QAUNA CE

BABI NA TAKWAS

by @ummasghar

*QAUNA CE*


*UMM ASGHAR*


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*


FREE PAGE 8.



A halin yanzu nasan babu abinda iyayena ke so da buri irin ganin sun kawar dani daga gabansu.


Tabbas ina so naga nayi biyayya ga umurnin Yaya Engnr ko babu komai nima ina da sha'awar ganin na cigaba da karatun nawa, yiwuwar hakan ne dai yake da matuqar wahala idan har Kamal na aura don a irin hirarrakin da muke yi yasha gwada mini baya da ra'ayin cigaban karatuna.


Sai dai ban san yadda zan yi dasu Baba ba idan har suka ga an daina aikowa kirana daga waje, ban san wane irin bayani zan yi musu ba, don haka na tsaida shawarar ba zan sallami Kamal ba tunda dai ban san me gaba zata haifar ba ba kuma lallai ne Baba ya amince na cigaba da karatun ba kamar yadda Yaya Engnr yake da buri. 


Duk shekara gwamnatin jihar Jigawa tana bada Jamb form kyauta ga dalibai uku mafi hazaka a dukkanin makarantun secondary na jihar.


Ko ban fada ba kun san ina daya daga cikin wadanda aka bawa a wannan shekarar.


Koda aka zo cike form din ban bayar da bayanaina ba sai da na kira Yaya Engnr ta wayar form master din mu Mallam Ghali na sanar mishi da abun alherin daya sameni tare da neman shawararshi akan makarantar da ya dace na cike duk da dai ba lallai ne Baba ya amince mini ba to amma ba zan so wannan damar ta wuceni ba.


Shi ya bani shawarar na cike BUK inda ni kuma na zabi karantar Medicine.


Muna ta cigaba da karatunmu har lokacin yin jarrabawar Jamb din yayi, daga makaranta aka kwashe mu zuwa center dinmu dake garin Dutse muka rubuta jarrabawar a ranar muka juya zuwa Taura.


Babu abinda zance sai Alhamdulillah domin kuwa maki 296 na samu a jarrabawar mu ta Jamb.


Ba alfahari ba amma Jarrabawar mu ta WAEC da NECO tazo mini cikin sauqi, koda yake na karantu iya karantuwa gashi kuma dama Allah yayi mini baiwar fahimtar Karatun don darasi ko ba na ajinmu bane idan har naji shi sau daya to na gama fahimta.


A ranar bikin yaye mu wato graduation sai ga Baba har da Inna tare da Mallam Isah sun zo mini.


Farin ciki kam iya farin ciki nayi shi a wannan rana haka nan iyayena da duk wani mai kaunata don na karbi kyaututtukan daliba mafi kwazo a cikin darussa har hudu wato Biology, physics, chemistry da mathematics.


Haka nan na karbi kyautar daliba ta biyu a cikin darasin geography.


A karshe dai ni na karbi kyautar overall best student na wannan shekarar.


A wannan rana fuskar iyayena ta kasa boye halin farin cikin da suke ciki, don Inna ma dai goge hawaye tayi tayi da bakin hijabinta.


Duk da Yaya Engnr bai samu halarta ba yasa Mallam Isah sun taho da mai hoto don haka sosai muka daddauki hotuna tare da iyayena, malamaina, kawayena da duk wanda yazo don tayani murna.


Bamu baro garin Taura ba sai bayan karfe biyu na rana cikin kewa da alhinin rabuwa da abokan karatun da muka shekara uku tare cikin zama na aminci da qaunar juna.


Tunda muka dawo gida nayi wanka nayi sallah na samu wuri na kwanta don ko abinci ban iya tashi naci ba sai furar dana sha itama sai da Inna ta matsa mini sannan na sha kadan na koma na kwanta.


Gaba daya gajiya da rashin baccin da muka yi ta fama dashi a makaranta ne suka saukar mini lokaci guda.


Sai magriba Inna ta tasheni ganin baccin nawa bana qare bane.


A kasalance na tashi nayi sallar, ban motsa daga inda nayi sallar ba sai da nayi sallar isha.


Aron wayar Baba na karba na kira Yaya Engnr don na gaisheshi na kuma yi mishi godiyar alkhairinshi a gareni don da jajircewarshi tare da taimakonshi na tako zuwa matsayin da nake akai a yau.


Ta jima tana ringing don ina tunanin ma kiran ya kusa tsinkewa kafin ya daga cikin sallama tare da cewa "Barka da dare Baba. Ina fatan kuna lafiya." 


"Ba shi bane nice Zaynu, Yaya ina yini?"


"Lafiya lau Zainab, ya exams din? Kun dawo lafiya?"


"Lafiya lau Yaya, jarrabawa Alhamdulillah".


"Masha Allah. Allah ya bada sa'a".


"Ameen, nagode". Sai kuma nayi shiru duk da ga magana a bakina ina son yi amma na rasa ta yadda zan fara.


Shi din ma shiru yayi yana jiran jin dalilin kiran.


Ganin ina ta qonawa Baba katin waya yasa na daure nace "nagode Yaya Allah yayi maka mafificin sakamako na alkhairi, tabbas ba don shigowarka cikin rayuwata ba da ban san a wane ajin ta ajiyeni ba. Kai din jigo ne kuma madogara ba ga kannenka da 'yanuwanka ba kadai har ma da al'ummar musulmi gaba daya. 


Bani da wata kalma da zan yi amfani da ita wajen yi maka godiya sai dai ka sani har kullum kana cikin addu'ata, ina fata Allah ya faranta maka fiye da yadda kayi mini ya biya maka dukkan bukatunka na alkhairi anan gidan duniya yayi maka mafificin sakamako da Jannatul Firdaus a lahira. Allah ya rabaka da iyayenka lafiya ya baka zuri'a ta gari masu albarka".


"Ameen Zainab, nagode da addu'a amma don Allah batun ya isa haka ni don Allah nayi don haka bana buqatar godiya".


Nace " haka ne Yaya na sani don Allah kayi amma bahaushe ma yace yaba kyauta tukwuici don haka addu'ar dai ce tukwuicin da zan baka. Nagode Allah ya saka da alkhairi"


"Hmm... Godiyar ce dai baza ki daina ba ko?"


Dariya nayi nace "To kayi haquri na daina".


Daga haka muka yi sallama na mayarwa Baba da wayarshi bayan na fada musu saqon gaisuwa daga Yaya Engnr.


Ajiye wayar yayi akan bedside drawer yana murmushi. 


Kallon agogo yayi yaga karfe tara saura kwata.


Da kwanciya yake da niyyar yi don yau din nan a gajiye yake tubus hutu kawai yake bukata, tunda ya shiga office bai samu kanshi ba saboda tarin ayyukan da ya tarar sai dai yunwar cikinshi baza ta barshi ya samu hutun da yake buqata ba idan har ba abinci ya nema yaci ba.


Saukowa yayi qasa ya nufi dining room, tsayawa yayi yana qarewa table din kallo wanda ke shake da warmers din da aka cika da girke-girke kala-kala tamkar masu ciyar da mutane da yawa ba mutum biyu ba.


Yayi-yayi da Badi'at a daina dafa abinci da yawa irin haka tunda dai ba iya cinyewa suke yi ba amma taqi ji tace su haka al'adarsu take ba'a dafa abinci kala daya.


Har magana yayi wa cook din yace ya daina girkin nan mai yawa idan kuma har sai anyi da yawan to kala biyu ma ya isa ko uku amma ba'a daina ba wanda kuma ya tabbatar Badi'at din ce zata hana.


Bai tsaya bude-buden warmers din ba kawai ta gabanshi yaja ya bude ya zuba abincin daidai cikinshi ya zauna ya faraci.


Ya kusa kammala cin abincin lokacin da ta shigo cikin gidan. Sanye take da baqar abaya tayi rolling da mayafin abayar a kanta jelar dodgon gashinta tana reto ta qasan mayafin.


Ajiye jakar hannunta tayi akan table din sannan ta saqalo da hannayenta ta wuyanshi tare da bashi peck a kumatu.


"Ashe ka dawo?" Tace bayan ta zauna a kujerar dake gefenshi.


"Umm" kawai yace mata ya cigaba da cin abincin shi.


Warmers din ta hau bubbudewa tana yatsina fuska alamun dai babu abinda yayi mata duk cikin abincin.


Juice ta dauka ta sha kafin ta miqe ta dauki jakarta ta haya sama.


Da kallo kawai ya bita har sai da ta haye kafin ya juyo ya maida kallonshi akan table din. 


Shi dama yasan zai yi wuya kwarai taci abincin nan tunda ba wai ta damu da yawan cin abincin bane amma duk da haka sai tasa anyi girki fiye da qima, bai kuma isa yayi magana ba yanzun ne cibi zai zama qari.


A rayuwarshi ya tsani almubazzaranci don bai taso yaga ana hakan a gidansu ba, abinda yake so Badi'at ta fahimta kenan ta kasa.





********


Sati daya nayi a gida ina hutawa daga nan na shirya na tafi Aujara wajen Yaya Indo nayi mata kwana biyu na dawo.


Taso ma ta riqeni nayi mata kwanaki fiye da hakan nice naqi don ina so na dawo na cigaba da zuwa Islamiyya don tun kafin na tafi wajenta na cike form din islamiyyar, duk da dai nayi saukar Alqur'ani dama wasu littattafan tun ina Guri amma dai shi ilimi kogi ne baya qin dadi.





*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*


INA KUKE MAKARANTA??


INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️


 SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA....


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B


INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.


1- *KAUNA CE* 

   NA UMM ASGHAR 


2- *RUKUQI*

  NA FEEDHOM 


3- *WANI SO*

   NA ZEE YABOUR 


4- *SO DA ALAKA*

    NA UMMI AISHA 


5- *MUGUN GANI*

  NA SADIYA NASIR DAN


6- *ABDUL_HAMEED*

   NA NANA DISO


7- *MUKULLIN ZUCIYA*

    NA MAMAN KHADY


Daya 200 

biyu 400, 

guda uku 500

Guda hudu 700 

Guda biyar 750 

Shida 800 bakwai 1000 da programs


DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA


(1000) DUBU DAYA KACAL


KAI KA KAI....!

TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N1000 KACAL, GA KUMA SHIRYE-SHIRYE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU MASOYAN MU...


1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA😍  

*DAGA CHEF RAHMA NA LELE*


2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI TSAFTACE JIKINKI, DA YANDA ZAKI ZAMO CIKIN KAMSHI A KODA YAUSHE WANDA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA

*DAGA AYUSHER MUH'D*


3-SHIRIN KOYOR DA YANDA ZAKI IYA HADA KAYAN NI'IMA A JIKINKI CIKIN SAUKI DOMIN GYARAN GIDAN AURENKI DA ZAMOWA FITILAR GIDANKI

*DAGA HAJJA CE 👈*


MASHAA ALLAH DUKA FA AKAN NAIRARKI *DUBU DAYA* KACAL ZAKI KASANCE ACIKIN GROUP DINNAN


_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_

2083371244

ZENITH BANK 

AISHA M. SALIS


*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼*

+447894142004


IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*

*** da Shaidar biya duk ta ciki


 _GA MUTANENMU NA QASAR NIGER🇳🇪 ZAKU IYA TURA KUDINKU TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR👇🏼_

+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.

MUN GODE.


*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022*


_Wannan garabasar tamai rabo ce💃🏻💃🏻 sa kud'i kad'an ki debi hani'an😍😂_


*UMMASGHAR*