RUHI BIYU! RETURN

EPISODE 06

by @abdull10k

🧟‍♂️🧟‍♀️☠️☠️🧟‍♂️🧟‍♀️


    

        *RUHI BIYU*

  _[a gaangar jiki daya]_

                       *RETURNS*


                       🧟‍♀️🧟‍♂️☠️☠️🧟‍♀️ 🧟‍♂️      ‍


*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

      _Kungiya d'aya tamkar da dubu._


        *_SPECIAL EDIT 2021/2022_*


*Written*

Abdul Alhaji musa 10k

*Phone no:*

***


         *REPORTS*


*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*


*📣📣📣SANARWA SANARWA📣📣📣*

_Ga masu Bin littafin Kofar aljali littafi na biyu Ina Mai Baku hakuri game da rashin posting da kuka ga ba'ayi gaskiya abubuwa ne sukayi yawwa..._

_dan hakan Ina Mai Mika sakon ban hakuri ga fans inshallah bada jimawa ba zaku jini love you all_


*😷😷STAY SAFE...  STAY AT HOME😷😷*


*FREE BOOK💯✅*

*📚LITTAFI NA BIYU*

*EPISODE_0️⃣6️⃣*




🆕⬇️

*Boka*

Cikin sauri ya taka da niyar fita daga Dakin da suka kasance ciki,Aiko sai daya Kai kofar fita kafin yayi Karo da Safwan na kokarin shigowa,Zura Idanu Safwan yayi yayinda yayi arba da Bokan,Faruq ko dake baya cen ya Mike hade da kurawa Safwan idanu.


"Safwan I ask you to stay at home."

Fadar Faruq kenan inda Safwan din ya taka ya shige ciki hade da basa ansar cewa.


"Oh really,Ka sakani na nuna masu Harun video,akan zaka tsare lafiyar su bayan nayi hakan,Amma wacce tabbaci nake da shi nacewa zakayi hakan...idan suka karaso nan

Am not sure kamar yadda na cika muku aikin ku zaku cikan nawa shiyasa nazo da kaina domin na tabbatar da faruwar hakan."


Bayan boka yajiyo Haka ya juya ya kalli fuskar Faruq,Aiko ko dakika guda bai sake ba ya wuce ya kyalesu tsaye.


"Safwan karka manta mun umurce ka,daka tsaya tare da mu'azz a gida Amma Mai yasa ka biyo mu anan guri?."


"Faruq! Mai ka dauke ni,? Sakare ko meye,tayaya Zan kyale wayenda suka yadda Dani suzo Waje Mai had'ari irin wannan, what will happen idan suka gano ku kuka sakani na dauki waccen tattaunawar taku,zasu tsaneni na har abbada, sa'annan ta bangarena Kuma idan wani Abu ya Sami su bazan yafe ma kaina ba Dan Hakan ba......."

Aiko bai karashe wannan magana ba sai sukaji gidan ta soma girgiza ta sanadiyar wata Kara Mai kama da saukar *newclear* a saman ginin,Nan da Nan Safwan yayi tsit yayinda ya zura idanu.


*Tirkashi Safwan a tawagar Boka bakin bawa,Kuma waccen daukar Jabuce kutt gaskiya wasu mutanen ba abin yadda bane,toh fa Allah Mana Mai kyau*


Al'amarin *Boka bakin bawa* kuwa cikin sauri yake sauka daga matattakalar yayinda zuciyar sa cike fat da burin ganin halin da Ramlah ke ciki...

Zuciyar tasa na bugun uku uku yayinda kwakwalwarsa ke raya Masa cewar Plan nasa ta Riga ta rushe.


tsintar kansa wajen da yake da tabbacin Nan ya baro Ramla, ya sakashi fadar cewa....


"Zance ya 'baci."


Domin kuwa illa fashesshiyar Kwan ya tarar Babu Ramla Babu Kuma alamarta,hada Rai yayi ya ciji yatsa..


"Taya hakan zai faru."

Tambayar daya kasa bawa kansa ansa kenan,Nan saiya sauke boron dake rataye a kafadar sa yasa hannu ya Ciro wata madubi dayake duba a ciki.


Shafar madubin yayi sai ya anbaci sunan Ramla,Aiko babu abinda madubin ta nuna illa hudu wacce wata haske ke ta yawo a ciki kamar walkiya,sai da wannan haske ta kusan dauke ganin sa kanfin yasa hannu ya ture.


"Zancen banza!"

Cikin fushi Bokan ya furta yayinda ya yunkura tsaye.


"Babu ta yadda za'ayi shirin Dana 'bata lakaci Ina tsarata ta rushe lokaci kalilan,Babu ta Yadda Safras zai shigo Nan ba tare da na kamashi ba."


Hmm bayan fadar haka sai ya tuno da zancen Safwan...


"Ka sakani na nuna masu Harun video,akan zaka tsare lafiyar su Amma wacce tabbaci nake da shi nacewa zakayi hakan...idan suka karaso nan

Am not sure kamar yadda na cika muku aikin ku zaku cikan nawa shiyasa nazo da kaina domin na tabbatar da faruwar hakan."


Bayan ya tuno hakan sai ya furta cewa...


"Hakan na nufin yabi bayansu domin sun ajeshi a gida ya kula da mu'azz...

That means Harun da Raihana sun shigo gaba dashi kenan."


Shiru yayi alamar nazari bayan nan ya sake madubin ya shafa hade da furucin.. "Madubi Mai cike da al'ajabi nunamin halinda Raihana da Harun ke ciki."


Fadar hakan keda wuya madubin ta cike da haton koren ganyaye bayan Nan sai ga Harun da Raihana taye bakin hanya yayinda Harun ke kokarin duba musu mota dankuwa motar ta tsaya cek.

😲😲😲


*Rud'ani*


Zura Idanu bokan yayi hade da share hoton da tafin hannun sa...

Sai yayi wani Batu a kasan ransa,cewar sa shine.


"Toh idan su Harun Basu karaso ba,waye to yazo a matsayin su?."


Taya zai gano suwaye su bayan kamarsu daya, Nanfa sai wani tunani ya zo Masa aka na cewa da ya sake umurtar madubin ya nuna Masa abinda ya faru da Ramla Mai zai Hana yayi anfani da karfin ikonsa wajen ganin hakan,gurbacecciyar shawarar da kwakwalwarsa ta bada kenan.


Aiko sa tafin hannu yayi Kan madubin ya kuma lumshe Idanu sai ya furta cewar.


"Madubi,madubi sihiri Nunamin abinda ya faru da Ramla...

Tsartsatsin wuta kurun yake ta gani cikin idanunsa yayinda Kuma Babu abinda hakan ke anfanar dashi illa cutar da lafiyarsa Danko jini fara zubo masa tayi daga hanci yayinda jikinsa ke rawar d'ari daga karshe madubin ta tsage ta dauke haske.


Nanko wannan boka ya iyya bude Idanu yayinda kuwa ya daga kafin hannunsa yasa Ido...

Aiko gani yayi tafin hannun nasa tayi kaca kaca ta tsastsage kamar yadda madubin tayi.


Mikewa yayi yayinda jiri ke makukar takura masa,dakyar ya iyya tsayawa da kafafun sa,bayan yayi hakan saiya Ciro waya wacce Faruq din ya tilasta masa daya rike da gudun bacin Rana,ya Soma cewa..


"Faruq! Faruq! Faruq!."

Shiru dayajine yasa ranshi ta tsinke Nan da Nan ya sake cewa.


"Faruq kana sauraro na?."

Still Babu amsa Aiko a guje ya sake hayewa steps din da niyar zuwa dakin daya Baro Safwan tare da Faruq a ciki.


Aiko sai daga haye izuwa floor ta biyar sai ya sake tarar da jakarsa da Kuma fashesshiyar madubin daya Bari ya downstairs.

Zura Idanu yayi Danko jikinsa duk gumi ne ta mamaye ko'ina Amma Kuma sai ya tarar tafiyar Babu yakeyi domin guri daya yake..


*Readers kar a Rude Dan Allah,Bari mu dawo baya kadan da labarin."


Aiko fitar Safwan keda wuya wannan mu'azz dake dakin Raihana wacce yake zaton bacci yake, ya bude Idanu..

Mikewa yayi Kai tsaye yajega kofar yasa hannu da niyar budeta Jin kofar ta rikene ya saka shi murmushi Hadi da zura Idanu wacce zura idanun da Yayi ne ta basa karfin ikon hango abinda ke bayan Wannan kofa.


Gani yayi Babu kowa a falon Haka ta sakashi yabi jikin kofar ya fita daga dakin,Nan sai gashi ya baiyana a wajen dakin Nan da Nan ya wuce saman upstairs da niyar zuwa waccen dakin wacce tunkan ya karasa wannan guri mu'azz daya kasance cikin Dakin yasan da abinda ke faruwa.


Karasawar sa keda wuya saiga Mu'azz1 shima ya fida daga dakin,kurawa juna Ido sukayi suna kallon cikin idanun juna,bayan Nan sai suka juya Karo daya suka kurawa Taga Idanu.

Aiko yin hakan keda wuya sai suka rikide suka koma wata bakar hayaki wacce ta tashi sama Aiko Saida suka Kai tololuwar gidan kafin suka rabe gida biyu Daya yabi bayan su Raihana dayan ko ta wuce bangare guda.


Wannan hayaki na tafiya a sararin samaniya, yayinda yakai kansu Raiha dake mota ko Sai sashi guda daga hayakin ya sauka Kan motar Nan da Nan motar ta tsaya cek..


Aiko yin Haka keda wuya sai Wannan hayaki ya dire a Tsakiyar titin, hayaki ya rikide ya dawo Mota ciki ko Raihana ce tare da Harun...


Haka motar ta wuce Kai tsaye izuwa wannan guri da Raiha da Harun ke kokarin zuwa...

Wacce sune Safwan yabi bayansu lokaci da suke wannan taku.


Safwan ko a hanyarsa ta zuwa wannan guri da shike hankalinsa gabaki daya a kan driving ne yasa bai hangi su Raiha yayinda suke duba motar tasu ba.


Al'amarin Faruq da Safwan ko ji sukayi gidan ta soma girgiza ta sanadiyar wata Kara Mai kama da saukar *newclear* a saman ginin,Nan da Nan Safwan yayi tsit yayinda ya zura idanu.


"What's Going on?."


"Safwan Taya Ni Kuma Zan sani."

Haka ya basa ansa yayinda yake kokarin bude kofa,aiko kamo hannunsa Safwan yayi hade da ce masa.


"Karka manta Faruq,malan yace karmu sake mu fice daga Nan."


"So what Safwan,Ina yake Shidin,bai dawo ba Dan Haka ya zaman Mana Dole muje mu duba lafiyar sa tare Dana Ramla."


"No way bazan kyale ka ka fita ba,ya kamata mu jira zuwan sa."

Aiko fadar hakan da Safwan yayi sai tayi daidai da 'barkewar ihu cikin Muryar Ramla...


"Ramla!"

Abinda ya fito daga bakin Faruq kenan,Haka shima Safwan ya zura idanu...

Aiko basa hanya yayi yayinda yabi bayansa fitarsu ko suka sake jiyo wannan Kara,sai Faruq yace da Safwan "this way" yayinda ya nuna Masa hanyar da zasu bi.. Kuma Haka sukayi suka wuce cikin sauri.


Aiko tafiyar su keda wuya saiga Raihana da Harun sun baiyana a gurin da Safwan da Faruq suka Bari...

Juya Idanu Raiha da Harun sukayi suka kalli juna,Aiko Bayan sunyi haka suka sake kwarma ihu dukkanin su biyu cikin muryar Ramla, sa'annan suka bacce.


Al'amarin wannan bakin hayaki dayabi bangare guda din ko,direwa yayi a Tsakiyar farfajiyar gidan Alhaji *Sunusi*


*Readers Hope zaku iyya Tino Alhaji Sunusi,Wanda yasha dakyar daga hannun Nainah*


Cikin suffar Mu'azz ya sauka a wannan gurin,bayan direba yayi Ido hudu dashi ko ya sumar dashi sa'annan ya dawo suffar sa...

Aiko yin Hakan keda wuya saiga Alhaji Sunusi ya fito daga falonsa yayinda bangaren hagunsa da Kuma Dama security ne da Kuma abokan aikin sa....


Cikin kasaita ya wuce izuwa farfajiyar gidan inda ya shige mota ya Zauna bayan direbar ya bude Masa ya shige ciki,bayan ya jasu sun fice daga gidan sai yace dashi.


"Airport zaka kaini,Bayan Nan sai ka koma kaje ka Sami professor Mamud a Uni kace nina turo ka,zai baka wani aike sai ka dawo min gida dashi."


"Okay Master."

Haka direbar ya bawa Alhaji Sunusi Ansan,yayinda yajasa ya kaisa airport din bayan ya sauka gurin sai ya Soma taku yana karasawa gurin.


Cek kamar daukewar ruwan sama ya taka biriki bayan yayi Ido hudu da direbar daya baro a baya,How possible tayaya Kuma ya sake arba dashi bayan ya baro sa a baya.

Aiko ganin Haka keda wuya sai airport din ya rikide ya dawo wannan tsohon gini da Faruq Safwan da Kuma boka bakin bawa ke ciki.😲


_*Bala'i ana wata ga wata*_

_Short Episode Mu hade a Next Episode...Comment birjik nake so kunji♥️_

_Love you all_