RAYUWAR SAMARI DA YANMATA A SOCIAL MEDIA

TASIRIN DA SOSHIYAL MIDIYA TA YI A RAYUWAR SAMARI DA 'YANMATA

by @arewamediawriters

Dandalin sada zumunta wata sabuwar duniya ce da ba mu gama sanin hakikaninta ba, duniya ce mai cike da annashuwa da raha da saukin sadarwa da saukin rayuwa da saukin mu’amala da saukin abota da hanyoyin samun fadakarwa da gabatar da harkokin rayuwa ce a wani tsari mai kama da hakika, kai ba kama ba ne rayuwa ta hakika ce.


Farkon abin da mafi yawancin samari da 'yanmata suke yi idan sun farka daga barci shi ne daukar waya domin duba sakonni daga masoyansu, ko kuma duba sanarwa, labarai da sauransu ta hanyar yanar gizo-gizo ko dandalin sada zumunta wato soshiyal midiya. Kafin mutum ya ankara ya cinye awoyi marasa adadi a soshiyal midiya.


Kafafen Sadarwa na zamani sun zame mana jiki a rayuwarmu ta yau da kullum, kamar dai misalin Mashayi da kayan shaye-shaye, idan bai sha ba to kuwa babu nutsuwa da zaman lafiya.


Sabbin kafafen sadarwar na zamani sun zame mana jiki a rayuwarmu ta yau da kullum, har ma ya kasance jama’a ba su cika kallonka a matsayin wayayye wanda ya san mai ya ke yi ba idan har ya kasance ba ka amfani da daya daga cikin shafukan sadarwa na zamani.


Duba da yanda kowane rukuni na mutane suna amfani dashi tun daga kan maza har zuwa mata, yara, matasa, attajirai, ‘yan siyasa, malamai, sarakuna, ‘yan kasuwa da sauran sassan jama’a.


Kai har ma kamfanoni da ma’aikatu sun kasance suna amfani da kafofin sadarwar zamani wajen tallata hajojinsu ko ayyukansu ga al’ummar Duniya.


Bincike ya nuna akwai abubuwa da dama wadanda kafofin sadarwar zamani ta haifar a cikin al’umma, wanda ba a taba samun wani makamancin irin shi ba.


Kafar sadarwa ta Facebook ta fi kowacce kafa tasiri a wurin samari da 'yanmata, a bayyane yake cewa akwai matasa da yawa a dandalin Facebook.


Ba za ka san hakan ba sai ka shiga, za ka ga mutane, tsakanin 'yanmata da samari da tsofaffi da zawarawa da gagware tuzurai, duk sun yi rajista kuma suna sada zumunci.


Babban abin da ya sauwake haduwarsu a wannan dandali kuwa dalilai ne guda biyu.


Abu na farko shi ne samuwar wayar salula a hannun jama'a, wanda ya game gari da duniya baki daya.


A kasar Nijeriya akwai layukan wayar salula sama da miliyan 100 inji masana kididdiga a shekara ta 2021, a Arewacin kasar aka fi samun jama'a masu dauke da wayar salula.


Galibin wayoyin salular wannan zamani kuwa duk karancin kudi da araharsu, za ka samu suna dauke ne da hanyar sadarwa ta Intanet, wannan ya sa duk wanda ke da wayar salula a hannunsa, to kamar yana da shafin Facebook ne, domin yin rajista babu wahala. Kari a kan haka, kamfanonin layukan sadarwa sun gina wata manhaja ta musamman na shafin Facebook, muddin ka shiga shafin, nan take za ka iya saukar da wannan manhaja, ka yi rajistar shafinka na facebook ba tare da wata matsala ba. Sannan, ko babu ko sisi a wayarka kana iya shiga, ka yi amfani da shi.


Abu na biyu shi ne saukin mu'amala, shafin facebook yana da saukin mu'amala, wannan ya sa duk wanda ya shiga sau daya sau biyu, ba ya bukatar wani darasi.


Wadannan dalilai biyu su suka taimaka wajen yaduwar matasanmu a dandalin Facebook, kowa na son ya shigo don ya nemi abokai ko 'yanmata, ko samari da dai sauransu.


Akwai majalisu da matasanmu suka kafa a dandalin facebook masu amfani sosai, da zaurukan tattaunawa na musamman.


Mutane da dama sun samu hanya mafi sauki wajen yada addini da shari'ar Musulunci, wasu sun yi abota ta Allah da Annabi, wasu sun yi kawance ta Allah da Annabi.