NAWAFF

Part 11

by @bilynabdul

Page👉🏻11


....koda daddare yasmeen k'in zuwa kai amarya tayi, ta langyare akan batada lafiya, ta kashe wayarta kuma dan kar akirata.

  Haka rayuwa tacigaba da gudu da sauri, Nawaf yagama hutunsa ya tattara ya tafi kasar Spain domin cigaba da biga kwallo.

  Har ya taho bai k'ara had'uwa da yaesmeen ba, hasalima yamanta da ita, yacigaba da harkokinsa kamar yanda yasaba.

  Itakam yasmeen bata manta dashiba, ko makaranta zata takan fita cikin d'ar2, kullum addu'ar ta kada ALLAH ya had'ata da Nawaff ko da amafarki.

  Dahaka dai aka shere wata uku bataji d'uriyarsa ba, ahan kali tafara sakin jikinta.


Yau agajiye tadawo daga school ta shigo falon tana jan k'afa kamar kazarda kwai ya fashewa aciki, yaseer ne kawai afalon yana cin abinci, idanunsa nakan TV ko k'yaftawa bayayi.

  Yasmeen tadaki kujerar dayake zaune dan taga alama baisan tashigoba, yajuyo da sauri yana kallonta.

  Yasmeen ta harareshi kaidai ALLAH ya shiryaka, shikenan indai kana kallon kwallo sai a rasa hankalinka gaba d'aya.

   Yaseer yay dariya, sorry my aunty ALLAH bansan kin shigoba, kinsan yau mutumina yake buga kwallo bana son komai ya katseni wlhy.

  Yasmeen ta tab'e baki, waye kuma mutuminka??, ata k'aice ya ce, "modeebbo mana, gaban yasmeen yafad'i ras danjin sunan wanda yazame mata baraxana arayuwarta ta yanzu, ta ce, "waye kuma modeebbo??.

  Idonsa na kan tv ya ce, "kalli tv zan nuna miki shi, shine number 10.

  Yasmeen taja flet d'in abincin dayakeci gabanta, ta hauci, saidai itama hankalinta yana kan tv d'in, wani uban ihu yaseer yatashi ya kwala tareda fad'in 🗣goooooooooooooo⚽!!!!!!!!!.

  Yasmeen tai saurin rufe kunnenta danjin zai fashe saboda k'arar da yaseer ya kwala🙉, cikin kara ta ce, "dalla malam karka fasamini dodon kunne.

  Ya zauna yana dariya tareda 👍🏻,yana fad'in sai modeebbo, kana wuta my gay.

  Sai asannan idanun yasmeen suka kai kan Nawaff tamik'e da sauri tana fad'in yaseer kana nufin wannan gay d'in, ta nuna Nawaf da aka nuno ya durkusa akasa yad'aga hannunsa samma yawani wage baki da alama shima ihun yakeyi dan murna, wasu 'yan kwallo sukazo suka rungumeshi suna ihu.

  Yaseer ya ce, "shine sistona, tauraro kenan mai haskawa a duniyar kwallo, yanzu su duniya take yayi dason gani, hala kin sanshine kika mik'e zumbur.

  Yasmeen taja ajiyar zuciya ta ce, "natab'a ganinsa dai, da sauri yaseer ya ce, "dan ALLAH dgsk kikeyi??.

  Yasmeen ta tab'e baki, ta ce, "kaji yaro natab'a yimaka k'aryane??, awajen bikin Asma'u natab'a ganinsa, dama d'an kwallone??.

  Yaseer yagyara zama Taf sisto idan kinji ana fad'in mai laya kiyayi mai zamani to modeebbo kenan!!, ai duk ranar dana had'u da bawan ALLAH nan to sainayi sadaka.

  Yasmeen ta tunysure da dariya, amma kaidai d'an wahalane wlhy, tafad'a tana mik'ewa.

  Yaseer ya ce, "kedai tafi dan bazaki tab'a ganewaba.


Nawaff zaune ad'akinsa akasar Spain, yana zaune bisa kujera mai zaman mutum d'aya, hannunsa rik'e da remote, yana neman tasha, wayarsa dake gefensa tayi wringing yakai hannu yad'auka.

  Saida yad'an murmusa sannan ya ce, "Hello my gay ykk?

  Daga can mas'ud ya ce, "ina lafiya my bro's, naga wasa d'azu yayi k'yau, ammafa kayi k'ok'ari, acinkin minti biyu na farko fa ka jefa mana kwallo a raga, ina alfahari dakai my bro's.

  Nawaf yay sassanyan murmushi tamkar yana gaban mas'ud, ya ce, "nagode d'an uwana, kana k'ara mini karfin gwuywa a rayuwa.

  Karka damu bro's, dama Anwar ne ya ce, "nakira masa kai, tun d'azu yake nemanka bai samuba, yanaso yayi maka murnar nasarar dakuka samu.

  Nawaf ya ce, "ayya my little bro's banishi.

  Anwar yakarb'a wayan cikin 'yar muryarsa ya ce, "yaya congratulation!!,

  Tnx my boy, ykk??.

 Ina lafiya yaya, momcy ma ta kalli wasanka na d'azu.

  Woow nice, kace ina gaisheta kajiko??.

  To yaya bye🖐🏻.

Okey bye autan momcy.

  Mas'ud yakarb'i wayan suka cigaba da tattaunawa, mas'ud ya ce, "to shikenan bari nabarka haka, amma gsky kayi k'ok'ari nanda 2month d'in kazo, indai kanada dama, ko kwana uku kayi ma ya isa.

  Okey I will try, my bro's

 Okey ALLAH yakaimu lokacin.

 Sukayi sallama kowa ya kashe wayar.

    Nawaf ya kwantar da kansa ajikin kujerar tareda lumshe idanu..................✍🏻