EPISODE 10
by @abdull10k
πππ
*KOFAR AJALI*
```[when in no way out]```
πππ
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
***
_________________________
*πMANAZARTA WRITERS ASSOCIATION πποΈ*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. π€π»```
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*π―β
*EPISODE 1οΈβ£0οΈβ£*
*THE DEATH*
Ihun Aljana Noor ce ta ratsa cikin wannan katafaren ginin inda karan ta ratsa ko'ina a fadin gurin ta Kuma kaiga riske *Forzy*, a firgice ta take biriki bayan ta duba ko'ina batare da taga komiba sai ta soma sauri danta hango wata hanya wacce take kyautata zaton Mai billewace.....
Cikin sauri ta Soma tafiya tana kokarin kaiwa ga kofar,Amma Kuma sai ta Soma jiyo wata murya Mai kama da nata sak nayi mata dariya..abaya,Aikuwa cikin razana ta juyo inda ta tarar da bayan nata Babu alamar kowa,nanfa kirjinta ya soma bugun uku uku...ta Kuma soma magana a kasar zuciyar ta.
"Shin kodai kunnuwa na ba daidai suka jiyo bane....? Kamar naji anayimin dariya"
Aiko Bata kammala fadar haka ba taji tafin hannun mutane sunkai goma a kan kafadar ta....
*#Samrah*
"Hakan bazai taba yuwa ba,bazamu sake barin Nina abaya ba..."
Haka tayi ta furtawa yayinda Atif da sauran mutanen ke kokarin shawo kanta Amma daga karshe ta kwace kanta daga hannun su ta ruga tana Mai dotsawa izuwa wannan Ramin daya fashe aikuwa sai daya saura taku talatin ta kaiga Ramin kawai sai taga wannan macijiya Mai girman bishiyar dafino ta billo ta wannan Rami....
Bayan tayi ido hudu da wannan macijiya ko tayi furucin "Oh no" cikin siririyar murya.
Aikuwa macijiyar batayi Wasa da damar taba,dankuwa ta wani shure ta kaikace Shirin film....
Haka ta tashi sama kamar kwad'o Kuma Babu abunda ya tokare ta illa kofan ga dake bayansu domin kuwa sun bawa kofar baya....
Aiko Sumewa #Samrah tayi Atif, mu'azz da sauran mutanen suko zura idanu sukayi Dan mamaki...
Macijiyar ko ta Soma wani jujjuyawa cikin salo Mai matukar tsoratar tana ta bubbude wuya kamar wata jegariya nanfa ta kurama taron nasu ido....
Can tayi kansu sulululu ta yadda idan ta kaiga su wub daya zatayi musu ta hadesu Dan kuwa a tsaye suke guri guda sunki motsawa sai ihun tsiya da suke....
Kamar walkiya sai ga wani santalelen saurayi ya diro gaban wannan macijiyar, saurayi Mai cikar Kamala da Kuma kwar jini,ga faffadar kirji irin ta jaruman kwarai.
Bayyanarsa a wannan guri yayi daidai da budewar bakin macijiyar da niyar hade taron su Atif... Amma Allah bai Bata damar haka ba ta sanadiyar bayyanar wannan saurayi,kabbara yayi hade da dafe saman kan wannan macijiya aiko cikin kankanin lokaci ta koma baya da karfin tsiya Danko karfin kabbaran yafi karfin ta ba kusa ba.
Zuru zuru mu'azz,Atif da sauran mutanen gurin sukayi domin kuwa abin yayi matukar Basu mamaki,ko kibta ido basuyi...
Wannan saurayin ko tsaye yake yayin da wannan macijiyar ke kururuwa tana komawa baya.... Fadiwa kasa wannan macijiyar tayi cikin sauri da Kuma zafin nama ta Mike hade da yunkurin sake farmakar su...
Aiko wannan saurayin bai Bata damar yin haka ba Dan kuwa soma karanta *Suratul Jin* yayi bayan ya karanta Aya goma na wannan Sura sai wannan macijiyar ta Soma ihu cikin kankanin lokaci ta rikide ta dawo Suffan mutum... Atif da mabiyansa ko mamaki takai makura domin kuwa sun rasa ta cewa sai kallon ikon Allah.
"Meye naka ciki,idan na hallaka su?"
Haka tayi masa tambaya yayinda ta nunashi da hannu sa'annan ta kuma sake da cewa.
"Zaka iyya dakatar Dani daga hallakasu yanzu Amma Ina Mai tabbatar maka bazasu Kai labari ba,Domin matsifun dake tinkaro su ya wuce karfin tunani...Zanga iyya gudun ruwan ka Dan nasan bazaka iyya Basu kariya na har abada ba"
Aiko cikin kasaita saurayin yace da ita....
"Zaku iyya fin karfin Yan Adam Amma bazaku iyya da Allah ba...
Yafi karfin ku,Kuma shi zai bamu damar kare kanmu daga muggan halittu irin ku,masu hukunta mutane ba tare da sunyi laifi ba"
Kelkelewa tayi da dariya sa'annan tace dashi.....
"Mayyasa kake alfahari da karfin da ba taka bace...ita
Karfin da kake ikirari dashi kowa zai iyya mallakar ta... Sa'annan inaso in sanar maka Yau ka Kona ni Amma inaso kasani wannan kuskure da kayi sai dukkanin ku kunyi nadama haka, dukka saikun biya bashin da kuka dauka".
Aiko kafin saurayin ya sake bude baki tuni ta bace tamkar warkiya a tsakiyar dare..
Muryar ta suka soma jiyowa tana ikirarin sai sunyi nadamar konata da sukayi,cen sai tayi shiru hakan ya bawa saurayin damar juyawa ya kurama taron su Atif din Idanu.
*Forzy*
#Forzy #Forzyy cikin Rad'a take jiyo muryar maishi na Kiran sunan ta,juyawa tayi inda ta sake guba lungu da sako na dakin Bata ga kowa ba....
"Wai maike Shirin faruwa da nine?,gaba daya na kimauce.. Hm"
Haka ta furta sa'annan ta girgiza Kai alamar takaici Hadi da tsaki.. bayan tayi hakan ko ta juya da niyar cigaba da tafiyar Tata.
Ihu tayi bayan tayi arba da Tarun Y'an mata maru kama da ita sak saidai banbancin su shine fuskar wayennan y'an matan nada abin tsoro domin wata iriyar dariya suke Mai sa gashin jikin mutum ta Mike tsaye...
Aiko bayan #Forzy tayi ido hudu da wannan matsifar sai ta lumshe Idanu Hadi da hada tafin hannayen ta guri guda Dan zunzurutun tsoro ta Soma karanta *Suratull-Baqara* a cikin ranta....takeyi Dukda cewar tana sauyawa ayoyin gurare haka baisa ta daina karantawa ba haka tayi ta karantawa bakinta na raga haka zalika jikin ta na 'bari.
Dukda karatun da take Bata daina jiyo sautin muryoyin nasu ba...Bayanta ko sai ga wani hannu yazo cikin sauri ya dafe ta aiko yadda kasan Danko haka tajita a yashe gefe guda.
Bude Idanu Forzy tayi cikin sauri bayan taji karan fadiwan mutum Hadi da son sanin waya dafe tan.
Bude ido tayi ta tarar da gurin Babu kowa Babu y'an matan ko daya,cen ko guri guda ta tarar da wani a kwance maishi na kokarin tashi...Aiko yadda kasan barbela haka ta ruga izuwa ga wannan mutumin.
"Karki Tabanin karki Tabanin"
Haka ta furta cikin siririyar murya inda #Forzy ta dakata da niyarta na tallafa mata ta Mike..
Dago fuska tayi suka hada ido inda #Forzy tayi furucin "You?" Cikin mamaki Hadi da zura idanu...
"Yes me"
Haka ta Bata ansa aiko Babu abinda Forzy ta Soma tunowa illa bakar hayakin daya biyota a guje dazun da Kuma yarinyar Nan data taimaka mata Mai fuka fukai a gadon baya wacce ba kowa bace illa budurwar Nan dake zaune gaban ta.
Sake shiga yanayi ta Sumewa tayi sai yarinyar tayi ceb ta cebko ta Hadi da girgiza ta Amma ko bayan tayi haka ta buga ihu ta fitar hankali dan jikin Forzy na d'aye mata fatar jiki yadda Kanan kunar wuta har gurin na hayaki.....
Bude Idanu Forzy tayi yayinda yarinyar tayi saurin cika mata hannu ta bada rata a tsakanin ta da Forzy.
"Maike faruwa?" Tambayan da Forzy tayi kenan inda ta Bata ansa da cewa
"Kina matukar Kona ni Yar uwa, kinada tsari a tartare dake,Kuma Zaki cigaba da tarwatsani idan na tsaya tare dake"
Cikin mamaki hade da daurewar Kai ta wangale baki tana kallon *#Noor*
Bagaren su Atif da wannan jajirceccen saurayin ko.... kafin saurayin ya budi baki tuni ta bace tamkar warkiya a tsakiyar dare..
Muryarta ko ya ratsa cikin ginin tana mai ikirarin sai sunyi nadamar konata da sukayi,cen sai tayi shiru hakan ya bawa saurayin damar juyawa ya kurama taron su Atif din Idanu.
"Gaskiya muna Mai Godiya Dan uwa"
Haka mu'azz ya furta inda Atif shima yace dashi mun gode matuka Amma shiko hada Rai yayi ya kura musu ido...
Y'an matan dake guri tuni sukayi caa kan Samra dake kwance...
Zuwansu suka soma yimata fifita hade da yayyafa mata ruwa haka a hankali ta farka budewar idanun ta ko tayi Karo da mitar wannan saurayin yayinda yace cewa.
"Wai wace irin mutane ne ku?,Mai yasa kuke manta mahalacci a lokacin da kuka tsinci kanku cikin had'ari,Mai yasa kuka manta koyarwar da addinin mu tayi Mana game da naiman tsari a lokacin da muka shiga sabgar mutanen boye maiyasa bakwa naiman tsari daga uban giji sai ihun banza....da bazata kareku da komi ba"
Haka ya jera musu tambayoyi Babu kakkautawa,suko saukar da idanun su kasa sukayi bayan yayi shiru Sai Harun yace dashi
"Gaskiya munyi kuskure na rashin Mikawa mahaliccin mu damuwar mu,Amma insha Allah zamu gyara"
Hm yayi hade da juya baya da niyar tafiya Nan sai Atif yace dashi
"Gaskiya Dan Uwa munyi mantuwar da Bata da amfani... Mun sha'afa ne"
Aiko #samra cikin naiman sani tace da y'an matan dake kusa da ita
"Wai waye wannan? Ya sunan sa Kuma Mai yake a Nan gurin"
Juyawar sa yayi gajeriyar murmushi hade da cewa...
"Shin wai har mun saba da zaku iyya yimin irin wayen Nan tambayoyin?, Yar uwa ba keba dukkan ku anan gurin zuciyar ku cike fal da burin sanin koni waye"
Haka ya bata ansa sa'annan ya sake da cewa....
"Amma Matsifu Sama da dubu dari suna birne a kasan wannan guri.....
Tsayawar ku anan gurin Babu abinda zata tsinana muku illa ta karashe ku baki daya domin wannan garkuwa ta Rezar uta tana gab da dauke wa"
Aiko bayan ya furta haka Harun ya jefesa da tambaya kamar haka.
"Kana magana tamkar ka haddace wannan matsifeffen guri Taya kasan duk wannan malam?"
Gajeriyar murmushi yayi hade da cewa
"da zakubi ta nawa da Kun gaggauta naimo takubba Nan da suka kasance sune makullen kofar domin tsiratar da rayuwar ku,domin kowace dakika sake shiga hadari kuke ya kamata ku fahimci haka"
Shiru sukayi Babu Wanda yace dashi kala domin yama fara Basu tsoro domin tunaninsu ba bil'adam bane
Shiko dayaga alamun haka a tattare dasu sai ya Soma cewa...
"Al-Hussien sunana na kasance Dan bincikena tarini ne sa'annan iftila'i ne yasana shigo Nan gurin,ku yadda Dani ku naimo takubban".
"Maiyasa zamu yadda dashi??"
Fadar #Samra kenan inda Atif yace da Al-Hussien..
"Taya kashigo wannan guri, sa'annan tsowon wani lokaci ka dauka anan gurin"?
"Labari ne Mai tsawo Baku da lokacin sauraron haka"
Haka ya basa ansa shiko yasake da cewa..
"Kana nufin idan mun samu lokaci zaka sanar damu kenan?"
Dajin wannan tambaya ko ya kyalkyale da dariya....
"Don't tag me in,we are not us sabida bana cikin tawagar taku".
"Amma Aiko kaji abinda waccen aljanar tace,Dukda ta nuna bazaka iyya bamu tsaro ba ai ya kamata ka jarraba"
Abinda Simon ya fada kenan shiko ya girgiza ka sa'annan yace dashi.
"Aiko gaskiya ta fada,domin nida kaina bani nake kare kaina ba Allah ne ke kareni kamar yadda nake kyautata zaton zai kareku"
Aikuwa bayan ya furta hakan Samra ta Mike tsaye hadi da furta cewa...
"Hold on Guys,What did I miss??"
Dukkan ninsu ko suka juya idannun su izuwa kanta....cike da mamaki
#Mufydah gajeriyar murmushi tayi sa'annan tace da ita
"Alot"
Al'amarin Forzy da Kuma Noor ko zaune suke yayinda suke nesa da juna...Nan Forzy tace da ita..
"Taya kike tunanin kwakwalwata zata dauki abinda kike fadane,tayaya"
"Forzy nasan bazaki amince ba Amma gaskiyar kenan, waccen da Kika ganmu tare ba Nina bace"
Haka Noor ta furta inda Forzy tace da ita...
"Bama wannan ba Noor,Taya kike tunanin Zan yadda dake bayan ke da bakinki kikace kin koro daya daga cikin mu izuwa wannan guri Kuma nasan ba kowa bane wannan illa Atif.. toh nasani ko kece kike shirya komi ma'ana shirya nitsewar Ahmed da Kuma bacewar Nina da sauran tawagar mu hmm, wannan guri ba gurin yarda da mutun bane Noor cikin kalaman ki na dauki wannan darasin domin kin yadda da wata wacce tazo Miki a suffar Yar uwata daga karshe taso tarwatsa ki,Ina ganin ba kuskure bane nima idan naki amincewa dake".
Gajeriyar murmushi tayi sa'annan tace da ita....
"Bada mugun nufi nazo gareki ba Forzy, Amma kina da damarki nakin amincewa da batuna domin nayi kuskure Dana kasance Ina tsutarwa domin nasan idan da badan Ina tsutarwa ba da tsarin da kike tattare dashi bazata konani ba....
Amma inaso ki fahimci wani abu da da mugun nufi nake bazan iyya tinkaro inda kike ba Forzy ki amince Dani"
Shiru Forzy tayi tana ta nazari Noor ko ta kura mata Idanu....
*ATIF*
Tsaye suke gaban wannan gabjejiyar kofa inda sukasa takubban jikin kofar kamar yadda wasikar da suka karanta ta nuna....
Takubban dake da kalmomin mutuwa suka naimo suka Kuma makalata a jikin kofar a inda suke tunani mazaunin takubban ne....
Shiru kakeji Babu alamar budewar wannan kofa... Nan Tina tace dasu
"Anya kuwa daidaine mukayi hakan"
"Wata kila ba haka suke son muyi ba" fadar Samra inda Al-Hussien yace da ita "ya kamata mudan jingirta...
Aiko Samra tayi salati Hadi cewa....
Garkuwar na karyewa Kuma gashi kunamun sun sake bayana...
Al-Hussien ko ya juya ya duba Hadi da cewa...
"Dama rufe Mana Idanu tayi da karfin tsafi,kunamun sun kasance na gaskene ba Aljanu bane suka rikide....shiyasa suka kasance har yanzu suna gurin Ya kamata mu gaggauta barin nan"
"Tayaya Al-Hussien kanafa ganin abinda ke Shirin samun mu Amma ka gindaya Mana sharud'a idan munaso mu tafi tare da kai...kace Babu Mai taba ka Kuma Babu aikin da za'a saka kayi sannan komi saidai ka fada Mana da baki bawai ka tayamu yiba... Taya kake ganin haka zaiyi"
Samra ce ta furta hakan shigo ko shiru yayi Hadi da dauke idanunsa kasa...
#Tina da Mufydah ko suka hadakai guri guda cikin rad'a Tina tace da mufy..
"Ko meye dalilinsa nayin hakane oho"
Atif,mu'azz duk sunyi sanyi da sukajiyo wannan magana ta Samra....
*"Meye Al-Hussien ke Shirin boyewa gaskiya da lauje cikin nadi,"*
Haka Atif ya furta cikin kasar zuciyar sa.....
*2Hour Ago*
*Awanni biyu dasuka wuce*
"Tafukan Hannu sune makullan Kofan nan I'm sure"
Taimakon da Nina tayi abaya kenan ta sadaukar da rayuwarta wajen ganin ta tsiratar da abokan tafiyar ta abinda ya faru da itako bayan Atif yaja kofar ya rufe shine....
Gani tayi kowani lungu da sako wasu irin halittune ke bullowa ta ciki...Hadi da wayenda tayi musu sata wato sangaranrun mutanen Nan masu kama da gumaka....
Aiko Nan tasan nata yazo karshe...ajiyar zuci tayi dan Babu yadda ta iyya domin hannunta na makale hallau a wannan guri data saka....su
Jitayi hannuwata sun guntule nanfa ta buga ihu na fitar hankali jini ko ta soma kwararowa.... Izuwa kasan gurin,caa halittun Nan masu kama da kadangaru sukayo kanta sukayi gutsigutsi da namarta...Gaskiya tayi mutuwar wulakanci....
πππππππππππππππ
@*Abdul Alhaji Musa comment*
"Ahmed Da Nina Allah Ya jikanku da Rahama"
*_Mu Hadu a Episode 11_*
_@Abdul Alhaji Musa *Return*_