mutanen gari Kuma na zaune a gefen sa, bayan sun gaida sarki ya amsa cikin satin fuska sai ya Fara bayani kamar haka.


"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah a yaune ya kamata a sa Ranar da Yarima zai zab'i amaryar sa kamar yadda al'adar mu ta tanadar, idan Allah ya ara Mana Rai gobe a dai dai wanna lokacin Yarima zai zab'i amaryar sa"


Jama'ar wurin kowa ya Fara fad'an Albarkacin bakin sa, "Allah ya jaaa zaminin sarki, Allah ya nuna Mana"


'daya daga cikin fadawansa ya Tashi yace "Ina Mika sakon gaisuwata ga sarkin da dukkan mutanen da suka hallarci taron Nan,Ina fatan Allah ya kaimu gida Lafiya kamar yanda muka Zo lafiya"


Duk suka amsa da Amin, sai ya d'aura da fad'in "Allah ja zamanin sarki, Ina so a bani izinin zuwa kauyen KURI don gayyato mawaka da masu rawa don ba a yin zab'en gimbiya ba tare da anyi amfani da kid'a da rayeraye ba"


Sarki yace "Tabbas hakane, ka ga har na manta da al'adar an baka izini" ya Karasa maganar cikin dariya.


"Toh ranka shi dad'e" Nan take yaje har kauyen KURI, Yana zuwa ya gaiyaci mawakan duk matane.


Washe gari


A fadar sarki kowa da kowa yazo yara da manya, sannan akwai emmata shida Wanda acikin su Yarima zai zab'a, rawa ake sosai ana raye Raye ana ciye ciye da shaye shaye, ana cikin hakan ne d'aya d'aga cikin fadawa Yace "Rawar ya Isa Haka yanzu lokacin da Yarima zai zab'i gimbiyar sa" wurin ya kaure da tafi da gud'a.


Tun da aka Fara wasanni Yarima Hankalin sa baya Kan Emmatan da ya kamata yayi zab'in sa aciki, duk Hankalin sa ya Koma Kan d'aya daga cikin masu Rawar, a zuciyar sa cewa yake "ita ce zab'ina"(Ni ko nace Anya Yarima Kai da aka zab'a maka kyawawan gari har shida Amma Kuma kake kallon Wata daban)


Wata budurwa ta Tashi ta gaida sarki da sauran magabatan su cikin ladabi da biya ta gabatar da kanta Kamar haka "Ni 'ya Ce ga marigayi Sani Hassan, nice wacce Zan gabatar muku da Emmatan da aka zab'a a wannan shekarar" aka Mata tafi.


Nan ta Koma kusa da Emmatan da, Kiran sunayen su ta farayi d'aya bayan d'aya tace "Yarima wannar kyakkyawar yarin da kake gani 'yace ga Mal Tanko, sunan ta Hafsah, bismillah Hafsah ki gabatar da Kan ki"


Bayan ta gaida su cikin girmamawa tace "Suna na Hafsah Ina so na mallaki Yarima sabida jinin sarauta a jinin jikina take nagode" ta na maganar cikin Ji da Kai da ta Kama, aka Mata tafi ta Koma mazaunin ta.


Sai ta biyu ta fito tace "Yarima na, suna na Fateemah,ka dube Ni da kyau" tana maganar tana karairaya tana juya jikin ta, ta d'aura da fad'in "Yarima nice irin macen da ko wani d'a na miji yake muradin samu sabida Allah ya min diri, Nagode" aka Mata tafi ta Koma ta zauna.


Ta uku ta fito, tun Kan ta karasa inda Yarima yake take washe Baki, kana ganin ta kasan wawayi ce Sai kace Mai tallan close up batada wayewa Tace "Hahaha Yarima suna na, Amina Burina shine na Zama matar ka a Kirani da sarauniya, Nagode" duk sai da akayi dariya Kan aka Mata tafi ta Koma mazaunin ta.


Ta Hud'u tana fitowa tafiya take da takama da izza tafiya take kamar baza ta taka kasa ba kana ganinta kasan maras kunya ce bayan ta gaida su tace "Yarima suna na Zainab, Babu wacce ta dace da Kai sai Ni sabida idan ka duba Ina Kama da Kai Kuma kana Kama Dani, Nagode" ita ma aka Mata tafi ta Koma ta zauna. (Ni ko nace Hajiya Zainab gaki baka kamar uwar mu d'aya dake kice kunyi Kama gani nayi Yarima fari ne)🤣


Ta biyar itace wacce ta fi su kyau, kaf cikin su shida Babu Mai kyawunta, Tace "Yarima ba sai na tsaya dogon surutu ba suna na Aisha, Kyakkyawa son Mai so kin Wanda bai samu ba, ka zabe Ni na tabbata baza kayi na dama ba Nagode" akayi Mata tafi ta Koma.


Ta shida tafiya take a nitse kana ganin ta kasan ta samu tarbiya Mai kyau, tace "barka da war haka Yarima da fatan kana lafiya,Suna na Salma, Yarima Ina so na zama zab'in ka sabi da Zan taimaka maka don ganin ka Zama cikekken mutum, zaka Zama sarkin da ba a tab'a yin irin sa ba sannan na Zama uwa ga 'ya 'yan ka na musu tarbiya ta gari, Nagode" ta Koma ta zauna aka Mata tafi fiye da yadda akayi wa sauran.


Sarki ya Mike yace "Masha Allah" fuskar sa d'auke yake da murmushi yace "D'ana Tashi ka nuna Mana zab'in ka"


Wani saurayi na gani ya taso, fari ne tass dogo Mai saje, Mai dogon hanci, da d'an karamin pink lips, yayi Shiga ta alfarma irin nasu na sarauta, murmushi yake Wanda ya sa dimple d'in fuskarsa ya bayyana, sai da yabi Kan su d'aya bayan d'aya, ya kad'a Kaai bai tsaya b'ata lokaci ba ya nufi inda masu kid'a suke gaban wata Yar budurwa ya tsaya Yana kallon ta Yana Kuma mamakin kyawun ta, farace ba doguwa bace Kuma ba gajera bace Yar madaidaiciya, tana da Kyan diri sai dai ace Masha Allah.


Yace "Sarki Wannar ita ce zab'ina" kowa na gun sai da ya tsorata da ganin zab'in sa, sarki, matar sarki da kanwar Yarima duk suka tsaya, suna kallon sa cike da mamaki.


Yarinyar da ya nuna babu Wanda ya ya kaita Shiga tashin hankali, yace "Mata ya sunan ki?"


Nuna kanta tayi tana duba bayan ta ko akwai wata Amma taga ita kad'ai ce murmushi yayi yace "dake nake ya sunan ki?" Ganin ta rikice yasa ya riko hannun ta ya kawo ta har gaban sarki, yace "Ita ce zab'ina"

Sarki yace "Khaleed baka da Hankali ne? Ka dawo cikin hayyacin ka"


"A cikin hayyacina nake Abbi, itace wacce na zab'a a matsayin wacce Zan aura"


Mahaifiyar sa Tace "Haba Khaleed Ina ka tab'a Jin anyi hakan? Yin hakan ya sab'awa al'adar mu"


Sai kanwar sa Mai suna Khairat tace "Yayana ka duba fa da kyau yarinyar Nan ba Yar garin Nan bace ba, Kuma kace zaka Aure ta?"


Yarima yace "Ya salam me yasa kuka d'auki abin Nan da zafi ne? Kunce na zab'i mata Kuma na zab'a me aibunta?"


Sarki yace "Ke" a tsawace sai da ta tsorata don ita tun da aka Fara maganar ta riki Ce "Ya sunan ki?"

"Suna na Hus... Husnah"

"Tare da masu rawa kuka Zo Nan ko?"

 Cikin inda inda tace "eh tare muka Zo"

"To maza ku fice min daga gari ko na sa a d'aure ku" Rai a b'ace.


Da gudu ta bar wajen sauran Yan uwanta suka bi bayanta sun Kai su goma wurin duk kura, Shima yarima bin bayan su Yayi a guje Yana musu magana Amma Basu tsaya ba, sarki Yana Kiran sa Amma yaki juya wa, gudu suke shi Kuma Yana bin bayan su Basu dai na gudu ha Shima Kuma Bai daina bin su ba, har suka fita daga cikin garin mutane biyu daga cikin su da suka gaji suka tsaya suna jaan numfashi, ba zato ba tsammani suka ji muryar Yarima Yana fad'in Ina take?"


A zabure sukayi niyar cigaba da gudu, sai yace "ku tsaya bazan cutar daku ba Dan Allah ku Sanar dani, Yar wace garice Kuma waye mahaifin ta?"


Sai d'aya daga cikin su Tace "Husnah Yar Mal isma'il sanenne mutum ne a Kuri"


"Kin tabbata idan naje Kuri na tambayi sunan za a kaini gidan su?"


"Eh insha Allah za a Kai ka"

"Toh Nagode sosai"Sai yayi tafiyar sa sai d'ayar tace "Khadija meyasa Kika fad'a Masa inda take?"

"Habiba Allah fa yace Kuma Husnah kawar mu ce ai abun farin ciki ne idan ya Aure ta"

"Wani irin farin cikin?"

"Kinga bani da lokacin ki in bazaki tafi ba Kinga tafiya ta"


Khadija tayi tafiyar ta, ta barta a tsaye a gun, Habiba kallon bayan ta ta tsaya yi kana ganinta kasan tana cikin b'acin raai, sai Tace "zamu gani" a bayyane, ita ma ta bi bayanta.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

 

Ya kuke ganin zata kasance zab'in wa za'a bi? Zabin Yarima Khaleed ko Kuma al'adar su za a bi?