EPISODE 03
by @abdull10k
💀💀💀
*KOFAR AJALI*
_The Return_
```[Hard way and the only way]```
💀💀💀
_________________________
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
***
_________________________
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
***
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
* EPISODE 0️⃣3️⃣*
"Are we going to leave abokan mu here?."
"We don't have much time."
Reply mu'azz.
"And we don't have a choice."
Fadar Atif Bayan yaji abinda Mu'azz ya furta.
"Run!!."
Al-Hussien ne ya sake furta hakan nan suka ruga a guje....
Haka sukayi ta guduwa yayinda cats din ke biye dasu,Aiko cen suka tadda wata kofa wacce take haske matuka tamkar tauraro.. Aiko Basu tsaya ko'ina sai cikin wannan kofa inda muzzaffar Atif da muka mu'azz sukaja kofan da karfin tsiya suka rufe..
Barinsu gurin keda wuya dukkan cats din suka bacce haka kuma Tina Ali and Simon suka bude Idanu birik👁️👁️tamkar kawowar utar lantarki...yayinda idanun nasu tayi jajir.
Mu'azz ne jagaba yayinda suka kasance cikin wannan kofa mai dan karen haske,da shigar su ko babu wanda ya naimi da'a tsaya domin kowanne daga cikin tunani yake akan wayencen mage(cats.) haka sukayi ta takawa yayinda Muzzaffar ya kasance a baya baya sabida soma jin jiri yayi bayan sun shafe wannan ɗan banzan gudu.
Aiko Yankar jiki yayi ya fadi kasa,nan da nan nunfashisa ta sauya,suko sauran abokan tafiyar nasa da shike baya suka basa basumasan lokacin da yayi hakan ba...har Saida sukayi nisa sosai kafin nan Mufy ta jiyo da Niyar ta dubi lafiyar sa....
Aiko buga ihu tayi bayan ta tadda bayan nasu babu kowa kuma babu alamarsa.
"Inane Kuma Muzzaffar ya shige?."
To wayake da Ansar da zai bata? babu domin duk kanninsu basusan lokacin da hakan ya faru ba.
"Wata kila a wajen kofar muka kyalesa."
Abinda Ya fito daga bakin Al-hussein kenan inda Samra tayi saurin mayar masa da cewa
"Noway,Bamu barosa a baya ba saboda lokacin da muka shigo wannan kofa he was standing next to me."
Bayan ta furta hakan sai Mu'azz yayi sauri cewa.
"That means bazaiyi Nisa da nan ba,we have to find him."
Aiko Koda dakika guda basu kara a gurin ba suka koma cikin saurin yayinda suke ambata sunan Muzzaffar din....
Cen sai Mufydah ta kwalla musu kira bayan ta hangi Muzzaffar din akwace kasa,aiko cikin kankanin lokaci suka risketa domin kuwa sun bazune a wannan guri dan gudun karya kasance ya shiga wani lungun na daban.
"Oh my God."
Abinda ya fito daga bakin Samra kenan inda Atif yayi gaggawar durkusawa yayinda yayi masa filo da Hannunsa Mufydah ko ta soma yi masa fifita.
"He's burning up,Ya kamata mu samo wani abu da zai saukar masa da tempure na jikinsa Danko zafin tayi tsamari."
Fadar Atif kenan inda Mu'azz yace dashi.
"Saifa ruwan nan da muka ketara ta ciki,domin shi na ɗiba kuma har yanzu yana nan."
Aiko da jiyo hakan sai ya kama bakin rigar dake jikinsa ya yaga izuwa tsumya sannan ya mikawa Mu'azz hannu hadi da cewa.
"Bani Ruwan."
"Noway Hakan bazaiyu ba Atif,kada ka manta fa ta cikin ruwan nan *Tina* ta dauki wannan cuta sai kuma gashi da tabawa daya tak tayi transfer izuwa jikin Muzzaffar ina ganin wannan ba shawara bane idan akace ayi anfani da wannan ruwan wajen saukar masa da tempure."
Fadar Samra kenan inda Atif ya anshi ruwan daga hannun Mu'azz ya jika tsummar dashi sannan ya soma gogewa Muzzaffar jikin nasa dashi.
"Samra na baki shawara,ki daina Furta mummunar abu akan komi da kika ga za'ayi anfani da shi domin yin haka kadai zaki bawa wayenda ke kokarin ganin bayan mu damar cutar damu,Dan haka dan Allah idan babu alheri a bakinki kiyi shiru."
Ansar da Atif ya Bata kenan,Itako ta haɗa fuska hadi da yunkurin cewa wani abun but sai Mu'azz ya tari nunfashi ta da cewa.
"Guys Have you notice that kwanakin mu biyu Kenan da shiga wanan guri amma babu ɗaya daga cikin mu wanda ya naimi abinci ko ruwa?."
"Nima abinda yake yimin Yawo kenan a brain nawa Amma nayi shiru ne dan kar ace na cika korafi."
Fadar Mufydah kenan inda Al-hussein yayi sauri cewa dasu.
"Uhm Gaskiya ne,Babu wanda zai ji yunwa ko ishi idan ya kasance a cikin wannan guri har na tsawon kwanaki uku."
"Tsawon kwanaki uku kuma,bayan nan fa toh?."
Tambayar da Mu'azz yayi kenan inda Al-hussein ya basa Ansar cewa.
"Kwana ta hudu zamu naimi abinda zamuci wanda zai rikemu na tsawon wani kwanaki ukun,idan kuma ba haka ba dukkanin mu zamu sheka izuwa barzahu."
Aiko da jiyo haka suka zura Idanu alamar mamaki.
*Al'amarin Amrita,Adam da kuma sauran abokan tafiyan nasu ko.*
"Guys shin kuwa kunna ganin abinda Idanu na ke nunamin kuwa?."
Haka Adam's ya tambaya But sukuwa sukayi shiru suka kyaleshi.
Kunnuwan wutan keda wuya Adam din ya tsinci kansa a taron wasu hallitu masu muni matuka,ga Kuma manyan Kaho dake goshin su,jikinsu Kuma yadda kasan jikin *Mesa* 🐍
Aikuwa ganin haka yasa Adam buga ihu tsiya yayinda wutar ta sake daukewa,Ji yayi an damke masa hannu ana kuma jijjiga shi kamar za'a cire masa kafaɗa ta cikin kunnuwansa kuma sautin ababen tsoro iri iri yake ta saurara.
Aiko sharara masa Tafi Amrita tayi bayan wutar ta dawo ta kuma tsaya...
"Are You Mad?,Adam maike damunka?."
Abinda Amrita ta furta ga Adam kenan,inda ya hau waige waige yana kuma fadin.
"Da wasu muggan halittu a nan gurin."
"Wacce tabbaci kake dashi?"
Fadar Harzad kenan inda Anwar yafashe da dariya hadi da cewa.
"Guys you know what?,a tunani na mazane sukafi rinjaye anan gurin but sai gashi it turns out to be maza biyune kacal anan gurin."
Haka ya furta cikin Muryar dariya,bayan ya kammala fadin hakanma saiya sake shekewa da muguwar Dariya inda Harzad shima ya basa nasa bayanin shima kuma ya soma dariya, but da sukaga Amrita ta haɗa fuska hadi da jiyowa ta kura musu Idanu sai sukayi shiru amma cen sai itama ta fashe da dariya hadi da cewa.
"Da wasu muggan halittu anan gurin."
Cikin Muryar naiman tsokana ta furta hakan,inda suka ci-gaba da sheka dariya hadi da kyakkyawa.
Ganin haka yasa Hafsa tsaki hadi da Karasawa wajen Adam dake zaune kasa tace dashi..
"Mai ka gani?."
Aikuwa cikin kankanin lokaci ya bayyana mata suffar abinda ya gani nan saita yunkura tsaye hadi da cewa.
"Guys ina son ku dakatar da wannan shashanci naku domin ba abinda ya kawo mu nan gurin ba kenan,Karku manta mun rasa abokan tafiyanmu a baya dan haka komi ma zai iyya faruwa da kowa dake nan dan haka dariyan ɗaya daga cikin mu ba abu bane mai kyau kamata yayi mu bar Wannan guri."
Haka suka tsuge baki Itako ta mikawa Adam hannu ya mike tsaye.
"Ok here we go."
Harzad ne ya furta hakan inda Anwar yaja fito hadi da sosa keya.
"Amrita! Muje ko."
Aiko fadar haka sai tayi daidai da taka step da tayi nan da nan ƙafarta ta shige sulub yayinda suka jiyo wata kara tamkar ana rufe kogo da katon Dutse.
Aiko bayan nan saika kifiyoyi biyu sun baiyana cikin zafin nama da alamun wannan sune tarkon da hafsa ta taka,aiko dojesu sukayi."
"Guys watch Your steps."
Fadar Hafsa kenan yayinda ta bushe guri guda.
Idan muka sake lekawa bangarensu Atif kuwa zamu tadda su yayinda suke tattaunawa....
"Kwana na hudu zamu naimi abinda zamuci,idan kuma ba haka ba dukkanin mu zamu sheka izuwa barzahu."
Aiko da jiyo haka suka zura Idanu alamar mamaki.
"Guys Ku duba,Muzzaffar na kakkarwa."
Abinda Mufy ta furta kenan inda Samra ta juya kallonta izuwa kan Muzzaffar.
"Ya kamata mu hada masa wuta domin ya dan sami ɗumi."
Fadar Samra kenan inda Mufy ta mayar mata da cewa.
"Ya kamata mu Duba ko zamu Sami itatuwa mu hada wutar dashi."
"Eh gaskiya kam Ni zan ɗan zaga ko zan samu."
Fadar Mu'azz kenan inda Al-hussein yace dashi.
"Zanbika muje tare."
Haka ya furta hadi da yunkurawa sai yajiyo Muryar Samra na cewa.
"No Zan bisa mu tafi tare,kayi zaman ka Al-hussein."
Kowa dake wannan guri yasan da manufa ta furta hakan amma tunda bata baiyana ba waye zai san nufin ta.
"Samra Ni da Mu'azz zamuje mu Duba itacen,dan haka tayani duba lafiyar Muzzaffar."
"Ok tunda kace hakan shi za'ayi Atif."
Aiko babu bata lokaci ya mike tsaye suka wuce tare da Mu'azz suka kyale Samra, Mufy Al-hussein sai kuma Muzzaffar dake kwance.
Mu'azz tare da Atif sukayi ta tafiya wacce kwata kwata itatuwan da suka samu bai wuci sanda biyu ba hakan yasa sukayi ta tafiya suna mai fira da juna.
Aiko cikin wannan tafiya sukayi karo da wata lambu wacce kayan ɗanyene iri daban daban ne a ciki....
Aiko cikin mamaki Atif yayi furucin wow inda Mu'azz ko jikinsa bata basa inda suke tsaye ba.
"Tayaya Kuma lambu a cikin kogo."
Akasan zuci ya furta hakan inda Atif yaje gurin da sauri hadi da cewa.
"Gaskiya gurin nan ya Matukar hadu, komai kake bukata ina mai kyautata zaton zaka samu Anan."
Aiko hakan daya furta daidai da kai hannunsa yayi domin ya ciro kayan ɗayen.
"Atif!."
Cikin kara Mu'azz ya furta hakan yayinda yaje gurin da sauri ya tureshi suka fadi kasa.
Aiko Gurin nan da Atif ke kokarin kai hannunsa ta dawo wata ƙatuwar hawainiya (camelion) 🦎 Ganin haka da Atif yayi saiya yunkura cikin sauri hadi da reke hannun Mu'azz cikin tsoro.
Fashewa Mu'azz yayi da dariya hadi kuma da cewa....
"Hawainiyace fa kawai."
Aiko fadar hakan keda wuya sai dukkanin ciyayin cikin lambun suka rikiɗe saiga taron chemilion.
"Oh my God."
Fadar Atif kenan inda ya sake riko hannun nasa da karfin tsiya....
"Atif Aiko hawainiya kullum cikin slow motion suke kaga kenan bazasu iyya cutar da mu ba."
"A'a dai Mu'azz nasa iyya launi suke iyya juyawa taya suko suka iyya juya halittar su haka."
Ansar da Atif ya basa kenan inda kuma ya ɗaga fuska ya kalli cikin idanun sa.
"Kumafa gaskiya ne,Gaskiya ya kamata mu koma tun kafin su fahimci muna na."
Aiko daukar step daya da sukayi sai wayennan ƴan kananan halittu suka fara tafiya cikin sauri kaikace harbasu akeyi aiko Ganin haka yasa Mu'azz ya kama hannun Atif suka ruga a guje.
Aiko cikin kan kankanin lokaci sukayi masu Atif zobe nan suka take biriki Inda wayennan halittu suka soma karasowa wajensu ahankali.
Aiko ƙasa sanin Mai zasuyi ne yasaka su tsayawa guri guda,nan sai sukaji dirar wani a gefensu hannunsa kuma wata ƙatuwar barkoce wacce ya kunna wuta akai tana ci kaikace runbun kara aiko basu san lokacin da wayenan halittu suka ja da baya ba.
"You have to follow me."
Aiko Forzy suka tarar...
"Forzy!."
haka suka furta cikin hadin baki aiko tuni ta mayar musu da martani cewa
"Eh Nice,Muje."
Haka suka bita a baya ba tare da sunsan inda suka nufa ba aiko kaiwa wata kofa tayi yayinda halittun ke biye dasu..
"Babu ta yadda zamuyi mu shige wannan bayan kasan mun baro abokan tafiyanmu a baya."
Fadar Atif inda Forzy ta basa Ansar cewa..
"To munada wata mafitan ne bayan wannan,idan muka tsaya daga zarar sun cijeka bushewa zakayi ka dawo gunki,dan haka dole mu shige."
Aiko bayan ta furta hakan ta riko hannunsa suka shige cikin kofar.
Aiko shigarsu kofar suka rufe yayinda camelion 🦎 da suka baro a baya ko suka fara harhadewa guri guda.
Bayan sun kammala hakan suka rikiɗe suka dawo bishiya mai cike da arbakatun Allah ajiki.
Cikin kofar da Atif suka shige ko bayan sun tsinci kansu a cikin wannan kofa ne yasa Forzy ta cika masa hannu.
Bayan ta saki hannun nasa ko ya ɗaga inda ya tarar da shafin hannu Forzy ya dawo Kore shar wacce tayi daidai da wannan koren haske daya shige jikin Muzzaffar.
Aiko ganin haka yasakashi zura Idanu dan mamaki.
*KOFAR AJALI*
_The Return_
```[Hard way and the only way]```
*_Ku kasance tare dani,Guys keep liking and commenting_*
***