Shafi Na ‘Daya
⚡️*GAMON JINI*⚡️
*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO*
*E.W.F*
*PAID BOOK*
*FREE PAGE ONE*
Wata Arniyar bakar BMW 840 IX ce ke tsula uban gudu a hanyar dake tsakanin sokoto, zamfara da dukkan alamu mamallakin motar sauri yake ya cimma duk inda ya nufa, sanye yake da wata bakar riga wacce ta fito da duk wata kirarsa ta cikakken namiji me kwanji tare da wando ta khakin sojoji kafafunshi irin takalmansu ne, hannunsa na hagu dake d'aure da wata Rolex watch d'insa ya d'ago ya duba lokaci dukda karfe 11 na dare ya wuce sede hakan be sa ya ji kaman ya nemi masauki In ya shiga Gusau ya kwana ba, ya riga ya kudurta ba inda ze kwana yau se birnin kano, a jikinsa yake ji mahaifiyarsa ba lafiya kaman yadda shakuwarsu ta zarce misali though akwai wannan alkunyar ta en fari sede duk wani abinda ze faru dashi kaman gaya mata ake a jikinta take jinshi fiye da kowa da komai dukda ba shi kad'ai Allah ya bata ba, haka ta 'bangarensa idan yaji uneasiness da yake ji yanzu ya rasa natsuwa kwata kwata to tabbas ya san mahaifiyarsa ce bata da lafiya.
Had'add'iyar wayarsa kirar Samsung Ultra dake ajiye ya sa zara zaran fingers d'insa ya d'auko yana murza motar da hannun hagu ba tare da ya rage gudun da yake zabgawa ba ya fara latsa wayar har ya iso number d'in da yake nema ya d'anna kirar tare da maida wayar ya ajiye da yatsa d'aya ya latsa Bluetooth d'in dake jikin motar tare da maida duk hannunshi kan stirring ya kuma murza motar yana me kara mata speed, fuskarsa Bata ta'ba nuna expression d'insa a rayuwa kullum yana nan ba'a had'e ba ba kuma a sake ba he has a blank expression face tun tashinsa, ringing na karshe wadda ya kira d'in ya d'aga daga d'aya 'bangaren ya furta
"Am sorry Yayanmu"
Be kula hakurin ba yace
"Abdulkadir ya jikin Amah?"
Da tsantsar mamaki Abdulkadir yace
"Yayanmu wa ya fad'a maka bata da lafiya? After All gargad'in Abbu...."
Shiru yayi kaman yadda yayan nasu yayi shiru, jin be da niyyar magana kaman yadda yake idan har ya d'auki waya ya kiraka to abinda yake so yaji kawai daga gareka ze ji ba wai ya saurari tambayoyinka ko ra'ayinka ba.
"Da sauki yayanmu ya ma sauka karin ruwa ake mata"
Ajiyar zuciya ya sauke se da ya ja iska yace
"Usual hospital?"
"Eh, ba de kana hanya ba? You don't have to come da safe fah Khalid yace za'a sallameta..."
Kit ya katse wayar yana taune lip, yaushe mutanen gidan nan zasu bar mishi mahaifiya ta huta ne? Idan fa Har ta sarara aka rasa me d'aga mata hannu to fah yana cikin birnin kano ne shi d'inma ba wai don yana magana ba kawai shakkarsa da sukeyi ne yasa amma yana bada baya abubuwa daban daban dukda ba wani ke gaya masa ba sbd shi ba mutum bane me jin maganganun mutane, ba mutum bane me kallon mutanen ma gabad'aya idan kuwa ya kalleka ka kai kololuwa wurin kular dashi ne musamman mata, a ko yaushe kanshi na a kasa bakinshi na d'an motsawa, shi ba malami bane sede shi d'in mahaddacin qur'ani ne wadda da wuya kaga mahaddacin qur'ani na zaune baya tilawarta ko da a zuciya ne kalilan ke fitowa kan lips d'insu kad'an kad'an, tsaki yaja yana tuna yadda Amah Bata so suyi magana akan abubuwan da ake mata bama ta so ya sani alhalin bakin cikin ke tada Chronic asthma d'inta da 'bacin rai ke motsa shi ko ya yake.
A hankali sassayar ringing tone d'inshi marar hayaniya ya karad'e motar kasancewar shi baya son hayaniya hakan yasa komai nashi marar hayaniya ne, kallon wayan yayi se yaga Abbu, Bluetooth d'in motar ya danna tare da gyara murya yace
"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Amsawa Abbu yayi tare da d'aurawa da
"Abrar Kana Ina da tsakar daren nan?"
Kai tsaye yace
"Hanyar kano yanzu na kusa Gusau"
"Abrar lafiyanka kuwa? A yadda hanyoyinmu suke yanzun nan zaka kama hanya da wannan daren? Ko ita mahaifiyar taka aka ce maka zata so ka taho a yanzu me yasa bazaka hakura da safe ba?"
Cikin tsadaddiyar muryansa da jinta ma aiki ne yace "Just pray for me Abbu In Shaa Allahu lafiya zan iso"
Ajiyar zuciyar da har yaji daga 'bangarenshi Abbu ya sauke kan yace
"Allah ya kawo min kai lafiya" Da "Ameen" ya amsa kan Abbu ya katse wayan.
Yanayin garin ya kalla da alamu ruwa ke gab da sauka sbd iska da kuma chida da ake sakewa lokaci zuwa lokaci, ya bar kauyen Maru Abadan yana dab da shiga Bungudu kaman daga sama ya ga Ana shirin shan gaban motanshi cikin zafin nama ya taka wani wawan birki yana d'ago kanshi don ganin wani me kasadar ne wannan.
Kukanta ne ya fara shiga kunnenshi a hankali, kan ya sauke ido kan figure d'inta sanye take da doguwar riga baka me dogon hannu, gashinta a warwatse hakanan kafafunta ba takalmi kuka take yi da karfi tana had'a mishi hannu Alamun roko, kan ya gama nazartarta yaji harbin bindiga.......
Rud'ewa ta sake yi tana shirin sake 'ballewa da gudu ya fito cikin zafin nama hannunsa d'auke da karamar pistol, for the first time in his life ya ta'ba jikin mace bayan Amah d'inshi, hannunta ya rike cike da tausayin ta da ya tsarga mishi sanin ita d'in tana cikin wani hali na bukatar taimako.
"Babu wanda zan bari ya zalunci marar gata ko na kasa dashi, idan muna cikin khaki hakan yana nufin a shirye muke don kare kasarmu da alummar mu, safety d'in duk wadda ke zagaye damu relay on our hands....
Sbd bandits ba za mu ga Civilians cikin bukatar taimako mu ja da Baya ba....
Dole talakawa su san mu d'in garkuwa ne a garesu, bandits su san mu d'in dodon ninsu ne kuma tashin hankalinsu ne....
Ba kisa da harbi kawai bane burinmu samar da zaman lafiya da lumana shine burin mu...."
Waennan kalmomi sun zama Kaman farilla ga rundunar shi ko wanni safiya su kad'ai yake nana ta musu, hakan ya sa idan ya kama wani da zalunci ko cin hanci baya ta'ba raga mishi.
Da wannan kwakwalwa yayi anfani ba tare da tunanin ko ita d'in muguwa bace, ko bakinsu d'aya da mugayen ko makiya bane, cikin tsananin zafin nama da Allah ya mishi ya ja hannunta ya 'balle gefen me zaman banza ya sanya ta kan ya rufe, inda yake jin hatsaniya da karar bindiga ya seta kan ya fara zagayawa don komawa mazauninshi.
Dukda duhun dajin Yana iya Ganin inuwansu, wadda yake tunanin na shirin sakar mishi harsashi ya sakarwa ya kuwa ji ihun shi alamun ta same shi da hanzari ya bud'e kofar motar ya shiga daidai lokacin suka sake mishi har'bi bata sameshi ba sede ta gogi dantsen hannunshi ta d'an ji mishi ciwo be damu ba ya karasa rufewa kan ya ja motar da mugun gudu......
Duk yadda suke harbin motar baya samunta sbd bullet proof ce har suka 'bacewa ganinsu....
Tsaki ya ja yana kallon inda suka goge shi da bullet, jini ke zuba Sossai sede be da alamun tsayuwa sbd sanin nan d'in kaman kasarsu ne zasu iya bullo musu ta ko ina cikin bazata, glancing inda take yayi ba tare da ya wani kalleta ba ya d'auke Kai....
Ta chusa fuskan ta tsakan kanin kafafunta jikinta har lokacin yana tsananin rawa gabad'aya a rikice take, Suna shiga cikin Gusau Ana 'ballewa da ruwan sama me karfi tare da tsawa da walkiya....
A bazata yaji ta sa hannu Ta rike riganshi tana kara sautin kukanta jikinta na fin Baya d'aukan rawa, kallonta ya sake yi idanunta a runtse da karfi ta had'e lips d'inta.... d'auke idanunshi yayi kan ya sa hannu ya kara sautin qira'ar da dama yake yi a hankali, muryar Sheik Maher Al-muaykil ya karad'e motar cikin suratul Anbiya'i......
Tafiyar nan yayi shi ne a matukar takure sbd yadda ake tsuga ruwa da tsawa tare da walkiya haka take sake shiga jikinshi tana kuma kankameshi zuwa yanzu kanta ma a dantsen hannunshi yake gabad'aya ta bar kusa da window...
Ya fahimci tana tsoron Ruwa kaman, ga shi Bata gama dawowa hayyacinta ba yana tsoron yi mata tsawa ta karasa birkicewa a haka ya hakura Har suka shiga cikin birnin kanon dabo, wuraren 2:30 na dare yana ta wuraren jan guza wayanshi ya hau ringing, a kano ba'a Ruwan se iska me sanyi ke kad'awa....
Sanya hannu Yayi ya amsa ganin Khalid ne ke kiranshi kaninshi na uku a wurin uba na biyu a wurin Amah, muryar kamillalliyar mace cikin natsuwa ne ta yi sallama, Lumshe ido yayi duk fad'in duniya ba muryar da ta kai ta mahaifiyarshi daad'i da sanya natsuwa a gareshi, a tausashe shima yace
"Wa'alaikumussalam warahmatullah Amah how are you feeling now? Ya jikin?"
Mace guda d'aya tal da yake iya doguwar magana da ita, cikin yanayin rashin lafiya ta ce
"Lamido me ya sa ka kamo wannan hanyar cikin wannan dare uhm? Da na sani da na kiraka tunda na fara jin alamun ciwon na gargadeka, yanzu in wani abu ya sameka fah?"
Shiru yayi yana sauraren ta seda ta gama kan yace
"Ba abinda ya same ni Amah na iso kano yanzu haka Ina wuraren Jan guza.."
Ajiyar zuciya ta sauke kan tace
"Lamido ka tabbatar ba abinda ya sameka??"
Kallon hannunshi da yaji ciwo yayi, a Malumfashi ya tsaya ya yage kasar rigan jikinshi ya d'aure hannun, Murmushi me sauti yayi ta bangarenta tace
"Hmm" kan ta d'aura da
"Ina jiranka"
Daga haka ta kashe wayan, kallon ta ya d'anyi sbd safety d'inta dake hannunshi, ko second uku be yi ba ya d'auke kanshi, ta koma jikin kujera ta sake kife kanta kaman ma bacci ya saceta.
Ajiyar zuciya ya sauke kan ya maida hankali yana ci gaba da gudunshi daré ya riga ya tsala titi ba kowa cikin lokaci kankani ya isa International hospital, bayan yayi parking a parking space se ya rasa yadda ze yi ya tashe ta, after like 5 attempts ya iya buga gaban motar ta inda take ya furta
"Baiwar Allah!" "Baiwar Allah!!"
A razane ta farka tana zazzare idanunta kallonshi ta d'anyi Kaman ta tuna wani abun se kuma ta kalli inda suke haske tar cikin asibitin ko ta ina d'aid'aikun mutane ne ke kai kawo, rike gefen rigarsa tayi a tsorace tana kalle kalle.
Seda ya kalli hannunta kan ya d'aga ido ya kalleta yarinyar ta sashi kallonta Sossai yau abinda ba sabonshi ba tsaki ya d'an ja kan yace
"Baiwar Allah ki natsu ba abinda ze sameki nan d'in hospital ne za'a duba lafiyarki"
Sake shi tayi ba tare da ta kalleshi ba ya fita ya zagaya ya bud'e mata door ta sauko suka nufi Amenity inda ya san nan Amah take...
In ka ganta zaka rantse aljana ce ta dukar da kanta gashinta gabad'aya ya rufe fuskanta ga bakin kaya a jikin ta kafafunta ba takalmi tana tafiya ne kaman iska ze kwasheta, Abun mamaki wani na zuwa ze wuce ganganta ta yi saurin matsawa kusa da shi ta rike riganshi da yake shima irin tafiyantan yake sbd Kar yayi sauri ta 'bace mishi gashi kaman ta zauce.....
Suna shiga cikin ward d'in se ga khalid ya fito daga wani room da ba tantama nan Amah take, wara idanu yayi yana kallon yayan nasu a tsorace yace
"Yayanmu kana ganin Abinda nake gani? Auzu bikalimatillahi tamat min sharri ma khalaka"
Kallon shi Abrar yayi kaman ze yi murmushi ya d'an kalli gefenshi yace
"Menene?"
Baya khalid ke komawa sbd nufo shi da sukayi yana cewa
"Wallahi Aljana ce da bakaken kaya ba'a ganin fuskanta......"
Yadda yake zazzare ido yana adu'o'i ya kusa saka Abrar dariya da yake shi ba ma'abocin dariyar bañe se yayi Murmushi, tare da cewa
"Mutum ce, zo mana"
Daga haka ya bud'e d'akin Amah suka shiga a tare da yarinyar da Har yanzu ko muryanta be ji ba banda muryan kukanta....
Zaune take kan sallaya dake fukantar kofan an shimfid'a sallayar kan wata tattausan center carpet in kaji kamshin d'akin zaka rantse da Allah ba hospital bane, turo kofar da yayi da sallama cikin natsatsiyar muryarsa me tsada yasa Amah d'agowa ta kalleshi tana amsawa da
"Ameen wa'alaikumussalam wa...."
Chak ta tsayar tare da mikewa ta nufe shi tana furta
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Lamido......."
🖤Gureenjoh🖤