CHAPTER 4
by @milhaart
```PREVIOUSLY```
Isah duk da hakan shine plan d'insa Amma baiso ta dawo da wuri ba don surarta ya rikitar da shi ya ji Yana mugun Jin sha'awarta Amma dole ya hakura.
Nan da Nan mutane suka cika gidan, Ana Allah ya wadaran da irin halinta.
Jiki ba Karfi Husnah ta Tashi ta tafi gida tana kuka, ga sharrin da aka Mata sannan ga duka.
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Tana Isa gida tarar da Mahaifin ta a zaune da jiki a sanyaye murya chan ciki tayi Sallama, ya amsa "har kin dawo?"
Ba Tace Masa komai ba, sai ya lura da jinin dake zuba a goshin ta da sauri ya tashi ya nufi inda yake, ga mamakin sa dukkan nin jikin ta ciwo ne, cikin b'acin raii da Rashin fahimta yace "Husnah me ya same ki? Waya Miki Haka?"
Kuka ta Shiga yi Mai cin Rai, Abba ba karamin rikicewa yayi ba don tunda yake Bai tab'a ganin Husnah na kuka Haka na ya ce "Husnah ki Sanar Dani me ya faru?"
Cikin muryar kuka Tace "Abba Meyasa? Meyasa sai Ni Abubuwa maarasa kyau ke faruwa Dani ne? Ko nayi wa Allah laifi ne?"
"Haba Husnah ki fad'a min me ya faru Kai tsaye ki daina jaan maganar"
Cikin kuka ta Fara msanar dashi abinda ya faru, Abba Nan da Nan zufa yake keto Masa jikin sa na kyarma, Bai ce mata komai ba ya fita Kai tsaye gidan Isah yaje a dai dai lokacin Isha ya fito daga wanka don jikin da duk a mace ganin Husnah da yayi, Abba riko Isah yayi da karfin gaske ya Fara Kai Masa duka tun Yana tsaye har ya Kai kasa Yana Kai masa naushi Yana ihu Abba ya toshe Masa baki duka yake Kai Masa sosai har sai da yaji ya gaji.
Matar Isah sallah take tana Jin ihun mijin ta Amma ba Hali ta taimaka Masa, sai dai Abba ya Masa tilis Kan yace "ka d'an ka gani Wallahi sai kashe ka idan baka fita days harkan 'yata ba."
Yayi tafiyar sa, ya bar Isah a kwance ko mutsi baya yi, da gudu matar Sa ta fito ta nufi inda Mijinta yake ganin yanda ya Masa jina jina ta Fara kuka magana take Masa Amma ya kasa Bata amsa da alama Suma yayi.
kanin Mijin ta Mai Suna Ahmad Ne ya shigo cikin sauri yace "Me ya same shi?"
A razane tace "Nima ban sani ba sallah nake najiyo ihun sa"
Yace ki d'auko taburma, ta Tashi ta d'auko, 'daga shi yayi ya kwantar ta dashi, da sauri ta tsinko wasu ganye ta daka ta Shiga sa Masa a Kan ciwon sa, sannan ta tafasa ruwa tana kama Masa jikin.
Abba na isa gida ya samu har yanzu Husnah na kuka, yace "Husnah ya Isa haka naje nayi maganin munafuki"
Cikin muryar kuka Tace "Abba ya fad'a wa mutanen gaskiya?"
"Husnah Ni hukunta shi kawaii nayi, ban Ce Masa komai ba"
"Abba naso ace ya Fadi gaskiya, Ni gani nake kamar ana bina da sharri so ake a rabani da yarima."
"Kar ki damu Husy Yarima yasan ki ya Kuma San halinki yasan baza kiyi haka ba"
"Allah yasa hakan ne"
"Ameen yanzu Tashi kije kiyi wanka kiyi sallah nasan ba kiyi sallar maghrib ba"
"Toh Abba"
Tashi tayi ta Shiga ban d'aki.
Kwanaki har biyu Isah bai sai inda yake ba.
Yarima na zaune a d'aki Bello ya shigo cikin girmamawa ya gaida shi yace "Yarima wani mumunan labari"
Gyara Zama Yarima yayi yace "me Kuma ta faru?"
"Yarima yanzun Nan wani ya fad'a min wai an Kama Husnah ta Shiga d'akin wani da niyar bashi kanta"
Cikin tsawa Yarima yace "Kai Bello baka da hankali ne? Ni kake fad'awa haka Husnah tawa kake b'atawa a gaban idona?"
Yace "Tuba nake Yarima Amma maganar Nan ba karya bace don na yarda da Wanda ya fad'a min"
Hawayene masu zafi suka Fara gangaro wa daga fuskar Yarima Yana fad'in "Meyasa, Meyasa Husnah Meyasa Kika min haka? Kin cutar Dani kin cuci kanki da wanne zanji Innalil lahi wa inna ilaihirraji'un"
Bello yace "Yarima kayi hakuri hakan ba dai dai bane kana d'an sarki kana kuka Akan mace"
Yarima yace "Ya ishe haka" a tsawace
"Ka fita kabani wuri ko in tsaba maka kamanni yanzun Nan"
Ba Shiri Bello ya fice daga d'akin.
Isah ne zaune a cikin gidan jikin sa ba Riga zanin matar sa ya d'aura don Shan iska, Sharif ne ya shigo da Sallama ganin Isah da zani yace "Kai Kuma wannan wani sabon salo ne ka daina sa wando ne ban sani ba?"
Wani irin kallo Isah yayi wa Sharif kallo cike da b'acin raai da Jin haushin sa, Sharif yace "Ya Ina magana ka yi shiru kana rarraba Ido kamar sabon munafuki"
Cikin b'acin raii Isha yace "Munafuki ma zaka ce min? Ba laifin ka bane ba, ka fita ka bani wuri"
"Yi hakuri Abokina me Ke faruwa ne?"
Yace "Au Sharif so kake kace min baka ji abinda ya faru ba?"
"A'a ban sani ba, shigowa ta garin kenan mafarauci ai bai ga ta zama ba, yau kwanaki biyu Kenan bana Nan"
"Toh Shirin da mukayi wa Husnah fa an wuce gun"
Cikin murna Sharif yace "Kai Haba Dan Allah?"
"Eh mana zan maka karya ne?"
"A'a bance ba, fad'a min ya akayi hakan ta faru"
Nan ya Shiga Sanar Masa yanda abin ya faru, Sharif yace "Amma ka kwafsa fa taya za'ayi kato da Kai baza ka iya yi wa yarinyar Nan fyad'e ba, Kuma ka bari wannan tsohon ya maka jina jina har ya sumar da Kai?"
"Kaji ka da zancen banza sai kace baka San shine sarkin yakin ya kin Nan ba? Har yanzu ba ayi kamarsa ba"
"Eh hakane Kam"
Isah yace "malam kawaii kaja min duka"
"Yi hakuri Abokina, Amma baka fad'a Masa gaskiya bako?"
"Inaaaa ai barni nace komai ba,Ina Mai tabbar maka Yarima ya samu labari Kuma ya yarda Wallahi"
"Alhamdulillah Nagode sosai Abokina,Amma Kai Dan Allah bakayi mamakin yarinyar Nan ba?"
Isah ya ce "Wace Yarinya?"
Shariff yace "Qawar Husnah Mana ka duba kaga yanda suke da ita Amma ta ke kokarin rabata da farin cikin ta"
Murmushin gefen baki Isah yayi yace " 'dan Adam Kenan hausawa sunce makashin ka na tare da Kai kaga don tayi hakan ba abun mamaki bane ba"
"Hakane Allah ya kyauta"
"Ameen"
"To ya jikin naka ne, da fatan kaji sauki"
"Sauki sosai ma sai yau da na Fara Zama"
Dariya Ne ta kub'ucewa Sharif Yana kokarin rufe bakin sa da hannu Kar Isah ya gane Amma Bai San sanda yayi dariya Mai Karfi ba, Isah yace "Kayi dariya da kyau gobe ma Rana Ne zaka nemi taimako na ai"
"Zan nema kuwa, Kuma Dole kamin"
"Au haka ma kace ko?"
Shariff yace "dad'ina da Kai Sam ba ka San Wasa ba, Kayi hakuri, Nagode sosai Allah ya bar zumunci"
Chan ciki Isah ya amsa da "ameen"
Khairat na jin maganar da Bello ke fad'a was Yarima, sai taji tausayin yayan ta, duk da ba son Husnah take ba, Amma tana ji a jikin ta Husnah baza tayi hakan ba, sai ta kudiri aniyar dai daita komai.
Husnah na gani zaune da Khadija kana ganin Husnah zaka gane tana cikin tashin hankali Khadija naji Tace "Husnah kukan Nan ya Isa haka tunda na shigo gidan nan na tarar kina kuka har yanzu ba ki Daina ba, Dan Allah ki yayyafa wa zuciyar ki ruwan sanyi hakan Zan iya cutar da lafiyar ki"
Husnah tace "Khadija idan banyi kuka ba me zanyi? Yau kwanaki bakwai Kenan Yarima bai Zo inda nake ba, baya kwana d'aya bai Zo gidan mu ba, Amma Ina ganin sharrin da aka min yayi tasiri a zuciyar sa"
"Kar ki damu na tabbata zai gane cewar sharri aka Miki"
Yarima na zaune a d'aki don tun sanda yaji labarin Nan baya fita ko Ina kullum sai zaman d'aki idan ya fita to mahallici za shi.
Khairat ta shigo da Sallama, dakyar ya samu ya amsa don a yanzu duk haushin su yake ji a fad'in sa da sun amince da zab'in sa hakan da Bai faru ba, da ta na d'akin sa.
Khairat Tace "Yaya Meyasa naga kwanakin Nan duk baka cikin walwala?"
Wani irin Kallo ya Mata sannan yace "Kice kinzo Jin gulma dai, don na tabbata Kun San komai,Kun San dalilin Shiga tashin hankali na"
Murmushi tayi ta Sosa keya Tace "Nasan komai don nice na fad'a wa Umma a lokacin da Bello yake fad'a maka ina Jin sa"
"Oh wato kin Zama Yar leke ko? Yaushe Kika Zama Yar leke ban sani ba?"
"Kayi hakuri Yaya wucewa nazo yi sai naji maganar da kuke"
"To naji Khairat me Kuma kike so kiji abinda Kika ji bai wadatar dake ba Kenan?"
"Yaya Dan Allah Kar Kayi fushi so nake na tambaye ka shin kana sonta da gaske kuwa?"
"Ina son ta Mana Khairat ke Kan ki kin San da hakan,tunda komai a gaban idonki a keyi"
"Yaya baka son ta kamar yanda kake fad'a"
"Kamarya bana sonta, Kar ki nema kin b'ata min Rai Mana"
"Yaya da ace kana son ta na tabbata zaka Mata uzuri, tunda kaji labarin Nan kaje gun ta?"
"A'a banje ba" jiki a sanyaye
"Toh ka gani ko ya kamata kaje ka ganta kaji abinda zata ce maka Kar kaza ma irin mutanen Nan Masu saurin yanke hukunci"
Shiru yayi Yana kallon ta na d'an wasu lokuta sannan yace "Khairat me ya sa kike goyon bayana yanzu bayan Nasan kema ba sonta kike ba"
Iska Mai zafi ta fitar sannan Tace "Haka ne bana sonta Amma a baya na lura kana Kaunar ta, Ni Kuma ina Kaunar ka kaga Dole naso abinda kake so idan na tabbatar da hakan ba zai cutar da Kai ba,na lura Husnah Yarinya Ce Mai nutsuwa da addini baza tayi hakan ba"
Riko hannun ta yayi yace "Nagode Nagode sosai"
"Kawaii ka Tashi ka tafi Kuri yanzun Nan Yarima Allah ne kad'ai yasan irin tashin hankalin da Husnah take ciki"
Murmushi yayi ya tashi yace "sai na dawo" ya fita a hanyar sa ta fita sukayi kicibis da Mahaifinsa, sarki yace "Yarima yanzu Kai irin Rayuwar da ka d'auka wa kanka Kenan?"
"Abba Dan Allah ka rabu dani naji da abinda yake damu na"
"Bazan rabu da Kai ba Khaleed Kai ne fa d'ana tilo, bazan Bari naga kana lalata Rayuwar ka ba"
"Abba indai a Kan Husnah ce rashin ta shine babban tashin hankali na"
A tsawace Abba yace "Khaleed Kar kaga in rarrashin ka Wallahi ka bi Ni a hankali ko in San a d'aure min Kai"
Murmushin takaici Yarima yayi yace "Wallahi Abba sai dai kasa a kashe Ni ko kuma kasa a cire zuciya ta idan aka cire na tabbata Zan Daina sonta"
"Husnah!! Husnah Yarinyar da Sam Bata da tarbiya, Yarinyar da bin mazan mutane take tana basu kan...."
Cikin tsawa Yarima ya katse Abba yace "Ya ishe ka haka Abba ka fad'i duk abun da ya maka Amma Kar ka zagi Husnah ta don wallahi sharri aka Mata"
"Kana nufin baka yarda ba Kenan?"
"Ban yarda ba Sabida ba gaskiya bane,yanzu Haka ma Kuri zani"
Yayi tafiyar sa Abba na kiransa Amma ko juyo wa baiyi ba bare ya saurari abinda zai ce, da sauri Bello ya bi bayan sa.
Suna Isah yaji maganar da Khadija da Husnah suke yi suk sai yaji ba d'adi, Bello yace "Yarima mu karasa ciki Mana"
Hannu kawaii ya d'aga Masa alamun yayi shiru.
Husnah Tace "Khadija Ke Kika sanda hakan Amma Yarima bai sani ba"
Khadija Tace "Wai ma ya akayi kika je gidan ne? Me ya Kai ki"
Husnah tace "Wallahi qawara tsautsayi na kasa fahimtar komai, yaro aka ai ko Wai matar Isah na nema na, ban b'ata lokaci ba naje, sai na tarar da isah ne a gidan daganan fa shine ya....."
Sai ta fashe da kuka, Khadija ta Shiga rarrashin ta, Tace "kiyi hakuri, Ina fatan dai bai ci nasara akan ki ba?"
"Eh matar sa ta shigo, shine inda Allah ya taimake Ni"
"Toh Alhamdulillah da sauki da abin yafi haka muni"
"Khadija da shikenan bazan Sami mijin aure ba ko?"
Kan Khadija ta amsa sai suka tsinkayo muryar Yarima yace "Husnah ki da hakan ya faru Wallahi Zan aure ki a Haka"
Duk su biyun suka Mike tsaye tsuman tsaye sukayi, don su Sam Basu San akwai Wanda yake Jin su ba, Husnah ta ce
"Ya... Yaaaa.....Yarima Kai Kai Kai ne?"
Murmushi yayi yace "Eh nine kina mamakin ganina ko?"
Kai ta d'aga Masa alamun Eh, yace "to ki Daina mamaki"
Matsawa tayi kusa dashi kanta a kasa Tace "Yarima kayi hakuri Dan Allah Wallahi ba lai...."
"Shshh ba sai kin rantse ba nine Zan Baki hakuri Sabida na kasa danne da zuciyata"
Khadija Tace "Sannu da zuwa Ranka ya dad'e" cikin girmamawa
Murmushi yayi "Kece Khadija ko?"
"Eh nice yallab'ai"
Yace "Nagode sosai Khadija, kina kulamin da sarauniya ta"
Murmushi ta maida Masa sannan tace "Kar ka damu Yarima Ni da Husnah mun wuce karfin ance Mana Kawaye ta Zama kamar Yar Uwata ta jini"
"Toh Allah ya saka ya Kuma bar ku tare"
"Ameen" sai ta maida kallon ta ga Husnah Tace Ni Zan tafi"
Husnah Tace "Haba ki d'an zauna Mana muyi Hira"
"A'a Husnah Zan baku fili ne kuyi Hira da farin cikin ki, Zan dawo gobe"
"Toh shikenan ba don na so ba ki gaida su Mama"
"Zasu ji na bar ku lafiya"
Tayi tafiyar ta.
Wuri suka samu suka zauna suka Fara Hira don sunyi kewar juna sosai, Mahaifin Husnah ya shigo tun daga kofar gidan ya hango su ya ji wani fairin ciki ya rufe shi, har kasa yarima ya gaida shi yace "Haba Yarima ai Ni ya Dace na gaida kai"
Yarima yace "A'a Abba ai tunda ka haifi Husnah Nima ka haife ni na d'auke ka tamkar wanda ya haife Ni"
Murmushi Abba yayi yace "Masha Allahu, Allah ya maka Albarka ya bar ku tare"
Duk suka amsa da Amin.
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Milhaat Ce
Yar Terawa
Please comment and Share ๐๐ป