RAYUWAR SAMARI DA YANMATA A SOCIAL MEDIA

GODIYA

by @arewamediawriters

ALHAMDULILLAH

Godiya ta tabbata ga Ubangiji Ma]aukakin Sarki wanda a cikin yardarsa da amincewarsa ya ba mu aron dama muka gabatar da wannan aiki, salati da daukaka da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) da zuri'arshi da sauran mutanan kirkin da suka rigamu gidan gaskiya.


An sami taimako daga duk wadanda aka tuntuba a lokacin gabatar da wannan muhimmin aiki. Ganin cewa yana da wuya a ambaci sunayen duk wadanda suka bada taimako, zan iya ambaton koda kadan ne.


Gagarumin taimako ya zo ne daga Sadiq Rabi'u Ahmad Kano, da shugaban kungiyar "Arewa Media Writers" na jahar Kano Umar Kabir Dakata, da shugaban kungiyar "Arewa Computer Library" na kasa Salisu Abdulrazak, da Abdulkadir Nafi'u Batsari (Dan Arewa) da Abdulrashid Abdullahi Kano da Ibrahim Elshalami Gombe.


Jinjina ga magatakardar kungiyar "Arewa Media Writers" na kasa Comr Haidar Hasheem Kano da babban mataimakin shugaban kungiyar na kasa Shehi Falalu Lawal Katsina da Muhammad Kwairi Waziri da Muhammad Chigari Kumo da Salisu Magaji Fandallafi'h da Abubakar Muhammad Bello (Habun Falo) da Muhammad Dahiru MD Gombe da shugaban kungiyar "Arewa Media Writers" na jahar Katsina Comr Nura Siniya Katsina, Abdurrahman Suleiman Zaria (USTAZ) da Anas Dan Falala Gombe, bisa shawarwari masu kyau da suka bada akan yadda za a tsara littafin.


Jinjina na musamman ga shugabannin kungiyar "Arewa Media Writers" na kasa da na jahohin Arewa baki]aya, da dukkannin membobin kungiyar na }asa bakidaya.


Malaman da sukayi nazari akan littafin;


1. Malam H. M. Khalid, malami a jami'ar kimiya da fasaha ta Tarayya (ATBU Bauchi).

2. Malam Lawal Umar Maradun, (ARPA, NIPR).

3. Hon Yusuf Dingyadi, Sokoto (Magaya}in Garkuwa Sakkwato) SSA na Gwamnan jahar Sokoto.

4, Hukumar tace fina-finai da ]ab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin shugaban hukumar Malam Ismail Na’abba Afakallahu, ta tace littafin tare da yin nazari akan shi. Allah ya saka muku da alkahiri, ya biyaku da gidan Aljannah Firdausi. Amin