QAUNA CE

BABI NA GOMA

by @ummasghar

*QAUNA CE*


*UMM ASGHAR*


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*


FREE PAGE 10.



Karfe hudu da rabi na yamma muka dauki hanyar Kano a cikin lafiyayyar motar Yaya Engnr.


Tunda muka shiga ya saka karatun Al-Qur'ani Suratul Maryam cikin qira'ar Sheikh Ahmad Ali Al-Ajmi.


Tun ina bi a hankali har ban san lokacin da bacci ya daukeni ba sai dai kawai naji Yaya Engnr na bubbuga jikin kujerar da nake zaune yace "oya tashi baccin ya isa haka nan mun iso".


Bude idanuna nayi naga har magriba tayi. Sai da na kalli wurin sosai na gane a harabar gidansu Yaya Engnr muke.


"Sannu da qoqari" nace ina qoqarin bude murfin motar.


"Yauwa sannu sarauniyar bacci, ke haka ake yi kawai daga shiga mota sai ki kama bacci ko dan kalle-kallen hanya baza kiyi ba".


Sunkuyar da kaina nayi ina dan murmushi don ni kaina naji kunyar sakin bakin da nayi na shaqi bacci kamar wacce ke cikin dakinta, sai dai kuma nasan har da baccin da ban samu nayi ba saboda zumudin tafiya ya sanya ni yin wannan din.


Bude motar yayi ya fita nima nabi bayanshi na fito. Ganin ya nufi hanyar fita daga gidan yasa na dan daga murya nace "Yaya kayana fa?"


"Jeki kawai idan na dawo daga masallaci zan sa a shigar miki dasu".


Hanyar shiga cikin gidan na nufa cikin dar-dar duk kuwa da ba wannan ne zuwa na gidan na farko ba.


Bangaren Hajiya Babba na nufa, daga bakin kofar parlour na tsaya ina sallama.


Daga ciki naji an amsa mini tare da bani izinin shiga.


Wata sallamar na sake yi yayin shiga cikin parlour. Hajiya Babba dake zaune akan sallaya tana jan carbi ta amsa.


Qarasowa nayi ciki na zauna daga kasa akan carpet ina gaisheta.


Amsawa tayi tana qare mini kallo ga alama dai bata shaida ni ba, ni dai na sunkuyar da kaina a qasa don sosai nake jin nauyinta.


Sai da ta kalleni sosai tace "sai naga kamar Zaynu ko?"


Nace "nice Hajiya. Mun sameku lafiya?"


"Lafiya lau Alhamdulillah, ai ban shaidaki ba Zaynu sai naga kin qara girma, koda yake ai ba yau bane ganina dake na karshe.


Yasu Innar taki duk qalau dai suke?"


"Duk lafiyarsu lau Hajiya sun ce ma a gaisheku".


"To madalla muna amsawa, tashi ki shiga ciki kiyi sallah kafin Jamila taji zuwanki tazo ta kanainayeki da zance, nasan duk sun shiga sallah shi yasa basu san da shigowarki ba".


Tashi nayi ina murmushi na shige dakin Hajiya, na dan jima a toilet din kafin na dauro alwala na fito.


Ina idar da sallah naga Jamila zaune a bakin gado, tana ganin na idar ta taso da gudu tazo ta ruqunqumeni tana ihu da tsallen murna.


"Wayyo Allah Zaynu da gaske kece? Ko dai gizo idona yake yi mini" tace bayan ta sakeni tana qare mini kallo.


Ni dai dariyar ta kawai nake yi ganin yadda take ta tsalle kamar wata karamar yarinya.


Tashi nayi na koma bakin gadon na zauna kafin na amsata da "gani kuwa, ku ai ba kwa nema na tunda ko saqon gaisuwar ku bai taba iskoni ba ni kuwa kullum sai nace a gaishe ku".


" Ayya Zaynu kada ki ce haka wallahi babu irin roqon da bamu yiwa Yaya Ismael ba yaqi kaimu, daga yace baya da time sai yace ba can zai wuce ba direct sai ya biya ta wani wuri amma wallahi kullum kina ranmu muna yawan yin zancenki da Ruffy, ko yau da tasan zaki zo da bata tafi gida ba don anan suka yini dazun nan suka tafi".


"Allah sarki Ruffy, nima ina yawan tunaku da dramarku nayi ta dariya ni kadai".


Hajiya ce ta shigo dakin tace "kina nan kin saka ta a gaba da zance maimakon ki rakata ta gaida mutanen gida gashi ko ruwa baki bata ba bare abinci".


Tashi tayi tana dariya ta ce "dama fa yanzu nake shirin raka ta Hajiya mun tsaya gaisawa ne da kuma hirar yaushe gamo".


Tabe baki Hajiya ta juya tana cewa "ke kam ai ba a kasa ki a magana".


Muna fitowa naga an shigo mini da kayana sai jarkokin nono guda biyu da na kawo musu tsaraba.


Daukar jarkokin nayi na qarasa gaban Hajiya na ajiye tare da ce mata "gashi Hajiya karamar ta su Yaya Engnr ce".


"Kai madalla mun gode Allah ya saka da alkhairi, ke da kika zo yin jarrabawa shine har da wahalar yin tsaraba, mun gode kwarai da gaske. Dama dazu Alhaji ke cewa bai san Ismael ya tafi Jahun ba ai da yace ya taho mishi da nono don yana son fura da nonon wajenku akwai kyau".


Jakar kayana Jamila ta dauka muka fita.


Bangaren Hajiyar tsakiya wato Hajiya Saude muka fara zuwa na gaisheta daga nan muka wuce bangaren Hajiyar su Jamila.


Dakinta taja ni bayan mun gaisa da Hajiyar.


Anan muka ci abinci daga nan muka dora da hira tana bani labarin school din su da kawayenta, hira dai kala-kala don ba a raba Jamila da zance, ni har mamakin surutun ta nake yi ita ko gajiya bata yi.


Waya ta dauka ta kira Rufaida, a handsfree ta saka wayar bayan ta dauka tace mata "guess what?"


"What" Rufaidan ta amsa daga nata bangaren.


"Kin ganni tare da Zaynu dazun nan bayan tafiyar ku suka iso ita da Yaya Ismael itama zata rubuta jarrabawar post utme kamar mu".


Ihun murna tasa tace "don Allah Jamie da gaske kike yi?"


"Wallahi kuwa gama ta nan tana jin ki don a handsfree na saka wayar"


"Hello Zaynu, wai da gaske ke ce?"


Dariya nayi nace "nice mana Rufaida, kuna lafiya? Yasu Yaya Binta?"


"Duk lafiyarsu lau Alhamdulillah, amma wallahi naji haushi da na san zaki zo ai da ban tafi ba amma ina nan tafe gobe In Sha Allah".



"Allah ya nuna mana goben cikin aminci".


Mun jima muna hira kafin muka yi sallama.


A wannan daren har wajen sha biyu muka kai kafin mu kwanta bacci don haka muka dan makara tashi sallar asuba.


Ni na fara tashi naga har gari yayi haske. "Subhanallahi" nace yayin da nayi zumbur na miqe.


Sai da nayi alwala na fito sannan na tashi Jamila ni kuma na tada sallah.


Koda na idar ban tashi ba anan na zauna ina azkar har gari ya karasa wayewa.


Dakin na fara tattarewa duk kuwa da babu wani datti a ciki.


Fita nayi na nemo tsintsiya na share dakin, daga nan na fita na share parlour zuwa dan tsakar gidan da ke bangaren nata.


Ina tattare sharar zan kwashe Hajiyar ta fito.


Riqe baki tayi tace "yanzu da sassafen nan kika hau shara maimakon ki koma ki kwanta ki huta, ina fa jin ku jiya har wajen sha biyu baku kwanta ba kuna ta hira".


Murmushi nayi na durkusa ina gaisheta.


"Lafiya lau Zaynu, sannu da qoqari kin ji".


Bayan wucewar Hajiyar ne na koma dakin. Bandaki na shiga nayi wanka, har wannan lokacin Jamila na kwance tana bacci.


Shiryawa nayi cikin atamfar clara wax dinkin riga da zani, sai na dauki hijabi na na saka.


Fita nayi naje na gaida Hajiyar tsakiya daga nan na wuce dakin Hajiya Babba.


Ban iske Hajiyar a dakin ba kawai sai na kama gyaran wurin.


Har na gyaro dakunan baccin Hajiyar zuwa babba da karamin parlours dinta bata shigo ba.


Ban dade da gama aikin ba sai ga Jamila ta shigo da food warmers a hannunta.


Ajiye su tayi anan tsakiyar parlour tace "shine kika tashi kika yi ta aiki maimakon ki tashe ni mu yi tare, gashi nan kin sa Hajiya sai fada take yi wai ga nan inda ake abun arziqi ba kamar ni ba da ban ajiye komai ba sai baccin asara".


Murmushi nayi nace "gani nayi kamar kina jin dadin baccin shi yasa ban tasheki ba amma kiyi haquri".


"Ai ba haushi naji ba, ita Hajiya ce ta kasa gane muhimmancin a bar mutum ya mori baccin safen shi tunda dai ba makaranta zani ba ai sai a qyaleni idan na tashi duk aikin da ake so nayi sai nayi, naga dai idan na fara karatu ba yi zanyi ba".


Kallonta nayi da mamaki nace "wai a Hajiyar kike wadannan maganganun?" 


"To ai Hajiyar ce bata raina abun fada komai kankantar laifi sai tayi magana".


"Kada dai ki manta su iyaye ba abun rainawa ba ne, idan ba ta fada miki gaskiya ba waye zai fada miki ki dauka".



"Kinga sauko muyi breakfast sai muje mu gaishe da Alhaji. Yaushe zaki rubuta exam din ne? Don ni sai gobe In Sha Allah". Ta canja maganar alamar bata so a cigaba.


Nima sai na kyaleta nace "Wallahi ban sani ba don Yaya Engnr bai fada mini ba kawai dai yace a cikin satin nan zan rubuta".


" Ok, ina ga mantawa yayi zuwa anjima sai mu kirashi a waya muji".


Muna gama karyawa Jamila ta jani part din Alhaji don mu gaisheshi.


Yana zaune a kasa kan carpet ya miqe kafafunshi, a gabanshi kwanukan da ya gama cin abinci ne da ba a kai ga kwashewa ba.


Zama muka yi dan nesa da shi kafin muka gaisheshi.


Cikin fara'ar da bata rabo da fuskarshi ya amsa gaisuwar tamu, kafin ya kalli Jamila yace "baquwa kika yi ne Goggo(haka yake ce mata kasancewar sunan yar mahaifiyarshi gareta)?".


"Zaynu ce fa Alhaji Zaynun Yaya Engnr. Jiya tazo itama zata rubuta jarrabawar post utme".


A take fara'ar fuskarshi ta fadada yace "au to Masha Allah, kun zo lafiya? Ya iyayen naki duk lafiya qalau suke?".


Murmushi nayi kaina a qasa nace "duk lafiya lau Alhaji, sun ce ma a gaisheku".


"Muna amsawa kwarai da gaske, Allah yayi albarka. Ai sun kyauta da suka barki ki cigaba da karatu. To wane bangare zaki karanta? Ga Goggo dai tace ita lauya(lawyer) take so ta zama".


"Medicine na cike Alhaji" na amsa har yanzu dai kaina a qasa.


"To Masha Allah ashe kice muna da manyan likitoci, kunga shikenan na huta da yawon zuwa asibiti tunda gani da likita a gida".


Dariya muka yi gaba daya jin ya shigo da barkwanci cikin maganar.


"Allah ya baku sa'a, sai ku dage da karatu don karatun Jami'a ba irin wanda kuka baro ba ne, karatu ne dake buqatar jajircewa da nutsuwa. Allah ya taimaka".


"Ameen Alhaji,mun gode" muka tara fadi.


A daidai lokacin Hajiya Babba ta fito daga cikin dakin baccin shi tana cewa "ai bana jami'a zata ga baqi, su Rufaida sarakan rawar kai". 


Dariya duk muka yi jin abinda tace. 




*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*


INA KUKE MAKARANTA??


INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️


SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA....


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B


INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.


1- *KAUNA CE* 

NA UMM ASGHAR 


2- *RUKUQI*

NA FEEDHOM 


3- *WANI SO*

NA ZEE YABOUR 


4- *SO DA ALAKA*

NA UMMI AISHA 


5- *MUGUN GANI*

NA SADIYA NASIR DAN


6- *ABDUL_HAMEED*

NA NANA DISO


7- *MUKULLIN ZUCIYA*

NA MAMAN KHADY


Daya 200 

biyu 400, 

guda uku 500

Guda hudu 700 

Guda biyar 750 

Shida 800 bakwai 1000 da programs


DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA


(1000) DUBU DAYA KACAL


KAI KA KAI....!

TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N1000 KACAL, GA KUMA SHIRYE-SHIRYE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU MASOYAN MU...


1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA😍 

*DAGA CHEF RAHMA NA LELE*


2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI TSAFTACE JIKINKI, DA YANDA ZAKI ZAMO CIKIN KAMSHI A KODA YAUSHE WANDA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA

*DAGA AYUSHER MUH'D*


3-SHIRIN KOYOR DA YANDA ZAKI IYA HADA KAYAN NI'IMA A JIKINKI CIKIN SAUKI DOMIN GYARAN GIDAN AURENKI DA ZAMOWA FITILAR GIDANKI

*DAGA HAJJA CE 👈*


MASHAA ALLAH DUKA FA AKAN NAIRARKI *DUBU DAYA* KACAL ZAKI KASANCE ACIKIN GROUP DINNAN


_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_

2083371244

ZENITH BANK 

AISHA M. SALIS


*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼*

+447894142004


IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*

*** da Shaidar biya duk ta ciki


_GA MUTANENMU NA QASAR NIGER🇳🇪 ZAKU IYA TURA KUDINKU TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR👇🏼_

+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.

MUN GODE.


*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022*


_Wannan garabasar tamai rabo ce💃🏻💃🏻 sa kud'i kad'an ki debi hani'an😍😂_


*UMMASGHAR*