ZAGON KASA

3

by @khadeejacandy

DOCTOR HILAL POV. 


Bayan ya gama abunda yake ya shiga ya yi wanka, sannan ya fito falo ya yayi breakfast, sai kuma ya sake dawowa ya tashi Rafiq ya shiya sannan ya fice.


Kamar yadda ya saba gidan Hajiya ya nufa dan kai Rafiq ɗin, kasancewar Hajiya na da ƴan aiki da yawa masu kula da shi, wani lokacin ya kan aje shi a falo yace a shiga dashi gudun kwankwamin Hajiya, ko kuma ya aje mata shi ya yayi saurin barin gidan.

Sai dai yau bai yi sa'ah dan yana shiga ya ci karo da ita cikin falon tana karyawa, sun-sun-sun yayi ya gaisheta.


“Hajiya Barka da tashi”


“Barka dai mijin Hajiya, har ta tafi aikin ko? Bari dai kaji na faɗa maka na kusa barin rainon ɗan ku”


Maganar tayi masa zafi, sai dai babu yadda ya iya tun da mahaifiyarsa ce, kuma idan sabo ya saba da irin waɗannan kalaman daga bakin Hajiya da Alhaji, Murmushi yayi ya shafa kan sa.


“Hajiya haƙuri dai za'ayi, kisan ƴan rainon nan ba tsoron Allah suke ba”


“Kai ai kana tsoron Allah, tun da har kakr barin Matarka tana shiga cikin maza tana gogaiya, ace mace idan ta fita takwas na safe ba zata dawo ba sai cikin dare? Bata da lokacin mijinta balle na ƴaƴanta”


“Hajiya kin san aikin banki ne, kuma ita ce Manager ta banki dole ne ta riƙa bada lokacin can”


“Toh ta bar aiki mana dole ne? Amman ace mace ta bar Yaro ƙarami mai shan nono dan kawai ta je aiki”


Murmushi kawai yayi ya tashi yana shafa kai yana faɗin


“Bari na wuce”


Har ya kai ƙofa bai ji tace masa komai ba, sai ya juyo yana murmushi yace 


“Hajiya ni fa bana son fushin nan da kike da ni”


Wani kallo ta watsa masa


“Yaushe na ce ina fushi da kai?”


“Toh ai ban ji kince Allah ya tsare ba”


“Ko ban ce ba ai Allah tsare ka zai yi”


Wata irin dariya yayi, ya dawo yayi mata side hug 


“Allah ya bar mana ke Hajiya, i love you”


Dariya tayi tana faɗin 


“Jeka ka aikinka kamin Alhaji ya fito, kasan nashi faɗan babba ne”


Ficewa yayi yana dariya, zuciyarsa cike da shauƙin son mahaifiyarsa.

Uku da ƴan mintuna ya tashi aiki, sai da ya biya ya ɗauko Yaransa daga makaranta sannan ya dawo gida, sai da suka yi sallah sannan ya zuba musu abinci suka ci, wani lokacin lokacin ta kan tashi da wuri ta dafa musu abinci, wani lokacin kuma sai dai yayi musu takeaway. Bayan sun gama ci suka shirya suka tafi Islamiya.


Haka Doctor Hilal yake fama da irin wannan kaɗaicin kamar marar mata, gashi shi ba mutun ba ne mai son yawa fita, indai ba gurin aiki ba kullum zaka tararda shi a gida. 

  Matarsa kuma ota da gidan sai dare, babu yadda ya iya tunda babanta ya tsaya kai da fata akan lallai sai tayi aikin banki kasancewarta babbar ƴarsa, tana da ƙanne maza amman ya tsaya akanta dan kawai yaga ya kashe mata aure, tun asali ba Doctor Hilal ya so ta aura ba, shiyasa baya ƙaunar surikin nasa ko kaɗan, shi kuma baya jin zai iya rabuwa da ita saboda yana son matarsa ita kuma tana sonsa.


Ulfah da Ezzah na dawowa daga makarantar islamiya, suka ɗauko Homework ɗin su Doctor Hilal ya yi musu. 

Gimbiyar tasa kan bata dawo gida ba sai bayan Isha'i. Da sallama ta shigo amman ko inda take bai kalla ba balle har ya amsa mata sallamar, sai ta kwanto jikinta tana masa shagwaɓa


“Yanzu zan yi sallah ka kasa amsa min haba Dear”


“Yaran ki har sun gaji sun yi bachi, yau kwatakwata Rafiq bai sha nono ba, idan ni ina iya haƙuri na su kuma ba? Rashin ba su lokacin ki da kike shi zai sa ki kasa karantar wane hali ƴaranki suke ciki”


Bata yi mamakin kalamansa ba, daman yakan yi fushi da ita wani lokacin, kuma ta lura da hakan tun daga lokacin da samu promotion. Yana tashi tayi saurin sakin handbag ɗinta ta riƙo shi, sai ya ture hannunta


“Zaki iya fushi da ni?”


“A'a ni Wallahi ba zan iya” 


Ta faɗa a marairaice


“Toh ki koya daga yanzu, ta yadda za mu iya yin sati ba muyi magana da junan mu ba”


Rumgume shi tayi tana kukan shagwaɓa.


KALSOOM POV.


Ko da ta isa, Zainab na kwance falo tana bachi. Mayafinta ta aje ta ɗauki hijabi ta saka, ta bi gidan gyara tass, sannan ta ɗora musu girki.

  Haka ta kwana huɗu tana musu aiki, cikin rashin sakewa dan gani take kamar Zainab ɗin da Mijinta zasu raina ta, ta kan abuɓda bai dace ba amman bata magana, sai dai kwallafawa zuciyarta idan har ta je gidan sai ta faɗawa Mony irin zaman auren da Zainab keyi. A kwananta na huɗun ne Momy tayi ma Mijin Zainab magana ya kawo ƙanwarsa dan ta taya Zainab zama, Ranar da zata dawo ranar ce Zainab ta fara awo cikin, dan haka dole ita ce ta rakata bata je aiki ba a ranar, asibitin ta je aka yi ma Zainab komai, sannan suka dawo gida tare, da zimmar ita Zainab ɗin zata koma gidanta da yamma. 

 Bayan sun gama cin abinci rana ne, Kalsoom ta ɗauko labarin dan Momy ta ja mata kunne.


“Gaskiya Momy ayi ma Zainab faɗa, ya kamata ace ta canja rayuwa ta riƙa lurar da mijinta abunda ya dace da wanda bai dace ba, kinsan mijinki fa kece makarantarsa ta farko, gareki zai fara ɗaukar darasi”


Momy tace 


“Mi akayi?”


“Sam sam sam mijinta baya son alheri kuma baya son yan'uwansa suna zuwa gidan, sannan idan za ayi girki sai dai komai yaje ya siyo ƙire-ƙire kamar ba mai kuɗi ba, idan fa kika saba masa da wannan rayuwar ita zai riƙa miki ko can gaba”


Zainab ɗin ta haɗe rai sosai irin bata ji daɗin maganar ba.


“Nifa gaskiya bana son haka, daga zuwa jinya sai kuma kizo kina faɗar sirrin gida na”


“Ba ina faɗar sirrin gidanki bane, gaskiya nake faɗa miki”


“Toh ya kike son nayi masa? Ai halinsa ne idan yaga dama zai canja, Anty Kalsoom kefa ba auren nan kikayi ba balle kice kinsan yadda abun yake, ki bari har kiyi auren sannan ki faɗa min abunda da zan yi da wanda ba zan yi ba”


Saleena tayi farat tace 


“Haba Anty Zainab daga an faɗa miki gaskiya”

  

Zainab ɗin ta yatsene fuska.


“Wane irin gaskiya, so take na masa bala'i ne ya sake ni nazo na zauna tare da ku”


Momy ta kalli Kalsoom tace


“Ki daina irin haka ba kyau, koma minene ki kyale ta can ita ta sani, ba kyau kana faɗin sirrin ɗan'uwanka, ita fa rayuwar aure sai da haƙuri kuma ke baki yi ba balle ki gane haka, ku daina wannan maganar bana so”


Duk maganar nan da Momy take kan Kalsoom na ƙasa saboda idonta daya cika da ƙwalla, daga bisani ta tashi ta nufi ɗakinta tana hawaye. Saleena ma ta tashi ta bar musu gurin tana harar Anty Zainab.


NAMRA POV.


Ranar Assabar aka yi walimar kamar yadda aka tsara, Namra na cikin ɗalibai talatin da uku da suka haddace wani ɓangare na Alƙur'ane, da ban aka ware su aka karramasu, aka kira manyan mutane suka yi musu kyauta.

Maryam na cikin Ɗaliban da suka sauka bana, bayan walimar makaranta sai da Anty Amarya ta shirya nata walimar a gidan dan karrama ƴarta. 

  Ƴan'uwa da abokan arziki da dama sun samu halarta, cikin har da Anty Yasmin da Ya Uzair. Anci ansha nama kam kamar mayankansa, ga uban takeaway da Anty Amarya ta

shurya gwanin ban sha'awa.

Ana sallah la'asar Ya Uzair ya tashi zai wuce dan Yasmin tace ita kam sai dare. Anty Amarya ta ɗauko masa takeaway, ƙin karɓa yayi sai yace a bawa Namra ta kai masa. Ba dan ta so ba ta karɓa ta nufi gurin Motarta fuskarta babu annuri. Shi ko yana cikin motar ya hakince yana kallonta.


“Ba nace karki faɗa Yasmin ba? Shine har da buga mata waya ko?”


Ya faɗa bayan ya kai hannu ya karɓa.


“An faɗa mata ba, amman zan faɗa mata very soon dan ba zan bar ta ta cutu da kai ba, ba zai yiyu ka laƙa mata cutar HIV ba ina zaune ina kallo”


“Wai miyasa idonki ya buɗe haka? Alaƙar dake tsakanin ki da Yasmin ita ce tsakani ɓa da ke, kuma Yasmin matata ce babu ruwanki da lamarin mu”


“Idona ya buɗe ne tun daga lokacin dana fahimci kai fasiƙi ne, kuma wallahi sai na tona maka asiri, har nema da kayi sai na faɗa”


Wani dogon tsaki taja, ta juya ta nufi hanyar falo.

Da wani irin kallo ya bita yana jin kamar ya kamo ta ya shaƙure, ƙwafa yayi ya rufe motarsa.


Sai bayan sallah isha'i kowa ya watse, a lokacin ne Maryam da Namra suka samu damar duba kyaututukan da suka samu, Ba wanda suka fi murna kamar na Abbah da yayi musu kyautar Zinari, ihu suka riƙa yi kamar zasu tashi gidan dan murna, ba ma kamar Marya data daɗe tana roƙon Abbah ya sai mata zinari.

A tare suka nufi part ɗinsa dan yi masa godiya, sai suka tararda shi zaune tare da Hajiya barau fuskokinsu shimfiɗe da murmushi.

Guri suka samu suka zauna suna masa godiya, sai ya amsa da far'ah kamar ba shine yake fushi da Namra ba, ita kanta abun ya bata mamaki sai dai kuma ta jidaɗin hakan. 

Daf da zasu tashi ne Abbah ya kira sunan Namra


“Khadija”


“Na'am”


Da faɗuwar gaba ta amsa, ta dawo ta zauna tana jiran ta ji abunda zai ce. Sai da yayi gyaran murya sannan ya ce


“Kisan yadda nake da Uzair ko?”


“Na sani Abbah”


“Toh ya aiko Hajiya gata nan zaune ne yace yana son ƙara aure kuma ke yake so ya aura idan na amince masa”


Dakan shida-shida gabanta yayi saɓanin uku-uku dana kowa ke yi, da sauri ta kalli Abbah sai kuma ta sadda kanta ƙasa kamar wanda bata gane abunda suke faɗa ba. 

Can ƙasa-ƙasa ta tsinkayo muryar Hajiya tana cewa


“Uzair kam ko wani gurin yaje neman aure ai mu zamu shige masa gaba, balle yace yana son ƴar mu”


Abbah yayi murmushin jindaɗi yace


“Sosai kan, wallahi yaron nan yana da tarbiya, ga hankali” 


“Kuma ina fatar Khadija ba zaki bamu kunya ba, zamu yi matuƙar farinciki idan har kika amince da wannan auren” 


Cewar Hajiya Barau. Abbah ya kalli Namra fuskarsa babu alamun wasa yace


“Zan baki kwana uku kije kiyi shawara, but lemme remind and warning you for the last time, kar damar dana baki na shawar ki zo ki ce min ba ki amince da Uzair ba”


Bata iya cewa komai ba har na tsawon lokaci, sai kawai ta tashi tayi baya-baya ta ƙara baya baya tana dafa kai kamar wanda zata faɗi, har sai da Maryam ta riƙa ta suka fita.