ZAGON KASA

4

by @khadeejacandy

Da kuka Namra ta shiga part ɗin Anty Amarya, sai ta zube ƙasa, ta jefar da sarƙar da ke hannunta cikin parlor.

Hindatu da Aisha duk suka kalleta, Anty Amarya kuma ta nufo ta da sauri tana tambayar ba'asi. Maryam ce ta faɗa musu abunda ya faru, dan Namra kuka kawai take kamar wacce za'a cirewa, zaunawa Anty Amarya tayi kusa da ita, ta kai hannu ta riƙa fuskar Namra idonta cike da ƙwallah ta soma magana


“Namra mi yake damun ki ne? Saboda Uzair yace yana son ki shi ne kike wannan kuka? Ni kike sakawa a damuwa, ni kike son jama matsala, duk rashin biyayyar da zaki yi ma mahaifinki laifin a kaina yake, ƙaurin suna zaki yi Namra, matuƙar kika ce ba ki son Uzair, kuma ni za'a zaga, miyasa a duk lokacin da za'a miki maganar wani Namiji sai kiyi kamar ki kashe kan ki? Namra mi yake damunki? Ke ce babba a gareni ke ya kamata ace kina nunawa ƙannenki dai-dai da rashinsa, haba Namra haba, haba, haba”


A take ta ji kukanta ya yanke, sai ta share hawayenta ta unƙura ta tashi, ta nufi ɗakinta.

 Saman kujera ta zauna tana tunanin dalilin Uzair na faɗawa Abbah cewar yana son ya aure ta.


‘Miyasa yaje ya faɗa Abbah? Ko ma ya aure ba auren Allah da Annabi bane zai min, baya tunanin zumuncin mu da Anty Yasmin zai iya lalacewa? Ko dai wani abun ya ke nufi da ni ne?’


Tashi tayi ta nufi gurin gadonta tana cigaba da tunani


‘Tabbas idan har na ƙi yarda da auren shi ni za'a zaga, Abbah zai iya ɓatawa da ni, zan saka Umma cikin damuwa,


Wata ƙila yayi hakan ne dan na rufa masa asiri, ta yadda babu wanda zai san abunda yake aikatawa’


Saman gado ta zauna tana murmushin takaici


“Idan kasan wata, baka san wata ba Uzair, kaine zaka zanje maganar auren ka da kan ka, ko kuma na tona maka asiri Wallahi, ba zaka ci riba biyu a kai na ba”


Wayarta ta jayo ta shiga contact ɗinta ta nemo number Ya Uzair ta danna masa kira, ringing tayi har ta katse bai ɗauka ba, haka ta jera masa kira kusan tara amman be yi picking ba at the end sai mai ya kashe wayarsa.

Jin wayar a kashe ya matuƙar harzuƙa Namra sai kawai ta yanke shawarar kiran wayar Yasmin, dan tana tunanin ko saƙo ta tura masa ba zai karanta ba.


Yasmin na kwance jikin Mijin mijinta wayarta ta yi ƙara, sai da tayi kamar ba zata tashi sai kuma ta tashi a kasale ta nufi gun da wayar take.

 Da far'ah tayi picking tana mata zolayar data saba mata a duk lokacin data kira ta


“Ke miyasa zaki kira ni yanzu, mijina baya son wayar dare fa”


Namra bata jin wasar, sai kawai ta ce


“Anty Yasmin Ya Uzair na kusa da ke?”


“Yana nan manne da ni mana, ya akayi?”


“Ba shi wayar zanyi masa magana ne”


“Okay”


Ba tare da kwan-kwanton komai ba, ta nufi inda yake ta miƙa masa wayar.


“Gashi Namra na son magana da kai”


Gabansa ya faɗi, ya kusan five seconds yana kallon wayar kamin ya karɓa ya kara a kunne


“Ina jin ki”


Cikin fusata Namra ta soma magana


“Ai daman so nake ka ji ni kuma ka maida hankali akan abunda zan faɗa maka. Uzair ina jan kunnen akan kayi saurin janye maganar aure na, ko kuma na tona maka asiri, ka je ka faɗawa Abbah cewar ka janye zancen aure na ko kuma ni naje na faɗawa Abbah waye kai.

Uzair zan iya kiran family meeting dan kawai na tona maka asiri, kaga har Anty Yasmin sai ta gujeka, kuma ka kunyata a idon duniya”


Murmushi yayi mai sauti


“Amman mi yasa ba zaki iya haƙuri na kunna wayana ba Namra? Wannan wane irin matsuwa ne haka? Be kamata kina min haka ba, sai ki bari har komai ya kama sannan kowa ya sani”


Be tsaya jiran abunda zata ƙara cewa ba ya kashe wayar yana girgiza kai, sai ya kai hannu ya janyo Yasmin ta faɗo jikinsa ya shiga mammatsa breast ɗinta yana hura mata iska a kunne.


“Bloody me Namra tace maka ne?”


Sai da ya kai hannunsa saman wandonta na bachi sannan yace


“Idan na faɗa miki zaki fahimta? Zaki min Uzuri?”


“Uhm”


“Bloody Son Namra nake kuma yanzu haka har na yi ma Abbah magana akan hakan, sai dai ita tana jin kunyar ki”


Ɗauke wuta tayi na ƴan daƙiƙu, sannan ta zare hannunsa daga jikinta ta juyo ta kalleshi


“Kasa a duniya babu wasan dana tsana irin wannan, dan Allah ka daina bana so”


Dariya yayi ya gyara zamansa ta yadda zata iya fahimtar zancensa


“Wallahi kin ji na rantse miki ko? Abunda na fada miki gaskiya ne, ƙara aure zan yi kuma Namra zan aura”


Tashi tayi ta matsa baya tana masa wani kallo kamar ta ga dodo


“Karka haukata ni Uzair, karka raba min hankali gida biyu”


“Ai na rantse miki, kuma idan har baki yarda ba ki kira Hajiya Barau ki ji, dan ita na aika ta faɗawa Abbah”


Kasa magana tayi, sai kawai ta rufe bakinta tana kallon wani gurin kamar mai tunani, zuwa can kuma ta jiya ta bar ɗakin, shi kansa Uzair ɗin bata nata yake ba, kalaman Namra yake tunani da nemawa kansa mafita.

A falo Yasmin ta dawo ta zauna, tana tunanin kalaman Uzair da son tantance gaskiyarsa


‘Idan har ba da gaske yake ba, mi zai sa yayi min wannan furucin? Ni kaina ina zargin irin yadda Namra take kula Uzair’


Bitar kalaman zuciyarta kawai take, wani ɓangaren tana ganin kamar Namra ba zata iya mata haka ban, bayan ma ta san babu wanda Namra take so kamar Asim, ko kuma dai tana yaudarar take dan ta karkatar mata da hankali?

Har garin Allah ya waye Yasmin bata iya tsayar da ƙwaƙwaran dalilin da zai sa Namra ta iya cin amanar ta ba, kuma ta kasa gasgata cewar Uzair ba da gaske yake ba.

  Tun da tayi sallah asuba, ta koma saman gado ba dan bachin ba, sai dai kanta da ta ji yana sarawa, kuma bata jin haɗa ma Bloody ɗinta breakfast a yau, dan tun jiya ta warewa kanta ɗaki daban ta bar masa wacan ɗakin dan zuciyarta ta soma ɗasuwa da ƙiyayyarsa.

 Shi kuma be bi sawunta, dan yasan she need a space, ta yadda zata gasgata kalamansa kuma ta san da gaske yake, shi kanshi da ace ya biyeta da be samuwa kansa mafita ba.


Tun bakwai na safe yayi shirinsa na zuwa office, be damu da breakfast ba ya fito ya nufi ɗakin da Yasmin take, yana taɓa ƙofar ya ji ta kulle, be tsaya komai ba ya sauko downstairs ya buɗe Fridge ya ɗauko ruwa ya sha, sannan ya fice.


Ba tare da fargabar komai ba ya nufo gidan Abbah, tun da yayi parking ya sauya yanayinsa zuwa na damuwa da ɓacin ciki. 

Part ɗin Hajiya Barau ya fara shiga har wani sauke ajiyar zuciya yake. Murya ƙasa-ƙasa yayi sallama, Jikokinta suka amsa masa. Be yarda ya zauna ba dan be ga alamun Hajiya a falon ba.


“Ina Hajiya?”


Sai duk suka haɗa bakin gurin amsa masa


“Tana part ɗin Abbah”


Be tsaya komai ba ya juya ya nufi part ɗin Abbah yana ƙoƙarin ƙirƙiro ƙwalla. Ƙwanƙwasa ƙofar ya fara yi sai da aka amsa masa daga can ciki sannan ya tura ƙofar ya shiga da sallama.


Guri ya samu ya zauna ya natsu, yana sauko da kalaman da suke ƙwaƙwalwarsa zuwa bakinsa.

  Ya kusan minti biyar zaune sannan Hajiya Barau ta fito, tayi mamakin ganin Uzair da wannan safiyar, a zatonta ma ko cikin yaran gida ne suka zo karɓa wani abu hannun Abbah, zaunawa tayi tana kallon yadda damuwa ke shimfiɗe a fuskarsa ƙarara.


“Uzair lafiya kuwa?”


“Hajiya lafiya ba ƙalau ba”


“Toh mi ya faru?”


“Abbah yana nan?”


“Yana nan”


“Dan Allah ki kira min wata magana nake son mu yi”


Ba musu Hajiya ta tashi ta nufi ɗakin Abbah. Bata ɗauki wani dogon lokaci ba sai gata ta fito tare da shi. Guri Abbah ya samu ya zauna yana amsa gaisuwar da Uzair yake masa


“Lafiya ƙalau, lafiya dai kayi mana sammakon nan?”


Jimmm yayi kamin ya ɗago kai ya kalle Abbah ya ce


“Abbah ka gafarce ni, kuma ka fahimci dan Allah”


“Mi ya faru?”


“Abbah...”


Sai kuma yayi shiru, kamar mai jin nauyin furta, har sai da Abbah ya ce


“Am... Uzair ni mahaifinka ne, kuma ina tunanin kasan da hakan, so ka faɗa min damuwarka kawai let your voice out”


“Abbah akan maganar dana aiko Hajiya ne na neman auren Namra, shine nake son a yanje...”


Wani kallo Abbah yayi masa yana karantar yanayinsa.


“Daman kace kana son ta dan ka dawo daga baya kace ka janye?”


“Ko kaɗan babu hakan a raina Abbah, kawai na lura kamar bata so nane kamar akwai wanda take so”


Abbah ya kalli Hajiya.


“Ke kika faɗa masa akwai wanda take so?”


“A'a Wallahi mi zai sa nayi haka?”


Cewar Hajiya tana ƙoƙarin kare kanta. Sai Abbah ya kalli Uzair ya ce


“Waya faɗa maka haka?”


“Abbah jiya ta kira ni da dare, gaban Yasmin tana min kalamai da basu dace ba, babu irin zagin da bata min ba, sannan tayi min barazanar ɓata min suna matuƙar ban janye maganar aurena da ita ba, tace min Asim take so kuma shi zata aura”


Abbah yayi murmushi yana gingina kai.


“Kurciya ho, ai Khadija ba ita zata aurar da kanta ta ba, kar wannan ya ɗaga naka hankali, sai dai ina son ka tabbatar min da zancen ka, shin har yanzu kana nan akan kuɗirinka na aurenta?”


Ɗagowa yayi ya kalli Abbah ido cikin ido.


“Abbah da bana son ta babu abunda zai sa na nemi aurenta, idan har zata amince da aure zan fi kowa farinciki, sai dai idan bata so kar a cilastata gudun abunda zai je ya dawo”


Abbah ya tashi tsaye yana faɗin


“Kar ka damu Uzair, kawai kaje ka fara shawarar date ɗin da kake so a saka musu na aure”


Murmushi Uzair yayi ya sauka ɗaga kan kujera ya ɗuka yana yima Abbah godiya.


“Abbah na gode sosai Allah ya ƙara rufa asiri yaja nisan kwana”


Sannan ya kalli Hajiya yana faɗin


“Hajiya a taya ni godiya”


“Ba komai Uzair, ai kai ɗan mu ne”


Cewar Hajiya. Cikin farinciki yayi ma Abbah sallama. Uzair na ficewa Hajiya ta kalli Abbah tace


“Amman ita kam Namra mi yasa tayi hakaɓ”


Abbah be ce mata komai ba ya kaɓe rigarsa ya nufi part ɗin Anty Amarya a fuce.

Haka ya shiga falo babu ko sallama sai sunan Namra yake kira iya ƙarfinsa. Duk fitowa suka yi har Hindatu dake kitchen da Maryam da Aisha, Anty Amarya ta nufo shi tana tambayar lafiya.


Wata harara ya watsa ma Namra sai da ta haɗe yawu da ƙarfi tayi ƙasa da kanta.


“Ni zaki watsawa ƙasa a ido? Ni zaki tozarta? Ɗan ƴar'uwata zaki kira ki ciwa mutunci dan kawai yace yana son ki?”


Kasa magana tayi sai kawai ta fara kuka. Anty Amarya ta girgiza ta


“Namra kin kira shi ne?”


Kai ta ɗaga. Anty Amarya ta shiga salati. Cikin kuka Namra tace


“Wallahi bana son sa ne, na zan iya auren sa ba, haba Abbah da wane ido zan kalli Anty Yasmin idan na aure shi”


“Da idon da kika kalle ni kika ce min kina son Asim”


Abbah ya faɗa a fusace yana zare mata ido. Anty Amarya tace


“Amman Namra ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, Uzair ɗin ne kike faɗin ba zaki iya aurensa ba? Da me kika fishi toh?”


Karkato fuskarta tayi ta kalli Anty Amarya tana kuka


“Wallahi Uzair ba mutumen kirki bane, yace yana so na ne da wata manufa”


Anty Amarya ta nuna ta da yatsa


“Ke ai mutuniyar kirkice tun da Mahaifinki ya shimfiɗa miki tabarma, kika naɗe kika jefar”


“Wallahi Uzair ɗan homo ne Abbah, maza ya ke nema ƴan'uwansa”


Lokaci ɗaya ta ji ɗaukewar wutar cikin kanta, wanda hakan ya haddasa mata ganin waɗansu ƙananan taurari sakamakon wani irin mari da Abbah yayi mata, bata ankaro ba ya ƙara mata wani, be tsaya komai ba ya sake marinta, kamin kace kwabo sai ga jini ya gangaro ta hancinta kamar mai haɓo.