RAYUWAR HUSNAH

CHAPTER 2

by @milhaart

 *PAGE* 2️⃣0️⃣↪️3️⃣0️⃣

 ```PREVIOUSLY```

Husnah na gani zaune a cikin gida tana wanke wanke, Sallama taji kanta ansa sai taji inuwar mutum akanta da sauri ta d'ago ganin Yarima tayi a saye Yana kallon ta Yana Murmushi.


Cikin sauri ta durkusa Tace "Barka da zuwa Yarima" kanta a kasa.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Yarima yace "Tashi, Tashi gimbiya matar sarki"


Kasa d'ago kanta tayi yace Murmushi yayi yace "kunya ta kike ji?"

Kai ta d'aga Masa alamun eh, murmushi ya sake yi sai yace "Husnah haka ake tarban bako? Babu gun Zama bare ruwan Sha?"


Da sauri ta mike Tace "tuba nake yallab'ai" Kai kawaii ya d'aga mata alamun ba damuwa,taburma ta d'auko ta shumfud'a Masa sannan ta Koma ta d'ebo ruwa Tace "Bismillah rankashi dad'e ka zauna"

 

Zama yayi sannan da bawan sa na tsaye a kansa,Yarima ya umurce ta da ta zauna a kusa dashi da fari taki ganin kamar baiji dad'in hakan ba yasa ta zauna, bayan ta zauna ya ce "Husnah nasan Kinyi mamakin ganina ko?"

"Eh rankashi dad'e" Kai a kasa.


"Husnah Kar kiyi mamakin ganina, ina matukar kaunar ki,Allah ne yayi halitta, halitarki daban ce cikin jinsin yan mata. Kina da faren idanu tas mai dauke da yalwatar bakin gashin gira, a kan su.Gaki da dogon hanci kamar ke kika wa kanki, dai dai tuwar labban bakin ki akan dogowar fuskar ki shi ya fito da cikar kyawun ki, ta yadda ko bakiyi kwalliya ba kyawun dirin ki hada da kyawun fuskarki shi yasa na fad'a tarkon son ki"


"Umm umm Yarima nagode sosai amma ina so kasani in da Wanda nake so Kuma yake Sona, kayi hakuri ka bi zab'in mahaifin ka dana al'adar mu"


"Husnah in dai Zaki karb'i Soyayya ta Sam bani da wata damuwa in Kuma matsayina ne bai Miki ba wallahi Zan iya ajiye shi don na rayu dake"


"A'a Yarima bado. Matsayin ja bane kawai ina son Sharif ba Kai ba, bazan cin amanar sa ba"


Jin hakan yasa Yarima yaji duk ba dad'i Amma Bai nuna Mata ba yace "Ki dai zauna kiyi tunani a Kai shi gaggawa aikin shaidan ne" 

Tashi yayi ya ce "Na barki Lafiya" ya d'aga wa bawansa hannu sai suka yi tafiyar su, fitar su ke da wuya, naga wani saurayi wankan tarwad'a dogo ne sosai Mai faffad'an kirji, kyakkyawa ne Amma ko kad'an bai kamo kafan Yarima ba, Rai a b'ace ya shigo tana ganin sa tayi Murmushi tace "Masoyina Ashe Kai ne?"


"Eh ni ne ba kiyi tunanin ganina a Wannan lokacin bako?"


Kare Masa kallo tayi da kyau sannan tace "Sharif kana Lafiya kuwa? Ya na ganka haka?"


"Tambayata ma kike? kinzo kin tsaya da wani kato" Yana magana Yana huci, dafe Kai Husnah tayi tace "Haba Sharif Kai Kan ka kasan kai nake so ba wani ba"


"Shigowar Yarima cikin Rayuwar ki babbar barazana ce ga Rayuwar mu, nagode wa Allah da yasa qawar ki Habiba ta Sanar dani, da ban San yazo ba"


Kallon sa take cike da mamaki tace "Habiba? Habiba ce ta fad'a maka,lallai habiba, wasu lokutan lamarinta na bani mamaki akan me zata fad'a maka?"


"Kar ta fad'a min ko? Sabida ba ki da gaskiya"

"Kaga ya ishe ka haka Kar kaga don ina rarrashinka ka tsaya kana gaya min magana, har kana min tsawa"


"Haba Husnah ke kanki kinsan bazan juri ganin wani ya rabe ki ba, Kuma kin San ina son ki"

"Kuma Kai ma kasan ina son ka, Kuma na fad'a wa Yarima ina da Wanda nake so"


Nan da Nan wani farin ciki ya bayyana a fuskar sa yace "Dan Allah dagaske kike?"

"Eh Mana muna irin wasar Nan da Kai ne?Dad'ina da Kai rashiin hakuri da rashin fahimta Sam baka fahimta ta Ni Wallahi na Fara gajiya da halinka, haba ace mutun sai uban zuciya sai kace ba musulmi ba, kaga Malam in baka da abin yi Ni ina dashi" ta shige d'aki, shi kuma yayi tafiyar sa.


Lokaci zuwa lokaci Yarima na kawo Husnah ziyara, kamar Wasa ta tsinci kanta da son kasancewa dashi a matsayin Mata, Habiba Kuma tun ranar da suka baro deba Bata sake waiwayar qawartata ba, Khadija ce take yawan kawo Mata ziyara.


Kamar kullum Husnah ce zaune a tsakar gida tana gyara Wake, taji sallamar Habiba, can ciki ta amsa ba don ta so ba sai dai don muhimmancin amsa Sallama a musulunce, bayan Sun gaisa habiba tace "Qawata Dan Allah kiyi hakuri nasan ban kyauta ba, kawai dai na damu dake NE shiyasa nace Khadija Kar ta fad'a wa Yarima, sannan na fad'awa Sharif cewar Yarima yazo gidan ku"


"Habiba Kenan Wallahi kin bani mamaki sai kace muna gaba dake, akan me Zaki Rika cin dunduniya ta?"


"Haba Husnah cin dunduniyar ki kuma? Ki yarda dani harga Allah Kaunar ki sosai, Kuma Ni Mai Miki fatan Alhairi ne, Ni dai Dan Allah kiyi hakuri" magiya take Mata sosai har ta durkusa kasa gwiwowinta a kasa, Husnah tace "Tashi Dan Allah me hakan na hakura Kar ki damu"


Da sauri habiba ta rungumi Husnah tace "Nagode Qawata, bari na taya ki" Nan sukayi ta hirar su kamar babu abinda ya faru.sun dad'e suna hira har sai yamma ta tafi gida.


Bayan tafiyar Habiba, Khadija tazo gidan su Husnah zaune suke suna hira, labari suke sosai sai Husnah tace "Kinga na manta ban fad'a Miki ba, d'azu Habiba tazo Nan"


"Habiba tazo?"

"Eh" 

"Me tazo yi?"

"Cewa tayi ta zo ta bani hakuri Kuma na hakura"

"Ya zakiyi Wannan gangancin? Habiba fa Bata son ki da Alhairi"

"Khadijaaaa habaaa Kar kice haka Mana"

"Gaskiya nake fad'a Miki, Amma duk da hakan kiyi taka tsantsan da ita"

"Toh Shikenan insha Allah Zan bi a Hankali"

"Ya dai fi Miki"

Nan suka cigaba da hirar su.


Bayan Sati biyu


Yarima ya dawo gidan su Husnah har yanzu dai bai janye kudirin sa akan ta ba, yace "Husnah Dan Allah, Dan Allah na roke ki, ki karb'i Soyayya ta gudun Kar na rasa raina, don wlh dab nake da na rasa Raina"


Murmushi tayi Tace "Yarima,kaine wanda zuciya ta ta aminta da shi. Ina son ka kara sani cewa babu wani d'a namiji wanda zuciyata ta gama aminta da dukkan soyayyar sa face kai"


Yarima suman tsaye yayi ya kasa cewa komai, baki a bud'e yake kallon ta, a zuciyar sa Kuma cewa yake "Anya Husnah ce kuwa ko dai mafarki nake ne?"


Murmushi tayi Tace "Ba mafarki kake ba"

 Zaro idon sa yayi yace "Ya akayi Kika ji abinda nace?"

"Zuciyata da taka sun Zama d'aya don haka ka daina mamaki"


"Nagode nagode Husnah ki Sanar dani dukkan nin abin da kike so yanzun Nan nasa a kawo Miki"


"Soyayyar ka kad'ai nake bukata a yanzu,Kai tamkar gishiri ne a cikin rayuwa ta, idan na rasa ka zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta"


"Yau zanyi bacci harda armashi,Ni Zan wuce Ina fatan zaki ci gaba da kula min da kan ki har zuwa lokacin da zan sake dawo wa?"


"Insha Allah ya tsare min kai"

"Ameen Marra'atussaleh"

Rufe fuskanta tayi da hannayen ta, Wanda hakan yasa yaji kaunar ta na ninkuwa a cikin zuciyar sa, maida kallon sa yayi ga bawansa yace "Bello kaga ikon Allah ko? Husnah ta karb'i Soyayya ta"


"Na gani yallab'ai Kun dace da juna Tabbas itace ta chanchani zama matar ka"

"Nagode Bello shiyasa na fi son tarayya da Kai fiye da kowa kana son abinda nake so"


"Yallab'ai ai chanchantar ka ce ta sa" 

"Toh Nagode Bello"


Nan suka Mata Sallama suka bar gidan, cikin d'an Kan kannin lokaci duk gari ya d'auka Husnah na Soyayya da Yarima, zab'in da a kayi wa Yarima Emmatan shida sun d'auki Karan tsana Suka d'aurawa Husnah a fad'in su ta asirce shi, sannan sun d'auki alwashin ganin bayan ta.



Tafiya ta ke hannun ta rike yake da tulu a yayin da ta rike wata doguwar sanda da D'ayan hannun ta tana Wasa dashi,ji tayi ana Kirin sunan ta, tana juyowa taga Shariff ne ji tayi kamar ta nitse kasa a yayin da take Jin tsanar sa na karuwa a cikin zuciyar ta, ya karaso inda take

 

Yace "Husnah yanzu dan Allah kin min adalci Kenan? Kin zab'i Yarima akaina, sabida Kinga Yana da mulki?"

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Ku kasance tare dani

 *MILHAAT CE* YAR TERAWA🥰

Comments and share please🙏🏻