KOFAR AJALI Book 1

EPISODE 04

by @abdull10k

πŸ’€πŸ’€πŸ’€

          *KOFAR AJALI*

'''[when in no way out]'''

                           πŸ’€πŸ’€πŸ’€


_________________________


*Written*

Abdul Alhaji musa 10k

*phone no:*

***

_________________________


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πŸ“šπŸ–ŠοΈ*


                        *M. W. A*


'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»'''


_________________________


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*


*FREE BOOK*πŸ’―βœ…

*EPISODE 0⃣4⃣*


Wani kara suka soma ji kamar ta motsin mutum nan sai Harun yace dasu....


"Dan Allah kowa ya kama inda yake,ku daina motsinnan dan kuna tsorata mu....

Atif and Samra nasan kune"


"Taya zakace mune bayan....."

Haka Samra ta soma furtawa amma sai taji Atif yayi shiiiiiiiiiiiit alamar tayi shiru.


Hakan ko sukayi suka kasance sunyi tsit suna jiran mai zata biyo bayan shirun da sukayi......


Soma jiyo wata sauti sukayi *DIM DIM DIM* kaikace sawun samudawane.......

⬇⬇

Wannan sautin bana komi bane illa wasu sanduna dake rarrataya a jikin bago bangaren ne,hagu da dama,suke kamawa da wuta.....domin bada haske.

Soma ci wayennan sanduna sukayi yayinda haskensu ta haskake farfajiyar gurin na y'an wasu dakiku kadan sa'annan suka sake kafewa,haka Suka sake tsintar kansu cikin wannan duhu a karo na biyu.


Sake jiyo wannan karar cen nesa na yowa ta gurin su inda suke iyya hango hasken ta daga cen nesan nanko suka yanke shawarar bin wannan haske da zarar ta karaso cewar mu'azz *wata kila hanya take son gwada musu.*


Haka ko suka laminci zancen suka kuma ankare suna jiran wannan haske ta karaso,kamar yadda suka tsara haka abin ya tafi ba sabani..... wannan haske na ratsowa inda suke suka bita a guje yayinda ta kasance tamkar fitulu dake haska musu hanya.....duk da cewar tana kunnuwa na bayanta na daukewa......


Haka suke guduwa yayinda duhun kebinsu a baya.....Basu kuma tsaya da gudunan ba har saida suka tsinci kansu a wani guri mai dan karen guhu ga kuma zafi har nunfashin mutum na yankewa ya kuma dawo....nanfa Mu'azz yayi danasanin shawarar daya bayar danko wutan nan ta dauke sa'annan basu da damar komawa inda suka fito,domin basuma  gane inda suke ba....


Suna cikin wannan yanayi na kaka nakayi sai Samra ta soma cewa.....


"Zamu iyya kwana uku batare da munci ko munsha ba,mako guda batare da mun sami hutu ba amma bazamu iyya minti goma ba tare da shakar iska ba....dukkan mu mutuwa zamuyi"

Cikin muryar kuka ta furta hakan...


,Furta wannan kalma ta mutuwan da Samra tayi keda wuya sai gurin ta dau shecking [girgiza] kaikace tashin Duniya..

Ga bakin Duhu ga rashin Nunfashi ga kuma girgizar....sa'anan basu masan akanmeye suke tsaye ba.


Al'amarin Wannan halitta Mai Kama da jamage kuwa tsintar kansa yayi a wata kazamemmiyar guri......Gurin na d'oyi matuka gakuma kukan kananun kwari da suka cike gurin.

Nan da nan ya kime ganin kansa cikin duhune yasakashi bude tafin hannunsa nan sai wuta ta tashi cikin tafin hannun nasa.


Ganin hakan keda wiya yawani jujjuya tafin hanun nasa cikin salon burgewa nan wasu abubuwa suka soma fitowa tacikin tafin hannun nasa.... Suna kuma haske yayinda suka kasance cikin suffar malam bude littafi.....haka suka mamaye saman sa.

Nan da nan Guri tadau haske matuka,ganin haka yasashi komawa halittarsa ta ainihi wato wata kyakyawar y'a mai farar idanu ga kuma gashi har gadon baya...


Cikin farar kaya take wacce akayi mata ado dajan furan ni.....

Nan sai tayi kama da y'ar shekara 15...


*Cigaban labari*


Wannan guri da take kuwa takasance tamkar bolar matattune.....Danko gawarwakine birjik a gurin.....

(Hmm Harna tuno da wani sharerren littafi na marubuci king articles, *Gidan matattu* )


Gani kanta cikin wannan yanayi yasa ta saki fuska alamar takaici,jujuwa take tana ta ganin gawarwakin iri daban daban,na muggan halitu ne,na aljanu ciki harda na Bil'adama......

Mafiyaa yawa a gurin sune Bil'Adam saikuma

Jinnu,sannan wasu halittu na daban.

πŸ’€

Al'amarin su Atif kuwa sun kasance cikin wannan duhu hade da girgizan kasa sa'annan nunfashi na yankewa na wasu dakiku kafin suka soma ganin wata jar haske na fitowa ta kasa yayinda kasar ke tsage.

Wannan hasken ne tadan yaye musu duhu suka soma ganin idanun juna.


Haka sukayi ta gujema wannan tsagewar ta kasa har ta kai ga rabasu gida biyu,bayan takai ga rabasun ne wannan girgiza ta tsaya haske ta haskake koyina sa'annan kasar ta daina tsagewa,kamar daukewar ruwan sama cek haka ta tsaya.....Harun ko yace.....


"Kar kowa ya motsa,bamusan maike lullube akasan wannan guri da muke ba.....

Dan haka karmuyi saurin fadawa wata matsifar kuma"


Haka ya furta cikin salon shawara....inda yake tsaye kuwa sunkasance su Biyarne, dashi da Samra da kuma Atif sai kuma Nina da Simon...

Sauran mutane kuma suma suna guri guda mu'azz mufyda da sauran su.

Saidai kuma Forzy data kasance tsaye take ita kadai... danko kasa motsi tayi har wannan abu tayi mata zobe.....


Dukkan ninsu dakwai y'ar Rata a tsakani,wacce da wuya mutum ya iyya tsalle ya dira wajen dan uwansa....


"Gaskiya a tsorace nake"

Haka forzy ta furta inda Samra Da Atif sukayi sauri cewa da ita cikin hadin baki.


"Forzy take it easy we are coming for you"

Bayan taji hakan yasa ta soma zubar da hawaye,ganin hakan ya dugunzuma hankalin Samra da sauran mutanen guri.


Tsoransu karsu motsa wani abun ya faru dasu..

Amma duk da hakan suna mai nuna kula ga Forzy din haka suka kasance suna mai kwantar mata da hankali cen sai Ahmad yayi wup yace dasu.


"Wait shin wai How long are we going to stay like this...... kuna nufin zamu kare rayuwan mu anan gurin kenan,Ya kamata mu naimi mafita bawai mu tsaya muna jiran tamu tazo garemu ba?".

Bayan ya furta hakan ne mufydah tace dashi.....


"Ahmad mayya taushe maka kwakwalwane wai?,maiya saka baka ganewa ne?,we are in danger Bamusan meye muke tsaye a kaiba taya zamu naimi hanyar barin nan.....so kake mu kuma jefa kanmu cikin wata rikicin na daban?."


Haka mufyda ta basa ansar marne kuma da tambaya....nan suka soma sa'insa a tsakanin su har takai ga Ahmad ya fusata yace dole saiya motsa izuwa inda Forzy take tsaye.


Shugabar tawargar tasu wato *Mu'azz* shima yayi dashi karya motsa but ina Ahmad yaki sauraransa yasa kafa yayi tsalle izuwa gurinda Forzy ke tsaye....

Dirarsa gurin suka Rungume juna.....yayinda Forzy ke zubar kwalla tana kuma furta kalmar godiya ga Ahmad....

Kwatsam sai sukaga gurin nan ta soma sauka dasu,yana nitsewa dasu cikin kasa.


Haka zalika guraran nan da suka tsastsage suka soma sauka kasa....har suka nitse cen

Nanfa Ahmad yayi nadamar abinda ya aikata danko gani yayi sun daina hango kawunan sauran abokan tafiyan nasu....

Sannan hallau gurin bata daina sauka dasu kasa ba.


Ji yayi gurin ta tsaya cek.....yayinda suko tuni a rungume suke sun kuma rufe idanu suna jirar saukar su kasan gurin....

Basuyi zaton abin zai tsaya suna da Raiba amma gashi sai suka kasance suna mai nunfashi kamar sauran halittu.


Kasar su kuma wuta ne ke ambaliya.....cikin wannan wuta kuwa koda dungulellen Bakin karfe datakai girman zuma Rock ka jefa ciki tofa nan da nan zata narke....

Haka gurin tadau haske....  Al'amarin Mu'azz da sauran ko tsaye suke yayinda suka kasa ganin komi ta sanadiyar bakar hayakin dake kashe musu ido.....


Kin bude idanu sukayi har sai da suka jiyo muryar Tina da Simon na cewa....


"Gasu cen!!" Cikin kara hade da murna....

Yayin da suke kuma nuna Ahmad da Forzy.....da yatsa.

Ahmad da forzy dai sun kasance rungume suke da a tuna ninsu sun ruga da sun hallaka basu san wannan shine mafarin wahala ga mai taurinkai ba.


Da jiyo hakan kuwa suka saki jikin juna yayinda suka kai ganin su sama.....

Yan misti mitsi suke ganin su....danko akwai nisa tsakanin su.....


Inda badan hasken wutar nanba da saidai suce sun sheka.....


Tsintar kansu sukayi akan wata y'ar *Gada* wacce iyya ganin ka bazaka yiya kureta da kallo ba.....sanadiyar nisa da kuma wannan bakar hayaki data jaguda gurin.


Wannan Gada dai tayi kama da Gadar mayu dan kuwa babu madafa sa'annan wannan gada ba wata fadi bace da ita.


Idan ka leko kasan wannan gada.....ko tsoro kurun zatasa hanjin cikin ka kad'awa.....


Kasar gurin nan gaba daya ta nitse cikin wannan wuta illa gadodi ukun Nan ne suka rage....


Wato wacce take dauke da Atif da Samra sai kuma wacce take dauke da su mu'azz sannan na Forzy da Ahmad dake cen kasa.


*Al'amarin* wannan kyakkyawar y'a kuwa tafiya take cikin kasaita....

Bayan takaiga indasu Atif suka baro daga farko sai wannan haske data kunna da karfinta na tsafi ta soma daukewa daya bayan daya.


Haka ta zura idanu dan bata zaci haka ba......

Bayan duk sun kafe,sai ta sake busar iska ta kunna wacce kunnuwar wannan haske keda wiya suka sake dauke wa.


"Tirkashi.....wannan bala'i da mai tayi kama?"

Furucin ta kenan....nan ta soma tafia cikin duhun ba tare da tasan inda take sa jafafunta ba....


Wucewarta keda wuya sai wasu muggan halittu suka baiyana a gurin data tsaya.....

Yayinda suka bita da kallo hade da rugawa suka bi bayan ta.....


Bangaren Samra ko taku suke a kan wannan Gada yayin da sunayi nisa sosai......

Cen suka soma hango karshe gurin yayinda Samra taja gwauron nishi hade da cewa....


"Ga cen hanyar da zata 'bulle damu"

Haka ta furta yayin da take yimusu nuni da yatsa...


Kwatsam ba shiri saiga wasu halittu sun ciko wannan guri......

Ta haryar da suka shigone wayennan halittu ke shigowa....


Wayennan Halittu sun kasance suna kama kadangaru amma kuma girman su da suffar su na tsorone....

Danko sunkai girman jakuna ga kuma kwara awaje kai kace *Kada*


Haka suka lodu cikin wannan guri ganin haka yasa Tina ta buga dan karan ihu yayinda take nunawa sauran abokan nata ta bayansu.....


Yin hakanko yasa duk hankulan halittun ya dawo kansu......

Nanfa wayen nan halittu suka soma rige rige wajen hayewa kan wannan gada domin zuga ga Wayen nan mutane wato su Atif....


Yadda suke kokarin hayewa kan wannan gada ko kai kace sun shekara dubi ba tare da sun ci ba....


Kai kace kudan zuma haka suka taru suna nufar inda su Samra da sauran mutanen suke.....

Ganin haka yasa suka ruga a guje.......


*HmmmmπŸ™„ I pity does guys wallahi*


Hakafa suka kasance suna gudun ceton ransu.....

Wayen nan halittun kuwa sai faman hayewa kan wannan Gada....

Nan gadar ta soma tsagewa....yayinda kuma wayenan halittu still na kokarin hayewa....


Rushewa gadar ta soma ta sanadiyar nawi nasu.....

Cikin kankanin lokaci suka riske su yayinda daya yayi Wup da Harun....

Kucelcila shi wannan abin yake yayinda ya kamosa a jakar dake gadon bayansa ganin hakan yasashi cire kansa cikin jakar ya dire kasa....


Nan ya saki rugawa a dari....haka wayennan halittu suka taru kan jakar tasa bayan sun tabbatar ba nama bace suka yowa kansu but it too late already sunkai kofar nan da suke hangowa daga nesa.


Karasowar Harun suka ja kofar suka rufeta........

Hmm Masu iyya magana kance Rashin sani tafi dare duhu....

Kuma duk wanda yaki jin bari zaiji oho......


Da sunsan inda suka tsusa kansu da basuyi gaggawar kai kansu ba......

Zai fi musu idan jira sukayi wayen nan halittu su cinye su.


Amma ya suka iyya tunda kaddarar suce......

Bayan sunja kofar suka rufe na iyya ganin wani rubutu da akayi a saman kofar.

Wacce itace *Mashigar ajali*


Yayinda suka kasance cikin wannan daki kuwa tsaye suke jikin kofar sai famar haki suke nan sai suka soma ganin haske na kunnuwa cikin sauri suka waiga baya.....


Abar sukayi da wani abun dayasa suka wangale baki Tina ko ta....sumewa tayi lokaci guda.......


*Toh fa meye wannan abin?*




*THANKS FOR READING*


*COMMENT  COMMENT  COMMENT*

Ku kasance masu comment idan har kunason cigaba comment naku kwarin gwiwarmu,saina jiku comment more typing always.


✍🏻...........Abdul10k Naku a kullum.