20
ASIM POV.
“Naje na biya kuɗin har na magani, sun ce Nurse zata riƙa baka”
Ta faɗa tana hita da ɗan ƙaramin mafecin dake hannunta.
“Mashallah har nawa aka biya ne?”
“Dubu ɗari da goma sha ɗaya, ni ban san dalilin yasa ta kawo ka wannan asibitin ba, ace allura guda dubu tara magani ma shegen tsaɗa”
“Asibitin kuɗi ce fa, ba kiga ɗaki suka ware mana ba”
“Allah dai ya baka lafiya mu bar Asibitin nan, ni ban ma ƙi mun koma gida ba gaba ɗaya”
“Gaskiya ni ba zan koma gida yanzu ba, ana kallo kayi aure ka auri masu abu sai kuma aga yadda na dawo da ciwo, kuma a can ai sai ma mun fi jin kunya tun da ƙyale ni zasu yi, maƙiya sai su mana dariya”
“Ai ba za a maka dariya ba kam sai dai a zagi iyayenta”
“Ni dai na fi son zamana nan, a cikin kuɗin ki bani dubu ɗari na bata sai ta siye wasu abubuwan, tun da tace BQ ɗin be ƙone ba sai mu zauna a cikin”
“A'a wane irin dubu ɗari kuma? Dubu shirin ai ya isheta ta siye komai”
“Mama har katifa fa da sauran kayan aiki, ashirin ba zasu isa ba”
“Ni zan je na siyo katifar, da kai na haka kawai za a ɗauki har dubu ɗari a bata, idan an bata nawa ya rage ni bana da lalurar ne? Ban ga dalilin da zata ci amfanin ka kai baka ci nata ba, wallahi tallahi na tsani yarinyar nan saboda iyayenta, sam basu da mutunci”
Asim ya sauke jiyar zuciya.
“Ni bana ma son tunawa da su Wallahi, rai na har ɓaci yake, hmmm Allah dai ya bani lafiya, na warke na tashi garau, Wallahi sai na basu mamaki”
“Ai kana da maƙiya kam Ibrahim Allah dai ya baka lafiya”
Da Amin ya amsa yana gyara zamam ƙafarsa.
RASHIDA POV.
Cikin mintuna ta isa gidan Asmee, tana fito mota Asmee na fitowa daga falo ta tarbeta.
Tashin hankalin dake fuskar Rashida ya ɓatar da na Asmee dan yadda taga Rashida ta rikice ta damu sai ita ta sassautama kanta, a tunaninta Rashida ta damu da matsalar ta ne har haka.
Da suka shiga falo kowanne kasa magana yayi sai kallon kallo suke, Rashida na tunanin ta ina zata fara, Asmee na fargabar irin amsoshi da zata bata.
“Wai ke ya akayi kika yi wannan kuskuren, Asmee dan me zaki cuci kan ki ki cece mu?”
“Rashida na faɗa wani haɗi ne yayi min wanda dole sai an samu sperm ɗin wani”
“Amman ke yanzu dan baki da hankali sai ki bar shi yayi amfani dake? A maimakin kije can waje ki samo wani? Yanzu kin ja mana masifa Asmee”
Rashida ta ƙarasa maganar da kuka.
“Ba ni da tabbacin ina shi ɗin ko bana da, an ban yi gwaji ba, wata mata ce da take zuwa gurinsa aka ce ta kamu”
“Amman yayi ta neman ki ne har da yawa ne?”
“Kin san duk lokacin da kaje da buƙata dole ne sai sun nemi su kwanta da kai”
Kuka ta fara, yana ta dana sanin abunda ta aikata. Sai kusan azahar Rashida ta bar gidan bayan taja mata kunne akan karta kuskure da bari kowa yaji ciki har da mijinta.
Banki ta dawo zuciyarta cike da tunani kala-kala, masu sokanar tama ganinta da rigar likita, dariya kawai take musu ba dan ta kula da zancen su ba. Ta shiga office ɗinta sai zama ya gagareta, ga takardun data tarar an kawo ma tayi sigh ko kallonsu ba tayi ba. Ta juya ta fita, office ɗin Alhaji Bashir ta nufa. Bata nemi izinin shiga ba ta tura office ɗin ta shiga.
Hannunta ta miƙa masa kamar yadda ta saba yayi mata kiss, sannan ya zauna saman teburin ta ɗora sama ƙafarta ɗaya saman ciyarsa tana masa wani irin abu, kamar wata gwaggwazajiyar karuwa.
“Security Camera, dai a kashe take?”
“Ai nasa an cire min ita tuni saboda ke”
Ta ƙara matsarda ƙafarta, izuwa cikinsa.
“Bashir akwai wanda ka sani a Alex Hospital, ɓangaren Lab?”
Hannu ya kai ya naɗe wandon suit ɗin nata, ya fara shafa ƙafarta.
“Ba za a rasa wanda na sani ba, miya faru ne?”
Shiru ta ɗanyi tana tunani, idan har ta yarda ta faɗa masa, asirinta zai tono, tun da dole ne yayi ma matarsa magana, wata ƙila ma ya sake ta.
“Wallahi wata friend ɗita ce za'ayi ma gwajin kasan asibitin sun fi ƙwarewa, sama data su Hilal”
Ya ɗauko wayarsa yana wani lumshe ido
“Bari na kira Doc Sabo sashen jini yake aiki”
Ta sauka daga saman teburin ta dawo saman cinyoyinsa.
“Kar wani ya shigo fa”
“Babu wanda zai shigo sai ya nemi izini”
Sai da suka gaisa da likitan sannan ya haɗa shi da Rashida. Gaisawa kawai tayi da shi sannan ta sanar masa zata karɓi number sa, su yi magana.
Sai da ta saka number a wayarsa sannan ta sauka daga saman jikinsa, daman tayi samana hakan ne dan kar ya gano damuwarta tun da ta saba masa a duk lokacin data shigo office ɗin.
Duk da irin kibar da yake da ita bata hanashi saurin unƙurawa ba ya riƙo hannunta ganin zata wuce.
“Yau da wuri zamu tashi babu aiki da yawa”
“Eh amman zan je gida akwai abunda zan yi”
“Aiko dai yau na so mu haɗu”
“Gaskiya akwai abunda zan yi, yanzu fa haɗuwar mu zata riƙa wuya, ƙara kaje gurin matar kawai”
Bata tsaya jiran abunda zai ƙara cewa ba ta fice daga office ɗin.
Lokacin data dawo office ɗinta zaunawa tayi ta ƙare duka aikin dake gabanta, sannan ta ɗauki wayarta ta kira likitan. Bayan sun gaisa ta gabatar masa da kanta.
“Sunana Aisha bee Omar, akwai wani cousin ɗina dake fama da matsala sai yaje asibiti aka bashi gwajin jini, to ina son idan ya kawo ka min a yi masa a kira ni a sanar dani dan Allah”
“Amman miyasa Hajiya?”
“Idan ka kawo ka sanar min zan faɗa maka ko minene, ka turo min account number ɗin ka”
“A wannan Asibitin bama yin abunda ya tsaɓa doka, hakan kan iya ja mana ɓacin suna a asibitin nan”
“Ba taka doka zaka yi ba, ceton rai ne idan har ya kawo ka faɗa min dan Allah”
“Miye sunan shi?”
“Sunan shi Hilal”
“Okay”
“Karka Manta ka turo min account number ɗin”
“Alright”
Yana kashe wayar ya turo mata account number ɗin. Ta jidaɗin ganin number, ga dukan alama zai yi saurin bata haɗin kai, jiki na rawa ta tashi ta fita daga office ɗinta, ta je ta cikin bankin ta masa transfer 100k.
NAMRA POV.
Yau ba laifi ta samu bachi dare, duk da ba mai nauyi bane sosai, minti goma ashirin zuwa ashirin da biyar take farkawa.
Sai dai a duk farkawar da take, a zaune take ganin Mardiya tana kallonta kamar wata mayya, tun Namra tana dauriya ta koma bachi har ta gaji ta tambaye dalilin rashin bachin nata.
“Wallahi na kasa bachin ne mafarkin tsoro nake, kusan kwana biyu yanzu haka na ke”
“Kiyi addu'ah kawai ki kwanta, babu abunda zai same ki, ki karanta Ayatul kursiyu ƙafa uku ko wace da bismillah wallahi har garin Allah ya waye babu abunda zai same ki”
“Toh na gode zan gwada”
Ta faɗa da damuwar a muryarta. Komawa Namra tayi ta kwanta ba ita ta fake farkawa ba sai asuba.
A kulolin gidan ta ɗauka ta zuba musu ɗumamen tuwo da Maman Mardiya tayi, sannan tayi wanka ta ɗauka ta nufi asibitin.
Ko da ta isa ta tarar har sun siye tea a bakin asibitin sun karya. Mama bata wani sake da Namra sun gaisa ba, ciki-ciki ta amsa masa gaisuwarta, ta fice tama watsa mata wani kallo a kaikaice kamar wata kishiryarta.
Hakan be dame Namra ba, dan ita ta san muhalin data aje ta a yanzu, tun da ta fara fahimtar tafiyarsu.
Bayan kamar minti talatin da fitar Mama Asim ya ɗauko dubu goma sha biyar ya miƙa ma Namra.
“Ga wannan ki siye wasu abubuwan na gida, Mama zata siyo katifa da wasu kayan”
Namra ta jidaɗi sosai, daman zama gidan su Mardiya ya fara isarta, duk da tasan kuɗin ba zasu isheta hakan be hanata nuna farincikinta ba.
“An biya kuɗin maganin ne har wasu sun rage?”
“Eh ɗari biyu matar ta ara mana, Allah dai ya ba ni ikon biya”
“Amin, amman Asim shabiyar zasu isa siyayya kuwa? Ba mu da komai fa kasan komai ya ƙone”
“Haka nan za a matsa ayi Namra, bafa irin siyayar gidan ku zaki yi ba, ta talakawa zaki yi, kamin mu ga abunda Allah zai yi kuma”
“Toh Allah ya taimaka”
“Amin, likitan yayi min allurar ɗaya ɗazu, kuma yace ya kamata na ɗan fara taka ƙafar, koda ina riƙa wani abun ne”
“Aiko ya kamata ka fara tun yanzu”
“A'a sai nan gaba, gaskiya ni tsoro nake ji”
Ta ɗanyi dariya, tana mamakin irin rakin da Asim yake da shi. Asibitin ta wuni sai da yamma ta koma da zimmar taje Mardiya ta raka ta kasuwa suyi siyayya. Bayan tafiyarta Mama ta siyo abinci a bakin asibiti ta ci, ta kawo mo Asim, dan kwata-kwata ƙwara tayi daga ɗakin har sai da Namra ta tafiyarta, sannan ta dawo, Mama irin mutanen nan ne da basu iya samun arziki ba, waɗanda idan abu ya same su a take suke canjawa mutum, ga shegen son su yi kuɗi kamar hauka, tana daga cikin mutanen da suka tsani masu arziki, suna ganin kamar Allah ya fi son su da su, ita a nata rayuwar bata ƙi Asim yayi arziki ba ta kowa ne hali, ko dan ya rama abunda iyayen Namra suka masa.
ABDOOL POV.
A hankali yake tsotsa bakinsa kamar mai shan minti, sai wasa yake da drink ɗin dake gabansa ya kasa sha.
“Saboda Mai Martaba yace yana son ganin ka shiyasa ka wani damu ko?”
Ya ɗan ɗaga kai kaɗan ya kalli Ummi da idonsa na marar gaskiya.
“Eh mana, na san ba zai wuce yayi min maganar aure ba”
“Ai dole yayi maka maganar aure, tun da kai baka san ka girma ba, ace ko wace mace baka so, kwana ki har ƙaryar ciwo kayi min sai gashi likitan ya ƙarya ta ka, wai anya ba aljana take auren ka ba?”
Yayi dariya yana kallon ƙannensa mata su huɗu da suke zaune a ɗayan ɓangaren na falo suna sha'aninsu.
“Abdool ya kamata ace kana yi ma kan ka faɗa, mahaifin ka yana son ka, kar kayi abunda zai sa kyaunka ya ɓace a gare shi, kasan ƴan da matan uban nan naka suke, basun ka suke su kuma zuga shi zasu yi ta yi har sai sun ga taren ku ya ɓace, duk kuma wanda bashi da uwa a cikin gida yana cikin matsala dole ne yayi taka tsantsan”
Ya shafa kansa, yana jingina da kujerar dinning ɗin.
“Ummi Mai Martaba na da wani buri akai na, shiyasa ya natsa nayi aure, ni kuma bana son sarautar nan, ni kwata-kwata ma ba dan shi ba Wallahi da ba zan zauna ƙasar nan ba”
“Amman ai ba kai kaɗai ya haifa Namiji ba, amman kai ne mafi soyuwa a ransa, to dan me ba zakayi masa abunda zai sa ya ƙara son ka ba? Indai baka fitar da wanda kake so ba sai ya kai ga ɗaukar wata a cikin gidan nan ya haɗa ku, idan kuma ka ƙi yarda kasan abunda zai biyo baya”
“Ummi wanda nake so ban san inda zan ganta ba, ban san yadda za'ayi na haɗu da ita ba”
“Kamar ya?”
Ta tambaya tana kai ƙwallon anabi a bakinta.
“A Funtua na ganta bakin wani pharmacy, na fita nayi mata magana, tace min matar aure ce ita”
“Ta faɗa maka ita matar aure ce kuma zaka so ta?”
“Sam bata min kama da matar aure ba mai igiya uku, sai da matar aure kalar aure, ina ganin wannan take nufi, irin ƴan matan nan ne masu aji sosai, har marina tayi fa”
Ummi ta gyara zamanta, irin na mutanen nan da naira ta zauna a jikinsu har ta nuna kanta, ga kuma milkin dake cikin jininta, na ƴaƴan sarakai.
“Wayw Uban ta a garin nan?”
“Wallahi nima ban sani ba, irin yaran nan masu mugun ji da kan su, kuma na rasa yadda zan yi na same ta, duk wata hanya da zata sadani da sake ganin ta nabi amman ba nasara, har abinci naje na raba a inda ake sa ran zan ganta amman ban ganta ba, kuma ni Wallahi ita nake so”
“To sai yaya kenan?”
“Sai na nemota duk inda na ganta zan gane ta, ba zata min marin banza ba sai na rama, kuma gaskiya ba zan haɗu da ita hakan nan ba ga dukan alamun ita ce, dukan matan da nake haɗuwa da su ban ji komai akan su ba sai ita”
Ya faɗa yana mai tashi tsaye.
“Anya ba aljana ka haɗu da ita ba Abdool?”
“Ba aljana bace Ummi”
A faɗa yana dariya, zuwa yayi ya mata side hug, ya ɗauki anabi ɗaya ya kai a bakinsa, na biyu kuma ya jefe ƙannensa da shi.
“Ummi ki tsara min yadda zan cewa Mai Martaba”
Be tsaya jiran abunda zata ce ba, ya fice daga falon yana murmushi. Da kallo Ummi ta bishi tana mamakin yadda ɗan nata yake ƙoƙarin zame mata aljani.
ANTY AMARYA POV.
Tun da Abbah yake maganar bata ce uffan ba har sai da ya kai aya. Sannan ta sauke ajiyar zuciya tace.
“Zan musu magana, ai dukan su suna da manema, daga Hindatu har Maryam ɗin”
“Ƙara ayi musu magana su fitar da wanda suke so, da ba zan sake zaɓawa kowa miji ba”
“To, Alhaji nacw har yanzu baka je ganin Mijin Namra ba, ya kamata ko a waya ne ka kira shi ku gaisa”
“Ko Namra ce bata da lafiya ba zan kira ba, balle mijinta, ki daina kawo min wani bato daya shafi Namra, baki san irin baƙin cikinta daya ke cikin zuciyata ba”
“Toh ni idan ka min izini ina son na koma naje na ganshi”
“Ba zaki koma ba, idan be gode da ganin da kika masa ba, ya bar shi, ba familyn ta ya aura ba ita ya aura, kuma na sallama masa ita har abada, babu hannuna babu ƙafata a lamarin Namra, ta zaɓi wanda take so sai taje ta zauna da shi”
Ko kaɗan kalaman Abbah basu yi ma Anty Amarya daɗi ba, nan take ta canja fuska, ɓacin rai dake zuciyarta ya bayyana.
“Haba dai, wannan wane irin magana ne? Shikenan bata da damar ta zaɓi mijin da take so? Wannan sam ba adalci ba ne, baka ƙaunar yarinyar nan kamar ba kai ka haife ta, ɗan abu ƙanƙane sai ka ɗauki karan tsana ka ɗora mata”
Ta ƙarasa maganar da kuka.
“Ke kin fi kowa sanin na yadda na nunawa Namra so, ai ke ya kamata kiyi tunani kiga rashin dacewar abunda Namra tayi min, ko da ace ba ni na haife ta, ya kamata ace tayi min biyayya tun da nina raine ta har ta kai inda take yanzu, be kamata ta zaɓi wani ta bar ni”
Kukan Anty Amarya ta cigaba da rera masa. Shi kuma ya ɗauki jaridarsa ya buɗe yana karatu, ba dan kuma yana son karatun ba, sai dan yayi avoiding kukan na Anty Amarya, tana da matsayi a zuciyarsa, ba kasafai yake son kukanta an itace mafi soyuwa a zuciyarsa, duba da yadda take masa biyayya da kuma yadda take da ƙuruciya, sama da Hajiya Barau data kwana biyu.
Idan kuma ya biye mata yasan halinta yanzu ne zata birkice masa, har ya rasa gane kanta.
Data gaji da kukan ne, ta share hawayenta, ta tashi ta bar masa ɗakin.
Tana shigowa part ɗinta duka ƴaƴanta suka lura da yanayinta, ba ma kamar Maryam data fi damuwa da ita sosai.
“Anty Lafiya?”
“Lafiya ƙalau, kawai ina tunanin Namra ne, ban san halin da take ciki ba babu waya hannunta, kuma Abban ku yaƙi ya bar ni naje na duba su”
“Inshallah tana cikin ƙoshin lafiya Anty, kwana ki ma sai da ta turo da text wai ki taimaka mata da kuɗi, ni kuma na goge text ɗin dan nasan Asim ne zai sata”
“Amman miyasa baki faɗa min ba? Baki san halin da take ciki ba, ƙaddara ce ta riga ta faɗa mata babu yadda za muyi”
“Nayi tunanin ko shine yasa ta”
“Nawa tace a bata?”
“Bata faɗa ba”
“Gobe kije ki tura mata 300.000k sai ki kira wayar Asim ki faɗa mata, kuma kice ta siye waya tasa layin ta, kwana kin nan mafarkin ta nake ta yi, ban san halin da ƴata take ciki ba”
“Inshallah zan tura mata”
“Abbah ku ba ban saƙo gare ku, amman sai gobe zan faɗa muku”
Tana kai wa nan ta tashi ta nufi ɗakinta, tana share hawayen da suka zubo mata.
RASHIDA POV.
Tana gama aikin office ɗin ta dawo gida, tasan abunda ta shirya ma kanta shiyasa ta dawo da ƙarfe shida tsaɓanin tara na dare data saba dawowa.
Ɗakinsa ta shiga tana masa bincike ko zata ga takardun results ɗin ko kuma jinin daya ɗiba tun da yace mata be kai, amman bata ga komai ba. Har ta gaji ta dawo dakinta .
Duk da tasan yau ba a ɗakinta Doc take ba, hakan be hanata chaɓa ado ba, dan ta ɗauki hankalinsa. Daman ya saba duk wacce yake ba girkinta ba yakan shiga yayi mata sai da safe, sannan ya wuce ɗakin da zai kwana.
Tun kamin ya shigo ɗakin, ta haɗa masa tea da lemun tsami dan tasan yana son haka, ta kuma saka masa zuma a maimakon sugar, sai ta ɗauko maganin dake jakarta ta buɗe ta kaɗa masa cikin tea ɗin har kusan guda biyar.
Tana mayarda jakar ta aje yana turo ƙofar ɗakin ya shigo, gabanta ya faɗi, abun ka da wanda bata saba ba, sai dai ta wayance taje ta rumgume shi.
To her surprise sai ya sauke hannayensa daga saman wuyanta, yana ɗan murmushi. Bata damu da abunda yake mata ba, dan a tunaninta fushin ɗazun ne na dress ɗin ta tayi. Cup ɗin tea biyu ne sai ta ɗauki ɗayan ta miƙa masa.
“Ga tea”
Hannu ya kai ya karɓa ya furta
“Thank you, good night”
Har ya juya, sai kuma ya juyo ya kalleta kamar zai ce wani abu, sai kawai ya sakar mata murmushin irin na fatar faki, ya juya ya fice.
Ɗakin Kalsoom ya nufa, ko da ya shiga ciki be ganta ba, ya duba bathroom bata ciki, sai kawai ya nufi ɗakin su Ezzah dan yasan ba wuce tana can ba.
A tsakiyar gado ya tsame ta tana ta tofawa yaransa addu'o'i, su kuma sai bachi suke tayi abun su. A bakin ƙofa ya tsaya yana kallonta yana murmushi, har ta gama ta taso ta nufo shi.
Hannu ya kai ya laƙƙamo kunkurunta, jikinta ya haɗe da nashi, ita kuma sai haɗiyar yawu take tana kallon kofin dake hannunsa, ƙamshin tea ɗin yana kai ma hancinta ziyara.
Kaɗan ya kurɓa ya kai mata kofin a baki, ɗan tsami tsamin data ji yasa ta jidaɗin tea, ta riƙe kofin da hannu biyu har sai da ta shanye tea ɗin gaba ɗaya.
Tana shanye tea ɗin ta saki kofin tayi masa kwance a jikin, wani irin bachi mai bala'in nauyi yayi gaba da ita.
“Hey...”
Ya faɗa yana girgizata, amman ina, tayi nisa har ƙoƙarin zubewa take a ƙasa, hannayensa yasa ya ɗauke ta cak, ya nufi ɗakinta da ita. Saman gado ya kwanatar da ita ya kwanta gefenta yana shafa fuskarta, zuciyarsa cike da mamakin abunda yake cikin tea ɗin.
Ya kusan minti talatin a gurin kwance, sai yaƙi yake da bachin dake son sace shi, yana unƙurin tashi yaji an turo ƙofar ɗakin, ƙin motsawa yayi sai ya lumshe ido kamar yayi bachi, sai ga Rashida ta ƙaraso har gurin tana leƙen fuskarsa, har da sa hannunta tana masa yawo da shi dan ta inda gasken yayi bachin.
Da sauri ta juya ta fita ta nufi ɗakinsa, keys ɗin motarsa ta ɗauka, ta fito waje ta buɗe motar tana masa bincike, seat ɗinsa na gaba ta buɗe ta fara bincikar takardun da suke gurin. Jikinta ne ya bata ana kallonta, da sauri ta fito daga motar, sai taga Doc tsaye ya rumgume hannayensa yana kallonta.
“Me kike nema? Jini ko result? Miyasa baki jira saƙon Doc Sabo ba?”
Kasa motsawa tayi, numfashita mai sai da yayi nisan zango sannan ya dawo, jin tayi kamar ƙasa ta buɗe ta shige ciki, a take mararta ta cika da fitsari.
NOT EDITED ⚠️
Bata taɓa sanin gume na da zafi ba, sai a wannan lokacin, wani irin nauyi ta ji kanta yayi kamar an ɗauki duniyar nan an ɗora mata, yau ganin Hilal take ya cika ko ina na duniyar idanunta.
Yau kam ba ranar kuka ba ce, tashin hankalin daya same ta ya fi ƙarfin kuka, hakan yasa hawaye ba kusanci idonta ba, ashe abu mai sauƙi ake ma kuka, ta kasa yarda yau ita ce Hilal ya kama dumu-dumu ba.
"Kin san kina da HIV kike ƙoƙarin ɓoyewa Rashida? Do you know what lokacin dana ɗibi jinin ki result ɗin ba ɓata yayi ba, nace miki haka ne saboda ban yarda da abunda idona ya gani ba, na dawo na ɗibi jininki da na yarana da na Kalsoom nawa dan na gwada, so that na tabbatar idan da gaske kina ɗauke da cutar ne, amman ke kin san kina ɗauke da cutar kika bar ni ina kusantar ki?
Da ba dan wanann cikin ba, da sai mu ɗauki dogon lokaci a tare da dake baki faɗa ba right? What if all of us mun kamu da cutar nan?"
Ƙiri-ƙiri tayi masa da ido, cikin ƙarfin hali ta cira ƙafarta da tayi mata mugun nauyi ta tako ta ƙaraso kusa da shi.
"Kana tabbacin ni ce kaɗai nake ɗauke da cutar? Kasan ta ina cutar ta shige ni? Miyasa idon ka zai rufe har haka?"
"Ke da kan ki kike zargin kan ki, dan me zakiyi ma Doc Sabo transfer 100,000k? Dan me zaki ce idan ya kawo jinin kamin ya auna ya kira ki? You late Rashida ko da kika kira shi na riga na kai jinin amman yaƙi ya faɗa miki saboda ya san ni kamin ya sanni kuma ya san aikinsa, daman nasan ziyarar da kika kawo min ɗazu a office bata banza bace cox na lura dake kwata-kwata hankalinki baya jikin,
Bincike da kika min da tambayoyin da kika min ya tabbatar da akwai wani abu, and now what kin sa abu a tea ki bani nasha so that kiyi iya binciken ki ko? To bari na faɗa miki if something happens to my wife hmmm you're in trouble"
Sai a yanzu hawaye suka samu damar cika idonta har suka silalo zuwa kumatunta.
"Saboda na san idan kasan ina da HIV ba zaka faɗa min ba, idan har ya tabba ina da HIV Hilal to ta hanya ɗaya na same shi, wato sex kuma wani namiji be taɓa kusantana ba sai kai, a lokacin dana bar ka ya kusance ni ban san komai ba, sai a ɗazu nasa an nemo min Doc Sabo saboda na tabbatar idan har da gaske ina cutar ne, do you know who i try to protect? You and your dirty wife, Asmee told me everything about your bride but very soon gaskiya zata yi halinta, kuma ba zan taɓa yafe mu ku ba, aje ayi gwajin"
Tana kai nan ta raɓa gefensa ta wuce cikin falon. Juyowa yayi ya bita da kallo zuciyarsa na raya masa abubuwa da dama.
Kalamanta basu kama zuciyarsa ba, amman suna ƙoƙarin zaunawa akansa, what he believe shi dai yana da protection ɗin da ba kasafai cutar zata yi saurin kama shi ba, ko baya da protection, he's Doctor ya san cutar bata saurin kama namiji kamar mace, dan namiji ɗaya mai hiv zai kwanta da mace goma to dukkan su sun zama patient living with hiv, wato sun shiga sahun masu dauke da HIV acikin al'umma.
Amman mace ɗaya mai HIV zata kwanta da namiji 10 a rana, abu ne mai sauki namiji 2 ko 3 suka mu da wannan ciwon mai karya garkuwar jiki. Namiji zai iya daukan HIV kawai idan yana da wata kafa a gabansa abunda ya shafi kurji, yanka ko tsaga.
"He's lie"
Ya furta a hankali, yana murza saman goshinsa, zuciyarsa ta kasa yarda da zancen ta, duk da yasan Kalsoom take nufi, dan ita daya auna jininta be nuna haka ba, amman yasan result ɗin zai fito kuma dole gaskiya tayi halinta.
Shigowa yayi cikin falon cikin tunani da sarƙaƙiya, a saman babbar kujera ya zauna, ya dafe kansa, ɗaurewar da kansa yayi shi ya hana shi bachi har safe.
Har yayi sallah asuba ya dawo, be ji motsin Kalsoom ba, ita daya san wani lokacin ma takan riga shi tashi, a falon ya zauna yayi addu'o'insa sannan ya shiga ɗakinta, yadda ya tararda ita kwance rigingim har sai da ya tsorata, wani irin ninshari take kamarmacijin nan mesa na bachi, yayi mata girgizar duniyar nan amman ina, in ma ban da ƙara nauyin bachi babu abunda take.
Da sauri ya fita ya shiga ɗakinsa duba keys amman be ganshi ba, sai a lokacin ya tuna da suna guri motarsa da Rashida ta saka su jiya, da sauri ya fita daga ɗakin ya nufi gurin motar, ashe ma buɗe ta kwana, shiga kawai yayi ya kunna ta ya bar gidan.
Rashida na jin tashin motarsa ta duba agogon ɗakinta, 6:55am ya nuna, bata damu da rashin warewar gari ba ta tashi ba tare data tsaya wanka ba, ta canja tufafin jikinta zuwa atamfa ta ɗauki abaya ta ɗora sama, sannan ta ɗauki handbang ɗinta ta fice daga ɗakin.
Cikin sauri ta shiga motarta tayi mata keys gudun kar Hilal ya dawo, dan yanzu kam sam bata son haɗa ido da shi.
Gidan su Asmee ta nufa, cikin ƙanƙanen lokaci ta isa, haka ta riƙa musu horn har sai da mai gadin ya buɗe mata gate, kusan da motar Alhaji Bashir ya faka motarta, daman tasan yana nan dan yanzu be isa fita ba. Ƙofar falon ta riƙa bugawa tana sallama kamar zata tashi gidan.
Alhaji Bashir ne ya buɗe mata ƙofar yana tambayar lafiya, dan tun da yaji muryarta hankalinsa ya tashi, a tunaninsa ko tazo tayi masa wani abun ne.
Tun daga samansa ta kalle shi har zuwa ƙasan shi, daga shi sai guntun wando, sai da ta kai zuciyarta nesa sannan ta iya ƙirƙiro murmushi ta yaɓa a fuskarta.
"Matar ka na nan?"
"Lafiya kika mana sammako haka?"
"Lafiya ƙalau, sirrin mu ne, saƙon zan bata"
Kamin ya ƙara cewa wani abu har Asmee ta ƙaraso gurin tana tambayar wanene.
"Nice na doko muku sammako, saƙon ki zan baki"
Rashida ta amsa da kanta, tana mata murmushi. Wani kallo Asmee ta watsa ma Alhaji Bashir, irin ya zaka zo daga kai sai guntun wando haka. Sai kawai ya juya ya shige ɗakinsa.
Asmee ta riƙo hannunta suka shigo falon.
"Ke lafiya kika zo haka?"
"Taimakon ki nake nema, idan har baki taimake ni ba, zamu iya rasa ran mu ni da mijina"
"Subhanallahi miya faru?"
"Mijina ya aiko ni zuwa gare ki, maganar da zan faɗa miki sirri ce bana son kowa yaji, ko da kuwa mahaifiyarki ce ko mijin ki"
"Ban taɓa sirri dake ba na faɗawa mahaifiyarta ba, balle kuma mijina taso muje ciki"
Dar ƙarshen gadonta, Asmee ta kai ta suka zauna, sannan ta kalle ta tace
"Faɗa min damuwarki, matuƙar ina da maganinta wallahi zan miki"
"Irin samarin nan nake nema kidnappers"
Asmee ta daki ƙirji.
"Aka yi da wani ko za'a miki?"
"Wani muke son a a ɓoye mana shi, saboda ta hanyar shi ne kaɗai ne, mijina zai cigaba da rayuwa da ni, dan Allah idan kin san inda irin mutanen nan suke ki faɗa min"
"Ni ɗan maye ma miye haɗina da shi balle kuma ɗan kidnapped, Wallahi ban san wani mai wannan aikin ba"
Rashida ta kama hannayenta ta riƙe ta fara kuka.
"Ko cikin ƙawayen ki ba kisan wacca tasan mai irin wannan aikin ba? Dan Allah Asmee ki ceci rai na"
"Bana da ƙawar da zata iya faɗa min sirrinta har haka sai ke, ko da suna da irin waɗannan mutanen ba zan iya sani ba, sai idan gurin wannan Malamin zaki je, sai ya haɗa ki da wani cikin masu zuwa gurinsa, dan yana basu taimako sosai"
"A ina Malamin yake? Dan Allah ba ni addireshinsa"
"Ba a cikin garin nan yake ba, a ɗan dutse yake da kin shiga garin ɗan dutse kika ce Malam mai gobe da nisa ko ƙaramin yaro yasan gidan sa, bari na baki number wayarsa, kamin ki isa zan kirashi na faɗa masa"
"Na gode Allah ya saka miki da alheri, samin number"
Ta faɗa tana miƙa mata wayarta. Sai da Asmee ta saka mata Number sannan tace
"Amman kin san garin kuwa?"
"Karki damu zan tambaya har na isa garin, ai bada motana zan je ba, gidan mu zan bina na aje motar, saboda gudun sa ido"
"Allah yasa a dace, amman ina jin tsoro Rashida"
"Babu abunda zai faru, ba mummunan abun zan aikata ba"
"Dan Allah aro min niƙab ɗin ki da Hijab"
Ba musu Asmee taje ta ɗauko mata ta saka.
A gaggauce ta fice da daga gidan, zuciyarta har wani ɗar-ɗar take, tana ayyana irin rashin mutuncin da zatayi Doc Sabo, lallai yau zata nuna masa ta fishi zama yar duniya, Zagon ƙasan da yayi mata ƙarami ne, yanzu zata masa babban.
Kamar yadda ta tsara, a gidansu ta biya ta aje motar, ko cikin gidan bata shiga ba, balle su gaisa da Momi, tana rufe motar ta fito ta tari Napep ta shiga, ya ɗauki hanyar tasha da ita.
HILAL POV.
Be daɗe ba ya dawo, daman allurai kawai yaje ya ɗauko, yana shiga ɗakin ya haɗa allurar yayi mata, sannan ya ɗauko tawul ya jiƙa shi da ruwa, ya riƙa dafa mata a goshi.
A hankali ta fara motsi tana nishi da miƙa irin ta gaji sosai ɗin nan, hankalinsa ya ɗan kwanta lokacin daya ga ta buɗe idonta, sai ya sakar mata murmushi.
Daker ta unƙura ta tashi zaune, saboda nauyin da jikinta yayi mata.
"Wane irin bachi nayi haka?"
"Magani na saka miki a tea ɗin, tashi kiyi sallah"
Ta ɗan kalli window taga yadda rana ta fara hudowa, sannan ta unƙura da zimmar tashi tsaye, sai Doc ya kai Hannu ya riƙa hannunta.
"I trust you Kalsoom dan Allah kar ki bani kunya"
Wani kallo tayi masa, irin ban gane ba. Sai kawai yayi murmushi yana ƙoƙarin ɓoye feelings ɗinsa.
"Yanzu idan aka ce ina da hiv zaki zauna da ni?"
Dawowa tayi ta zauna, ta kai hannayenta ta riƙa fuskarsa.
"Idan har kana da hiv zan zauna da kai, kuma idan har kana da shi nima nasan ina da shi, so babu dalilin ƙyamar juna"
"What if aka ce ke kike ɗauke da shi ba mu ba?"
Shiru ta ɗan yi tana nazarin tambayoyinsa, anya Doc zai mata irin wannan tambayar haka kawai.
"Idan har ni nake ɗauki da cutar zan nisanta kai na daga gare ku, gudun kar ku kamu da cutar, har sai ta zama aids, domin wannan kwayan cuta HIV (human immunodeficiency virus) bata rayuwa da keu a wajen jiki, saboda haka akan iya kamuwa da ita ta hanyar kissing ko kuma yin anfani da wani abu wanda me dauke da cutar ke anfani da shi, kamar kofin shan ruwa, abun yanke farce, da brush.
Amman da zarar cutar ta kai marhala na karshe ma'ana AIDS (acquired immunodeficiency syndrome) zan cigaba da mu'amala da ku kamar yadda na saba, saboda ba'a kamuwa da ita ta hanyar kissing, cin abici tare da me dauke da ita, amfani da kayayyakin ko abubuwa da me dauke da ita ke anfani da su, kamar kayan sawa, wayan salula, agogo, wanka a swimming pool, zama a kujera, cizon sauro, ma taci comb, tawul, da kuma tafiya, hada hanu, zama,da yin aiki tare da me dauke da cutar, amman ba zan bari ka kusance ni ba, ko da kuwa zaka na shan magani da amfanin da kororon roba, saboda it's risk.
Sai dai kuma ka sani, rayuwata zata tarwatse zan nisanta da ƴaƴanka, duniya zata ƙyamace ni, kuma dole na rabu da kai"
Ta ƙarasa maganar hawaye na bin fuskarta. Ɗan murmushi yayi ya tashi yana ƙoƙarin ɓoye hawayen da suka cika masa ido.
"Intelligent woman, je kiyi sallah zan haɗa ma yara breakfast"
Har ya fice hawaye take, zuciyarta cike da tunanin abunda yasa Doctor yayi mata wannan tambayar.
NAMRA POV.
Ko ta koma gida, ta samu duk sun tafi walimar aure, ta wata maƙociyarsu, da ake yi yau jumma'ah. Mardiya ce kawai a gidan, ta zauna cikin ɗakin ta rafka uban tagumi.
Sallamar da Namra tayi ma sai da ta firgita ta.
"Ke lafiya kike kuwa? Ke kaɗai aka bari a gidan?"
Namra ta tambaya tana zama kusa da ita. Ajiyar zuciya mardiya ta sauke.
"Kawai ina tunanin rayuwa ne"
"Rayuwa kuma kamar ya?"
Shiru tayi tana tunanin irin ƙaryar da zata yi ma Namra, dan bata son faɗa mata asalin abunda yake damun ta.
"Inna ce duk ta bi ta dame ni akan rashin auren nan, kamar ni nayi ma kai"
"Ayyah wai wani abun ba'a kusa yake ba, komai yana da lokaci"
"Na sani matsalar iska ne yake damuna, ina ganin kamar shine ya hana ni aure, amman ita inna ta kasa ganewa"
Ta bijiro da damuwarta a fuskarta kamar da gaske abunda yake damunta ɗin kenan. Ita kuma Namra sai tausayinta take.
"Ki riƙa azkar kina faɗawa Allah damuwarki, inshallah zai miki magani"
"Ina yi Wallahi babu inda ba mu shiga akan neman taimako ko ina sai ace mana Aljani ne ya aure ni"
"Subhanallahi, amman Mardiya, ai dole aljani ya aure ki tun da kina yawo babu ɗankwali, gashi kina yawan sauraren waƙe-waƙe, da ace baƙara kike yawan karantawa nayi imani ba zai samu nasara akan ki ba"
Ajiyar zuciya Mardiya ta sake saukewa, a karo na biyu, ta ƙara gyara zamanta.
Namra ta kalleta cike da tausayawa tace
"Ki samu allo ki rubuta suratul azari, daga farkon ta har ƙarshe, idan kin yi alwala la'asar kika rage ruwa sai kiyi amfani da su ki wanke rubutun ki shanye har kwana uku, indai matsalar aljani ne mai hana aure inshallah zai rabu da ke"
"Na gode sosai Inshallahu zan gwada"
"Allah yasa a dace, da naso ki raka ni kasuwa amman naga kamar kina cikin damuwa bari mu bari har gobe"
Kamar kar Namra tayi maganar nan da nan Mardiya ta kai idonta gurin ƙaramar jakar da Namra take riƙe da ita, sai kuma ta kawar da kai.
"Mu bari har goben dai yanzu yamma yayi"
"Eh nima ai haka na gani"
Ƴar nokiyar dake hannun Mardiya ce tayi ƙara, sai ta tashi ta bar ɗakin tana amsa wayar.
Tashi Namra tayi ta cire hijabinta, ta rataye, sannan ta ɗauki jakar wanda kuɗin suke ciki ta saka a cikin akwatin Mardiya na kaya, da zimmar ta aje a cikin dan kar taje ta jefar da ita wani gurin, sannan ta fita ta kama ruwa.
RASHIDA POV.
Data isa tasha, shatar motar ta ɗauka ita kaɗai, ya kai ta ƙauyen. Bata sha wahala ba gurin gane gidan, tambaya ɗaya suka yi aka nuna musu gurin, gidan ne mai kyau kamar ba ƙauye ba. Sun tarar da layin mata sosai a gurin haka ta samu guri ta tsaya har aka kai gareta. Sannan ta shiga.
Ƙaton ɗaki ne mai cike da kayan alatu, ba dan rawanin da taga ni a kansa ba, da zata iya rantsuwa da Allah tace wani attajiri ne ba malami ba, sai dai hakan be bata mamaki ba, dan tasan duk mutumen dake aiki da manyan yan siyasa dole ne ya tara komai.
Kallo ɗaya yayi mata ya soma gyara ƙasar dake gabansa yana faɗin ta cire niƙabin ta, ba musu ta cire niƙab ɗin tana gaishe shi. Be amsa ba har sai da ya gama bugun ƙasar sa, sannan ya kalleta yace.
"Kin zo nan ne dan a haɗa ki da wani yayi miki wani aiki"
"Haka ne ni ƙawar Asmee ce, tace zata kira ka"
Sai da ta ciro dubu hansin ta aje masa a gabansa, sannan ta koro masa da bayani. Sai da ta gama sai yayi murmushi yace
"Zan haɗa ki da wani, saboda kawai Asma'u ce ta turo ki, amman ba dan haka ba, babu abunda zai sa na haɗa ki da shi, saboda shegen mutum ne, ni kaɗai zan iya sashi abu yayi nan take"
"Na gode Malam, idan har aiki yayi kyau, kai ma zaka jidaɗi inshallah"
Wayarsa ya ɗauka ya kira, yayi tsowon minti ashiri yana lalasar mutumen sannan yaba Rashida waya suka yi magana ya faɗa mata inda zata same shi.
Bayan sun gama malamin ya kalleta yace
"Idan buƙatata da biya ki dawo ina son ganin ki, dan gaskiya akwai matsala a tare da ke, kuma akwai abunda yake shirin faruwa da ke, dole ne sai kin nemi taimako"
"Inshallah, zan dawo"
Da tsoro tayi masa sallama, tana ta tunanin wane irin matsala ne, zuciyarta nata raya mata lallai wannan malamin yana aiki kam.
Tafiyar mintuna arba'in suka yi, suka dawo cikin gari, kai tsaye tace direban ya nufi American Unique Estates da ita, a dai-dai inda ya kwatanta mata ta tsaya, ta kira number da Malamin ya bata ta mutumen tace masa tana gurin, sannan ta sallami direba fiye da yadda suka yi jingar.
Tsaye kawai take a gurin amman babu natsuwa a tare da ita, ji take kamar wani zai zo ya ganta. Bayan kamar mintuna asirin da biyar wata ƙafirar mota ta faka gabanta.
Wani Namiji ne mai shigar mutunci ya fito cikin motar tare da Amira.
"Ke ce Rashida wacca Malam ya aiko?"
Namijin ya tambaya.
"Eh nice"
Amira ta buɗe mata Motar.
"Shiga muje"
Da tsoro ta shiga motar, zuciyarta duk bata natsu da su ba.