14
Yau kusan two weeks kenan, babu gara babu labarinta. Sosai da sosai hakan ya dami Asim, sai dai ya ɓoye maitarsa, be yarda ya nuna mata komai ba. Ya kan yi ƙoƙarin siyo duk wani abu na buƙata wanda za'aci ko ayi amfani da shi a gidan. Sai dai duk tsawon wannan satin biyu Namra a wahale tayi su dan kullum yana manne da ita, bata da wani dogon hutu indai yana gida.
Bayan sun gama cin abinci ya aje Spoon ɗin hannunsa yana sauke ajiyar zuciya. Kallonsa tayi dan ta lura da yadda yanayinsa ya canja.
“Lafiya dai?”
Ya ɗan kalleta kaɗan ya ɗauke kai yana ɗan murmushi, fuskarsa na nuna alamun damuwa.
“Ba komai”
“Haba Hubby ai ni da kai yanzu mun zama ɗaya, ya kamata ace damuwarka ta zama nawa, babu wani ɓoye-ɓoye”
“Wato bana son nayi maganar ne kiyi mata wani ɗauka, wata ƙila ba zaki fahimce ni ba”
“Idan ban fahimce ka, wa kake tunanin zai fahimce ka? A tunanin ka idan ka ɓoye min damuwarka zan jidaɗi ne?”
Tashi yayi daga ginciren da yake ya gyara zamansa yana tsara kalamanta, ta yadda zasu zaunu a ƙwaƙwalwarta.
“Namra ina gudun ki shiga cikin irin rayuwar ta ne, kin min abubuwa da yawa, zuciyana bata da muradi illah na kyautata miki. A kullum tunani ina zan zam sama mana mafita muyi rayuwar jindaɗi, sai dai gaskiya I'm scared”
Sai yayi shiru be ƙarasa ba yana auna yadda kalamansa zasu kamata.
Ita kuma sai ta tambaya zuciyarta cike da shauƙin kalaman nasa.
“Scared of what?”
“Namra ba ni da wani aiki ko sana'ah mai ƙwari da zan iya riƙe ki da ita, ƴan kuɗi dana ke tunanin zasu ishe ni na kama sana'ah da su na kama hanayar gidan nan 50,0000 per year dan kawai na burge ƴan'uwanki da ke kan ki, nasan ke kika bada kuɗin amman naso nayi saving ɗin su dan mu samu wata madafa, sauran da suka rage min kuma gasu muna cin abinci da su kamin Abbah ya yi mana aike”
Ta ɗan ji babu daɗi da kalmar ta fito daga bakinsa, kusan kullum da tunanin take kwana take tashi, na rashin garar da Abbah yayi mata, a tunaninta hakan da Abbah yayi mata ya mata ne dan ta auri Asim, tun da ba haka yake ma sauran ƴaƴansa ba, ita kam ya kasa sai mata girma.
Can ƙasa-ƙasa ta fara magana, zuciyarta cike da rauni.
“Abbah ba zai aiko mana komai ba, da zai aiko da yanzu ya kawo mana ai, sai dai mu yi tunanin wata mafitar”
Sosai da sosai gabansa ya faɗi, kalamanta sun haddasa masa ciwon kai, har zufa na ƙoƙarin karyo masa. Janta yayi jikinsa ya rumgume.
“Toh Allah yayi mana mafita, ai Abbah ya gama mana komai tun da ya yarda na aure ki, Allah dai ya ƙara masa nisan kwana da ƙyaƙƙyawar rayuwa”
“Ameen”
Ta faɗa tana shafa rigarsa.
“Amman yanzu wace sana'ah kake gani yafi? Nifa da zaka bi shawarana da ka koma makaranta, ka cigaba da karatun ka”
“Bana son karatun nan a yanzu kwata-kwata ya fita rai na, na fi son sana'ar da zata riƙa kawo min ƙuɗi sosai ta yadda zan riƙa kyautatawa matana”
“Wace sana'ah zaka yi?”
“Wai da naso na kama wani shago dake nan Uguru Plaza na zuba atamfa haka da lace da shaddodi na gwada na gani, na ma yi maganar shagon dan akwai wani abokina daya ce babansa yana ba da rancen kuɗi ko nawa kake so kayi sana'ah kuna raba riba, toh shine nake son na masa magana”
Ɗagowa tayi ta kalleshi, damuwa ƙarara a fuskarta.
“Kamar nawa zaka kashe?”
“Zai kai 1.5 million, har kuɗin hayar shagon, indai ana son a saka kaya masu kyau”
“Tau me zai hana na siyar da motana sai na...”
Bata ƙarasa ba yaja wani dogon tsaki, ya tureta daga jikinsa ya tashi ya nufi ɗakin. Da sauri ta rufa masa baya tana karantar yadda ransa ya ɓace nan take.
“Kuɗin ba zasu iya ba ne?”
Ta tambaya lokacin data kunna kai cikin ɗakin. Sai ya juyo kamar a fusace yace
“Ban taɓa sanin baki da wayo da hankali ba Namra sai yau, da badan na sanki ba da sai nace shaye-shaye kike yi, taya zaki ce a siyar da motarki saboda na kama sana'ah? So kike zargin da mutane suke min ya tabbata gaskiya ko? Daman ance na auri ki ne dan dukiyarki, dan Allah dan Annabi ki taimaka wajen shanye raɗa da riƙe amanarki”
Sai yanzu hankalinta ya kwanta, data ji dalilin fushi nasa. Murmushi tayi tasa hannyenta ta laƙamo wuyansa tana kallon hawayen da suka cika masa ido.
“Bana nufi komai sai alheri, kai kan ka yanzu ai abun kunya ne kaje wani guri neman rance bayan ni ina da hanyar samo maka wannan kuɗin. Zai zame kama abun magana ace kana angonka kaje wani guri rancen kuɗin da zaka yi sana'ah, kuma ni Wallahi ba zan faɗawa kowa ba.
Nasan motar zata yi 2.5 ko ma 2 million, kaga idan ka kama sana'ah sauran sai mu siye abinci da sauran kayan gida, ni kai na ina buƙatar ƙuɗi a yanzu”
Kai ya girgiza mata ya cire hannayenta daga wuyansa.
“A'a kima daina wannan maganar dan Allah, kin san ko kuɗin da kika bani na haɗa lefe sai da nayi baƙinciki karɓar su? Nayi nadama sosai da zuciyata ta yaudareni na karɓi kuɗin”
“Amman ai baka da wata mafita Asim, idan ban baka kuɗin ba a ina zaka samo? Wannan ma ai dole ka karɓa”
“Da baki bani ba, da dole zan nemo mafita a duk inda take, ko wane hali zan iya shiga dan na samo kuɗin aurenki”
“Wannan ma ni zan taimaka maka da yardar Allah, kawai ka amince da buƙatata dan Allah, ba ma acan za'a siyar ba, kawai zan yi ma Anty waya nace zaka zo ka karɓa min motana, idan an zo nan sai a siyar Asiri rufe”
Kai ya girgiza mata, irin shi fa sam ba zai karɓa ba, ya nufi ƙofa yana wani huci kamar gaske.
Da kallo ta bishi tana murmushi har ya fice, zuciyarta cike da shauƙin son Asim, tana jin lallai tayi dacen miji.
Tun da yasa kai ya fita be dawo ba sai dare, da daren ma ƙin sake matayi yayi har sai ya kawo mata buƙatarsa, ita kuma ta nuna ba zata amince ba har sai ya amince da nata buƙatar.
Daker ya amince, a bisa sharaɗin zai biyata idan Allah ya hore musu.
A cikin dare ta kira wayar Anty Amarya, bayan sum gaisa tace mata Asim zai zo ya karɓa mata motarta.
“Aiko jiya jiya nan Aisha take cewa wai kin manta motarki, na bar mata key ɗin kawai”
Dariya Namra tayi
“Lallai Aisha ita uwar wayo ko? Gobe ma zai zo ya karɓa min abuna, ai ban mutu ba balle su ci gado, su ƴan gaban goshin Abbah ai zai iya siya musu mota a take”
“Kema ai ƴar gaban goshinsa ce, kawai halin ki ne da nasa baku jitu ba, kin ga yanzu kuma yasa Maryam gaba, wai ta fitar da miji yayi mata aure tun be mutu ba, ita kuma sai murna take abun nema ya samu”
“Hahaha Allah ya kyauta Maryam babu ko kunya, fitsararriyar yarinya”
“Uhm Maryam Allah dai ya kyauta, amman ita rayuwarta daban yake. Kuna dai lafiya ko?”
“Lafiya ƙalau muke”
“Yanzu Namra shikenan kin bar maganar karatun nan na ki? Ga Maryam yanzu sauran wata shida su ƙare, kowa tambayar karatun ki yake”
Shiru tayi tana tunanin ta yadda zata amsa ma Anty Amarya, har ga Allah ita ma tana son karatun sai dai babu yadda ta iya tun da ta nisanta kanta da shi.
“Nima zan cigaba nan gaba Inshallah”
“Taw Allah ya kyauta”
“Amin, Anty a haɗo masa da dukan takarɗuna da suke ɗakina”
“To akwai sauran kayan ki ma duk za a bashi”
“Na gode sai da safe Anty”
“Allah ya tashe mu lafiya”
Daga haka suka yi sallama. Duk sai ta ji ranta ya sosu da maganar Anty Amarya. Shi kansa ya lura da yanayinta. Sai ya matsa daf da ita yaja ta jikinsa ya rumgume.
“Allah ya bani ikon faranta miki Namra”
“Amin. Amman ba kai zaka ɗauko motar ka biyo hanya da ita ba ko?”
“Saboda me?”
“Naga driving zuwa wani gari ne sai ƙwararre”
Wani ɗan mirmushi yayi yana nuna mata maganarta ta taɓa zuciyarsa.
“Kin ɗauke ni talaka ko Namra? Ai shi driving ba dole sai ɗan masu kuɗi ba, talakawa ma suna yi dan neman na abinci”
Da sauri ta ɗaga daga jikinsa tana girgiza masa kai.
“Ko kaɗan ba haka nake nufi ba, kaga nima ai na iya tuƙi amman bana iya zuwa wani gari, bana nuna komai Wallahi”
Murmushi ya sake mata irin by force ɗin nan, dan har ga Allah maganarta ta sosa ransa a tunaninsa so take ta nuna masa shi ɗin ba ɗan kowa bane. Yasa hannayensa cikin nata.
“Is okay i understand”
“Thank you”
Ta amsa tana mai son kawar da damuwarsa, tare da ƙoƙarin karɓar saƙonsa.
*** *** ***
Washe gari tun da sayin safiya Asim ya kama hanyar sokoto gurin zuwa karɓar mota, duk yadda Namra taso ya tsaya ya karya sai yaƙi wai kamin ta gama rana yayi shi kuma so yake yayi saurin dawowa, ɗan baya jin zai kwana can sai dai yayi tafiyar dare.
Tafiyar da yayi ta samu damar fita ita da wata ƴar yarinya, suka leƙa maƙota, daman tun zuwanta suna ta shigowa amman ita bata samu shiga nasu gidanjen ba.
Bata daɗe sosai ba ta dawo. Ta ɗora girkin rana, sai daf da zata gama sannan ta ɗauko wayarta ta kira line Asim. Da far'ah ya ɗaga wayar a lokacin yana ɗakin Mama.
“Hubby ina ta trying line ka ban samu, kun isa lafiya?”
“Lafiya ƙalau tun ɗazu na isa har na karɓo motar ma, ina gida ne gurin Mama da mun gama gaisawa zan kamo hanya”
“Toh Allah ya tsare, bani Nama mu gaisa”
Miƙa mata wayar yayi yana faɗin.
“Ga Namra zaku gaisa”
Sai ta karɓa baki har kunne
“Ƴata”
“Na'am Mama an wuni lafiya?”
“Lafiya ƙalau Allah yayi miki albarka, kina lafiya ko?”
“Lafiya ƙalau Al-hamdulillah, to Mashallahu Allah ya taimaka”
“Amin Mama na gode”
Sai ta miƙa masa wayar, suka yi sallama.
“Ai Wallahi ita yarinyar ma tana da abun albarka”
Cewar Mama cike da jindaɗi har cikin kai.
“To Mama idan bata min wa zai min? Ubanta be kawo min gara ba ai dole ta nema mana wata mafita, tun da bata son mu wahala”
“Shima ai ƙeta ce ta ganin iyakar mai rai, ai yasan baka da aikin yi, kuma ko ƴar matsiya aka auro sai an mata gara balle ƴar mai kuɗi”
“In ma wahala ce ai ni da ƴarsa zamu yi ta, kuma idan shi be bani ba dole ƴarsa ta ba ni”
“Uhm Wallahi mutumen be da zuciyar musulunci sam. Ai Allah dai ya yi maka hanya kaima kayi kuɗi susan Allah ne yake badawa ba su ba”
“Ai Wallahi duk nayi kuɗi sai na bashi mamaki, dan sai na auro ƴar da ubanta yafi shi kuɗi, naga ƙaryar iskanci”
“Ai shiyasa bana son ka yi wasa da sana'ar nan da zaka yi, kuma dashen nan ba fasa shi za'ayi ba, dan shima idan an ɗauka ai duk cigaba ne ko shago sai a buɗawa ƙanenka a nan, gashi zubi biyu kawai akayi, idan muka sa wasa sai su cire mu wasu su hau na mu”
“Amman sai naga kamar dubu ɗari uku na baki fa?”
“Eh sai na zuba ɗari biyu ba, kasan ai dubu ɗari-ɗari ne, sauran ɗari ɗin ai sune akayi hidima da su. Yanzu dai ka siyar da motar sai ka kawo ko dubu ɗari biyar ne a zuba, yadda za mu daɗi ba a zuba ba, kamin lokacin ma kaga sana'ar naka ya karɓu”
“To yanzu ai dana koma gobe zan kai Motar kasuwa, dan har na yi magana da mai shagon yace min ɗari da hansin zai ba ni hayar shagon, ina son na zuba lace da atamfofi da jakunkuna dan gurin babu shago ko ɗaya a gurin”
“To Allah ya taimaka, ga ƙanenka shima inda hali ai sai a biya masa ƙuɗin makaranta. Ka tashi ka kama hanya dai kar kayi dare”
Miƙewa yayi tsaye yana faɗin.
“Komai za'ayi Mama, har abinci za a siye muku mai yawa Inshallah”
Har gurin ƙofar gida ta rakoshi, tana masa Allah ya tsare, sai kallon Motar take, zuciyarta cike da jindaɗi.
Sai da ya biya wani restaurant ya ci abinci, sannan ya kama hanya. Gudu yake sosai, gashi kai ba wani ƙwararre ba. Yana cikin motar Namra tayi masa kira tana tambayarsa ya hanya. The way he's driving kamar baya son ransa, anyhow yake over taking kamar baya son rayuwarsa, shi dai kawai yaga ya kawo gida.
KALSOOM POV.
Saman gado ya zaunar da ita, yana duba idonta.
“Since when baki jindaɗi?”
“Lafiya na ƙalau fa kawai dai haka aman yake zo min kwana biyu”
Yasa hannunsa ya buɗe bakinta ya kalli halshenta.
“Baki jin wani abu?”
“Bana jin komai”
Hannunta ya riƙa ya duba, daga bisani ya tashi ya ɗauko wani ɗan roba ya miƙa mata.
“Unko wannan je kiyi fitsari ki kawo min”
Ba musu ta karɓa taje banɗaki tayi fitsarin ta kawo masa. Yana ganin result ɗin sai yanayinsa ya canja, damuwa da bacin rai suka bayyana a fuskarsa. Sai dai a ransa jindaɗi da farinciki ne amman ya kasa bayyana.
“Tashi kije ɗakin ki”
Ta masa kallon rashin fahimta
“Lafiya?”
“Tashi kije ɗakin ki nace a need a space”
Ya katsa mata tsawa iya ƙarfinsa, jikin tsoro ta tashi ta fice, zuciyarta na raya mata abubuwa da dama.
Tana fita ya kwanta saman gado ya dafe kansa.
“What is wrong with me? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Daga bisani ya tashi zaune idonsa a lumshe. Wani irin tsanar Kalsoom yake ji yana masa yawo a zuciya. A ƙoƙarinsa na gusar da abunda yake ransa, yasa shi tayi ya shirya ya bar gida duk kuwa da kasancwar yau weekend ne.
Tana jin tashin Motarsa, wani abu ya ratsa zuciyarta, ita kanta a yanzu ta fahimci ciki ne da ita, amman miyasa ya ɓata fuska ya nuna mata ɓacin ransa a fili? Ko dai baya son haihuwa ne?
No no no.
Tayi saurin kawarda tunanin idonta na mai cika da ƙwalla. Haka ta wuni cikin zullumi da tunani kala-kala. Har la'asar bata fito ɗakinta ba, gashi bata karya ba amman sam yunwar ta ɓace mata.
Ta san ita ce da girki a yau amman taƙi ta fita ta girka komai, sai da tayi Sallah magariba sannan ta fito ta haɗa ma kanta tea ta koma ciki. Tana shiga su Ulfah da Ezzah suka shigo ɗauke da Rafiq.
“Anty ga ɗan ki yau duk be gan ki ba”
Ɗan Murmushi tayi ta karɓe shi.
“Bana jindaɗi shiyasa, kuje falo ku yi wasa bana son hayaniya”
Sai suka fita da gudu suna mugun wasa, suka bar mata Rafiq. Sai bayan sallah Isha'i Doc ya dawo, da gudu yaranshi suka je suka tarbe shi suna karɓar ledar dake hannunsa.
“Daddy Momy tace mu faɗa maka yunwa muke ji”
Ya shasshafa kansu.
“Baku ci abinci ba ne?”
“Eh ba'a girka ba, tun abincin safe sai doyan da muka ci da rana”
“Miyasa ba'a girka ba?”
“Nima ban sani ba, Daddy mu ɗauka?”
Ta faɗa yana barke ledar chocolate ɗin data karɓa hannunsa. Kai kawai ya ɗaga musu ya nufi ɗakin Kalsoom rai a ɓace, abun ka da mai neman.
Kamar an jefoshi haka ya shigo mata cikin ɗaki rai a haɗe.
“Miyasa ba'ayi abinci ba?”
Sai da ta kalli yanayinsa sannan ta sanda kanta ƙasa tana masa sannu da zuwa.
Be damu daya amsa ɗin ba sai kawai ya katsa mata tsawa.
“Miya hana ki yin abinci nace? Ko baki san yau girkin ba bane? Kin bar yarana da yunwa baki san ba'a barin yara da yunwa ba?”
“Ban girka bane saboda bana jindaɗi, amman bari na tashi na ɗora musu indomie”
“Baki jindaɗi kamar ya? Ban ke da kan ki kika ce min lafiyarki ƙalau ba? Game da yarana bana da kyau, Kalsoom karki sake barin yarana da yunwa”
Miƙewa tayi tsaye tana masa wani kallo.
“Yau ne kawai ban girki musu abinci ba, kuma naga mahaifiyarsu ma tana cikin gidan, ita miyasa bata tashi ta girka musu ba? Bata fini sanin zafin su ba, haba Hilal miyasa zaka ɗaga muryarka akan abun da be kai ya kawo ba”
Ya nuna kansa.
“Au sa'insa zaki da ni? Good of you”
Duk faɗan da suke Rashida na tsaye jikin ƙofar tana jinsu. Tana jin alamun fitowarsa tayi sauri komawa saman Sofa ta zauna, ta tattara dukan hankalinta ta mayar gurin tv.
Tana ganin ya fito ta tashi ta bishi ɗakinsa.
“Ashe ka dawo...”
Tsayawa yayi cak, ya juyo fuska a haɗe ya nuna mata ƙofa.
“Bita ki bani waje”
“Pyar...”
“Fita ki bani waje na ce”
Da sauri ta juya ta fita. Tun daga ranar Hilal be sake cin girkin Kalsoom ba, indai ita zatayi girki ba zai ci ba babu ruwansa da ita, kallonta ma baya son yi. Daga ita har Rashida sun kasa gane kansa, har ita yanzu yi ma faɗan yake.
Sai dai ba wanda abun yafi damuwa kamar Kalsoom, dan ita gani take dan tana ɗauke da cikin ne yake nata haka, sai dai yanzu ra fara karantar Rashida ganin yadda take sakewa da ita sosai da sosai kamar ba kishiyarta ba, har da wani sirri na Hilal da bata san da shi ba, yanzu faɗa mata take tana ƙara janta a jiki.
Shi kansa yana zargin kansa, tunanin sauyin rayuwarsa yake, a dare ɗaya, duk wannan ba halinsa bane. Shi yafi kowa tausayi da son Kalsoom a cikin ransa amman ya kasa sakewa da ita, ya kasa nuna mata kulawa da jindaɗin data buƙata. Kuma ya rasa dalilin haka.
Kallonta yayi tana daga gefensa tana bachi, numfashinta na fita a hankali. Wani irin tausayinta ne ya kamashi, ga ƙaunar abunda yake cikinta. Kansa ya ɗora saman fuskarta ya kai hannu ya shafa cikinta, ya lumshe ido yana sauraren bugu zuciyarsa.
Kirgigit ta farka. Sai yayi saurin rumgume ta yana shafa kanta.
“Shiiiiiiii ni ne Okay?”
Sai da ta ɗago ta kalleshi, sannan ta sauke kanta. Haka ya suka kwana yana rumgume da ita.
NAMRA POV.
Tana falo ita da yarinyar maƙotansu. Wayarta tayi ringing, ganin number Asim yasa ta yi saurin ɗauka, sai da gabanta ya faɗi lokacin data ji ba muryarsa bace.
“Wa'alaikassalam, ina mai wayar?”
“Mai wayar ya samu haɗarin mota ne tare da wasu, a nan hanyar Funtua, yanzu haka muna babbar Asibitin Funtua”
Saki wayar Namra tayi ta kwarara wani uban ihu.
Haka ta cika gidan da ihu sai kuka take duk ta bi ta rikice, zuciyarta na nasaltama Asim ya tafi ya bar. Yarinyar da suke tare ne taje da gudu ta faɗawa Mahaifiyarta, sai gata ta zo da gudu cikin gidan tare da Babbar ƴarta.
Dafa Namra tayi tana girgiza ta.
“Haba ke kuwa sai kace ba musulma ba? Cewa akayi ya mutu ne?”
Cikin kukan Namra ta amsa mata.
“Ban sani ba, sun ce yana asibitin Funtua”
“Yanzu ba kuka ya kamace ki ba, tashi ki wanke fuskarki Mardiya ta raka ki, kuje Asibitin”
Da sauri ta tashi ta shiga ta wanke fuskarta ta ɗauko Hijabinta ta saka, keys ɗin gidan ma sai da Mardiya ta karɓa ta rufe mata gidan, sannan ta koma gida ta shirya sannan ta suka kama hanya Mahaifiyarsu na mata Allah ya tsare.
Keke Napep suka hau ta kai du tasha, sannan suka shiga motar Funtua.
Tun cikin Motar Namra take kuka, har suka isa Funtua, kowa sai tambayar yake lafiya, Mardiya ce kawai take iya amsawa, Namra kan ji take kamar ta yi tsalle ɗaya ta ganta gaban Asim, sam zuciyarta ta kasa aminta da be mutu ba.
Suna isa cikin asibitin suka tambaya, sai a nuna musu emergency ward. Hankali a tashe ta shiga gurin, sai rabon ido take, akwai mutane da yawa a gurin ga kuma ɗakunan bata san wanda zata shiga ba.
Daga gefe ta tsaya ta kira wayar Asim, ringing biyu aka ɗauka.
“Ga mu cikin Asibitin yana ina?”
“Yana ciki suna duba shi, bari na fito yanzu”
Ba a ɗauki dogon lokaci ba, sai gashi ya iso gurin sanye da uniform ɗin road safety. Sai ya miƙa mata wayar hannunsa yana faɗin
“Hajiya ki kwantar da hankalin ki be mutu ba, sai dai ɗan abunda ba za'a rasa ba, ba shi kaɗai yayi haɗarin ba tare da wata babbar mota da kuma ƙananan motaci uku, duk babu wanda be ji ciwo ba, motar ma da yake ciki duk ta ƙone”
Wani sabon kuka ne ya dawo ma Namra.
“Dan Allah da gaske yana da rai?”
“Ko da muka kawo shi nan yana da rai, mutun biyu ne kawai suka rasa rai ciki, amman shi yana da rai”
“Na gode...”
“Ba komai, amman ki kwantar da hankalin ki babu abunda zai faru”
Hawayen idonta ta share, ta fidda wayarta ta saka number Anty Amarya ta kira ta, sai da kiran ya katse bata ɗauka ba, sai ta sake kiranta, sai a uku ta ɗaga.
“Assalamu Alaikum, Namra kin kira ina sallah”
“Anty Asim yayi haɗarin mota yanzu haka muna asibiti”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Da sauki dai ko?”
“Eh sun ce be mutu ba, amman har yanzu likitoci suna kansa”
“Wace Asibitin?”
“Specialist dake Funtua”
“Toh ki kwantar da hankalin ki kin ji? Kin san abunda Allah ya ƙaddara ma bawa baya wuce shi ko? Ki daina kuka ke ma malama ce Namra, ki fawwalawa Allah komai”
“Toh Anty”
“Kin kira mahaifiyarsa?”
“A'a”
“Toh ki kira ta yanzu ki faɗa mata, Allah ya bashi lafiya, gobe zamu zo inshallahu”
“Tau Anty”
Daga haka ta kashe wayar. Ta ɗauki tasa wayar ta kira number Mahaifiyarsa. Ringing ɗaya ta ɗauka tana faɗin.
“Yanzu nake cewa a sawo min kati na kira ka, na ji ko ka isa lafiya”
“Mama ba shi bane Namra ce, yayi haɗari ne a hanyarsa ta dawowa, yanzu haka muna asibitin Funtua”
“Wayyo ni Allah na shiga uku, ya mutu ne? In ya mutu ki faɗa min Namratu”
“Be mutu ba yana da rai”
“Ba shi waya muyi magana”
“Likitoci suna duba shi yanzu, ba zai yiyu ki yi magana da shi ba”
“Kice min kawai ya mutu, wayyo Allah ni Halimatu, na shiga uku na lalace”
Kuka take sosai cikin wayar, Namra na amsa mata da nata kukan. Daga bisani ta kashe wayar, ta risina a gurin tana kuka.
“Haba Namra, ki gode Allah mana da ba mutuwa yayi ba, ki tashi muje muyi Sallah”
Cewar Mardiya tana goge ma Namra hawayenta. Tashi tayi suka nufi wani ɓangare na asibitin suka siye pure water suka yi alwala Mardiya ta shinfiɗa ɗankwalinta tayi Sallah, sannan Namra ta yi.
Ta daɗe tana yi ma Asim addu'ah kamin ta tashi su koma cikin emergency ɗin. Sai kusan goman dare likitoci suka fito da shi tare da wasu mutane maza da mata kusan mutum shida.
Wani ɗakin aka kai shi, irin ɗakin da ake aje majinyata, aka ware masa gado ɗaya, suka saka masa jini. Kusa da shi ta zauna tana kallon fuskarsa. Idonsa a rufe, gefen kansa an saka masa bandeji, an ɗaure ƙafarsa ɗaya, da cinyar hannunsa.
Wani irin tausayinsa take ji, ji take kamar ta cire ciwon ta maida a kanta. Sam bata ji maganar da likitan yake mata ba har sai da Nurse ɗin dake tare da shi ta taɓa ta.
“Kece Matarsa?”
Kai ta ɗaga mata, dan bata jin zata iya magana a yanzu, saboda bakinta kumshe yake da kuka.
“Ki zo likita yana son ganinki”
Tashi tayi tabi bayan Nurse ɗin dan likitan tuni ya tafi duba wasu masara lafiyar.
A kusa da wani marar lafiya likitan yake tsaye yana masa tambayoyi, sai da ya ƙare dashi sannan ya kalle ta ya miƙa mata wata takarda take cikin file ɗin dake hannunsa.
“Ki siyo masa wanɗannan magungunan yanzu, kuma ki siyo masa ɗan ƙaramin wando da riga a saka masa, kin ga yanzu zane kawai aka rufa masa”
Hannu biyu tasa ta karɓa, sai ta koma gurin da Asim yake, Mardiya na zaune a kujerar dake kusa da shi. Namra ta dafa ta.
“Zan je na siyo magani yanzu na dawo”
“Amman kin san guri?”
“Zan tambaya”
“Toh Allah ya tsare”
“Amin”
Haka ta sa kai ta fice ba dan tasan inda zata ba, bata ma jin kuɗin da yake jakarta zai isa ta siye duka maganin. Da tambaya ta isa pharmacy dake cikin asibitin, suka duba magungunan suka ce mata babu irinsu a cikin asibitin sai ta fita waje.
Bata bar gurin ba sai da ya kwatanta mata inda zata samu, can unguwar dake kusa da asibitin. A harabar Asibitin ta hau Napep ta faɗa nasa inda zai kaita. Be direta ko ina ba sai bakin pharmacy ɗin. Sai ta ciro naira ɗari ta miƙa masa. Ta taka da ƙafa ta shiga pharmacy ɗin, sai da aka gama da wasu mutanen sannan ta miƙa musu takarɗar maganin.
Dubawa mutumen yayi ya rubuta kuɗin ko wanne a jikin rubutun.
“Duka dubu shida da dari takwas da naira arba'in”
Gabanta ya faɗi, kwata-kwata kuɗin da yake jakarta be wuce dubu ɗaya da wani abu ba. Wayarta ta ciro ta miƙa masa.
“Dan Allah ka riƙe wayar idan na kawo maka ƙuɗin gobe sai ka bani wayana, mijina ba lafiya kuma bani da kuɗin yanzu, amman nasan gobe Mamana zata zo”
Ba musu ya karɓi wayar, ya miƙawa ɗayan
“Duba mana wannan ba fake ba ce?”
Sai da ya duba gabanta da bayanta, ya ce ta cire mishi password ya duba komai, sannan suka bata maganin.
Tana fitowa cikin pharmacy ɗin, wani ƙaton mutum ya sha gabanta.
“Malama ana magana da ke a can”
Ya nuna mata wata shegiyar Mota mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Ɗauke kai tayi kamar bata ji shi ta cigaba da tafiyar tana kallon ti-ti ko zata samu Napep.
Jin tayi ana binta a baya, kuma ba takun mutum ɗaya ba, juyowar da zata yi sai ƙamshin wani daddaɗan turare ya daki hancinta.
Tsayawa tayi cak tana masa kallin jin dalilin binta da yake shi da bodyguards ɗinsa. Shi kuma ya tsaya a gurin yana mata wani kallo mai wuyar fassara.
Mashallah kyakkyawa ajin farko kuma ajin ƙarshen a kyau. Manyan idanuwansa, su suka fi komai kyau a halinta dake fuskarsa, manya ne sosai farin yayi fari, baƙin kuma kamar an shafa masa kwalli, hancinsa ya zauna a tsakiyar fuskarsa kamar anja masa layi, a ƙasan hancin an yanka masa wani hot lip pink color, shape ɗin fuskarsa mai faɗi kamar ƙirginsa. Robe ce a jikinsa mai kyau da ɗaukar hankali.
Ganin be ce mata komai ba, yasa ta juya da nufin cigaba da tafiyarta. Sai kawai yayi kuskuren kai hannunsa ya riƙa hijabinta, da nufin juwo da ita.
Tassssssss. Ta sauke masa lafiyayyen mari a fuska. Da sauri Bodyguards ɗinsa suka zaburo za su kai mata duka, sai yayi saurin ɗaga musu hannu.
“Baka da hankaline da zaka kai hannunka ka taɓa min Hijabi? An faɗa maka kowa wace mace ce ƴar iska? Kasan muhimmancin hijabi da zaka saka wulaƙantacen hannunka ka taɓa min Hijabi? Ni matar aure ce dan haka ka shiga hankalin ka”
Duk balbalin bala'in da take masa, kallonta yake fuskarsa da murmushi, har yanzu sanyin da laushin hannunta yake ji a gefen fuskarsa.
“Nima Mijin aure ne”
Ya faɗa lokacin daya ga tana ƙoƙarin juyawa. Awww Mashallah his voice was soft and sweet, such a nice voice irin ta larabawan nan masu ƙalƙala, wandanda baka gajiya da jin muryar su.
Wani dogon tsaki taja dai-dai lokacin data tsayar da mai Napep ta shiga tayi tafiyarta.
Har cikin ransa yake jin tsakin nata, yana yawo a ƙwaƙwalwarsa kamar wani blood.
“Abdul”
Da sauri wanda ya kira da Abdul ɗin ya matsa kusa dashi yana tsare masa.
“Sir”
“Rubuta Number Mai Napep ɗin can. 771A97K Funtua”
“Yes Sir”
Da sauri ya juya ta nufi gurin da suka yi parking ɗin motocinsu. Shi kam sai da ya daina hango Napep ɗin sannan hankalinsa ya dawo kansa.
‘For the first time in history wata mace ta ɗaga hannu ta mari Abdullah Ahmad Mai-doki’
A zuciyarsa yayi furucin yana mamakin kansa.
“Unique one”
Ya furta a fili. Sannan ya ce su zo da motocin ya shiga suka kama hanya.
Tana isa cikin asibitin ta kai ma likitan maganin yace ta bawa Nurse. Haka suka kwana a kansa ita da Mardiya, ko wanne ya shimfiɗa ɗankwalinsa ya kwanta. Sai dai Mardiya ce kawai tayi bachi Namra kam har safe idonta biyu.
Da safe ita ta bawa Mardiya kuɗi tta siyo abinci a ƙofar asibitin ta karya, ita kam jasa cin komai tayi har likita ya shigo.
Bayan ya gama duba shi ya sake sa masa drip, a cikin drip ɗin yayi masa alluran da aka siyo sannan ya miƙa mata wasu magungunan yace idan ya farka ta bashi.
“Amman likita har yanzu be buɗe ido ba”
“Zai buɗe yana da rai fa, kawai yaji jiki ne, mai yiyu juwa anjima ya buɗe idon, amman inda hali ku kai shi babbar asibitin Katsina dan akwai yiyuwar sai an masa aiki a ƙafarsa, saboda kashinsa na cinya ya shige ciki”
“Innalillahi wa'inna ilaihi”
Ta faɗa tana faɗuwa zaune saman kujerar roba dake gurin.
“Allah ya bashi lafiya”
Wucewa ya yi gurin wasu marar lafiyar ya barta tana aikin kuka. Likitan be yi minti talatin da barin gurin ba, Sai ga Mama ta iso da kukanta. Aiko hankalinta ya tashi sosai da taga yadda fuskar ɗanta ya kumbuɗe kamar an busashi, gaba ɗaya halittarsa ta canja.
Yadda take rusa kuka sai yasa hankalin duk wanda yake gurin ya koma kanta, ƙanwar Asim sai haƙuri take bata tana kuka.
Guraren shaɗaya da rabi Anty Amarya ta iso tare da direban su da Aisha. Namra na ganinta ta fashe ta sabon kuka ta kwantar da kanta jikin Anty Amarya.
Anty Amarya ta danne kukanta, tana lallasar Namra.
“Ki yi haƙuri, Namra ki kwantar da hankalin ki, duk abunda ya kamata ayi masa za'a masa kinji? Idan ma waje ya kamata a fitar da shi za'a fitar, amman ki kwantar da hankalin ki”
Karaf Mama ta tsuma baki, tana mai jin zafin yadda Anty Amarya take lallarsar Namra ita ga ɗanta kwance.
“Ta kwantar da hankali kamar yaya? Ga mijinta kwance ki ce ta kwantar da hankalinta, ta nata ma kike ba ta Ibrahim ba, daman ai nasan ba son ƙwarai kuke masa ba, ni wannan aure bai zo da komai ba sai abun baƙinciki, gashi nan daga shigowarki gidansa ya koma da ƙafa ɗaya”
Da kuka ta ƙarasa maganar. Kallonta kawai Anty Amarya tayi ta ɗauke kai, tana mai jin zafin kalamanta. Bata wani daɗe ba ta tashi ta fito harabar asibitin tare da Namra.
“Allah ya sauwaƙe Namra mu kan za mu koma”
Da sauri Namra ta kalleta
“Yanzu Anty?”
“Eh daman Abbah ki yace min kar na kwana, ƙara mu kama hanya yanzu kin san tafiyar dare bata da kyau, Maryam tace tana gaishe ki”
Nan da nan sai tasa kuka, a zatonta Anty Amarya zata kwana ne. Har suka ƙarasa gurin mota Namra kuka take, daker Anty Amarya ta lallaɓata tayi shiru.
“Anty ba mu da kuɗin biyan Hospital bill, kuma ba ni da ko naira yanzu a hannuna”
Ta faɗa tana ƙara share hawayenta.
“Ai ga mahaifiyarsa can sai ta biya masa”
Anty Amarya ta faɗa tana shirin zama cikin mota. Namra bata ƙara cewa koma, sai idonta dake zubar da ƙwallah.
Sai da Anty Amarya ta rufe motar ta zuƙe gilashin sannan ta ce.
“Zan miki transfer 100k Allah ya bashi lafiya”
“Amin na gode Allah ya kai ku lafiya”
A haka suka yi sallama. Namra ta bi motar tasu da kallo har suka bar asibitin.
____________________________________
Share it please.