12
Kalsoom na fita tare da Salma, Rashida taja tsaki.
“Aifa an auro min iyani, ina ruwana da wata ƙawarki can”
Wayarta ta jawo ta danna ta nemu number Asmee ta danna mata kira.
“Ke ƴar gari ya akayi?”
“Toh gani nan dai, kin san yau ba'a zuwa aiki”
“Haka ne nima ina gida ai. Ina Amaryarki ance jiya an kawo miki amarya?”
“Tana nan yanzu ta fita raƙa ƙawarta”
“Hmm wai kisan yarinyar nan da taurin kai, babu irin zugar da da ban mata ba amman Wallahi ta tsaya kai da fata ita sai ta aure shi”
“Ai dole ta aure shi mana, babu mace da zata ga Hilal bata so shi ba balle har shi da kan sa yace yana son ta, kuma ance fa kwantai tayi babu mijin aure ba dole ta laƙe masa ba”
“Aiko dai ce ni na faɗa miki gurin aikin mu ɗaya da ita Wallahi, ƙanenta duk sun yi aure ita tana nan, Allah ya agaje ki dai kar tace zata fitar dake a gidan”
“Idan kuma bata fitar da ni ba ta karɓe min gida ba, dan naga yana ta wani rawar kai akanta”
“Ke ma ai kin sani duk mace data daɗe bata yi aure ba idan zata shiga a gidan ai sai ta shirya, kuma irin su ne suke ƙwace maza su tiyar da matar gida”
“Shiyasa fa nake tsoron auren nan na zamani”
“To ai laifin ki ne Rashida, shi kenan dan kana aiki sai miji yaje ya ɗauko maka wata banza da hujjar wai baka bashi lokacin ka! Ai wannan zancen banza ne, ni ɓa gani ina aikin ba amman mijina shiru kake ji ko ƙorafi bayayi”
Rashida tayi dariya tana mire baki
“Asmee kenan ke ai mijin ki be isa yace ze ƙara aure ba, wanda ko kallo mata ba yayi. Ke nima fa da nake matar abokinsa, sai da wani ƙwaƙƙwaran dalili yake min magana balle kuma har ya shiga office ɗina”
Asmee tayi dariyar jindaɗi, daman haka take son ji, kuma Rashida ta kan yawaita faɗa mata mijinta babu ruwanshi da mata, kasancewar gurin su ɗaya da Rashida.
“Kema ai idan kin tashi sai ki zo aka kama miki kan shi, wallahi ba dai wata ta gane kan gidan ki ba, dan kin san ba'a shedun Namiji anjima kaɗan zai canja miki, ballantana kin ga wannan Uwar tasa ba son ki take ba”
“Toh yanzu ya zamu yi kin san ai ba nida lokacin zama ma balle na fita”
“Ba ki da matsala da wannan, indai kin yarda kuɗin ki kawai zaki bada, ba sai kinje ba”
“Haka zai yi, amman ta san muna abota dake ?”
“Bata sani ba ai ban taɓa nuna mata ba, ce mata nayi mijinta ne abokin mijina kuma ni maƙociyarki ce, na nuna mata sam bana ma shiri dake”
“Hakan yayi kyau sai kiyi ta bugun cikinta”
Ƙyaƙyalewa Asmee tayi da dariya. Rashida tace
“Kin ga suna min warning wai kuɗina ya ƙare, ki shigo gobe ganin amaryar mu daman gobe monday bana gida”
“Toh Allah ya kai mu, na gode sai anjima”
Tana kashe wayar ta tashi ta nufi kitchen daɓ ɗora girkin rana.
DOC. HILAL POV
Tun da ya fita be dawo ba sai dare, da ledodi ya shigo gidan, sai da ya fara biyawa part ɗin Rashida ya kai mata nata, sannan ya shiga ɗakin Kalsoom. A bakin ƙofa ya tsaya ya ware mata hannyensa yana murmushi.
“Taso ki tarbe ni mana”
“Ka ƙaraso dai kawai tun da ka riga ka shigo”
Ta ƙarasa da murmushi tana mai sauke idonta daga gareshi. Ba dan yaso ba ya ƙarasa kusa da ita ya zauna, ya aje ledar gefe ya jata jikinsa ya rumgume yana shinshinar ƙamshin turarenta yana wani lumshe ido.
“Wannan ƙamshin na nawa ne?”
Hannunsa ya saka mata a riga, unƙurin tashi tayi sai yayi saurin walƙatowa ya danne ta, a kunne ya raɗa mata.
“Kin fa san daren yau nawa ne, jiya ma dan nasan kin gaji ne shiyasa na ƙyale ki”
Dariya tayi, cikin dabara ta zame jikinta daga nashi ta tashi tana faɗin.
“Bari na haɗa maka ruwan wanka”
Kai kawai ya ɗaga mata ya bi bayanta da kallo a zuciyarsa yana ayyana lalai yau sai ya shiga gonarsa.
Fita tayi daga ɗakinta ta shiga ɗakinsa ta haɗa masa ruwan wanka, sannan ta fito ta dawo ɗakinta ta same shi still yadda ta bar shi.
“Ga ruwan can na haɗa maka”
Kwantawa yayi saman gadon, yana wani nuna jikinsa ya mutu.
“Ni da zaki taimaka min ki ɗauke ni ki kai ni bathroom ɗin kiyi min wanka da na gode Wallahi”
Dariya ta suɓuce mata, sai tayi ƙoƙarin rufe bakinta.
“Na ɗauke ka kuma?”
“Yes wannan ɗan jikin da kike gani ba wani nauyi da ni ba, kina ɗagawa zaki ji nayi sama suuuu”
Kai ta girgiza still tana murmushi.
“Baka tashi wanka ba, bari na ɗauko maka abinci”
“Wait...”
Sai ta tsaya, har ya taso ya ƙaraso kusa da ita ta yadda zasu iya shaƙar numfashin junansu, ya kama hannayenta, yana kallon tsakiyar idonta yace
“Kalsoom I love you with all my heart, ina fatar auren ki ya zame min alheri kuma farinciki”
“Inshallah”
Ta faɗa tana kawar da fuskarta daga kiss ɗin da yake ƙoƙarin aika mata.
Hancinsa ya goga saman nata yana murmushi mai sauti.
“Wannan kunyar ta ki tana burge ni My Queen, shi yake nuna min lallai ke mace ce”
Ya tsunsa yasa cikin nata, sai ta zame jikinta tana dariya.
“Ruwanka yana hucewa”
Cikin sauri ya janyota, ya walƙato da ita cikinsa, ya riƙe ƙugunta kanshi saman wuyanta, ya tura ta.
“Aya muje ki taya ni”
Ƙofar ɗakinta ta riƙe suka riƙa ja-in-ja, shi yana son ta bishi ɗakinshi, ita kuma tana jin kunya, taya zata iya taya shi wanka, daga kawo ta jiya-jiya. Ganin ta kafe masa yasa yace
“Kema kije kiyi wanka yanzu, or else na taya ki idan na fito”
“Nayi wanka fa tun ɗazu”
“Wannan be min ba, a sake wani”
Kai ta ɗaga masa. Sannan ya saketa ya nufi ɗakinsa.
Wanka yayi ya feshe jikinsa da turare ya saka kayan bachi, sannan ya fito falo ya kashe kayan kallo ya nufi ɗakinta.
Zaune ya tararda ita tana cin naman daya shigo da shigo dashi.
“Kai....!”
Ba shiri ta zabura tana masa kallon tsoro. Ya ƙarasa shiga ɗakin.
“Waya ce ki min nama?”
“Ba ni na siyo ma ba?”
“Dana kawo na aje cewa nayi gashi na siyo miki? Aiko dai yau sai kin biya ni”
Dariya tayi ta ƙara ɗaukar wata ciɓyar kazar ta kai baki.
“Anƙi a biya ka ɗin sai kace wani yaro”
Kusa da ita ya zauna ya buɗe mata bakinshi.
“Toh ɗan sammin na ci, amman fa sai kin biya ni gaskiya”
Ledar kazar ta tura masa, sai ya girgiza mata kai
“Na bakin ki zaki ba ni”
Sai tayi saurin haɗewa tana zare ido. Fuskar shanu yayi ya riƙa kunnenta ya murɗa har sai da tayi ƴar ƙara
“Oh ouch that hurt”
“To dan nace ki sammin shine zaki cinye?”
“Ɗauko min abinci ne na ci, ba zan ma ci kazar ba”
Bayan sun gama cin abincin, sukayi shirin kwanciya, sai ya rigata hawa saman gadon ya kwanta yana kallon yadda take ƙoƙarin canja kayan jikinta zuwa na bachi. Ita kuma duk ta tsargu ganin yadda ya sakar mata, tasan jira yake tayi kuskuren saki wani ɓangare na jikinta ta kallah, hakan yasa ta nufi bathroom, sai kawai ta ji an riƙe ta.
“Wallahi ba zaki je bathroom saboda canja kaya ba, ni dodon ki ne hala?”
“To ka sakar min ido kana ta kallo na”
“An kalle ki, ke ya kika yi kika ga ina kallon ki?”
Ta ɓata rai kamar zata masa kuka
“Haba Doc”
“Haba Mrs Doc”
Zata ƙara magana, ya saka mata yatsunsa biyu na dama cikin baki immediately ya soma wasa da halshenta, ɗayan hannunsa kuma a jikinta yana murza fatarta. Ba yadda ta iya daman tasan ƙarshen wasan kenan, a dole ta lumshe ido yana karɓar saƙwannin da yake aika mata.
Da haka yayi nasarar kwantar da ita saman gado, ya ƙarasa cire mata kayan, sai ga komai nata bayyane, wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da haɗe yawun, ya shiga aikama mata da saƙwannin cikin salo na musamman. A take jikinta ya mutu sai dai duk abunda yake mata jikinta rawa yake abun ka da wace bata saba ba, daker ta iya buɗe idonta karaf ta sauke su cikin nasa, yadda taga launin idonsa ya riƙiɗe yasa gabanta faɗuwa, gashi kuma ta ganshi a yanayin da take ganin be kamata ta kalle shi a haka ba, sai tayi saurin maida idon nata ta kulle gam.
Hakan ya bashi damar riƙe kanta yana karanto addu'ar da Annabi ya koyar da mu kamin sexual intercourse.
“بِسْمِاللَّهِ، اللَّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْـتَنَا“
Bismillaah. Allaahumma jannibnash-Shaytaana, wa jannibish-Shaytaana maa razaqtanaa”
*** *** ***
Tun da asuba ya tashi ya haɗa ruwan wanka yayi sannan ya tashe ta, duk yadda yaso ya taimaka mata tayi wanka ƙin yarda tayi a dole ya ƙyaleta tayi da kanta sai zolayarta yake, wai jiya duk ta hajiyar da shi.
Ita kam kunyarsa ma take ji, ta gasa kanta sosai gurin wanka saboda yadda ƙasanta yake mata zafi da raɗaɗi, a tare suka yi sallah. Ita kam bata tsaya komai ba suna sallamewa ta hau gado sai bachi.
Bata farka ba sai tara har da tabi, a lokacin Hilal har ya gama haɗa musu breakfast dan yau Rashida da wuri ta fita ko gaisa bata bari suka yi ba, shi ya kai yara makaranta, sannan ya shigo ɗakin ya tashe ta.
NAMRA POV.
Ta daɗe a gurin tsaye tana tunanin abunda zata cewa Anty Amarya, ita kanta tana buƙatar karatun dan tana da yaƙinin zai taimaki rayuwarta, sai dai tana ganin hakan kamar ba me yiyu bane, tun da Asim yana nuna mata alamun baya son ta cigaba da karatun, gashi ma yace ba nan zasu zauna ba.
“Anty naga zan yi aure shiyasa na bar zancen karatu”
Duk kallonta suka yi suna mamakin irin sakarcin da take ƙoƙarin aikatawa.
“Namra kenan, ai karatu baya hana aure kuma aure baya hana karatu, karki yarda ki bar karatun ki”
“Anty yace ba a nan zamu zauna ba, a katsina zamu zauna”
“Katsina kuma?”
Maryam ta amsa, sai ta taso ta dawo kusa da Namta ta zauna.
“Dan Allah, karki yi haka Anty Namra taya zaki bishi zuwa katsina? Kibar karatun ki? Idan shi be san darajar nashi karatun ba ke ya kamata ace kin san naki, yanzu kina son ki zubar da duk shekarun da kikayi ki zubar da su?”
Anty Amarya ta riƙa hannunta.
“Namra karki yi ma kanki zaɓen tumun dare dan Allah, kar kije kiyi abunda zaki yi nadama”
Fashewa tayi da kuka
“Anty idan nace na zan aure shi zai ce naci amanarsa kuma kin ga yanzu har an yanka masa sadaki taya zan ce na fasa? Bayan kuma Abbah ya bani dama, baya da gurin aje ni a nan sai can, ɗan zuwan nan yayi ya samu aiki da zai iya taimakawa kansa da shi”
Anty Amarya ta dafe kanta tana sauke ajiyar zuciya. Zuwa can ta ɗago ta kalli Namra
“Ki masa magana idan ya aminta zan baku gidan da zaku zauna a nan garin, in yaso sai ku cigaba da karatun ku muga abunda Allah ze yi kuma”
Namra ta jidaɗin abunda Anty take ƙoƙarin mata, cikin murna ta share hawayenta tana mata godiya.
“Na gode sosai Anty, zan masa magana anjima inshallah”
“Ba komai Allah ya sanya alheri”
Daga haka Anty Amarya ta tashi ta nufi ɗakinta. Sai da ta shige sannan Namra ta kalli Maryam tace
“Dan Allah Maryam ina son na nemi taimakon ki”
“Na me?”
“Abu nake son ki ara min dan Allah”
“Minene faɗa min mana, kina abu kamar mai jin kunya na”
Sai da ta sosa gefen wuyanta, cikin jin nauyi da kunya tace
“Kuɗi naƙe son ki ara min, zan yi wani abu ne, kuma kuɗin da yake account ɗina be wuce dubu ɗari takwas ba”
“Kamar nawa kike so?”
“Zan samu 1.5 million?”
“Zaki samu kan, ai kin san budurwar Sadiq ba za'a rasa kuɗi a account ɗin ta ba, kullum Sadiq samin kuɗi yake min Wallahi”
Namra ta harareta
“Dan kuma nace ki ara min kuɗi ai ban ce ki min gori ba, muma na mu lokacin yana zuwa ”
Dariya Maryam tayi ta kai ma Namra dudu a baya.
“Dole nayi miki dariya mana, duk manyan garin nan wasu-wasu ne kawai basu nemi aurenki ba, amman kika ƙi kula kowa ke sai Asim, Allah yasa dai ba auren jari zai yi dake ba”
“Dan Allah ki daina zargin Asim mana haba, ni dai kiyi min transfer kuɗin gobe”
Tashi tayi ta bar mata falon cikin jin zafin furucin Maryam.
*** *** ***
Sai da aka kwana biyu sannan Asim ya samu damar zuwa gurin Namra, duk kuwa da damuwarsa da take da waya, sai yace mata wai neman kuɗi yake.
Guraren takwas da rabi na dare ya shigo gidan, bata ɗauki lokaci ba ta fito cikin hijabi. Sai da suka gaisa sannan ta koro masa da bayanin da gidan da Anty Amarya tace zata basu su zauna.
A maimakon ta ga jindaɗi a fuskarsa sai kawai ta ga ya canja fuska kamar ransa be so ba.
“Har yanzu ƴan gidan ku basu yarda dani ba Namra, har yanzu basa son aure na dake, a tunani zaki iya zama a duk inda zan aje ki, kwata-kwata bana da ra'ayin zama garin nan, a can nake da sana'ah”
“Idan mun zauna a nan zamu iya cigaba da karatun mu, kuma a nan ɗin ma ba zaka rasa sana'ar yi ba”
Miƙewa yayi tsaye irin ya fusata ɗin nan sosai.
“Ba zan zauna a nan ba, Katsina nake son zama, idan kuma baki da ra'ayin aure na kawai ki faɗa min”
Ita miƙewa tayi tsaye tana girgiza masa kai
“Abun be kai ga haka ba Asim, magana ce ta fahimtar juna, bana nufin ƙin aurenka ko kaɗan a cikin rai na”
Takardar dake hannunta ta miƙa masa tare da zinarin da Abbah ya bata ranar da aka musu walima.
“Kaje ka cire wannan kuɗin miliyan biyu ne da dubu ɗari uku, nasan ze isa kayi komai, na mai ƙaramin ƙarfi, ba sai kayi lefe mai yawa ba kala ashirin ma ya isa amman kasa me ɗan tsada dan Allah”
Kawar da kai yayi yaƙi karɓar kuɗin.
“Ni bana buƙatar wannan kuɗin Namra”
“Idan baka amsa ba kana da wata mafitar ne? Wallahi ba zan faɗawa kowa kai na ba ba, dan Allah ka karɓa Asim”
Sai da tayi ta masa magajiya har da kukanta sannan ya karɓa. A fuska yake nuna mata baya son karɓa amman a ransa farinciki ne fess shi da be taɓa mallakar dubu ɗari biyar nasa na kansa ba yau gashi ta miƙa masa million biyu har da wani abu.
Bayan sun yi sallama ta samu Anty Amarya a ɗakinta ta faɗa mata yadda suka yi da Asim, akan ƙin amincewar da yayi na zama garin, sai ta nuna mata wai har ƙanen Babansa ya bashi gida a can, kuma sana'ar da yake acan mai ƙarfi ce wai a ƙarƙashin kamfanin Dangote ya samu suka ɗauke shi.
Bayan Allah ya kyauta babu abunda Anty Amarya tace mata, sai ta taso jiki ba ƙwari ta dawo ɗakinta, zuciyarta a cunkushe, tunaninta a kulle, ya rasa abunda yake mata daɗi har wani jiri take jin yana ɗaukarta.
Baki har kunne Asim ya isa gida da kuɗin, tun daga yanayin sallamarsa Mama ta gani yana cikin farinciki. A ƙuryar ɗaki ya same ta tana zaune saman sallaya ya zauna kusa da ita yana murmushi.
Wani kallo tayi masa ta ɗauke kai, dan ita yanzu wani haushi ma yake bata ji take kamar tayi ta dukansa. Takardar kuɗin dake aljihunsa ya ciro ya aje mata gaban sallaya tare da zinarin da Namra ta bashi.
Ba a ɓoye zinari yake ba, ko yanzu ka tashi daga bachi aka nuna maka shi zaka iya gane shi, musamman irin wannan na Namra da aka siya daga Dubai. Gabanta ya faɗi, sai ta kalli sarƙar ta kalleshi kusan sau huɗu sannan ta ce
“Ina ka samo wannan sarƙar Ibrahim?”
Da dariya ya amsa mata
“Nawa ne”
“Na ka? Sata ka fara ne? Kamar fa zinari nake gani”
“Ba kama bace zinari ne, wannan kuma takardar kuɗi ce na miliyan biyu da dubu ɗari uku”
Ta daki ƙirji ta da ƙarfi.
“Miliyan biyu Ibrahim? Ina ka samo wannan kuɗi?”
Yanayin yadda tayi masa tambayar da ƙarfi, yasa ƙanensa shigowa ɗakin da gudu suna tambayar miya faru.
“Kuɗi na samo mana miliyan biyu da dubu ɗari uku, ga kuma sarƙar zinari”
Ƙanensa ya zauna kusa da shi da mugun mamaki.
“Ya Asim taya ka ɗauko?”
“Ba ɗaukowa nayi ba, Namra ta bani tace nayi hidima da su”
Duk tsalle suka saka suna murnar Yayansu ya samo kuɗi, sai Mama tayi saurin riƙe so
“Dan Allah ku rufa mana asiri, kar aji a dirar mana cikin daren nan”
Sai da suka natsu sannan ta kalli Asim
“Da gaske ita ta baka Ibrahim?”
“Wallahi ita ta bani yanzu nan, sai da ma nayi kamar ba zan karɓa ba, sannan na karɓa kuma tace ba zata faɗawa kowa ba”
Hannu Mama ta ɗaga sama.
“Al-hamdulillah Allah mun gode maka”
Ƙanensa yayi dariya yana faɗin
“Mama ke da baki son ta”
“Ai suma ba dan Allah zasu aura masa ita ba, kai kana ganin masu kuɗi kamar Alhaji Usman zai yarda Ƴarsa tayi aure irin gidan nan idan ba da wani dalilin ba”
Asim ya sauke ajiyar zuciya kana yace
“Wallahi haka kowa ke faɗa, ni kwata-kwata ma ta fitar min a rai, kawai dai zan aure ta saboda na fita kunyar masu ganin kamar ɓa zata iya auren mutun iri na ba”
Mama ta mere baki
“Wallahi ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba, da abun nan be faru ba ba zasu taɓa yarda kmsu barta ta aure ka ba, Amman wannan shi ake cewa gobarar ti-ti ko ba komai dole dai a kira ka da surukin Alhaji Usman kuma ko yaƙi ko ya so dole ne ya samo maka wata hanyar, kuma Allah kaɗai yasan ribar da zaka ci akan wannan auren”
“Haka abokaina ke faɗa, wai wata hanyar ce Allah yayi min”
“Sosai tun dai baka ci amanarta ita ta nemi ta ci taka ai dole Allah ya saka maka”
“Yanzu wannan kuɗin tace min aje a haɗa lefe dasu kuma da su zan kama gidan hayan da zamu zauna a katsina”
“Amman Ibrahim zaman ka a nan be fi ba? Karatun ka fa?”
“Can ɗin zai fi Mama, kin ga zan samu sana'ah mai ƙwari, kuma ƴan'uwanta basa zasu sa mana ido a zamantakewar mu ba, idan muna da shi aci idan babu a haƙura, babu wanda yasan mun ci ko ba mu ci ba”
“Haka ne, sana'ah ma yafi, kuma nan kan sai sun sa maka ido har dai wata yarinya na nan marar mutunci kai yarinyar nan bata da kunya kaga yadda ta riga min fitsara sai da ta tara min jama'ah a gida kamar nayi sata! A nan ma saurin kashe auren zasu yi”
“Ai Maryam bata da mutunci ni kaina ina haƙe da ita Wallahi”
Ƙanwarsa ta risino.
“Amman Ya zaka gyara mana gidan nan ko?”
“Gyara gida ai dole ne yanzu kan, bari dai na ciro kuɗin kawai komai ma za'ayi da yardar Allah”
Duk tsalle suka hau yi. Mama na musu dariya zuciyarta ta cike da farinciki.
*** *** ***
Shi da kansa yasa ta faɗawa Abbah cewar ƴan'uwan babansa zasu zo su kawo sadaki da aka yanka tare da lefe.
Sai da Abbah ya sake sa musu rana sannan Anty Amarya ta faɗaata ita kuma ta faɗa masa.
Da daren ranar ne Aisha take faɗawa Anty Amarya irin maganganun da ake tayi a makarantar ta islamiya.
Namra na zaune parlour tana jinsu, har suka yi maganganunsu suka gama bata ce uffan ba, shiru kawai take tana saurarensu ƙwaƙwalwarta na juyawa.
“Amman gaskiya Anty Namra karki bar karatun ki, idan har ba zai iya bari ki ƙare makarantar ba kawai ya haƙura da auren ki, ai ba akanki aka fara cin amanar ba, kuma wallahi duk mai maka son gaskiya dole ne yaso cigaban ka, amman gani nake kamar cin amanarki kawai zai yi”
Maganar Hindatu ce ta ɗago da hankalin Namra har tasa ta kalleta, sai dai bata iya tace musu komai ba ban da ruwan hawaye daya fito daga idonta.
Maryam ta tsire baki
“Ke dai kika sani, tun da baki da ra'ayin kan ki sai na Miji, kuma wallahi kina daf da yin nadama dan duk mace da bata da ra'ayin kanta wahala tana tare da ita, ina tunanin wani abu ne ya ƙire kuma sauran kaɗan ya faɗa miki, ko kuma a ɗaga auren har sai kin ƙarasa karatun ki”
Hannu Namra tasa ta share hawayenta ta tashi jiki ba ƙwari ta nufi ɗakinta tana wata tafiya kamar marar lakka.
Sai a lokacin Anty Amarya ta kalli Maryam tace
“Kar na sake jin kun mata wata magana akan auren nan, kuyi mata fatar alheri kawai, wannan maganganun ba zai haifar mata da komai ba sai baƙinciki, idan kuna mata wannan maganar damuwa zata mata yawa.
Gani nake yi abun kamar zai taɓa ƙwaƙwalwarta, dan Allah karku sake mata magana nan, ita kan ta a yanzu bata iya banbance fari da baƙi, bata daɗe da fita lamarin Uzair yanzu kuma ta faɗo wannan, ko wane ɗan'adam baya wuce ƙaddararsa, no matter how you try baka iya tsallake ƙaddararka,
Kuma ba musan alherin da yake cikin wannan auren ba”
Maryam ta tsire baki.
“Wallahi babu wani alheri a ciki, daga gani ma amanarta zai ci shiyasa yake son yaje can nesa da ita, kuma ya hanata karatun ta tun da shi be san muhimmancin karatun ba”
“Babu alheri a ciki kin san gaibu ne? Idan ma amanarta zai ci ai ita ba yarinya ba ce, idan bata iya karatun duniya ba ai sai duniyar ta karantar da ita, ai kowa ya ƙona rumbunsa, ya san inda toka ke kuɗi”
Daga haka Anty Amarya ta tashi ta nufi ɗakin Namra, zaune ta tararda ita tana aikin kuka. Kusa da ita Anty Amarya ta zauna ta jata jikinta tana rarrashinta.
“Ki riƙa sauraren zuciyarki Namra, Allah yasa wannan auren ya zame miki alheri, kada Allah ya bar ki da kanki Allah ya dafa miki lamarin ki”
Rumgume Anty Amarya Namra tayi sosai tana wani irin kuka mai taɓa zuciya. Anty Amarya bata san lokacin da nata hawayen suka zubo ba.
*** *** ***
Ranar Assabar suka kawo lefen, tarba ta musamman akayi musu, tun daga kan drinks har zuwa abubuwan ciye-ciye, Hajiya Barau ta soya musu kaji da wasu abubuwan. Sai dai wannan karon ba'a tara mutane kamar wacan ba, iya su ƴan gida ne kawai suka tarbi lefen.
Su basu ga wani abun a'zo a gani ba, a lefen tun da abun masu hannu da shuni idan ba an saka tufafin dubu ɗari, ɗari biyu ba su ba ƙimarsa suke gani ba. Sai dai Anty Amarya bata bari sun yi magana a gaban idonta ba, sai dai idan bata nan, a fuska kuma sai tasa suka nuna mata ai yayi ƙoƙari. Ita kanta tasan yaba mata ne kawai suke dan su ƙarfafa mata gwuiwa, amman ba dan sun ga darajar kayan ba.
Tun daga ranar da aka kawo mata lefen Namra tayi sallama da abinci, duk yadda aka tursasata sai tacw bata iya ci, sam bata ma jin sha'awar abincin balle ta ci. Iyakarta abu mai ruwa, ko kuma tea, gashi ta yi baƙi sosai kamar ba farar mace ba, ta rame kamar marar lafiya.
Ita kaɗai tasan abunda yake cin ta a zuciya, tana jin son Asim, wani ɓangaren kuma tana jin kamar ta fasa auren amman babu dama, ta kasa samawa kanta mafita. Haka take wuni a ɗaki kamar wata marainiya, duk wata hidima da ake na zuwa siyen kayan aurenta ba da ita ake yinsa ba.
Da dare Maryam ta samu Namra ɗakinta tana nuna mata pictures ɗin gadaje wato furniture ɗin da za a zuba mata.
“Kin ga wannan miliyan ɗaya da rabi, wannan kuma miliyan ɗaya da ɗari bakwai Abbah yace ki zaɓi wanda kike so”
Kasa zaɓa tayi, ita sam zuciyarta bata mata daɗi.
“Kawai ki zaɓa min wanda duk kika ga yayi miki”
“Amman Anty zaki yi event ko?”
“ Babu abunda zan yi Maryam wanda ya wuce walima”
Kallonta Maryam tayi kamar tace wani abu sai kuma wani tunanin ya zo mata, sai kawai tayi shiru ta shiga nuna mata kujeru.
Sai da suka kai ƙarshe sannan Namra ta riƙa hannunta cikin rashin kuzari tace
“Maryam dan Allah kar ku yi fushi da ni dan na aure Asim, ku yi miki kyakkyawar fahimta dan Allah”
“Babu wanda yake fushi dake, kuma kin yi ma Asim halacci iya halacci Allah yasa kar ya zamo butulu, ya riƙe ki Amana”
“Amin na gode”
Daga haka Maryam ta tashi ta bar mata ɗakin. Ita kuma ta gincira tana sauke ajiyar zuciya.
KALSOOM POV.
Yanzu kam ƙofar farinciki ta buɗe mata dai-dai gwargwado bata da wata matsala a gidan mijinta.
Tun da safe zata tashi ta haɗa yara breakfast, tayi musu shirin makaranta, sannan ta tashi Doc. Sai dai yanzu kusan wata ɗaya kenan, Rashida babu ruwanta da Kalsoom duk kuwa da kasancewar yaranta ne take yima hidima, da ranar girkinta da ba girkin ta ba duk Kalsoom ce take girki, sai dai da dare ne zaka banbance ba ita ke da girki ba, kasancewar kwana biyu-biyu yake musu.
Doc. Hilal kam ji yake kamar ya ɗauki Kalsoom ya haɗeye, saboda yadda take masa komai daki-daki a gidansa, yana jindaɗin yadda take tashi tun da asuba tayi aiki, daman maza basa son raguwar mace. Gashi tana nunawa yaransa so hakan ba ƙaramin daɗi yake masa ba. Sai dai a ɗayan ɓangaren yadda Rashida taƙi ta sake Kalsoom abun na sosa masa rai, dan duk wahalar da zatayi da yaran Rashida ba zata iya ce nata sannu ba, balle na gode, ko kuma ta nuna mata jindaɗinta a kansu.
Yau ma kamar kullum bayan ta gama sallamar yara, sun karya sai ta raka shi bathroom suka yi wanka tare.
Ita ta shafa mishi mai ta murza masa turare, jaka yazo ya zauna ta saka mishi tufafi ko kunya. Har ta ɗora masa hula akai bakinta yake kallon.
“Perfect everything clear”
Ta faɗa tana ƙara gyara masa girarsa. Bakinsa ya miƙa mata.
“Na siye wannan lips ɗin”
“Yau ba za'a sai da maka ba”
Lumshe mata ido yayi, ya langaɓar da kai
“Haba Ma'am... Pity me”
Sai taja kumatunsa.
“No Toy”
Miƙewa tayi tsaye. Ganin da gaske ba zata masa kiss ɗin ba yasa yayi hanzarin fisgota ya jefar saman gado.
“Idan ban samu kiss ba toh zan nemi abunda ya fi kiss ɗin”
Hannu ta ɗaga masa
“Tsaya Wallahi zan baka, amman kiss kawai”
“Naji kiss kawai aya tashi”
Ya faɗa yana nuna mata bakinshi. Kamin ta miƙe tsaye ya buɗe durowa ya ɗauki sweet candy yasa bakinsa. Riƙe ta yayi gam kamar wanda zata tsire masa sai da ta tsosar masa bakin da kyau da kyau sannan ya sake ta bayan ya mayar mata da sweet ɗin cikin bakinta.
Sai ya zaunar da ita.
“It my turn”
Mai ya ɗauka ya fara shafa mata, sannan ya shafa mata hoda, sai janbaki. Sannan ya ɗauki underwears ya saka mata, ya ɗora mata da gown, haka ya mundula mata ɗankwali saman kai sai dariya yake.
Bayan sun gama, ta rako shi har gurin mota, sai da yayi mata side hug sannan ya shiga motar tana masa addu'ah.
“Allah ya haɗa ka da halak komai ƙanƙantar ta, ya nisanta ka da haram komai yawanta”
“Amin I Love You Dude”
“I love you more”
Bayan ya wuce ta dawo falon ta ƙarasa gyarasa. Guraren goma da rabi Rafiq ya tashi, sai tayi masa wanka ta bashi abincin sannan ta ɗauko shi suka dawo falon suka zauna.
Ƙonƙosa ƙofar data ji anyi ne ya ɗago da ita ɗaga kallon MBC2 da take.
“Waye?”
Daga inda take zaune ta tambaya.
“Nice Amarya”
Jin muryar Asmee yasa ta tashi ta buɗe mata ƙofar fuskarta a sake.
“Amarya gida sai ƙamshi yake”
Ta faɗa bayan ta zauna. Kalsoom tayi dariya
“Daman gidan mace a gidan ƙamshi ne, ya aikin ya kwana biyu?”
“Lafiya ƙalau, kina nan kina fama da rainon yara ko?”
Murmushi Kalsoom tayi.
“Asmee ke nan, ai yara na kowa ne, kuma ƴaƴan Hilal ai ƴaƴana”
Asmee ta wani gyara zama tana tsire baki.
“Ke ni dan Allah raba ni da abun haushi, ke kika zama ni nake miki kishi”
“Asmee kenan nikan na so naga kishiyarki”
Kalsoom ta faɗa tana dariya. Da sauri Asmee ta matsa
“A'a Wallahi mugun abin ki ya biki, ke daman Allah be raba bakin ki da tsaɓo ba, bari ma na bar miki gidan daman wani haki ne na siya nace bari na sam miki”
Ta faɗa tana fiddo wani baƙin abu a ƴar ƙaramar roba.
“Kin ganshi ɗan matse ne mai kyau Wallahi, sai kin ban labari, nasan ai kayan amarcin ki sun ƙare yanzu ai”
“Wallahi sun ƙare, duk na kyautar da su ni ba son irin abubuwan nan nake ba, nafi son masu zaƙi ko kuma ƴan fruits haka, kin san suma suna gyara jiki”
“Amman gaskiya kiyi amfani da wannan dan Wallahi yana da kyau sosai”
“To na gode zan gwada”
Bata daɗe ba ta tashi ta fita, har gurin gate Kalsoom ta rakata, sannan ta dawo gida.
Tun kamin Asmee ta isa gida ta buga Rashida tana labarta mata cewar saƙonta ya samu isa yadda ake so. Daga ɗayan ɓangare Rashida tayi murmushi tayi mata godiya sannan suka yi sallama.
Tana aje wayar ta tsire baki. Mutumen dake zaune saman wata huge chair ya kalle a ƙasaice yace
“Wacece?”
“Matar ka ce”
Yayi saurin ɗagowa
“Miya kai ta gidan ki? Bayan baki nan?”
“Ai abokiyar zama na nan, gurinta taje”
Ɗan murmushi yayi
“Mata Allah be raba ku da kicihiba”
Dariya tayi ta ɗauki documents ɗin da suke saman teburinsa, ta nufi ƙofa.
“Ki kai min waɗancan documents ɗin a guesthouse”
Ya faɗa yana kallon mazaunanta dake cikin suit.
“Gaskiya yau ba zan samu shiga ba da wuri zan koma gida”
Daf da zata fice ta amsa masa, sannan ta fice.
___________________________________________
Assalamu alaikum Habibaties💖. To all those that are asking about Amira and Uzair labarinsu zai zo nan gaba, so please wait patiently. And masu cewa kaza ya kamata ayi ba kaza ba, blah blah blah, yen yen yen, this and that, na gode duka amman please ku bar tafiyar nan ta tafi a yadda na tsara ta. Ba ku san dalilin da yasa Yasmeen ta fito a Barrister ba, ba ku san miyasa asiri ya koma kam Amira ba instead of Uzair, so please judge less.
Na gode Sosai Jazakallahu Khairan 🌺
I Love You All Fisabilliah 😘