QAUNA CE

BABI NA SHIDA

by @ummasghar

*QAUNA CE*


*UMM ASGHAR*


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*


FREE PAGE 6.



Wajen dinner ya cika ya batse da matasan samari da 'yammata na garari masu ji da kyau da kuma iya ado. 


'THE AVENUE' naji su Jamila sun kira wajen da ake yin taron. Ni dai sai binsu nake yi a baya tamkar jela, jina nake yi a matuqar takure saboda shiga irin wadannan wuraren baqon abu ne a wurina.


Cikin hall din muka shiga muka samu teburi daga gaba-gaba muka zauna, a cewar su Rufaida wai gara mu zauna daga inda zamu iya ganin komai da ake yi.


Muna hirarmu jefi-jefi muna kuma 'yan kalle-kalle.


Mutane ne iri-iri kala-kala a wurinnan, kowa ka kalla ya qure adaka cikin kwalliya ta burgewa da iya ado ta wannan na wane ta wannan.


A haka har hall din ya cika kowa ya nemi wuri ya zauna.


Babu dadewa MC ya fara sanarwar isowar amarya tare da angonta.


Wakar 'DUDUKE' ta Simi aka saka yayin shigowar amarya da angon bayan da aka nemi duka mutanen wajen da su miqe tsaye.


"Masha Allah" na samu kaina da furtawa a lokacin da Yaya Engnr da amaryarshi suka ratso cikin hall din.


Yara ne guda biyu 'ya'yan larabawa da baza su wuce shekaru biyar ba a gabansu suna watsa wata irin gutsatsarin flowers a duk inda amaryar da angon zasu taka.


Sai kuma wasu biyun da suka dan dara wadancan daga bayansu suna rike da rigar amaryar dake jan qasa.


Sanye take da wata irin wedding gown mai azabar kyau kalar cream, ta saki dogon baqi sidik din gashinta da aka yiwa wani irin ado mai ban sha'awa da wasu abubuwa masu kyalkyali da ni dai bazan iya tantance menene ba.


Shi kuma angon yana sanye a cikin shadda getzner mai bala'in tsada kalar brown mai haske dinkin babbar riga, anyi aikin jikin kayan da zare mai kalar brown mai duhu.


Hular kanshi ma kalar dark brown din ce inda aikinta dana jikin kayan suka kasance iri daya, takalman kafarshi ma duk dark brown din ne.


A gaskiya amaryar Yaya Engnr kyakkyawa ce ta bugawa a jarida ma kuwa.


Sai dai kuma abin da ya daure mini kai ganin yadda ta ratso cikin taron mutanen nan ba tare da ta saka ko dan gyale ne ta suturta kanta ba.


A take na tabbatar da maganar da Yaya Saratu tayi da tace wasu matan basu dauki tsiraici wani abu ba don a ganinsu hakan shine wayewa.


Na samu kaina da yin tur da Allah wadai da irin wannan wayewar da zata ja mutum ga halaka.


Sai bayan da ango da amarya sun zauna a wurin zamansu kafin kowa ya koma ya zauna.


Daga nan kuma aka fara gabatar da programme.


Ni dai na bude idanu ina kallon biki irin wanda ban taba zaton ana yi ba.


Yadda aka tsara bikin ya qayatar matuqa, bayan amarya da ango sun yanka cake ne har sun ciyar da junansu aka fara serving abinci table by table.


Wasu irin abinci kala-kala da aka raba a wurin nan da yawa ma ban taba ganinsu ba.


Bayan gama cin abincin ne aka bude photo session wato daukar hotuna da amarya da ango.


Muma munje mun yi hotunan dasu anan ne Yaya Engnr ya gabatar dani a wajen amaryar tashi yace mata "Babe ga nan Zainab ku gaisa, yarinyar da nake baki labari, ai kin tuna ko?"


Kallona tayi sama da qasa ta tabe baki tace "um na tuna, ko ba ita ce yarinyar da kake sponsoring karatunta ba?"


Daga haka ta juyar da kanta tana magana da wata 'yar uwarta ba tare da ta amsa gaisuwar da nayi mata ba.


Jikina yayi sanyi da yadda amaryar Yaya Engnr ta karbeni sai dai ban bari hakan yayi tasiri a tare dani ba nayi mata uzuri tunda a cikin hidima take ba lallai ne da wata manufa tayi mini hakan ba.


Sai karfe sha daya da wajen rabi muka koma gida. Yau a gidansu Yaya Engnr zamu kwana saboda motar data dauko mu daga wajen dinner direct nan tayi damu.


Lokacin da muka shiga gidan da yawa mutane sun kwanta bacci, muma kayan jiknmu kawai muka canja muka kwanta baccin saboda gajiyar da muka kwaso.


Tun bayan da muka yi sallar asuba bamu koma mun kwanta ba sai muka dasa hira duk da ma dai hirar tafi karfi a tskanin Jamila da Rufaida ana yi ana haurawa idan sun yi abin dariya na dara.


"Yauwa Zaynu ina taso na roqeki don Allah mana ki zauna kiyi hutunki anan" inji Rufaida.


Dariya nayi kawai jin abinda tace.


" Eh wallahi, don Allah Zaynu ki zauna kiyi mana hutu wallahi dan kwana biyun nan da muka yi tare nayi sabo dake sosai har bana so ki tafi, kinji?" Ta hade hannyenta bibbiyu alamar roqo.


"Kuyi haquri amma Baba ba zai barni ba zai ce ne zan daurawa su Hajiya nauyi koba haka ba nima bazan iya zama ba don hidimar ai sai tayi yawa, ina ma laifin zuwan da nayi na kwana har hudu ku kuwa".


Hararata Jamila tayi tace "wannan zuwan ai biki kika zo, mu kuwa hutu muke so kiyi mana tunda kuma ba zaki zauna ba ai shikenan amma kada ki soma kiyi wa Baba sharri don nasan ba zai taba hanaki zama anan ba".


Ban qara tanka musu ba har suka yi magiyarsu suka gaji suka kyaleni don nasan duk bayanin da zan yi musu ba fahimta zasu yi ba.


Bayan daurin auren Yaya Engnr ya shigo tare da abokanshi yayi hotuna da mutanen gidan.


Ina kwance a dakinsu Jamila Rufaida tazo ta kirani wai nazo mu dauki hoto inji Yaya Engnr.


Tashi nayi na gyara daurin dankwalina daya sunce na yafa gyalena muka fita zuwa harabar gidan inda anan ne ake daukar hotunan.


Tunda nasan Yaya Engnr ban taba ganin fara'arshi ba kamar yau, ya kasa rufe bakinshi alamun dai yana cikin tsantsar farin ciki.


Qarasawa nayi na gaisheshi tare dayi mishi Allah ya sanya alkhairi tukunna aka daukemu hoton na koma daki.


Karfe hudu na yamma aka fara shirin tafiya dauko amarya.


Sai da aka dauko amaryar aka kawota nan gidan kafin aka wuce da ita gidanta dake unguwar Lamido crescent.


Gidan Yaya Engnr yayi kyau, sosai tsarin gidan ya burgeni.


Interior decorators ne suka shirya gidan a yadda naji su Jamila na fada.


Mamakin irin dukiyar da aka narkar a cikin gidan nan kawai nake yi. Duka dakunan gidan guda shidda, biyu a qasa, uku a hawan farko sai makeken dakin masu gidan a hawan karshe wanda naji su Jamila sun ce pent house ake ce mishi, babu wanda ba'a shirya ba cikin gadaje na alfarma.


Faluka hudu ne gidan, biyu a qasa, daya a hawan farko sai dan karami acan pent house din. Su din ma an shirya su da kujeru masu matuqar kyau da tsada.


Lallai kudi suna inda suke. 'Alhamdulillah ala ni'imatihi tatimmu salihat' kawai nake ambato a cikin zuciyata a lokacin da su Jamila suka jani wani kebantaccen wuri da ya tsaru iya tsaruwa ga wata irin ni'imatcciyar iska da take kadawa a wurin suka ce wai wajen wanka ne wato swimming pool.


Koda muka koma gidan idan banda santin gidan Yaya Engnr babu abinda muke yi.


A ranar kusan raba dare muka yi muna hira don sai kusan karfe biyu da wani abu muka kwanta bacci.


Washegari da wuri muka kama hanyar Jahun bayan an cika mu da kayan biki himili guda kamar don mu kawai aka yi.


Mu muna murna da karramamun da suka yi suma suna farin ciki da zuwan da muka yi. Haka muka rabu ana ta begen juna, su Jamila harda kukansu wai basa so na tafi ni din ma sai da nayi kwalla don a 'yan kwanakin da muka yi ba qaramin sabo nayi dasu ba.






*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*


INA KUKE MAKARANTA??


INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️


 SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA....


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B


INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.


1- *KAUNA CE* 

   NA UMM ASGHAR 


2- *RUKUQI*

  NA FEEDHOM 


3- *WANI SO*

   NA ZEE YABOUR 


4- *SO DA ALAKA*

    NA UMMI AISHA 


5- *MUGUN GANI*

  NA SADIYA NASIR DAN


6- *ABDUL_HAMEED*

   NA NANA DISO


7- *MUKULLIN ZUCIYA*

    NA MAMAN KHADY


Daya 200 

biyu 400, 

guda uku 500

Guda hudu 700 

Guda biyar 750 

Shida 800 bakwai 1000 da programs


DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA


(1000) DUBU DAYA KACAL


KAI KA KAI....!

TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N1000 KACAL, GA KUMA SHIRYE-SHIRYE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU MASOYAN MU...


1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA😍  

*DAGA CHEF RAHMA NA LELE*


2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI TSAFTACE JIKINKI, DA YANDA ZAKI ZAMO CIKIN KAMSHI A KODA YAUSHE WANDA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA

*DAGA AYUSHER MUH'D*


3-SHIRIN KOYOR DA YANDA ZAKI IYA HADA KAYAN NI'IMA A JIKINKI CIKIN SAUKI DOMIN GYARAN GIDAN AURENKI DA ZAMOWA FITILAR GIDANKI

*DAGA HAJJA CE 👈*


MASHAA ALLAH DUKA FA AKAN NAIRARKI *DUBU DAYA* KACAL ZAKI KASANCE ACIKIN GROUP DINNAN


_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_

2083371244

ZENITH BANK 

AISHA M. SALIS


*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼*

+447894142004


IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*

*** da Shaidar biya duk ta ciki


 _GA MUTANENMU NA QASAR NIGER🇳🇪 ZAKU IYA TURA KUDINKU TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR👇🏼_

+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.

MUN GODE.



*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022*


_Wannan garabasar tamai rabo ce💃🏻💃🏻 sa kud'i kad'an ki debi hani'an😍😂_


*UMMASGHAR*