Kofar ajali Book 2

EPISODE 05

by @abdull10k

💀💀💀

*KOFAR AJALI*

_The Return_

```[Hard way and the only way]```

💀💀💀

_________________________


*Written*

Abdul Alhaji musa 10k

*phone no:*

***

_________________________



*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


*M. W. A*


```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```

***

_________________________



*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*




*FREE BOOK*💯✅

* EPISODE 0️⃣5️⃣*

*_Ina Mai bada hakuri game da Hutu dana tafi na 1month ba tare da na sanar da mabiya littafina ba ina mai bada hakuri kwarai da gaske,bayan wannan ina kuma da Bad news tare da Good news the Good news is that Kofar ajali zata fara zuwa muku sau biyu a sati kuma an kara yawan typing and the bad news is that Dayan littafina mai suna kunfa Yakun zata daina zuwa muku a both WhatsApp da Kuma Facebook dalilin kuwa shine na shiga gasar marubuta na Arewabooks da wannan littafi Mai suna #kunfa Yakun wacce dokar shiga gasar shine banda posting a wasu guraren illa Arewabooks dan haka reads Ina Mai gaiyar ku izuwa chakwalkwalin Marubuta Hausa wato #Arewabooks domin karaya littafin Kunfa Yakun a kan farashi mai Rahusa wato ₦100 Only ga wayenda Kuma bazasu iyya bi ta Arewabooks ba zasu iyya jira izuwa karshen wannan wata ta march wacce bayan gasar farashin littafin zata koma kamar yadda take Da wato ₦300 dan haka kada ayi babu ku,ku gaggauta wajen garzayowa Arewabooks domin karantawa tare da manyan marubuta. Fans I need Your support ta yadda zamu lashe gasar Lets win wannan tare Fans_*





_*LABARIN*_

"Hm dakace basira sai nayi mamaki,to ina basira zatayi aiki anan,duba kaga cikin dakin koda tsinke babu a ciki toh taya zamu naimo hanyar fita?."


*Atif* juya Idanu yayi izuwa kusun ruwa huɗu na wannan ɗaki kafin nan ya saki kakkaurar nunfashi hadi da naiman guri jikin kofar ya zauna,haka Mu'azz shima zama yayi a gefen sa inda kafaɗar su ke hade da na juya...


Nan Atif ya lumshe Idanu inda Mu'azz shi kuma ya kura masa Ido ko kibtawa bayayi,a wannan lokaci kuwa da zaka umurce sa da yayi maka bayani yadda fuskar Atif yake ka zana dako zai fada maka komi ba tare da ya canza komi ba... Yana kan hakan kuwa sai Atif ya buɗe Idanu inda suka hada nan da nan Mu'azz ya murmusa hadi da ɗauke Idanu..


"What?."

Haka Atif ya tambaya inda Mu'azz yayi sauri mayar masa da cewar.


"Babu."


"Ehyee wato ana murmushi Babu dalili Kenan?,Toh bari kaga yanda zan saka ka fadi dalilin yin hakan."

Haka Atif din ya furta yayinda yayi kamar zaiyi masa cakulkuli,aiko Ganin haka yasakashi cewa...


"Wait! wait! wait!,zan fada maka."


"Okay muje ina sauraran ka."


Gajeriyar murmushi ya sake saki kafin nan ya sake cewa...


"Nothing oo."

Aiko juyo hakan yasa Atif ya Soma yi Masa cakulkuli, Mu'azz ko Idan da Abinda ya tsana a duniya to cakulkuli ne,Haka ya bada Gari inda yayi gaggawar cewa zan fada..


Kwanciya da gadon bayansa yayi gefen Mu'azz domin kuwa lokacin da yake yimasa cakulkuli tuni ya baje a kasa yana birgima, Soma cewa yayi...


"Kawai ina mamaki ne."


"Mamaki,akan me?."

Haka Atif ya sake mayar masa da tambaya inda ya soma da cewa..


"Ina mamakin yadda yanzu nake iyya tsayawa na kalli fuskar ka, sa'annan na saurari muryarka yayinda kake nuna kulawa ga ƴan tawaga ta,back then Babu wa'yanda muka tsana a duniya sama da ku amma gashi yanzu mune muka kasance killace a daki daya muna fira hade da wasannin... Gaskiya ko wannan ne kaɗai ya issa ya sakani murmushi kuma koda yanzu na daina numfashi bani da kaico sabida nasan Zaka kula da tawagar kamar yadda ya kamata."

Haka Mu'azz yayi ta suburbudo bayani babu kakkautawa yayinda idonsa na saman rufi na wannan daki...

Batare da Atif ya ce dashi komi ba amma hakan bata saka ya daina zuba ba haka yayi ta tunowa Atif ire iren mugunta da kuma nuna tsaya a fili da kungiyar sa sukayi ta musu hada yazo karashe labarin saiya yunkura ya zaunu inda ya soma kame kame da kaga yanayinsa ko kasan yana sone ya bada hakuri amma mai zai faru bayan ya juya Idanu ya kalli Atif yayinda ya soma cewa...


"Atif Ina da wata alfarma da nake bukata daga gare ka a matsayin kana....."

Haka ya fara cewa amma sai yayi tsit bayan ya tarar da Atif na yanayi na bacci..

Aiko gajeriyar murmushi yayi sannan yayi wani batu cikin kasan ransa..


"Hm a tunanina wannan itace dama dana samu da Zan basa hakuri amma sai gashi Bacci ta raba."

Bayan ya furta hakan a kasan ransa ko sai ya sake da murmushi hade da ciro *jacket* dake jikinsa domin yayiwa Atif barko da ita aiko saida ya lulluba masa wannan jacket kafinnan ya yasa hannu da niyar gyara masa kwanciyar....

Aiko taba jikin nasa keda wuya ya zura Idanu hade kuma da yaye jacket din daga jikinsa cikin sauri.........



"No!!!."

Cikin kara *Amrita* *Hafsa* da kuma sauran abokan tafiyan nasu suka Kwarma bagidajiyar ihu inda kuma suka mika hannu kamar zasu cabko igiyar daya tsinke da *Adam* Haka kuwa Wannan igiyar tayi ta sauka sulululu tana gangarawa da Adam din izuwa ramin tsutsotsin nan,saura kiris ya fada cikin ramin tsutsotsin sai yaji cek igiyar ta tsaya dashi ta sanadiyyar makalewa da igiyar tayi tsakanin wasu manyan duwatsu...


Aiko ganin haka da sauran sukayi yasa suka ruga baki daya izuwa inda igiyar ta makala suka Danko igiyar dakyar suka iyya jawosa suka mayar dashi mazaunin sa....Finally sauka yayi daga igiyar bayan sun tallafa masa da hakan,aiko ganin kafafunsa sun diro a kasane yasakashi kwanciya da gadon bayansa a gurin.


Sai faman haki yake bayan nan ya fashe da dariya inda Anwar da Harzad suka biye masa suna kyakyatawa,nan sai Amrita tahau yimasa surutu kamar haka...


"Adam Maike damunka kane wai,mai kake daukar kanka shin kamasan yadda na kimauce a kanka yayinda kake samar wancen abun?."

Haka Amrita tahau Mita yayinda Idanuwan suka cike da kwalla ganin haka yasa Hafsa Anwar da kuma Harzad suka dubi juna sai suka sake mayar da ganin nasu Guri guda inda Hafsa ta soma cewa...


"Guys Ya kamata mu kara gaba sabida zama da yawa Guri daya tsautsayine."

Bayan ta furta hakan yasa Amrita tayi shiru hade da juyawa gefe guda ranta a bace tasa hannu ta dauki jakarta haka yasa Hafsa da Harzad suma sukayi hakan Anwar ko mikawa Adams hannu yayi inda ya kama ya mike tsaye....


Takawa sukayi izuwa kofar inda da zuwa su gurin Adam yasa hannu jikin kofar bayan nan ya soma yaye yanar dake jikin kofar inda kuma yace da sauran...


"Kunga I'm not sure idan kofan nan zata bude,ku gamawa wannan kofa kallo wannan kofa akalla tayi shekaru dubu ba tare da an bude ta ba."


"Oh hakane?,toh mai zai hana mu jarraba bude ta kafin kayi wannan bayani naka."

Haka Amrita ta furta inda Anwar ya mayar mata da cewa....


"Ta ina zamu fara kenan?,kundai san koda karfinmu baki daya za'a tare guri guda bazamu iyya bude wannan kofa ba."


"toh yanzu mai kuke so muyi kenan?,shin komawa baya kukeson muyi kenan?, kundai san mutuwa muka baro a baya so mai yasa kuke kashe jikine haka."

Aiko ambatar mutuwa datazo cikin zancen Hafsa yasa guri ta soma girgizar yayinda suke jiyo wata kara kamar ta direwar *newclear*


Idan muka Laika Ɓangaren su Samra ko still zaune suke a wannan guri suna dakon zuwan Mu'azz da kuma Atif inda Al-hussein ke zaune cen gefe guda yayinda Samra tare da Mufyda ke duba lafiyar Muzzaffar...


"Guys Ya kamata mu kara gaba sabida They are not coming."

Haka Al-hussein ya furta inda Samra ta mike tsaye inda ta soma cewa...


"a tunanin ka kai waye da har zaka bamu ummurni Al-hussein,You Are not part of us,Kai dayane Al-hussein You Are on your own and dan Allah ina rokon ka Ka rabu damu ka daina jefa rayukan mu cikin Haɗari..."

Haka Samra ta furta yayinda idanunta suka cike da kwalla nan sai taji Mufyda ta dafe kafaɗar ta..


"Samra Abinda nakeso ki fahimta anan shine Komai na duniya na faru ne da dalili,kamar yadda nayi imani cewa zuwan namu wannan guri ma nada dalilin sa saidai har yanzu mun kasa fahimtar meye dalilin zuwan namu nan Gurin."

Ajiyar Rai tayi kafin ta sake da cewa...

"Ni a ganina barin mu nan Gurin nada anfani domin idan har Atif da Mu'azz zaku iyya dadewa haka basu dawo ba toh akwai muhimmiyar dalilin da yasa zasuyi hakan mu kuma da muke nan jiran nasu dalilin da zai saka mu bar wuri shine zama guri daya a wannan guri nada haɗari kinga kenan komi nada dalili Samra."

Aiko bayan ta karashe fadar haka sai Samra ta soma zubar kwalla yayinda tayi saurin rungume ta haka dai suka kasance cikin yanayin kuka.... Babu kuma abinda ta fado mata a ka sai tunanin Ranar nan da suke hanyar zuwa wannan Gurin inda daya daga tawagar tasu take yiwa tawagar su Mufyda Dariya "anyway yanzu dai ba lokacin bane na shiga irin wannan yanayi yanzu lokacine na gyara kurkuren mu, gaskiya ya kamata kowa ya koma ga iyyayensa domin War haka dukkanin iyyayenmu suna cikin damuwa."

Haka Samra ta furta cikin Ranta bayan nan ta juya ta kalli Al-hussein,batare data ce komi ba ta fara da Hada gado da zasu dauki Muzzaffar din akai dan gudun kamuwa da cutar da Muzzaffar din ke dauke da....


Haka suka dauki Muzzaffar din bisa wata gado na sanduna da suka hada yayinda Al-hussein ke rike da sanduna biyu ta gaba Samra da Mufy ko suna rike da ɗaddaya a baya...

Haka suka taka suka bar wannan guri inda da barinsu wannan guri wata jar hayaki ta Soma bullulowa daga kasa bayan wasu dakiku saiga Wannan ƴar karar ramar yarinya ta baiyana gefen ta kuma Ali ne da Simon inda suke tsaye a bayan nata tamkar wasu bodyguards, murmushin mugunta wannan Yarinya tayi kafin nan ta bude tafin hannu ta nan da nan saiga hotunan guraren hudu sun baiyana a tafin hannu nata....


Daya na dauke da Forzy da Tina yayinda na biyun kuwa ke dauke da tawagar su Amrita na Ukun ko Atif da Mu'azz and the last one shine Al-hussein da Samra....

Fashewa tayi da muguwar dariya yayinda tayi ta kyakyatawa su Ali ko Sudin da suka kasance wata halittan ko kula da dariya da take basuyi ba tsayawa sukayi kamar wasu gumaka...

Aiko bayan ta karashe wannan dariya ta juyo suka hada Idanu nan da nan suka bace ita kuma tabi sahun su Samra....


Al'amarin Su Mu'azz ko buga kara yayi cikin salon kiran sunan Atif...


"Atif!!!."


Domin kuwa ji yayi jikin Atif na tafarfasa Kai kace garwashin wuta lokacin daya yaye jacket din da yayi masa barkono dashi ko abinda ya tarar shine hannun Atif ya kumbura sosai yayinda jijiyoyin hannun suka baiyana...

Da shike fari ne Atif din shiyasa zaka iyya ganin wannan koren abar nabi ta jijiyoyin sa a hankali,aiko ganin haka yasa Mu'azz buga wannan ihu haka yayi sauri yage bakin rigar dake jikinsa ya daure hannu Atif din dashi Domin dakatar da shigar cutar jikinsa...


Masu iyya magana kance *"Boys don't cry"* Amma Zan iyya karya wannan fada domin yau naga jajirtatce jarumi kuma kyakkyawa saurayi yana zubar da hawaye ta dalilin abokin gabarsa ta da....

Yana zubar kwalla yayinda yake kokarin daurawa Atif Hannun haka kuma babu abinda ke fitowa daga bakinsa illa "Atif karka barni cikin wannan duniya Ni kadai, dukkanin mu muna da bukatar ka Atif karka barmu shugaban tawaga."

🥺🥺

Abin Haushi Atif bazai Iyya sauraran hakan ba Haka yayi ta zubar kwalla domin yasan bashi da zabi daya wuce hakan..

Mikewa yayi ya soma zazzagawa cikin wannan daki yana bubbuga jikin bangon wannan daki hade da ihun cewa...


"Wani Ya tallafa mana."

Aiko yana cikin wannan yanayi sai yaji mashi ta tsaga jikin bango ta kuma makale a ciki...

Aiko ganin Haka yasaka shi zura Idanu Danko tunanin sa wata bala'i ce take shirin tukaro su haka ya koma izuwa ga Atif....


Idan muka Laika bayan wannan bango kuwa ba kowa zamu tarar ba illa Forzy dake tsaye tana jujjuya tafin hannunta tana kuma cike da mamaki.....

*Previously* *Maimaita Abinda ta wuce*

Forzy ko still tana wannan shesshekar kuka sai taga wata koren haske ya fito ta cikin kasa...

Haka ta tsaya kallon wannan haske har ta rikide ta dawo mutum ganin haka yasa Forzy ta dauki wata karfe mai kama da mashi ta cilla aiko saida wannan karfe yayi kusa da shiga jikin wannan haske amma saita doje haka wannan karfe ta wuce da karfin tsiya ta bugi jikin bango ta tsaga jikin bangon ta shige.....


*What is the secret??* Shin sadaukar da Rayuwar da Noor tayi gareta ne yasa ta mallaki wannan Ikon? Hm waya Sani.


Cigaban labarin...

Haka wannan wanda ta baiyana cikin Haske ta juyo inda suka kuma haɗa fuska aiko ba kowa Forzy ta haɗa ido dashi ba illa Tina...

Yayinda Kuma ta riga ta rikiɗe izuwa abin tsoro domin fuskarta rabi a rube rabi kuma fresh haka zalika jini na zubowa daga bakinta nan sai tayi kama da zombie...


Haka ta juyo a guje ta karasa wajen Forzy ta bugata da jikin bango har Saida ilahirin gurin ta girgiza....

Haka inda wannan mashi ta makale itama hakan daya faru daɗa tsorata Mu'azz yayi wacce tasashi daukar Atif ya Goya a gadon bayansa...


Forzy ba ƙaramar azaba take sha a hannun Tina ba domin har fasa wata bango dake cen nesa da wacce Su Atif ke ciki sukayi izuwa wata daki haka dai baisa Forzy daina azabtuwa ba tana cikin wannan yanayi amma babu wacce take gani a idanunta illa Noor wacce take cewa...


"Forzy zaki iyya kare kanki..."

Haka dai take ta gani hade da jiyo Muryar Noor na cewa aiko bayan daukewar Hoton Noor a idanun nata sai ta tuno wata muhimmiyar bayani data taba saurara cikin wa'azi game da mutane boye wacce Mai wannan wa'azi ke cewa...


"Babu wani ko wata a doron kasa daya fi karfin *Allahu subhanahu wata'ala* kuma babu wani halitta cikin halittun dasuka kasance ba bil Adams ba da karatu Alkur'ani mai tsarki bata konasu yayinda suka kasance suna Yiwa bil Adam mugunta saidai Idan Mai naiman tsarin baiyi imani da hakan ba...

Dukkanin halittu wacce suke a boye hanyar rikesu ko nace dakatar dasu daga aikata mummunar abin kuna su kasa motsawa shine rikesu a goshi...."


Aiko tuno hakan da Forzy tayi ya saka ta koma duniyar zahiri wato jibgarta da Tina take yimata..

Aiko da Tina tayi kurkuren Kawo goshita kusa da Forzy sai tayi anfani da wannan fada data jiyo cikin wa'azi wajen kama goshin Tina inda da yin Haka ta soma karanta *Ayatul kursiyu* wacce tasa Tina buga ihun tsiya tana kuma kokarin kwace goshin nata daga hannun Forzy amma ta gagara yin hakan....


Bangaren su Amrita kuwa Girgiza gurin ta soma yayinda suke jiyo wata sauti mai kama da dirar nakiya haka yasa suka soma tura kofar suna dugun abinda zata biyo bayan Wannan kara....

Aikuwa basu iyya bude wannan kofa ba Haka kuma hasken dake wannan Guri ta kafe...nan Gurin tayi shiru babu karan wannan abu kuma babu abinda ya faru...


Nan suke sai sukaji Wata sauti na tashi tamkar ganga ake bugawa sautin kuwa sautin kide kide na Afrika ta da...ne ke tashi

Cen nesa suka hango wata haske na yiyowa ta inda suke yadda kasan kerosin aka zuba a guri domin kuwa hasken ta wutace wacce bata cutar da fata haka wannan wuta ta karaso inda suke ta kuma yi musu wata alama wacce duk cikin babu wanda yakeda Sani akan wannan...


Zane da wannan wutar tayi na nuna wata gini da kuma mutane dake rayuwa a ciki wannan gini haka kuma da akwai wasu dake cikin wannan zane suna haske sosai Kuma number su daya da nasu Amrita.... ma'ana yawansu daya


Wannan ne yasa nake kyautata zaton taswirar ginin wannan haske take gwada musu haka suka tsaya kallon wannan haske babu wanda yake da sani akan abinda wannan haske take gwada musu har daukewar ta bayan nan fitulun gurin suka sake haskawa.... Hafsa ta tambaya...


"Shin cikin ku da wanda ya fahimci wani abin?."


"Not really gaskiya Ni babu abinda na fahimta."

Haka Anwar ya furta inda Amrita da kuma Harzad suma suka furta hakan....Shiru da Adam yayi bai furta komi ba yasa suka juya ganinsu kansa,Shiko ganin yadda suke kallo nasa yasan suna expecting wani abun daga garesa..


"What?."

Tambayar da yayi Kenan inda Amrita tayi sauri cewa dashi..


"A tunanin mu akwai abinda ka fahimta."


"A'a babu komi."

Haka ya mayar musu da ansa inda suka juya suka kuma cigaba da tattaunawar su, Adam shiru yayi yana nazari yayinda yake wani batu cikin siririyar murya...


"Wannan alama da abinda take gwada mana saidai mun kasa fahimtar ko meye wannan, gaskiya ya kamata mu naimi sani akan wannan alama amma taya zamuyi hakan.."

Bayan ya furta hakan sai yayi shiru na wasu dakiku kafin nan ya sake da cewa..


"Kodai Taswira take son gwada mana?."


Idan muka koma bangaren su Samra ko tafe suke yayinda suke dauke da Muzzaffar nan sai Samra ta kalli cikin idanun Mufydah kamar da abinda take shiryawa aiko yin haka yasa ta Mufyda ta anshi sadar datake rike dashi hakan ya bawa Samra damar takawa izuwa inda Al-hussein yake...


"Ah Samra kin gaji ko?"


"A'a kawai dai inason mu tattauna wata abace..."

Da dukkan alamu so take ta bada hakuri game da abinda tayi masa amma bata sami damar hakan ba ta sanadiyyar Mufy Domin tayi furucin cewa...


"La kunga wata bishiya."

Haka hakullansu ta koma kan bishiyar haka ta rasa dama itama Al-hussein ko cewa yayi...


"Finally kunga kwa sami abinda zaku taba, sannan mu futa."

Aiko bayan fada hakan suka soma tafiya but sadly sai Al-hussein ya yanki jiki ya fadi kasa haka kuma ya soma kakkarwa hade da birgima kamar mai farfadiya.


Shin Kuna bukatar sanin abinda yasa hakan ta faru da Al-hussein??. Idan Ansar ku eh ce toh dole sai mun dawo baya sosai da labarin.....


Idan zaki iyya tuno lokacin da Al-hussein yake kukar cewa this is the End of me still a lokacin kuma Harun ya kasance a dakin nan dake saman wannan gada wacce gadar ta fadi dakin kuma ta kulle dashi....


A wannan lokaci dai a cikin duhu mai tsanani tsoratarwa Harun ya kasance da shike yaga Akwatin gawa kafin dakin ta kulle kuwa yasaka shi takawa a hankali yana dafe dare har ya kaiga wannan akwatin gawa wacce aka kera da ƙatuwar dutse...

Aiko bayan ya kaiga akwatin yasa hannu da karfin tsiya ya turu inda wata haske ta baiyana wacce wannan haske har inda su Atif suke a lokacin takai, haka Harun ya yanki jiki ya fadi wacce haka sai tayi daidai da samuwar gangar jiki ga Al-hussein harma suka iyya barin wannan guri...da suke


Sa'annan duk wayennan abubu da sukayi ta faruwa bayan barin su wannan wuri Harun dai ya kasance sume yake kuma a wannan ɗaki haka yakasance har sai a wannan lokaci ya sami damar farfadowa haka ya tadda daki na dauke da farar haske wacce ta cikin wannan akwatin gawan take fitowa... Haka yasakashi mikewa izuwa gurin da akwatin yake aiko babu abinda ya tarar aciki illa wata hula wacce sarakai suke daurawa a kawunan su wato 👑 krawun...


Aiko daura wannan Hular a kansa keda wuya sai wani baki abu mai kama da hayaki ya mamaye jikinsa babu inda ake iyya gani daga cen wannan aba ta yaye saiga Harun yadawo wani abin na daban dukda cewa still shine Amma yanayinsa da kuma shigarsa ta sauya ta dawo Baki Kirin yayinda Idanuwan sa suka dawo jajir hakan ya sakashi takawa izuwa kofar nan dake bayansa bayan ya kurawa kofar Idanu sai yayi murmushi wacce wannan murmushi da kaganta kasan ta muguntace... Sa'annan yayi furucin cewa


"I'm Back." Abinda ya furta kenan sanan ya sake murmusawa.



*KOFAR AJALI*

_The Return_

```[Hard way and the only way]```


*_Ku kasance tare dani,Guys keep liking and commenting_*


***