RAYUWAR SAMARI DA YANMATA A SOCIAL MEDIA

ILLOLIN DA SOSHIYAL MIDIYA TA KAWO A RAYUWAR SAMARI DA 'YANMATA

by @arewamediawriters

Duk da irin dumbin alkhairi da soshiyal midiya ta kawo a tsakanin samari da 'yanmata, haka zalika

akwai manyan illoli da ta kawo wadanda dole sai iyaye, yayye sun dinga saka ido kan abokanai da 'yayansu suke mu'amala da su a soshiyal midiya.

Babban abin da zai fi ba ka mamaki cikin al'amuran matasanmu a soshiyal midiya shi ne, rashin manufa takamaimai a yayin da suke shawagi da shantakewa a dandalin.

Abu na farko da aka sansu da shi shi ne "YAWAN RU[UWA  DA  'YANMATA"  duk  wacce  ka  shiga shafinta a soshiyal midiya in dai budurwa ce, za ka ga kashi 90 cikin abokananta maza ne.

Da zarar ta yi tari, ko "mhmm" ta rubuta a shafinta, nan take za ka ga ta'aliki "comments" daga daruruwan maza kafin sa'a guda.

Duk abin da tace sai an ce wani abu a kai, balle ta loda hoto a shafin, ba sai na gaya muku abin da zai faru ba, su kansu 'yanmatan haka suka fi so, musamman wasu ke daukar hotuna su loda a shafinsu, don su ji me samari za su ce.

Idan kana karanta sakonnin da matasa ke rubutawa dangane da wadannan hotuna sai ranka ya baci, wai duk nan yabonta ake.


Abu na biyu shi ne "CIN MUTUNCIN ABOKIN MAGANA" da yawa daga cikin matasa a soshiyal midiya ba su da da'a, musamman dai a majalisun da ake tattaunawa kan abubuwan da suka shafi al'umma.

A wasu daga cikin manyan majalisun da ke soshiyal midiya musamman facebook, kusan kullum sai na karanta zage-zage, da surutan cin mutuncin abokin zance, ba kunya ba tsoro, wannan bai dace ba, sai kuma batun batsa da ashararanci. Wannan kuma ya kasu kashi biyu, akwai zantuka da wasu matasanmu ke yi kan hotunan 'yanmata da niyyar yabo, ko kokarin gamsar da 'yanmatan cewa suna da kyau.

Idan ka karanta ire-iren wadannan zantuka sai ranka ya baci, da yawa cikin mutane kan rubuta abin da ba shi ba ne hakikanin rayuwarsu, wanda hakan ta sa idan kana karanta bayaninsu a "Profile" sai ka ga akwai tufka da warwara Misali, yarinya ko matashi zai ce Musulmi ne shi, mai son Manzon Allah, mai kishin Musulunci, littafinsa shi ne Alkur'ani da Hadisi, amma idan aka zo wajen "Hobbies" ko "Interests", watau abin da yake sha'awa a rayuwarsa ko rayuwarta, sai ka ga ya zayyana sunayen manyan makiyan Allah daga cikin mawakan Turai, da miyagun fina-finan da a zahiri suna cin mutuncin Addini ne, ko ma wasunsu duka cike suke da batsa da rashin tarbiyya.

Wannan tufka da warwara ne ko shakka babu, galibin matasa idan ka shiga "Profile" dinsu za kata cin karo da irin wannan.


Abu na gaba shi ne "RASHIN SIRRI" da yawa daga cikin matasa har yanzu sun kasa fahimtar mummunan hadarin da ke tattare da rashin sirri, idan kana son fahimtar hakan kuwa sai ka shiga dandanlin facebook, da wanda ke kwance a kan gado yana hutawa, da wanda ke cin tuwo miyar kuka, da wanda ke zance da budurwarsa, da wanda ke shan shayi, da wanda ke kan hanyar tafiya zuwa wani garin, da wanda zai shiga wanka, da wanda ke sanya tufafi, duk za ka gani a soshiyal midiya matasanmu sun shigar, ba ruwansu da mai zai je ya dawo.

A sauran kasashen da suka ci gaba a fannin sadarwa, zantuka irin wadannan sun yi sanadiyyar mutuwar wasu, da hasaran rayuka, da ta'addanci, da rasa matsayin siyasa da shugabanci, da karyewar arziki, da mutuwar auratayya da dai sauransu, amma matasanmu ko a jikinsu.


Kari a kan haka har da hotuna marassa kan gado, wasu hotunan ma ba su kamata a ce an nuna su ga duniya ba, amma a shafin soshiyal midiya duk za ka gansu.


Abu na gaba "LALATA TUNANIN SAMARI DA

'YANMATA" babu wuraren da suka kai soshiyal midiya lalata tunanin matasa musamman mata.

Domin zaka dinga ganin rayuwar mutane kala-kala kuma daban-daban, mutum zai hadu da wanda suka fi shi, da wanda suke daidai da wanda ya fi su.

A maimakon matashi yayi hakuri da yanda yake, da yawansu su kan kasa jurewa, suna ganin dole sai sun yi koyi da wane da irin rayuwarsa.


Da yawan matasa suna matukar daurawa kansu irin wannan fitinar rayuwar na cewa sai sun samu irin abun da wasu ke samu.


Abu na gaba "YANCIN MAGANA" samari da 'yanmata da yawa suna ganin yanzu sun kai su yi kafada- da-kafada da kowane mutum a cikin rubutunsu a soshiyal midiya.

Sai ka ga matashi ya kira sunan wani mutum mai kima da mutunci a cikin al’umma, babu kunya babu tsoron Allah ya zage shi ta tas! Ko ya yi masa muguwar Addu’a.

A duk zage-zagen da ake yi a soshiyal midiya babu wanda ya fi daga hankali irin zagin Malamai.

Ka ga wani jahili wanda ko karatun Sallah bai iya da kyau ba, amma yana tsinewa ko muhawara da babban malamin da ya fishi sani a Addini.

Wani kuma ko "brighter grammar" bai taba karantawa ba yana tsinewa Farfesa, kawai laifinsa shi ne ya rubuta abun da ya sha banban da akidarka ko na malaminka haka nan ra’ayinka ko na malamanka.


Abu na gaba "KARYA DA RIYA" soshiyal midiya ta yi sanadiyyar lalacewar aikin matasa da yawa.

Domin a halin da ake ciki duk abun da mutum ya yi na ibada zaka ga sai ya saka shi a soshiyal midiya yana fadawa duniya cewa ai shi mai kaza ne ko yana yin kaza.

Akwai wadanda ko sallar dare suka tashi sai an dauki hoton an yi posting, da yawansu ko sadaka suka bada ko


wani aikin ladan da ma ba sai duniya ta sani ba to sai sun sanar.

Har ya kai ga wasu suna ganin idan suka yi wani aikin Alkhairi ko na neman yardan Allah in ba su yi posting ba ba sa jin kamar sun yi aikin.


Abu na gaba "HASSADA DA kYASHI" na daya daga cikin abun da ya ke saka matasa fada, gaba, gulma, kiyayya, da hassada ga juna shi ne kwaikwayon wani a cikin abun da yake yi.

Wurin kokarin son ganin ka kamo wata ko wani, sai ka mayar da kanka sauna ko sakarai, domin idan kana kwaikwayon wani a komai nasa, hakan yana nuna tabbas ba ka cika mutum mai iya tsayawa da kafafuwan sa ba.

Kuma ba ka godewa Ubangiji taka baiwar da ya yi maka ba, saboda duk yanda kake raina kanka akwai abun da Allah ya yi maka mai muhimmanci.

Amma kallon na wani, da son kwaikwayon sa, da kokarin kamo shi zai hana ka fahimtar irin taka baiwar.

Wata kila kwata-kwata kyautar ka ba a cikin irin abun da kake ta kwaikwayon wancan bane, amma saboda yana burge ka sai ka yi damarar kwaikwayon komai nasa.

Daga karshe idan ka kasa kamoshi, ko zama kamarshi, sai abun ya koma Hassada.

Sai ka rika jin haushin sa bai maka laifin komai ba, ko digo ya rubuta sai ka zage shi.

Haka zalika da yawa daga cikin 'yan soshiyal midiya sun koma cin mutuncin Mutane da sunan soshiyal midiya,


ko wasu su dinga daukan nauyinsu suna cin mutuncin abokanan siyasarsu ko don bambancin akida.


Abu na karshe shi ne "YAUDARA DA KARYA" yaudara da karya wajen bayyana asali da tarihi a tsakanin samari da 'yanmata, wannan matsala ce mai girma.

Da yawa cikinmu kan rubuta cewa, mun yi makaranta a kasa kaza, ko mu mazauna kasa kaza ne, alhali watakila ko kwaryar jiharmu ba mu taba bari zuwa wata jaha ba.

Wasu kuma mazaje ne, amma sai su bude shafi na musamman da sunan mata da hotunan mata, har da lambar waya ta bogi.

Su ma 'yanmata suna da ta su yaudara cikin zance da yaudara cikin hotuna, wasu kan loda hotuna masu motsa tsimin Namiji, don su ji me za a ce.

Manyan dalilan da ke haddasa su su ne, sakakkiyen ’yanci da rashin tarbiyya da yawan ruduwa da kyale-kyale da kuma rigima wajen latse-latse.

Da yawa cikin mutane a wasu kasashe sun rasa rayuwarsu, wasu sun rasa dukiyarsu, wasu sun rasa mutunci da darajarsu, wasu kujeru da mulkinsu, duk ta sanadiyyar latse-latse marasa kan-gado a soshiyal midiya.

Wadannan kadan ne daga cikin kalubalen da ke fuskantar samari da 'yanmata a soshiyal midiya.