RAYUWAR SAMARI DA YANMATA A SOCIAL MEDIA
TAKAITACCIYAR NASIHA GA SAMARI DA 'YANMATA MASU AMFANI DA SOSHIYAL MIDIYA
Duba da yanayin rayuwar matasanmu a yau, wannan dalilin ya sa zan yi nasiha ga 'yan uwana matasa dangane da abin da ya shafe mu ni da ku.
⦁ Ka/ki mu'amalanci mutane da mu'amala mai kyau, kada ka yaudare su, ka ha'ince su ko ka ci amanar su bayan sun yarda da kai.
⦁ Ka/ki zama mai gaskiya wanda baya sabawa abin da ya fada, wato idan za ka yi zance ka yi adalci, kuma kada ka zama mai sassaba zancenka a kowani lokaci.
⦁ Kada Ka/ki rika yi wa mutane karya, domin kuwa Hausawa suna cewa "karya fure take ba ta 'ya'ya"
⦁ Ka/ki zama mai amfanar da jama'a ta kowani
bangare na abin da Allah ya azurtaka da shi; Ilmi, kudi, sarauta, mulki, sana'a ko kasuwanci.
⦁ Ka/ki zama mai tsoron Allah wajan rubuta gaskiya.
⦁ Ka/ki ji tsoron Allah ka gujewa yada batsa ko abun da bai dace ba, a soshiyal midiya.
⦁ Ka/ki gujewa yada labarun karya, wanda za su jawo fitina a tsakanin al’umma.
⦁ Ka/ki guji cin mutuncin al'umma a soshiyal midiya.
⦁ Ka/ki maida hankali wajan rubuta abin da zai amfani al'umma.
Na tabbata idan dukkannin samari da 'yanmata dake ta'amuli da soshiyal midiya suka karbi wadannan shawarwarin suka yi aiki da su, za a samu cigaba mai dorewa a ‘yankinmu na Arewa da ma kasar Nijeriya baki daya.