NAWAFF

Part 6

by @bilynabdul

Page👉🏻6


........Nawaff kuwa tafiyarsa yayi yabar mas'ud, mas'ud bai damuba dan dama batare suka zoba, komawa yayi wajen taron dan baikama ta ace suduka sun tafi ba.


NAWAFF kwance afalonsa dayaji kayan more rayuwa iri2 yana kwance saman doguwar kujera idanunsa lumshe, tamkar maiyin barci, amma idanunsa biyu, yana cikin tsananin b'acin raine kawai, tunani yake mizaima yarinyar nan ya huce haushinsa, dan ya tsaneta, hangota kawai yake lokacin data maresa, yakai hannu yashafa fuskarsa.

Yay kwafa, wlhy sai yarinyarnan ta raina kanta inhar yana numfashi.

Kofa aka kwankwasa, ya ce, "kowaye ya shigo.

Wata 'yar aikin gidansu ce, d'auke da tiren kayan marmari, ta d'ora asaman tebirin dake tsakiyar falon, tad'an jawo tebir d'in gaban kujerar da Nawaff yake kwance.

Watama tashigo da kuloli, ta d'ora inda 'yar uwarta ta d'ora, sannan suka duk'a suna kai gaisuwa wajen oga Nawaff!!.

Hannu kawai ya d'aga musu sannan yay musu nuni dasu tafi.

Da sauri suka wuce dan sunsan halinsa baya son wargi.


D'aya acikinsu ta ce, "wlhy talatu yaya Nawaff yana burgeni, dama zaice yana sona!,

Talatu ta rik'e baki, lallai ladidi yau na tabbatar bakida hankali, garama tu wuri ki fidda wannan tunanin a ranki, tun kafin wanima agidannan yajiki, in banda wuce gona da iri, yazaki had'a kanki da wannan had'ad'd'en mutumin, mai ilimi da kud'i, ga k'yau, wanda duniya tasan da zamansa.

Ladidi tayi dariya kujimin wannan talatun, to kika San abinda ALLAH zaiyi ne??.

Talatu ta ce, "A'a.


Tunda suka fita baiko motsaba bare yaga abinda suka kawo masa, wayarsa tashiga k'ara cikin sauti mai dad'i, idonsa arufe ya mik'a hannu ya d'auka, ahankali ya bud'e idanu dan ganin wake kiransa, momcy yaga ansaka.

Wayar ta k'atse aka sake kira.

Cikin ladabi ya ce, "momcy barka da dare.

Daga can ta ce, "barka dai, wai lfy banga kashigoba?, kuma ance mini kadawo.

Wlhy babu komai momcy ina d'akine, nagajine shiyyasa kika ga ban shigoba, inaso nayi barcine da wuri, dan gobe d'aurin auren SAFWAN, banaso nak'i zuwa gashi kuma na safene.

Okey to shikenan, dama nazata ko bakada lfy ne??.

A'a lfyta k'alau momcy na!!.

To shikenan saida safe.

ALLAH yakaimu my sweet mom!!!!.

Saida takashe sannan ya kashe.

Number mas'ud yakira, batareda yayi sallamaba ya ce, "waikai malam kana inane??.

Gani nanma shigowa gidan mas'ud yafad'a.

Kashe wayar yayi batareda ya ce, "komaiba.


Mas'ud yaturo k'ofan yashigo da sallama, bai saurari amsaba, dan yasan bazai samuba, saboda mutumin yau cikin fushi yake.

Kujera yanema ya zauna, tareda fad'in gani neman mi kake mini??.

Nawaff yatashi zaune, yad'an tsurama mas'ud idanu, bayan kamar minti d'aya ya ce, "bro's plz inaso ka taimaka mini??.

Mas'ud ya ce, "to wane irin taimako kenan??.

NAWAFF yad'an cije leb'ensa na kasa, ya ce, "na nemo yarinyar nan, inaso nasan ita wacece?, 'yar kuma wacece?.

Dan wlhy idan banyimata rashin mutunciba zuciyata zata iya fashewa, ALLAH na tsaneta, kuma saina koya mata hankali, daga kaina bazata sake rashin kunyaba, ko kuskurwn marin wani.

Mas'ud yay masa kallon tsaf dan ganin yanda yafita hayyacinsa yau d'aya.

Yaja numfashi, Nawaff! Yakamata kadawo hayyacinka, karka manta kaifa kafara tsokanar yarinyarnan, kamareta, kayimata dariya.

To dankuma yau tarama saikaji haushi, yakamata ku tsaida fad'annan haka tunda kowa yayima kowa, sannan ka janye k'udirinka na d'azu, dakace marin data yimaka shine zai zama fansar budurcinta, Nawaff bansanka da irin wannan halinba, kar ka aikata abinda zaizo ya dami kowa, wannan ba hanyar bullewa bace, kai dama soyayya kuka koma dan wlhy kun dace da juna sosai.

Harara Nawaff ya watsama mas'ud, wadda dama tun d'azu ita yake masa bai ganiba.

Ya ce, "ALLAH kuwa mas'ud yau dawanine yafad'a mini maganar nan wlhy dasai na bubbugeshi, amma............. yay kwafa kaiwai batareda ya karasaba.

Mas'ud yay murmushi ya ce, "amma mi....?, ka karasa fad'a mana, to konima zaka bibbigeni ne?, ka huce haushinka!!,.

Tsaki NAWAFF yayi yatashi zaibar falon, mas'ud ya tuntsure da dariya, tareda fad'in sakai a wahala kenan,, duk wanda dai yaga wannan fad'an naku yasan na masoyane😜.

Har Nawaff yakai k'ofa yadawo ya ce, "kai dallah malam sauraramin!, mixanso a jikin wannan faratun yarinyar mai kama da aljana, kai dana so wannan yarinyar gara naso 'yar k'auye wlhy.

Dariya mas'ud yake tuntsurawa harda hawaye, cikin dariya ya ce, "aii kaima faratunne Nawaff, koka manta?, amma mudai 'yan kallone mijin faratu, mas'ud yafad'a cikin tsokana😜.

NAWAFF ya kula mas'ud yana neman maidashi wani sakaraine, dan haka yashige bedroom yay kwanciyarsa.

Dak'yar mas'ud ya lallab'ashi yafito sukaci abinci.



WAYE NAWAFF SA'EED MODEEBBO???????, kubiyoni danjin wannan amsar😜.