RAYUWAR SAMARI DA YANMATA A SOCIAL MEDIA
AMFANIN DA SOSHIYAL MIDIYA TA KAWO A RAYUWAR SAMARI DA 'YANMATA
Soshiyal midiya ta hada duniya wuri guda ta zama wani kan karamin gari wanda ake kira "Global Village" a Turance, ko kuma a ce duniya a tafin hannunka a Hausance.
Ta dalilin soshiyal midiya, a yau matasa Maza da Mata suna haduwa su tattauna da juna daga bangarori daban-daban na duniya.
Ta hanyar soshiyal midiya samari da 'yanmata suna musayar ra’ayi da tafka muhawara a junansu, sannan kuma su na samun bayanai da labarai da kuma samun dumbin damarmaki daban-daban.
Uwa uba soshiyal midiya ta hada dubun nan 'yanmata da samari aure, wanda suna nan sun haifi 'ya’ya, wasu kuma suna nan sunata kokarin yin auren, duk a sanadiyyar soshiyal midiya.
Soshiyal midiya ta ba wa samari da 'yanmata damar yin sababbin abokai, haka zalika ta ba da damar samari da 'yanmata gano tsofaffin abokansu wadanda a baya suka yi gwagwarmayar karatu tare ta hanyar ganin sunayensu ko sunayen makarantar da suka yi.
Soshiyal midiya ta taimakawa samari da 'yanmata masu saye da sayarwa in da su ke bude shafuka na musamman domin tallata abubuwan da su ke sayarwa ko kuma su biya samari da 'yanmata wadanda suka yi suna su tallata musu hajojin nasu, su kuma su biya ladan tallatar da suka yi musu.
Sannan soshiyal midiya ta na bawa Samari da 'yanmata damar hada kai da zama jakadu kan harkokin kasuwanci da ayyukan jama’a.
Haka zalika, soshiyal midiya tana samarwa samari da 'yanmata kudi ta hanyar Blogging da ayyukan watsa labarai da harkokin tallace-tallace da sauran ayyukan fasaha.
Sannan kuma soshiyal midiya wurare ne da samari da 'yanmata su ke amfani da shi wajen bayyana ra’ayinsu da sanar da duniya tunaninsu cikin sauki ba tare da wata shakka ko fargaba ba.
Haka zalika soshiyal midiya ta ba da dama ta yadda a sanadiyyarta za ka iya yin aiki a ko’ina ka ke a fadin Duniya.