Kofar ajali Book 2

EPISODE 06

by @abdull10k

💀💀💀

*KOFAR AJALI*

_The Return_

```[Hard way and the only way]```

💀💀💀

_________________________


*Written*

Abdul Alhaji musa 10k

*phone no:*

***

_________________________



*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


*M. W. A*


```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```


_________________________



*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*




*FREE BOOK*💯✅

* EPISODE 0️⃣6️⃣*




"La kunga wata bishiya."

Haka hakullansu ta koma kan bishiyar, Samra ko rasa dama tayi inda Al-hussein kuma yace dasu....


"Finally kunga kwa sami abinda zaku taba, sannan mu huta."

bayan fada hakan suka soma tafiya but sadly sai Al-hussein ya yanki jiki ya fadi kasa ya kuma soma kakkarwa hade da birgima kamar mai farfadiya.


Bangaren Forzy ko tuno bayani game da mutanen boye da tayine ya saka ta dawo duniyar zahiri wato jibgarta da Tina ke yimata.. Tina kurkuren da tayi wajen Kawo goshita kusa da Forzy ne ya saka Forzy tayi anfani da wannan fadar data jiyo cikin wa'azin wajen kama goshin nata hadi da soma karanta *Ayatul kursiyu* wacce tasa Tina buga ihun tsiya tana kuma kokarin kwatar goshin nata daga hannun Forzy amma ta gagara yin hakan....


"Wani Ya tallafa mana." Yanayin da Mu'azz ya kasance ciki kenan yayinda yake goye da Atif a baya Aiko yana cikin wannan hali na tsoro da kuma fargaba sai ya fara wata magana cikin siririyar murya.


"Gaskiya ya kamata na gaggauta fitar damu daga wannan guri,tun kafin wannan abin ya juyo idanunsa kanmu."

Haka Mu'azz din ya furta yayinda kuma ya cike da tsoro dan kuwa karar da yake jiyowa daɗa karuwa take... yana cikin wannan yanayi sai ya jiyo wata sauti wacce wannan sautin ne ya sakashi tsayuwa guri guda kem,wannan sauti kuwa bana komi bane illa ɗigar ruwa dake sauka tana kuma bada kara sosai...Haka Mu'azz yayi saurin ajiye Atif shiko ya Mike izuwa bango na wannan daki ya aza kunne sa niyarsa shine ya jiyo inda wannan kara ke fitowa..


Haka ya zaga dukkan bangare hudu na wannan ɗaki ba tare da ya jiyo inda wannan sautin ke fitowa ba Hakan kuwa tayi matukar kashe masa jiki nan ya sake yanke shawarar komawa ga Atif Amma a hanyarsa ta zuwa sai ya taka wani guri da kafa a tsakiyar wannan ɗaki wacce ta bada kara wannan karan kuwa alama ce na da akwai wani abun a shunfuɗe a wannan gurin,haka kuwa tayi matukar bashi mamaki,sauri yayi wajen durkusawa hade da daura kunnen sa a kasan wannan guri.... yin hakan keda wuya ya jiyo wannan kara,hakan kuma ya tabbatar masa da akwai daki kasan wannan guri kuma itace kadai mafita da suke dashi a halin yanzu....


"Al-hussein!."

Cikin kara Samra ta furta hakan inda kuma ta zura Idanu cikin sauri Mufyda ta kasance tana duba lafiyar Muzzaffar sabida fadiwar da Al-hussein yayi sanadiyar fadiwarsa shima...


Cikin sauri Samra ta rusuna gefen Al-hussein da niyyar kai masa tallafi amma bayan ta kai hannu da niyyar taba jikinsa sai hannun nata ya nitse jikin Al-hussein din... Zura Idanu tayi hadi da furta cewa.


"Taya hakan zata faru kuma taya hakan ta kasance,How possible?."

Haka ta furta yayinda kuma ta tsaya kallon hannun nata data gagara taba jikin Al-hussein dashi.... Haka ta kurawa hannun ido yayinda ta daidaita hunnun da fuskanta,ihu ta sake hadi da ja da baya....


"Samra lafiya?."

Fadar Mufy dake gefen Muzzaffar kenan bayan ta jiyo karar da tayi,Samra ko saurin tayi wajen yi mata nuni izuwa jikin bishiyar da suke fuskanta,Mufyda ko kai Idanu tayi kan bishiyar sa'annan tace da ita


"Meye wai?."


"Simon na gani a tsaye jikin waccan bishiyar."

Dajiyo hakan ta sake ɗago Idanu izuwa gurin da take kokarin nuna mata sa'annan ta sake cewa da ita.


"Samra nidai banga komi ba,kuma a tunani na kawai gane gane ne kike domin ni ba wani Simon dana gani,kuma ma taya wanda ya mutu zai dawo?kina jina dama duba lafiyar Al-hussein kike da yafi,kinga ya kamata kiyi kokarin farfadar dashi,domin kuwa bazamu iyya daukar su muyi tafiya da su ba a wannan yanayin."

Haka Mufyda ta furta yayinda takai hannu da niyar taba jikin Al-hussein but sai taji an cabko hannun nata...


"Yadai Samra?."

Haka Mufyda ta furta bayan Samra ta rike mata Hannun.


"Muzzaffar!."

Haka Samra ta furta Itako Mufyda tayi saurin juyawa hadi da karasawa wajen sa ta soma yi masa fifita,Samra ko tayi wani batu a kasan ranta yayinda take yiwa Mufyda wani irin kallo.


"Ya zamanto mini dole na boye wannan daga gare ki, domin bana so naga tsoro da karaya a fuskar ki,ki gafirce ni Mufyda."

Bayan ta furta hakan sai ta sake juyo Idanu izuwa kan Mufyda dake yiwa Muzzaffar fifita.


AMRITA

"Shin cikin ku da wanda ya fahimci wani abin?."


"Not really gaskiya Ni babu abinda na fahimta."

Haka Anwar ya furta inda Amrita da kuma Harzad suma suka furta hakan....Shiru da Adam yayi ba tare da ya furta komi bane yasa suka juya ganinsu izuwa kansa suna kuma zaton ya fahimci wani abin,Shiko ganin yadda suke kallo nasa yasan suna expecting wani abun daga garesa.. nan saiya furta cewa


"What?."

Tambayar da yayi Kenan inda Amrita tayi sauri cewa dashi..


"A tunanin mu akwai abinda ka fahimta,shiya saka kayi shirun."


"A'a babu komi, babu abinda na fahimta."

Haka ya mayar mata da ansa inda suka juya suka kuma cigaba da tattaunawar nasu, Adam ko shiru yayi yana nazari yayinda yake wani batu cikin siririyar murya...


"Wannan alama da abinda take gwada mana saidai mun kasa fahimtar ko meye wannan, gaskiya ya kamata mu naimi sani akan wannan alama tun kan mu faɗa wata hadarin amma taya zamuyi hakan?.."

Bayan ya furta hakan sai yayi shiru na wasu dakiku kafin nan ya sake da cewa..


"Kodai Taswira take son gwada mana?."

bayan yakai ga furta hakan sai ya jiyo Muryar Hafsa na cewa.


"Ok Tunda duk cikin mu babu wanda ya fahimci komi ina ganin Jimawanmu Guri daya tsautsayine ya kamata mu cigaba da tafiya ko Allah yasa mu fahimci abinda wannan alama ke gwada mana a nan gaba."


"Maganar ki haka take Captain ya kamata mu kara gaba."

Fadar Harzad kenan inda Anwar dake zaune kan gwiwowinsa ya ɗago fuska hadi kuma da mikawa Harzad din abincin matafiya na laida sannan yace dashi.


"Haka ne kam gaskiya amma ga wannan ka ɗan taba domin mun dibi awannin ba tare da mun taba wani abun ba."


"Aww so Yanzu cin abinci ma za'ayi mana wariya kenan?,Anwar idan kana tunanin Harzad zaiji yunwa inaga mu,kowama zaiji yunwar,Why not kace da kowa Bismillah?."

Haka Amrita ta Kai Masa martani cikin salon wasa inda both Adam da kuma Hafsa suka fashe da dariya inda Adam yayi saurin cewa.


"don't be jealous Dear,Ni zan baki Abinci idan kina bukata."

Gajeriyar murmushin da Amrita tayi ne yasaka Hafsa cewa.


"Oh Guys Don't act lovey dovely here because ba double date ko kuma couples trip muke ba kunji."


Aiko da jiyo wannan batu,Amrita tsinke da muguwar dariya hadi Kuma da cewa.

"Aiko da daya daga cikin abubuwan nan da kika lissafa ne dako zaki kasance officially fifth wheel."

Haka dukkanin su suka fashe da dariya kafin ta sake cewa.


"Kai kuma da kake cewa zaka bani naka guzurin yaushe ka dauko,ko ka manta karawa kowannen mu nawin ɗawainiya da kai kayi ne?."


"Karta kaiga haka Amrita,muje ko?."

Haka Hafsa ta furta yayinda take gwada mata hanya da hannu, Amrita ko Bata sake cewa komi ba she just grab her bag ta karawa bujenta iska..

Haka suka kasance cikin salon taku ɗai ɗaya in Group suna kuma fira hadi da wasannin har suka kaiga bangon karshe na wannan hanya da suka dauka wanda yasa suka take biriki, Amrita daga Idanu tayi izuwa saman wannan guri domin kuwa wata gabjejiyar kofa sukayi arba dashi,jikin wannan kofa kuwa shuffan kawunan kwarangwal ne jiki yayinda kuma idanun wayennan kasusuwan suke bada wata haske jajir kamar garwashin wuta.


"Wannan kofar badai mutum ba."

Fadar Amrita Kennan inda Adam yace da ita


"Saidai basamuɗe ko,Amry?."


"Tayu ilahirin wannan guri ta kasance masarauta yayinda kuma akayi duk wannan domin a kayata guri,watakila wannan ne fada shiyasa kofan shigarta tasha banban da sauran."

Fadar hafsa Kennan inda Anwar ya karasa jikin kofar hadi da sa hannun jikin ta ya tura aiko cikin ikon Allah sai kofar ta bude inda dukkanin su suka cike da mamaki domin tunanin su shine kofar zatayi wuya su iyya bude ta,amma sai gashi da hannu daya Anwar ya bude sa.


Cikin wannan kofa dai babu abinda ake iyya hangowa dan zunzurutun duhu hakan yasa Amrita jujjuyawa ta hando sanduna masu ci da wuta dake rataye jikin bango wannan hanya da suka biyo ta ciki ta zaro guda biyu sannan ta mikawa hafsa daya ta shige gaba Hafsa kuma ta tsaya bayan tawagan suka tsunduma cikin wannan kofa aiko shigarsu kofar taja kanta ta rube bayan ta rufe kuwa wannan haske dake idanun kawunan kwarangwal dake jikin kofar ta dauke.

*Kutt wannan shine lokacin na farko danaga an shige kofa irin wannan ba tare da shawara ba."


Idan Muka gangara bangaren MU'AZZ kuwa bayan ya yaye shinfudar dake wannan guri ya tarar da wata ƴar kararramar kofa mai kama da bakin rijiya,dukda cewar idan kasa Idanu ciki zakaga tasha banban da rijiya domin tana da fadi sannan kuma tana da kusun ruwa hudu,tayi dai kama da dam amma kuma zurfin da kuma fadi na wannan daki madaidaici ne.


Mu'azz bayan ya gamawa wannan daki kallo sai ya fahimci da ruwa kwance a kasan wannan daki wanda wannan ruwan ne ke bada sautin,amma kuma bayan ya fahimci hakan ya kuma samar musu da mafita amma saiya gagara sani ta yadda zasuyi su sauko izuwa wannan dakin ba tare da sunji rauni ko raba hanya ba? Tambayan kenan domin idan Mu'azz ya tura Atif zuwa kasan wannan daki ba tare da yasan zurfin wannan ruwan ba zai iyya gindayar da rayuwan Atif din,idan kuma ya dira farko ina da tabbacin zasu raba hanya domin babu ta yadda za'ayi ya kuma komawa gare sa.


Abubuwan dake yi masa yawo a cikin kwakwalwa Kennan aiko bayan wasu dakiku sai ya yanke shawarar tura Atif first Amma bayan ya saka Atif ciki yayi masa rikon buga sai wata shawara ta fado masa aka na cewa ya goyesa a baya su faɗa tare,aiko yunkurin cire sa da yayi sai wata farar macijiya ƙatuwa mai kama da mesa ga katon kai da kuma tsawo tamkar bishiyar dabino ta fiddo kai cikin kasan wannan ruwa ta tashi sulululu Mu'azz na ganin hakan har macijiyar ta ciro Atif din daga hannun sa sannan ta sauka kasan wannan ruwa aiko kafin kace kobo tuni Mu'azz yayi tsalle ya dira cikin wannan ruwa, dirar sa keda wuya wannan marufi mai kama data rijiya tayi tsalle ta koma ta rufe dakin da Atif da Mu'azz suka shige cikin bayan nan wannan dadumar da aka shinfida a gurin ta dawo ta lullube hanyar aiko hakan sai tayi daidai da fadiwar wannan katanga dake dauke da mashin nan da Forzy ta harɓa, faruwan haka saiga Forzy da Tina sun baiyana cikin salon kokuwa yayinda Tina ke kokarin naima hanyan guduwa amma ta gagara samu.


Cikin wannan gajeriyar lokacin Tina ta jikata marar misaltuwa kuma abin mamaki da kuma farin cikin shine koda ta samu ta kwace goshin nata daga hannun Forzy kwata kwata bata kokarin kai farmaki naiman hanyan tsira take kawai amma kuma hakan bata yuwa domin ko tayi kokarin tashiwa sama ta fire daga zarar Forzy ta rike mata kafa shikenan sai kagan ta a kasa,haka tayi tashan bakar azaga daga hannun Forzy.


Hmm Gaskiya Allah da girma yake, domin duk lokacin da bawan sa ya shiga cikin damuwa kuma ya dauko wannan damuwar ya mika garesa babu shakka shi mai cire sa ne daga wannan damuwan, kamar kuma yadda ta faru da Forzy ahalin yanzu domin cikin kankanin lokaci taga anfani mika kai ga Allahu subhanahu wata'ala.


Tina cikin salo na shure shure ta kasance yayinda ta tashi sama tana kuma jujjuya a guri guda Idanuwan ta kuma sun juye sun dawo fari fal, Forzy ko kura mata Idanu tayi tana kallon ikon Allah aiko babu jimawa ta budi baki kamar wata mai hamma yin hakan da tayi sai wani koren abu mai kama da hayaki ya soma fitawa daga sassan jikin ta kama daga ƙafafuwan ta har izuwa kan, bayan wasu sa'o'i sai wannan haske mai kama da Koren hayaki ya kammala fita daga jikin ta nan sai gangar jikin nata ya faɗo inda Forzy taje a guje kan wannan gangar jikin,aiko hakan sai tayi daidai da warakan Muzzaffar domin wannan koren haske dake zazzagawa cikin jijiyoyin sa ta dauke sannan zafin jiki da kuma raɗadin duk tabi ta dauke tuni ya koma bacci.



AMRITA

Shigarsu cikin kofar kuwa sukayi arba da wata ƙatuwar mujiya wacce tasa Amrita sheka uban kara, wannan mujiya dai tayi matukar razana Amrita domin ta bayyana babu zato babu tsammani amma bayan Amrita ta fahimci mafita wannan aba take naima sai hankalinta ya kwanta....


Kara tafiya sukayi suna tsusa kai cikin wannan daki ba tare da sunyi shawarar tsayawa ba har sai da suka kai wani guri mai matukar duhun tsiya ga kuma ɗan karan zafi... Baki wuluk suke iyya gani da ga cikin idanun su wacce yasa Amrita cewa.


"Taya hasken suka dauke lokacin guda!."

Faɗar haka tayi hade da kai hannun ta na dama saman sanda da take rike dashi a hannu aiko bayan takai hannun nata saita Kwarma bagidajiyar ihu hadi da jefar da sandan ta kuma rike hannun nata na dama...


Abin mamakin shine wannan wuta dai tana kan ci saidai kuma duk cikin su babu mai iyya ganin hakan shin Makancewa ne suka yi ko kuwa....??

Idan muka duba bangaren wannan sanda da Amrita tayi jifa da ita kuwa fadiwarta gurin ya kama ci da wuta ta sanadiyyar wata bakar ruwa mai kamada Kwalta dake kwance a wannan guri..


Aiko wannan wuta ci take babu fashi yayinda ilahirin gurin ta dau haske ta yadda lungu da sako na wannan daki zaka iyya gani amma kuma su ganin hakan ta gagara su.


Inda Amrita ke tsaye kuma taku biyar gaban ta Harun ne ke tsaye yayinda wannan bakar ruwa ke gangarowa daga jikinsa fuskansa kuma babu annashuwa ko kada domin kuwa ya haɗe fuska..... TIRKASHI


Idan muka dawo baya da labarin kuwa zamuga Lokacin da Harun ya daura Hular daya tsinta cikin akwatin gawa kansa,nan da nan sai wata bakar hayaki ya mamaye jikinsa babu inda ake iyya gani daga cen wannan hayaki ta yaye saiga Harun yadawo wani abin na daban dukda cewar still shine Amma yanayin jikinsa da kuma shigarsa ta sauya ta dawo Baki Kirin yayinda Idanuwan sa suka dawo jajir hakan ya sakashi takawa izuwa kofar wannan dakin daya kasance ciki ya kurawa kofar Ido bayan nan yayi murmushi wacce wannan murmushi da kaganta kasan ta muguntace... Sa'annan yayi furucin cewa


"I'm Back." Abinda ya furta kenan bayan nan ya sake murmusawa,sannan ya haɗe fuska yayinda idanuwan sa suka kara haske aiko yin hakan keda wuya kofar ta bude kanta da kanta yadda kasan nakiya aka saka mata...


Haka harun din ya taka yayi inda wannan Gada ta karye cikin salon taku kasaita ya kai wannan guri da zuwan sa wannan guri wannan bakar ruwa ta soma yi masa matattakala yana kuma hayewa harya sauka kasan wannan guri! Wato inda yabar taron tawagar nasu a baya cen.


"What did I miss?."

Faɗar sa Kenan.