RAYUWAR SAMARI DA YANMATA A SOCIAL MEDIA
RUFEWA
Kafin mu karkare, ya kamata mu tuna da wadannan abubuwan guda biyu, suna daga cikin manyan dalilan da ke haddasa aikata abubuwan da basu dace ba, a soshiyal midiya, wadannan abubuwa kuwa su ne kamar haka: samun sakakken 'yanci, da kuma rashin tarbiyya.
Galibinmu idan muna dauke da wayar salula a cikin dakunanmu sai mu ga komai ma muna iya yi. Sannan idan hakan ya hadu da rashin tarbiyya sai lamari ya lalace.
Galibi muna shiga soshiyal midiya ne kawai mu yi shashanci ba wai mu karu da wani sabon ilmi kan abin da ba mu mallaka ba, wannan shirme ne.
Abu na biyu shi ne; rashin manufa, ba mu da manufa ta gari, abin da muka ga ana yi sai kawai mu buge da yi, meye amfaninsa? Oho! wannan ya fi yawa a bangaren matasanmu maza.
Wajibi ne mu rika lura da manufarmu kan abin da muke yi a soshiyal midiya, duk abin da ba zai samar maka da wani alfanu ba, kayi hakuri dashi, shi ya fi alheri.
Na tabbata idan dukkannin samari da 'yanmata da ke ta'amuli da soshiyal midiya suka yi amfani da wadannan shawarin suka yi aiki da su, za a samu cigaba mai dorewa a yankinmu na Arewa dama kasar Nijeriya baki daya.
Soshiyal midiya za ta tsaftace ta koma dandalin cigaban al’umma.
Allah sa mu dace. Amin