ONE.
by @maikosai53
*MATAR MAMMAN*π§π§π§π§π§
Gajeran Labari.
Story and writing by Maryam Abdul'aziz.
*(Mai_'Kosai)*
Follow me on Wattpad@Maryamad856.
*DAGA FARKON SHI HAR 'KARSHEN SHI SADAUKARWA NE GA WANNAN 'KUNGIYA MAI SUNA A SAMA*
Bisimilillahir rahmanir_raheeem.
Dukkan yabo godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani dama da ikon soma rubuta wannan littafi nawa, Ina fata ya bani ikon kammalashi kamar yadda na soma.
Tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W), da ahlayensa, da sahabbansa da dukkan mabiyansa......ameeeen.
*Ban yarda afitar da wani 'bangare daga littafin ba ko duka littafin ta hanyar juyaminshi ba tare da izini na ba, yin hakan ya Sa'ba doka ne kuma ban yafe ba wallahi*
Ina fata zaku nishad'antu da wannan littafin nawa kuma Gajeran labarin....fatan alkhairi gareku masoya na.
Page 1_2.
________Da sauri ta ke sakkowa daga kan matattakalar benan da ke cikin tsakiyar falon gidan, kamar wacca ake hankad'owa .
Hakan yayi dai_dai da 'karasowar wata matsakaiciyar mata ita ba yarinya ba kuma ba babba, wacca a shekaru ba zata wuce shekara 34 ba.
" A'a *Ramlatu* meyake faruwa?, lafiyarki qalau kuwa kike gudu kamar wacca ake hankad'owa??"
Ta fad'a had'e da tambayarta.
So sa kai tayi kafin ta ce "Aunty Rahma ba yaya Saudat ce ta ke cemin *Ramlatutu* ba kuma alhalin tasan ba suna na haka ba, kuma na gayamata tun da jimawa Suna na *Matar Mamman* kuma Ammi ta ce adinga kira na da hakan tunda inason sa " ta 'karasa fad'a cike da shagwa'ba.
Tsaki wacca aka kira da aunty Rahman tayi kana ta ce " Amma Dai wallahi anyi shashasha shine kika kwaso a guje haka, kinga fuskarki kuwa yadda ta jagwale da ruwan hawaye??"
Ta 'karashe fad'a tana mai tuntsirewa da dariya.
Cikin zun'buro baki Ramlat ta ce " to ba Ammi ta ce a dai na gayan ba wallahi sai na gayamata bari ta dawo".
"To Ki ta fad'a shashasha Kawai, a haka zaki 'kare da wannan haukan na ki, ni matsa ki ban waje" ta ce tana mai 'ko'karin giftawa dan ta wuce .
" Wallahi sai na fad'a kuma haka zan ce kun taru ke da ita kun min shegen duka dan na ce " ni ba Suna na *Ramlatutu ba* Suna na *Matar Mamman*, ai dai kinsan halin Ammi Ehhh!"
Ta tsinkayi muryar ta na fad'in haka.
Juyowa tai gami da ri'ko ma ta hannye kana ta ce " haba *Matar Mamman kuma Matar Manya* abun harda sharri Plz kinsan dai Ammi taji ba za tamin da sauqi ba ke taimaki ni dan Allah kiyi haquri " ta qarasa tana mai had'a hannyenta waje guda, Alamar neman afuwa.
Kauda kanta tayi gefe tare da d'age kafad'a kafin ta ce "ohoo! ni ina ruwa na "
" Ai kin banza dan Allah Karki fasa ki fad'a d'in Allah sai na 'karasa ruguza miki wannan 'katon kan naki shegiya kamar yarinyar aljanu "
" oho! dai ai dai duk girman kai na be kai naki ba Kefa kamar basamudiya 'kirar samudawan da, kin ga yadda gefan Kanki ya loma kuwa kamar latsattsiyar tasa " ta qarasa fad'a tana mai 'kyal'kyalewa da dariya ga me da ri'ki ciki.
A zafafe aunty Rahma ta yo kan ta cikin 'kunar rai .
Ganin hakan ya sanya Ramla kwasa a guje ta juya zuwa benan da ta ke shirin sakkowa.
" mahaukaciyar yarinya ki tsaya ma na, ai da kin gane kuran ki wallahi " aunty Rahma ta ce.
Itakam ta na shigewa d'akin da ta baro ta zu'be a kan gadon d'akin tare da fashewa da wata mahaukaciyar dariya kamar ba gobe.
Saudat da ke zaune ta na gyaran farce ta kalle ta tare da Kauda kanta gefe kana ta ce " Allah wadaran Wanda ya girma amma baisan ya girma ba wallahi, anyi asarar kudin tara "
Tsuke fuska tayi kamar ba ita keyin dariyar ba kafin ta ce " ai dai duk lalacewa ta bankai wata ba da take Kiran 'katan mutum basamude kuma kwarto da suna *Baby* "
Cikin fusata Saudat ta ajjiye abin yankan farcen ta juyo gareta kafin ta ce "ke dan ubanki ni sa'ar ki ce ko kinga ina wasa da ke ??" ta fad'a cike da tambaya.
Turo baki Ramla tai kafin ta ce " to ni Allah na tuba kinji na ce wani Abu ne?, to barshima na ce to kinji na ce da ke na Ke ?"
"To da wa kike in ba da ni ba, akwai wani a wajen ne ??" ta tambayeta.
"Yo to ai ni dai ai har yanzu Bakiji na ce komi ba "
Ta fad'a ta na mai mi'kewa , Sai da ta je dai_dai saitin bakin 'kofar d'akin zata fita kana tajuyo game da fad'in " to ai ni daman can asali da ke nake 'katuwar banza mai kwarto "
A guje Saudat ta biyo ta, sai dai ina kafin ta cimma ta tuni ta fice daga d'akin had'i da jan 'kofar da 'karfi kamar wacca zata karya ta.
"Zaki dawo ne Sai na 'ballaki anan, shashasha mai kalar Adawa ".
In ji ruwan *comment* mai yawa game da danna mini *Vote*
Editing is not allowedβββ
Har kullum taku ce *Real Mai_"Kosai*βπ»βπ»βπ»βπ»βπ»