QAUNA CE

BABI NA HUDU

by @ummasghar

*QAUNA CE*


*UMM ASGHAR*


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*


   


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*


FREE PAGE 4.


Alhaji Mahmoud Gezawa shine mahaifin su Ismael. Yana da matan aure guda uku.


Hajiya Salamatu itace uwargida, auren saurayi da budurwa itace kuma uwar manyan 'ya'yan gidan. Binta ce babba sai Saratu, Ismael, Kasim, Suleiman, Hafsa da autanta Abdurrahman.


Sai Hajiya Saude, ita kuma 'ya'yanta shidda mata hudu da maza biyu.


Sai kuma Hajiya Kubra itace mai yara qanana guda hudu, Jamila ce babbar 'yarta.


Akwai kyakkyawar alaqa wajen mutanen gidan don basa jarabar kishin nan irin na wasu gidajen, kan 'ya'yansu a hade yake duk da yawan sun nan babu 'yan ubanci a tsakaninsu. Karami na girmama babba, babba na jan girmanshi da tausayin na qasa dashi.


Don haka hankalin maigidan a kwance yake kullum kuma qarin budi yake samu a harkar kasuwancinshi. Sana'arshi da yayi suna a kanta itace saida goro sai kuma noma da kiwo da suma yake yi.


'Ya'yan Alhaji Mahmoud nada qoqarin neman ilimi daga na bokon har na Muhammadiyya. Mawuyacin abu ne kaga yaro ya gama makarntar secondary ba tare da yayi saukar AlQur'ani ba.


Suna da ladabi da biyayya kwarai da gaske.


Yawanci 'ya'yanshi mata duk an aurar dasu, Jamila ce yanzu babbar budurwa a gidan sai qannenta.


Jamila da Rufaida kusan lokaci daya aka haifesu. Rufaida ce babba don watanni uku ta bawa Jamila don haka suka taso tamkar kawaye.


Sa'anni na ne don suma jss3 suka gama. Hira sosai suke yi mini suna ta son na sake jiki dasu, ni kuwa gani nake yi nayi musu ma domin kuwa bani da saurin sabo, sannan kuma bani da yawan magana.


Illa iyaka idan sun yi abun dariya na dara domin suna da abin dariya kwarai da gaske. Ita Jamila sai tace Rufaida 'ya ce a wurinta don haka dole ne tayi mata biyayya, ita kuma Rufaida tace dole ne Jamila ta girmamata tunda kuwa itace babba, daga nan sai kaji sun kaure da musu, ni dai murmushi ne nawa.


Sai bayan sallar magrib Yaya Engnr ya shigo gidan. Muna dakin Hajiya Babba muna cin tuwo a lokacin. Yaya Saratu ma sun iso ita da iyalinta, itama mai kirki kamar 'yan uwanta.


Ya shigo da murmushi yace "ah lallai Zainab har kin yi sabo haka?"


Murmushin nayi nima na sunkuyar da kaina qasa ina gaishe shi.


"Ya school din?" Ya tambayeni.


"Lafiya lau Alhamdulillah, mun yi jarrabawar placement ma" yace "to Allah ya taimaka, bari naje wurin su Inna mu gaisa".


Yana fita Jamila tace " wai! ashe Yaya Engnr na sakewa yayi hira haka?" Nace "ni kuma bana iya sakewa dashi duk da sauqin kanshi gareni".


Rufaida tace "ai don kina da qoqari shi yasa, kin san shi Uncle Engnr yana son yaga mutum na maida hankali wajen karatu, mu yace shiririta ce damu shi yasa baya shiga shirginmu".


"Ai sai ku dage ku maida hankali wajen karatun kuma".


Yaya Binta ta jamu gidanta mu kwana duk da Hajiya taso na zauna nan a wurinta Yaya Binta tace "Hajiya ki bari mu tafi da ita don Allah, zata fi sakewa cikin yara sa'anninta".


Itama gidanta mai kyau mai tsari anan Court Road. A dakin Rufaida muka kwana, nayi ta kallon kauye ina mamakin wai nan dakin yarinya budurwa ne.


Na kwana a gadon da ban taba hawan mai kawa irinshi ba ga katifar mai laushi da sa dadin bacci kamar auduga, ai kuwa sai da na makara sallar asuba tsabar dadin bacci.


Sai sha dayan safe muka fita daga gidan Yaya Binta. Wurin tela muka fara zuwa wai zasu karbo dinkunansu.


Bayan mun karbi kayan ne tace wa drivernta mu wuce kasuwar sabon gari.


Rufaida tace "yauwa Umma takalmin da kika ce zaki saya mini" tace "ina sane ai".


A shagon takalma suna ta zaba suna gwadawa ni dai ina zaune a gefe guda ina kallonsu.


Yaya Binta ta kalleni tace "a'a Zainab ya ke ba kya zabar takalmin?"


Murmushi kawai nayi ba tare da nace komai ba.


Jamila tace "wanna kunya ne da ita Yaya bari ki gani na zabar nata naga size dinmu daya".


Ta zaba mini wani coffee color mai kyau, ita kuma ta dauki farinshi Rufaida kuma baqi.


Harda su sarqoqi da mayafai suka zaba mana.


Yaya Binta tace "sai kace wasu 'yammatan kirki sai wani iyayi kuke yi".


"Haba Yaya senior class fa zamu shiga, nan da 2yrs zaki ji muna shirin gama secondary School sai mu zama 'yammatan jami'a".


Dariya tayi tace " lallai jami'a zata ga 'yammata, duka shekarunku nawa? Sha hudu fa amma har kuna zancen tafiya jami'a".


"Kai Umma idan kina fadar haka sai a dinga ganinmu yara, su Nana(kannenta) rainamu zasu yi wallahi".


Yaya Binta tace "manya kenan iyayen yara" suka yi dariya ita da drivernta.


A gida Hajiya tace "Zainab kin sha yawo ko?" Ta kalli Yaya Binta tace "ina fatan kin karbo dinkuna nan don yanzu Ismael yayi waya yana jaddada lallai kada a manta a karbo kayan".


"Ai can muka fara zuwa" ta fito da kayan tana nunawa Hajiyar.


"Namu fa Yaya Binta?" Yaya Saratu tace.


"Tuni suna hannu, Hajiya bata nuna miki ba?"


Hajiyar tace "shaf na manta kuma tunda Hafsa ta gani ban san inda ta sakasu ba sai dai ku bari ta qaraso".


A daki na bar su Jamila suna ta gwada kayansu na tafi wurinsu Inna da akace suna waje ana aiki tare dasu.


Rufaida tazo ta kirani wai nazo inji Hajiya.


Kaya ne ta miqo mini a leda tace "ankon biki ne da Yayanku ya bayar aka dinka miki, shiga ciki ki gwada".


Durkusawa nayi nasa hannu biyu na karba ina cewa " nagode Hajiya Allah ya qara budi ya qara girma".


Cikin dakin Hajiyar muka shiga su Rufaida suka sakani a gaba wai dole sai na gwada kayan sun gani.


Abun mamaki duk wanda na gwada sun yi mini sosai kamar sai da aka gwadani sannan aka dinka.


Jamila tace "gaskiya kayan sun fi yi miki kyau ma Zainab, kina da kyau gaki da karuwan jiki".


Dariya nayi cikin jin dadi nace " kinji ki, miye kuma karuwan jiki?" 


Tace "duk kayan da kika saka sai sun amshi jikinki duk rashin kyaun kayan kuwa, kiyi hakuri fa ina da fadin duk abinda ke raina".


Murmushi nayi na kuma yadda da maganar Jamila don mawuyacin abu ne na saka sutura bata karbi jikina ba don ko uniform na saka haka zaku gansu cif a jikina, kullum Farida sai tace ita bata taba ganin wanda kayan makaranta ke yiwa kyau ba irina.


A parlourn Hajiya kuwa Yaya Saratu ke cewa "wallahi Hajiya da Ismael ya sani da ya jira Zainab din shi, ina son yarinyar don daga ganinta zata yi haquri gata da hankali da nutsuwa".


Tabe baki Hajiya tayi " shifa ya sani, ni kwata-kwata hankalina bai kwanta da wannan Badi'ar ba gashi na lura iyayenta nada rainin arziki gani suke yi kowa bai isa ba, to nayi-nayi ya haqura yaqi ya nace yace sai ita Alhaji kuma ya goya mishi baya yace nayi tayi mishi addu'a Allah ya tabbatar da alkhairi.


Amma ko ni ina son yarinyar nan Zainab tun jin labarinta a wurinshi, nayi zaton ma sonta yake yi yace a'a shi dai domin Allah yake yi".


Yaya Binta tace "to jiya ma muna tare nake ce mishi naga Zainabunka yarinya mai nutsuwa sai yace au tawa cema? Nayi dariya nace ai haka kowa ke ce mata. Ni kuwa nayi maka sha'awarta dama ka aureta".


Sai cewa yayi "nayi yaya da Badi'a kuma? Nifa ba don komai nake kulawa da Zainab sai domin Allah, bani da wata manufa akanta bare buri, fatana kawai rayuwarta ta inganta. Ina matukar tausayinsu, don Allah ki bar wannan maganar".


"To kunji fa yadda muka yi dashi".


Yaya Saratu tace "Allah dai ya bamu rai da lafiya, zaku ce na fada muku sai Ismael yazo ya qaryata zanceshi, yanzu ma don yayi nisa a son Badi'ar ne shi yasa kuma yana ganin kamar yarinyar tayi mishi qanqanta, ni kuwa zanyi ta addu'a Allah yasa kada yarinyar nan ta wuce gidannan".


Hajiya tace "a'a to idan baya so baga Kasim nan ba ko Suleiman".


"Lallai Hajiya kina son yarinyar nan" inji Yaya Binta.


"Wallahi tashi guda naji yarinyar ta shiga raina har inaji inama ita din tawa ce, kunga kuwa duk wanda ya aureta a cikinsu ai ta zama tawa".


Addu'a tabbatuwar alkhairi duka 'ya'yan nata suka yi ta amsa da Ameen.




*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*


INA KUKE MAKARANTA??


INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️


 SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA....


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B


INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.


1- *QAUNA CE* 

   NA UMM ASGHAR 


2- *RUKUQI*

  NA FEEDHOM 


3- *WANI SO*

   NA ZEE YABOUR 


4- *SO DA ALAKA*

    NA UMMI AISHA 


5- *MUGUN GANI*

  NA SADIYA NASIR DAN


6- *ABDUL_HAMEED*

   NA NANA DISO


7- *MUKULLIN ZUCIYA*

    NA MAMAN KHADY


DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA


(1000) DUBU DAYA KACAL


KAI KA KAI....!

TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N1000 KACAL, GA KUMA SHIRYE-SHIRYE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU MASOYAN MU...


1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA😍  

*DAGA CHEF RAHMA NA LELE*


2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI TSAFTACE JIKINKI, DA YANDA ZAKI ZAMO CIKIN KAMSHI A KODA YAUSHE WANDA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA

*DAGA AYUSHER MUH'D*


3-SHIRIN KOYOR DA YANDA ZAKI IYA HADA KAYAN NI'IMA A JIKINKI CIKIN SAUKI DOMIN GYARAN GIDAN AURENKI DA ZAMOWA FITILAR GIDANKI

*DAGA HAJJA CE 👈*


MASHAA ALLAH DUKA FA AKAN NAIRARKI *DUBU DAYA* KACAL ZAKI KASANCE ACIKIN GROUP DINNAN.


_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_

2083371244

ZENITH BANK 

AISHA M. SALIS


*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼*

+447894142004


IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*

*** da Shaidar biya duk ta ciki


 

MUN GODE.


_HAKA ZALIKA KOFA A BUDE TAKE GAME BUKATAR 'DAYA DAGA CIKIN TOP 10, AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 ONLY_


*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022*


_Wannan garabasar tamai rabo ce💃🏻💃🏻 sa kud'i kad'an ki debi hani'an😍😂_


*UMMASGHAR*