2
by @mssxoxo
*ASALIN MU*
(TAK’AITACCEN TARIHIN MU)
*GWANI IDRIS NAJIBULLAH*
Marigayi Gwani Idris Najibullah shine sunan mahaifin baban mu, Tare da matar sa Malama Halimatu Alkali. Ya kasance Malami a garin na kaduna, matar sa wato mahaifiyar su baban mu ita kadai ce mai dakin sa, ALLAH ya albarkace su da ya’ya shida: Kawu Ishaq, Kawu Dawood, Gwaggo Aminatu, Kawu Khamis, Sai mahaifin mu Salis, Sai Kawu ilyas wanda ake kira da baba ila shine karamin cikin su. Dukkanin yan dakin nasu a Zaria suke gidan mu d’aya, Banda Gwaggo Aminatu wadda ke aure a Kaduna. Gidan da muke ciki a Zaria gida ne na gado, wanda iyayen mu suka hada karfi da k’arfe suka siya. Dakuna tara ne acikin sa, kowanne guda d’aya d’aya ne ba ciki da parlor, Sai dakin baba ila dake ‘kasa shine mai ciki da parlor. Dukkanin yan uwan mahaifin mu a gidan suke da zama da matan su. Gidah ne mai hawa biyu, mune a saman karshe dake dakuna uku ne: Muna cikin d’aya, sauran biyun kuma Bintalo da y’ay’an ta na d’aya. Sai Usaiba mahaifiyar su Larai da Talatuwa, Usaiba matar Kawu Ishaq ta farko, sai amaryar sa Rabi’atu ita takansace juya ce bata haihuwa, sannan a dakin k’asa take, Dakuna uku na ‘kasan mu kuma, Kawu Dawood ne da matar sa Hafsatu sai yan biyun su Fareed da Fareedah. Sai Kawu Khamis da matar sa Innatuwa da Yayan su maza biyu ‘kanana wato Yusha’u da Bala. Sai dakin karshen saman nasu wanda Rabi’atu take ciki wato matar Kawu Ishaq ta biyu. Sai Kawu ila wanda ke dakunan ‘kasan karshe shi da matan sa Ummita da Hajara, dakin farko mai ciki da parlor Ummitan ce aciki wato matar sa tafarko Ita da tawagar yayanta su biyar dake yawan haihuwa take yi akub’i akubi. Sai d’aki dayan karshe na amaryar sa Hajara wadda ya aure ta bayan rasuwar mahaifin mu. Takasance tanada tsohon ciki wadda zata iya haife shi a kowanne lokaci saboda ya tsufa.
Marigayi Malam Salis Idris Najibullah shine mahaifin mu, Malama Kaltume Rabiu shine sunan mahaifiyar mu. Mahaifin mu kafin rasuwar sa ya kasance yanada mata biyu, Innar mu Kaltume sai Baba Zara’u wacce ake kira da Bintalo. Mahaifin mu dan asalin cikin garin Kaduna ne, almajiran ta takawo su shida yan uwan sa Zaria. Anan kuma ALLAH yayi zasuyi aure su hayayyafa. Mahaifin mu lokacin da suka fara sana’ar tashi zuwa garin katsina anan Allah yayo zai gamu da mahaifiyar mu a kauyen Shema. Mahaifiya ta irin fulanin nanne na jaub’awa, Mahaifin mu kuwa bahaushe ne gaba da baya. Domin kakan su ma kafin Allah yayi mai rasuwa ance a garin kano yake. Baba Bintalo y’ar uwar mahaifin mu ce, da kakanta da mahaifin baban mu uwa suka hada uba kuma kowanne da nasa. Auren nasu ma auren had’i ne ko nace auren zumunci ne, mahaifiyar mu kuwa itace matar sa ta ladan noma wato auren saurayi da budurwa. Mu bakwai ne awajen mahaifin mu, dakin mu mu uku ne, Yaya Najibulla wanda yaci sunan kakan baban mu ana kiran sa da Najib. Sai ni Fadimatuz-Zahra’u, wadda ake kira na da Batoul. Naci sunan mahaifiyar maman mu wadda ALLAH yayiwa rasuwa tun ina yar ‘kankanuwa. Sai autar mu Aminatu. Wadda taci sunan Yayar mahaifin mu dake garin Kaduna. Sai ‘ya’yan Bintalo guda hud’u, Yaya Zabba’u wacce ke aure a kauyen kod’e dake lahadin makole a Kano. Sai Alawiyyah da Hindatu wacce muke kira da Hinde, Sai autar su Hauwa.
Nasan mai karatu zai yi mamakin yawan gidan mu da kuma ahalin dake cikin sa, Toh kamar yadda kuka gani a baya, ‘Gidan Mata Tara’ gida ne mai dakuna guda tara. Sannan gidah ne wanda mahaifin mu da yan uwan sa su hudu suka hadu suka siya tun kafin a haife mu.
Mahaifin mu marigayi Malam Salis ya rasu ne shekaru bakwai da suka wuce lokacin autar mu Aminatu na jaririya, ya rasu ne akan hanyar sa ta zuwa gidah sakamakon hatsarin mota daya rutsa dasu, wata jibgegiyar gingimari ce tabi takan mashin din da yake kai alokacin yayo cefanen sunan kanwar mu Aminatu. Tundaga lokacin rayuwar mu ta canza zuwa halin rashi da kuma ‘kunci.
Ashe haka ‘kanne da yayyun uba suke? Tabbas mun shiga garari na rayuwa domin duk juya mana baya su kayi, abincin da za’a ci da rasuwar ma sai makwabta ne suke temakawa su bayar, sai da Gwaggo Aminatu tazo daga kaduna ne ta fuskanci halin da muke ciki, ta bamu hakuri sannan ta bayar akayo mana cefanen kayan abinci. Hakika Gwaggo Aminatu ita kadai ce mai kirki acikin yan uwan mahaifi mu, itace keyin mai yiwuwa don ganin ta tallafa mana ta tsaya har aka raba mana gado, mahaifin mu bashi da wata kadara fyace gidan da suka hada kudi suka saya shi da yan uwan sa, inda mahaifiyar mu da Bintalo kowanne ya kasance yanada rabo biyu biyu, tanada mata hudu mu kuma namiji daya mata biyu wato biyu kenan muma. Kowanne b’angare daga cikin mu ya tashi da daki d’aya d’aya. Sai da’ki d’aya wanda Rabi’atu take ciki wato matar Kawu Ishaq ta biyu, shine ya zamto a tuminin takabar su Innar mu. Nasan zakuyi mamakin toh a'ina Yaya Najib yake kwana ko? Toh Yayanmu yana d'aura net a tsukukun kofar dakin mu ya kwanta a kan yar tabarmar sa, wani lokacin kuma yakan kwana a langa langar makarantar almajiran dake kallon kofar gidan mu.
Tunda mahaifin mu ya rasu mu kai sallama da farin ciki, Innar mu ta kanyi wankau a gidajen masu hannu da shuni saboda rufin asirin mu. Yaya Najib kuma ya kasance yana kanikanci don samo mana abunda zamu afa a baka. Ni da autar mu kuma mu kadai ne keyin makaranta, itama ta gwamnati, wanda Yaya Najib da yanayi ya dakatar saboda bamuda halin da duk kanin mu zamu dinga zuwa makaranta, duk kuwa da ta gwamnati ce, Amman akwai tsarabe tsaraben kudin fom nera talatin duk wata, ga kudin littafi da fensir. Hakan yasanya Yayanmu dakatar da zuwa makaranta ya fara sana’ar kanikanci dan kare mana mutuncin mu, sannan muna zuwa Islamiyya duk wata naira hamsin itama yayan mu ne ke biya mana kudin. Duk kuncin rayuwar nan muka d’ai ne muka shige ta banda Bintalo da ‘Yayan ta domin ita su Baba ila suna taimaka mata. Hakan yasanya na qudri niyyar tsayawa tsayin daka don yin karatu sosai, Saboda inaso nayi amfani da damata na cika mana burikan mu. Hakika ALLAH ya yoni da saurin ‘daukar karatu da kaifin basira, komai yawan karatu cikin sauk’i nake gane shi na kuma hadde shi, Shiysa haddar AlQur’ani da muke baya min wahala, cikin kankanin lokaci nake haddace ta akai na.
Tabbas ALLAH ya yoni da zatin halitta da kyakkyawar sura, Idan ka kalle ni dole ne ka sake kallo na duk kuwa da kankancin shekaru na amman halittar jiki na a tsare take, ko’ina ya cika, sannan na kasance mai wata irin kalar fata ni ba fara can ba ba kuma baka chakulet ba. Na kasance tsaka tsaki wadda turawa ke kira da ‘brown skin’. Inada tsawo sosai TubarkAllah. Idanuwana farare ne tas da su kamar ruwan madara, kwayar idanu na kuwa burawun ce sosai, sai yalwar gashin gira domin saura ka’dan su hade da juna, baki na dan mitsi-tsi ne jawur dashi kai kace jambaki na shafa, hanci na dogo ne sosai, ga kuma tawadar ALLAH a gefan hancin wanda ya kara kyawun fuska ta, Inada yalwataccen gashin kai tubarkAllah tamkar ni na kera abuna, har gadon bayana yake zuwa. Shekaru na goma sha hudu a dunia, inada sa’oina sosai a gidan mu, Wanda suke kula-kulen samari kamar tinkiyoyi. Idan kaga layin da ake a kofar gidan mu za kwi mamaki. Na kasance ina da dinbin samari, Sai dai basa kulani saboda rashin ganin fuskar hakan. Sannan Yayan mu ya hanani kula kowanne daga cikin su. Hakan ba damu na yayi ba domin nima banida ra’ayin kula samari yanxu. Nafison sai nayi karatu sosai, kuma inada burin auren wanda ya girmemi ni sosai domin agani na sunfi hankali da nutsuwa.
Duk abokanan Yaya Najib kallon yara nake musu, har a sujjada nake rok’on ALLAH karya sa na auri wanda ya girme mini da shekaru biyar, nafuson na auri wanda ya bani shekaru goma da yan kai saboda wasu dalilai na dana barwa zucia ta. A karamin aji na biyu nake a jiniya sakandire, wadda ake kira da gwanmen gels jiniya sakandire sukul, shekaru na sha hudu a duniya, banida burin da nake so na karanta irin karantar bangaren zallar ingilishi. Kuma har farfesa nake so na zama a fannin.
Gidan mu ya kasance mai dakuma tara aciki, kuma Idan ka lissafa matan auren dake ciki su tara ne, Hakan shi yasanya yan layin mu dama unguwoyin gaban mu, yiwa laqabi da gidan mu 'Gidan Mata Tara'
Wannan shine takaitaccen tarihin gidan mu dama nawa a tak’aice.
*WASHE-GARI*
Tun asubar fari dana tashi ban koma ba, bandaki nai hanzarin shiga nayo wanka na, saboda ban’daki d’aya ne kawai a gidan mu, kuma har layi ake yi akan sa. Ina gama wanka na na tado autar mu itama na sab’e mata jikin ta. Innar mu ma tayo nata bayan mun gama kintsawa. Uniform dinmu na zaro mana a karkashin kwallar da muke ajiye kwanukan abincin mu. Domin anan nake mana ninkin guga sai na zura su a leda na dora kwallar akai sai kuga kuma sun ninku tamkar an goge shi. Rogowar dumamen shinkafar jia muka ci, na koma gefe ina azkhar, Innar mu kuma tagama nata tuni, ta kunna yar rediyon ta tana jin labaran jamus. Autar mu kuma ta kishingid’e tana bacci, daria taba ni yadda ta kanannade tana baccin ta da yar ledar littattafan ta a hannu. Gyara mata kwanciyar nai yadda zata ji dad’in baccin ta. Haka dai nai ta jira har rediyon hannun Innar mu suka sanar da ‘karfe bakwai da ‘kwata’. Mikewa nayi na dan diga turaren ‘dan duwalar da shi kadai ne turaren mu na shafe jikina dashi. Tashin autar mu nayi ta kara wanko bakin ta da fuskar ta. Innar mu dake gefe ta mik’o min naira talatin,
“Ungo ki dau ashirin din ki barwa auta goman, ALLAH ya bada sa’ar karatu mai amfani.”
Rissinawa nayi na karba cike da girmamawa,
“Mungode Innar mu ALLAH ya ‘kara bud’i.”
“Innar mu mungode..”
Autar mu tafada tana rufe bakin ta sakamon hammar data taho mata, da alama baccin bai gama sakin ta ba.
Haka dai na tasa keyar ta muka fara sauka a bene, a lokacin su Alawiyya ke wanka, kamshin soyayyan kwai sai tashi yake daga dakin su. Da alama dashi zasu tafi makaranta. Nida autar mu ne kawai ke yin makarantar gwamnati. Su Alawiyya firabet suke zuwa duk tam dubu d’aya da dari biyar. Makarantar su d’aya da Fadila babbar k’awata. Ina ta jan hannun autar mu muka tafi makaranta, har ajin su na kaita sannan na wuce namu ajin. Koda aka fito birek awara da wainar fulawa na siya mana ni da autar mu. Goman ta kuma muka sai ruwan biyar da alawa. Ana tashin mu muka dauki hanyar gidah, Muna tafe a hanya ina bitar haddar Ashmawin da za’a karba an jima a islamiyya. Tun a kofar zauren kofar gidan mu muke jiyo hayaniyya, kai na na dafe da hannun dama ina girgiza shi, shin yau ko da suwa ake dambatuwa oho? Muna shiga na jiyo muryar usaibatu maman su Larai tana lailayo ashar tana durawa Bintalo. Nan dai suka hau gumirzin fada, Baba ila dake tsakar gidah ya janyo bokitin karfe ya zauna akai yana duban su da kallo. Sunne kai nayi a ‘kasa na fara hawa bene, muryar Baba ila na jiyo yana doka wa suna na kira,
“Batoul, Ke Batoul...”
Gaba na ya fadi jikake ‘ras, Shin menayi ni kuma?! Cikin rawar baki da jiki na fara komawa kasa ina nanata,
“Na’am Kawu...Gani!”