Book 1 (End)
by @takori
ABOULKHAIR DA WAYAR AALIMAH!
Sai da ya gama komai da ya saba yi kafin ya kwanta, kama daga wanka, brush, shan black tea, ya daura pajamas sannan ya shige cikin quiltdinsa da wayar Aalimah a hannunsa. ‘Yar kankanuwar waya Daddy ya saya mata kirar Iphone. Contact list shi ne abin da ya fara shiga, contacts din ba su da yawa, ba su fi ashirin ba. Ya ci gaba da scrolling contactsdin, akwai mamere, watau Mamanta kenan, mon pere (Babanta), sai Bhaiyya, wato Yayanta Aboubacar da harshen India. Sai ta Daddy, ta Basma, ta Khaleesat, Malam Raazii, Kawu Oussama, Kawu Edrissa, Balkissa Eedrissa, Grandma Kasisi, Grandma Bintou. Sai lambobin maza guda biyar wadanda ya ga ba zai jurewa zamansu ba.
Alex ya fara gogewa, ya goge Harrison, ya goge Mr. Edward Proffessor. Bai san cewa course tutor dinsu ne ba ma. Harrison kuma course mate dinta ne. Lambar da ta rage guda daya ce ta tsaya masa a makoshi, kuma ya kasa goge ta. Akwai bukatar ya dauke ta a tasa wayar, sannan ya goge. ‘MAHMOUD’. Ba don komai ba sai don ya kawo karshen alakarsu ko ma wane ne. Har wani heart ta makala masa bayan ta rubuta sunansa. Bai yi mamaki ba, don yarinya kamar Aalimah ba yadda za a yi a ce ba ta da mashinshini har zuwa wannan lokacin. But he’s jealous, in ya ce jealous to guda daya kenan. He is very-very jealous! Don ya lura ko ma wane ne wannan Mahmoud din ba yau ya fara son Aalimah ba, kuma bai fara don watarana ya daina ba.
Zuciyarsa ba ta gama tsinkewa ba sai da ya shiga message inbox. Sakonnin Mahmoud din ne rututu masu barazanar tarwatsa kwanyarsa. Bai iya ci gaba da karantawa ba ya hada su duka ya goge su daga doron kasa. Abu daya ya dan kwantar da hankalinsa, ba reply mai zafi daga Aalimah, ga dukkan alamu ba ta damu da yin rubutu cikin waya ba, babu wani social media da ta bude, she only text Mahmoud twice, saying that she saw his messages, she’s doing morethan fine. She will call him when she is opportune, he know how tedious her studies is. (Sau biyu ta yi ma Mahmoud sako, inda tace ta ga sakonsa, tana nan lafiya, zata kira shi in ta samu dama, ya san yadda karatunta yake da tsauri). Wannan ne kadai ya dan sanyaya ransa. Amma ya rantse gobe sai ya raba Aalimah da Mahmoud yadda zuciyarsa za ta buga ya mutu ya huta.
Ya dauki lambar Daddynta, mamanta da ta Yaya Aboubacar. Lambobinsa ya zuba cikin wayar tata, ya yi saving da Mon Amour (MY LOVE da harshen faransa), sannan ya yi mata downloading din whatsapp application. Da niyyar cewa shi kadai zai dinga mata magana ta cikinsa, not even Daddy karshenta kenan. Sannan ya koma cikin gallery na wayar, duka yawanci selfie ne ita da Basma a makaranta, wani a mota, he can guess that she adores Basma a lot (tasu ta fi zuwa daya).
Murmushi ya yi da ya tuna Khaleesat ko Daddy bai cika shiri da ita ba sabida I don’t care attitude dinta. Tafi shiri da Mummy. Ya dade yana kallon kyakkyawar fuskar da ta zame masa madubin zuciya daga jiya zuwa yau. Ta rusa duk wasu plans da ya yi wa rayuwarsa, ta kuma zamo babban kalubalensa na rayuwa a yanzu. Mallakarta is the greatest challenge of his life now. Ban da barci ya fi kowa iya sata da Aboulkhair yau ma bai runtsa ba kamar yadda ya ga dare da rana jiya.
Amma yau ya yi barci yadda ya kamata da wata irin nutsuwa da ya dade bai samu ba a rayuwarsa.
Washegari, Aboulkhair ya yi wanka ya shirya cikin shirt da wando ‘yan gidan Nordstrom, rigar orange ce da ratsin baki, wandon fari tas. Sumar nan ta sha taza ta kwanta luf a kansa. Samun kansa ya yi da zakulo turaren da ya fi kowanne kamshi mai sanyi cikin tarin turarukansa masu ban sha’awa, sannan ya fesa. Ya fi son shi fiye da dukkan turarukansa, saboda Mu’az ke ba shi (SAUVAGE Dior). Duk wani abu kuma da ya fito hannun Mu’azzam is preciousa gun Aboulkhair. Ya san dai ba yau ya fara fesa turare ba, amma shi kansa ya san wanda ya fesa yau bai fesa shi don radin kansa ba.Is meant for AALIMAH ta ji yana kamshi.
Wani murmushi yake saki shi kadai yana yi wa kansa dariya. Sanda ya fito su ma duk sun yi shirin makaranta suna dining suna karyawa har Daddy, sai Aalimah da ke ta shige da fice daga kitchen zuwa dinning area din tana miqo musu abubuwan da suke bukata.
Sosai ya ji haushi, amma bai ce komai ba har ya zauna. Shi ma ita ta yi serving dinshi ba tare da ta yarda sun hada ido ba.
Ya dubi Basma, “Ina mai aikin Mummy?”
“Aal, ta hana ta zuwa by 6am ta ce ita za ta dinga yin breakfast, Easther ta yi lunch and dinner”.
Ya dubi Daddy ko zai ce wani abu? Ya ga bai ce komai ba, sai shi ma ya yi shiru. After all ita mace ce kuma rainon Nigeria, she might be willing to do so. Shi kansa ya fi son cin nata abincin a kan na Easther, tunda ya ci pounded yam sau daya. Amma anya hakan ba zai zamo takura a gare ta ba?
Muryar Daddy ya ji yana yi wa su Basma fada kan su dinga shiga kitchen din da safe tare da ita za su fi sauri, kuma su ma su koya. Ajiyar zuciya ya yi cikin jin dadi.
Fara cin abincin ya yi, su kuma suka koma sama don dauko jakunkunansu da mayafansu. Khaleesat da Yesmin da ma uniform ne a jikinsu. Daddy ya riga su ficewa, su ma mota suka wuce don su jira shi, bai dade ba ya gama ya fito. Kofar direba ya shiga ya rufe, sannan ya mika hannu ya bude kujerar gefensa. Basma za ta shiga, ya ce, “No, koma baya, daga yau seat dinta ne”.
Ta ce, “Who?”
Harara ya galla mata ba shiri ta shige bayan don ta lura daga zuwansa zuwa yau he’s a changed person. Aalimah ba da son ranta ba ta zauna a gaban, ba ta so ko kadan su Basma su fahimci tsakaninta da Yayansu akwai wani abu, kunya ta ke ji sosai balle ta san Basma da digimi da maida allura garma. Sai da suka hau titi sosai ya dan juyo ya dube ta. Ta yi masa kyau sosai cikin doguwar riga ruwan kasa da veil dinta sakar kasar Kuwait. Takardun hannunta ta ke dubawa tana da gwaji yau (test). A duk lokacin da ya dube ta his feelings for her heightened bai san dalili ba. Cikin tattausar murya ya ce, “Babu gaisuwa Aalimah?”
Ko su Basma da ke baya ba su ji abin da ya ce ba, sabida raunin muryarsa. Ba tare da ta dago ba ta ce,
“Bonjour?”
Ya amsa, sannan ya ce, “What time is your interval (lokaci na hutu tsakanin wata lakcar da wata). Ta gaya masa.
Daidai lokacin da suka shigo Boston campus ya ajiye su ya juya. Ko da ya koma gida kasa hassala komai ya yi, sai tunanin Aalimah. Tashi zaune ya yi daga kan resting chair ta falon da yake kwance a kai, ya hau saman gidansu. Akwai wani balcony da galiban daddy ke zama da yamma ya yi karatun jarida a weekends can ya je ya zauna. Wayarsa ya lalubo ya nemo lambobin da ya yi saving jiya daga wayar Aalimah ya kira ‘UNCLE MONSOUR’. Gara ya fara yi wa kansa yakin neman auren Aalimah kafin Daddy ya gama yangarsa ya fara nasa.
Dr. Monsour Raazee, na zaune cikin ofishinsa da ke cikin sabuwar jami’ar Bayero yana marking takardun dalibai ya ga shigowar kiran mai dauke da lambobin kasar Amurka cikin wayarsa. Amma kuma ba Aalimah ba ce ba, kuma ba yayansa Ishaq ba, sannan it is not his darling son MU’AZZAM ISHAQ RAAZII, wanda sati ba ya shigowa ya shude ba tare da ya kira shi ya gaishe shi ba, musamman a ranakun karshen mako. To ko Aalimah ce ta canza layi? Haka ya mika hannu ya sanya ta a handsfree yana ci gaba da marking din da yake yi saboda tsabar kwarewa da aikinsa.
“Assalamu alaikum Uncle”. Ya jiyo muryar saurayin mai wani irin accent shi ba bature ba, shi ba balarabe ba, ba ma kuma za ka sanya accent dinsa a jerin na Hausawa ba duk da uwarsa cikakkiyar bakanuwa ce.
“Ameenwa’alaikumus-salam warahmatullah, da wa nake magana?”
Kunya da jin nauyi da nadama baki daya sukayi rubdugu a kan Aboulkhair, a girmansa ba zai iya tuna rana ta karshe da ya kira wani cikin dangin mahaifinsa ya gaishe shi ba, tun suna yara Mummy ke gaya musu they don’t love them, they are always saying ‘baku da tarbiyyah’ don kawai ba sa sona!’
Ya runtse idonsa yana jin wata irin nadama tana ratsa shi. A shekarun girmansa kuma he is very busy with schools musamman da ya fara karatun jami’a ya bar iyayensa ma bakidaya ya tare a jami’a, sannan ga yanayin karatunsa, he hardly find time for himself ma balle ya tuna mutanen da suka shafe shi. Ko askin kansa ba ya samun damar yi sai gashin na neman rufe masa ido. Ko kadan bai dauko Mummy ba, sai idanunta da duhun fatarta, he is a perfect photocopy of his father. Mu’azzam ne mai kama da ita, sai dai shi kuma ya yi hasken fatar Daddy, bai yo yawan sumar kai ba, sannan he shaves regularly (yana yawan yin aski).
Ya yi nisa a tunani, wanda ya mantar da shi cewa ya kira waya har kawun ya amsa. Muryar Kawun nasa ya ji yana tambaya cikin sanyin murya,
“Ko ABOULKHAIR ne?”
Ya cije labbansa cikin mamaki mai cakude da jin kunya da jin dadi duk a lokaci daya, ya ce,
“Ni ne Uncle”.
“I guessed”. Inji Dr. Mansour, “Ya ya ku ke, ya Babanka da ‘yan uwanka da mahaifiyarku?”
“Suna lafiya Uncle, I’m sorry for not calling you. Nayi nadama uncle.Uncle na ji kunyarka, amma ka yarda da niban taba mantawa da ku ba. Bana tare da iyaye na, ina karatu a Louisiana shekaru hudu kenan. Yanzu ma hutu na zo, kuma nanda sati hudu zan koma.I need your blessing!”.
Hausa yake iyakar iyawarsa tana subuce masa yana cakudo ta da turanci.
Dr. Monsour ya yi murmushi kamar yaron na kallonsa. Hamdala yake yi cikin zuciyarsa, addu’ar mahaifinsu da kalaman mahaifiyarsu ba su fadi a banza ba. Inna Kasisi ta sha cewa kowa ya daina damuwa da rayuwar Ishaq da ‘ya’yansa, idan ‘ya’yan na halal ne da kansu za su neme su. Malam kuwa ya sha cewa, “Da izinin Allah kan ‘ya’yansa da jikokinsa ba zai rabu ba ko bayan ransa. Ishaq da ‘ya’yansa da suka zama saniyar ware, yana rokon Allah ya karkato da hankalinsu gida, su rungumi ‘yan uwansu da iyayensu.
Kiran sunan yaron ya yi wanda ya fada cikin damuwa da shirun Kawun nasa.
Ya ce, “Aboulkhair, Aboulkhair! Kana jina?”
“Eh Uncle, I’m still online”.
Ya ce, “Ka daina damuwa, I’m your father, an halicci iyaye da dabi’ar zama masu karbar uzurin ‘ya’yansu. Na ji uzurinka, kuma in gaya maka ban taba damuwa da hakan ba, tunda na san lafiya ku ke. Amma ka dinga koyi da dan uwanka wajen kula da zumunci. Ya fi ka yawan hidimomi tunda shi babban ma’aikaci ne, still ya rike danginsa kam-kam. He is not with us, but we are feeling him beside us. (Baya tareda mu, amma jinsa muke kamar a gefen mu). Sallar bara da ta wuce tare da shi muka yi sallar idi a Nijar, ya je Zinder (garin su Inna Kasisi), ya je Tessaoua (garin su Malam Ibrahim Razee), har Arlit (garin su Inna Bintou) ba inda bai je ya ga dangi su ma sun ganshi ba. Ga albarkar kakanninsa da iyayensa yana sha ta ko’ina, ba ka yi wa kanka kwadayin hakan?”
Ya ci gaba da kawo masa ayoyi da hadisai da Allah ya yi umarni da zumunci, da kyautata shi, musamman ga maza kuma manyan jikoki a family. A karshe ya saka masa albarka, shi kuma ya yi alkawarin zai ci gaba da kiran kowa. Ya ce yana son kiran Maman Aalimah da yaya Aboubacar, amma bai sani ba ko sun manta shi?
Dr. Mansur ya ce, “You are welcome to call everybody within your family, babu wanda ya manta da ku ko don Mu’azzam. Allah ya yi muku albarka bakidaya”.
Bayan sun gama waya da Daddyn Aalimah ya dade a wurin, ya jingina da karfen balcony din zuciyarsa ta yi masa dadi. Sai kuma ya fada wani tunanin. Wato duk yadda yake da tabbacin ya fi kowa sanin YayansaMu’az har gobe bai zo rabi a sanin nasa ba! Abubuwan mamakinsa yawa gare su, kuma ba wanda ya isa ya san cikinsa hatta da iyayensuidan aka zo maganar abin alkhairin da yake yi a rayuwa. Sai dai ya tsinta nan da can kuma bai isa ya yi masa zancen ba, yanzu zai ce bai san maganar ba, ko ya ce ya kyale shi da unnecessary magana, ba ya son yin magana mai tsawo.
Ajiye tunanin Mu’azzam ya yi a gefe, don abubuwan mamakinsa ba masu karewa ba ne. He is just far beyond everyone’s assumption (ya wuce da sanin kowa). He is a patient, amma abubuwan da yake yi da yadda yake gudanar da rayuwarsa masu lafiya dari bisa dari ba za su iya ba.
Maman Aalimah Hajiya Aseeyaita ce mutum ta biyu da ya kira. Ita kam ba ta gane shi ba, sai da ya kara da bayanin kansa sannan ta gane. Sosai ta shiga janshi da hira, tana tambayar kannensa da mamanshi. Abin da ya ba shi mamaki, ba ta tambayi Aalimah ba, sai su Basma. Abin ya burge shi kwarai da gaske. Kawaici wani abu ne mai kyau cikin al’adun malam bahaushe, wanda Mamansa ba ta sanshi ba. A gaban kowa, kiri-kiri ta ke nuna son ‘ya’yanta da nuna babu ya su a duniya. Su ne kadai ‘ya’ya. Sannan ya kira Yaya Aboubacar.
Aboubacar sa’an Aboulkhair ne, bai fi watanni biyu Aboulkhair ya ba shi ba. Don haka hira sosai suka yi, irin ta ‘yan uwa. Ya ce ya gaida Aalimah duk da ba a fi kwana biyu ba sun yi magana shi da ita.
Yau dai Aboulkhair ya yi wa kamfanin wayarsa na VERIZON ciniki mai dumbin yawa, don bayan gama wayarshi da ‘yan gidan su Aalimah ‘yan Nijar ya hau kira, duk wasu manya a dangin ba wanda bai kira ya wanke kansa ba.
Inna Kasisi na yi masa tirjiya da hutsancinta, haka ya yi ta lallashinta har ta ware suka yi hira. Ya yi mata alkawarin he will keep calling kuma zai zo Nijar next hutunsa. Albarka kuma ya sha ta wajen malam da manyan Uncles dinsa. Ba su da riko ko kadan sai kaunar junansu. Ya kuma yi mamakin matsayin da Mu’azzam ke da shi a family dinsu. Ya raina kansa, don ba wanda zai yi magana da shi har ya kare bai tambayi Mu’az ba, bai fada mishi alherin da yake masa ba. A karshe da ya gama wayar Mu’azzam din ya kira. Yana dagawa cikin sauri ya ce da shi,
“At office, call later”.
Murmushi ya yi yana jin kaunar Yayan nasa na kara ratsa shi.
A fili ya ce,
“Ni ma ba wani abu zan ce maka ba. I just want to hear your voice, (kawai ina son jin muryar ka ne) kuma na ji”.
Zuwa lokacin azahar ta yi, dakinsa ya koma ya yi sallah, ba ya bukatar abinci don haka ya je ya yi sabgoginsa a cikin gari zuwa lokacin da Aalimah ta gaya masa tana da sarari. Yana yin parking kuwa ya gansu suna fitowa, daga dakin laccar tana rungume da folder.
Tsura mata ido ya yi tana nufo motarshi. A zuciyarsa tambayar kansa yake yi, me ya fi so a Aalimah? A gaggauce amsar ta halarto zuciyarsa… Yana son komai nata… komai ta yi abin burgewa ne a idonsa. He loves her dearly.
Har ta shigo ta zauna a gefensa bai sani ba. Sai da ta hada yatsunta biyu suka yi kas! A kunnensa. Kallonta ya yi, sannan ya dauko wayarta daga inda ya ajiye ta ya lalubo lamba ya danna kira. Ba ta ankara ba ta ji muryar Mahmoud na amsawa da sallamarsa, yana tambayar ina ta shiga kwana biyu? Kafin ta kwace wayar ya bada amsa,
“Ba ita ba ce, mijinta ne, kuma Yayanta, wanda ya bada sadakinta ga iyayenta. This is for your information not to call or text my wife again”. Ya datse kiran.
Aalimah ta ji ba dadi har fuskarta ta nuna.Mahmoud yana da mutunci a idonta ko don Yaya Aboubacar. Ko rabuwa za ta yi da shi ba za ta so su yi irin wannan rabuwar ba.
Kallonta yake kai tsaye cikin idanunta don ganin reaction dinta, amma ya kasa fahimtar komai ban da rashin jin dadin da idanunta suka nuna. Magana ta yi a hankali cikin rarrashi don fahimtar cewa so yake su yi rigima.
“Haba Yayan Basma? Abokin Yaya Aboubacar ne kuma…..” Ta yi shiru ta kasa ci gaba.
“…... Kuma saurayin ki”, yayi maza ya karasa mata. “Kawai ki fashe da kuka na raba ki da saurayinki…”.
Turo baki ta yi cikin shagwaba, “…Ni ba saurayina ba ne, cewa zan yi muna mutunci ni da shi fa… Ni ba ni da saurayi…”.
Ganin yadda yake kallon bakin nata admiringly ya sanya ta maida bakin nata ta kintse, ta kuma sunkuyar da kanta. Murmushi ta shiga saki kasa-kasa a sanda ya sanyaya murya ya ce da ita,
“Har NI?”
Tafukanta ta kai ta rufe fuskarta tana murmushi,
“Kai ma Yayana ne”.
“Ko?” Ya tambaye ta.
Bai jira amsarta ba ya ci gaba, “Za mu bambance hakan ranar da aka daura mana aure”.
Ta kara tusa fuskar tata cikin tafukan nata, cikin matsananciyar jin kunya.
Wayarta ya jefa mata kan cinyarta ya tada motar, “Na bude miki Whatsapp, Daddy ya amince min in dinga magana da ke ta waya, daga yau har zuwa ranar da zai karbi sadakinki. Idan ki ka yi chatting da wannan mutumin Allah ya isa”.
Dariya ta soma yi tana fita daga motar. Ganin yadda yake maganar with confidence kamar ta furta masa tana sonshi ita ma. Tana son mutum mai courage, wanda ya iya yarda da kansa.
Ko da ta koma class ta bude littafin da ta ke rubutu, samun hannunta ta yi da rubuta haruffan guda tara, ‘A…B…U…L…K…H…A…I…R, ta zagaye su da zanen zuciya (heart). Kafin ta ankara cewa a cikin littafin daukar laccarta ta ke yi. Hannu ta kai ta dafe goshinta tana ambaton sunan Allah, me ke damuna ni Aalimah? Me ya shiga kaina? Me zuciyata ke nufi da ni a kan Yayan Basma? Ina zan kai Mahmoud wanda ke can wata duniya yana jirana? To amma me? The feelings are entirely not equal! Ko kusa da juna ba su zo ba, infact, abin da ta ke ji a kan Aboulkhair ba ta taba jin irinsa a kan kowa a duniya ba.
******
Shi ya dawo ya dauke su. A kofar gida bayan su Basma sun fito daga mota ya dakatar da ita. Tsare gida ya yi sosai, sannan ya jefo mata tambaya.
“Will you call him (Za ki kira shi)?”
Da lumsassun idanunta masu gazar-gazar eye-lashes ta dago ta dube shi. Ita ma ta jefa masa tambayar, “Who?”
Don ita shaf! Ta manta sun yi zancen Mahmoud dazu.
Runtse idanunsa ya yi ya kasa budewa, shi kadai ya san kishin Mahmoud da ke cinsa a zuci. Bai sani ba ko bayan lambarsa da ya goge daga cikin wayarta ko ta haddace lambar a cikin kanta. He don’t know how intimate they are. Daga yadda Mahmoud ke magana da kuma sakonninsa da ya karanta ya fahimci sun jima tare, kuma ta sabakiransa. Wannan tunanin ya tsaye masa a zuciya ya hana shi sukuni. Wani zazzafan so yake wa Aalimah, wanda shi kanshi yake ba shi tsoro.
Sai da fuskarsa ta yi jajawur sannan ya ce da ita,
“Saurayinki!”
Murmushi ta yi ta dauke idonta a kansa, sannan ta ce, “Ba zan iya sanin cewa zan kira shi ko ba zan kira shi ba, sai ka gaya min sunan budurwarka”.
Bata fuska ya yi ya yamutse ta abin dariya kamar wanda aka nunawa kashi.
“But, I don’t have, I have only friends”.
Murguda masa baki ta yi ta fice daga motar, sai kuma ta dawo ta zura kanta ta tagar murfin motar a hankali ta ce,
“Ni ma Mahmoud abokina ne!”.
Da gudu-gudu ta bi bayan su Basma ganin yadda yanayin fuskarsa ya canza bakidaya. Tana tsoron ya kife ta da mari, duk da ta san ba zai yi hakan ba.
Ficewa ya yi da motar ya fasa shiga gidan. Yana fitowa mota kirar RollsRoyce ta sanyo hancinta harabar gidan, wadda ke cike da korran shuke-shuken grass carpet. Tun daga nesa ya gane ko motar waye, “Mummy”. Fasa zuwa inda ya yi niyya ya yi, ya yi reverseya dawo da baya. A tare suka yi parking a harabar adana motocinsu, suka kuma fito a tare. Da sassarfa ya karasa gare ta ita ma ta taho suka hade, ta rungume shi. Sun dade ba su ga juna ba, kewar mai yawa ce. Duk da yana kallon mahaifiyarsa matsayin mai laifi ga rayuwar mahaifinsu, hakan ba ya nufin matsayinta ya canza a zuciyarsa ko wani abu makamancin hakan. A mother is always a mother!
Tana rike da hannunsa suka shiga gidan, su dai su Basma, Aalimah, Khaleesat da Yesmin sai ganin Mummynsu suka yi a tsakiyar falonsu. Wani ihun murna da kowaccensu ta saka ta yo kan Mummyn ta rungume ta, ba ka jin komai sai kalaman kewar juna da soyayyar junansu.
Aalimah ta koma gefe tana kallon soyayyar UWA da ‘ya’yanta, wata irin kewar iyayenta ta kama ta. Ta koma gefe ta rakube kamar marainiya.
Sam ba ta ga tahowar Abulkhair gare ta ba. Hannunta ya kamo ya soma janyo ta har gaban Mummy. Ta gintse farin cikin da ke kan fuskarta lokaci guda. Duk wata fara’a da ke kan fuskarta sai ta dauke. Girgiza mata kai Abulkhair ya shiga yi, sannan cikin nutsuwa ya soma magana.
“Mummy, Aalimah is saying welcome back to you”.
Aalimah ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na son zubowa. Kamar Anty Zulaiha ba za ta yi magana ba, sai kuma kwarjinin dan nata da ya kafe ta da kyawawan idanunshi ya cika mata ido.
Ta sassauta grinning din fuskarta, ta ce, “Ita ba ta da baki? Ko kai ne bakinta?”
Aalimah ta zube a kan gwiwoyinta a gaban Mummy Zulaiha cikin sanyin murya ta ce, “Welcome Mummy. And I’m sorry if I hurt you. I’m very sorry!”.
Aunty Zulaiha ta dan rufe idanunta, sannan ta bude ta dubi yarinyar. She’s innocent, tana da innocence looks. She’s looking just like her husband kamar shi ya haife ta. Yanayin su na sanyin hali iri daya ne. Wannan ya sa ta ke kama da su Basma. Tunda ta zo ba za ta ce ga wani abu da ta yi da ya bata mata rai ba. Tana shaping tarbiyyar su Basma ne kawai, ba lalata su ta ke yi ba. Sunkuyar da kanta ta yi kasa.
Basma ta ce, “PleaseMum talk to Aal, she’s our sister”.
Khaleesat ta ce, “She is nice Mummy, she cooks for us, she’s taking care of us very well in your absence (ki yi mata magana Mummy ‘yar uwarmu ce)”. In ji Basma (tana da kirki Mummy, tana dafa mana abinci, tana kula da mu da ba kya nan sosai)”. In ji Khaleesat.
“And she bought for me sweets also”. In ji Yesmin.
Duk sun daure ta da jijiyoyinta. Ko ita ce tafi kowa rashin adalci a duniya. Sai ta mika hannu ta kama hannun Aalimah. A hankali ta ce,
“Thank you”.
Dadi ya kama sudukkansu, kar dai Abulkhair ya ji labari. A haka Daddy ya shigo ya cimmasu. Tsaye ya yi a tsakiyar falon ya kama kugu yana kare mata kallo. Ga hannunta cikin na Aalimah shi ne abin da ya dan sanyaya zuciyarsa. Sama ya wuce rike da suitcase dinsa ba tare da ya ce da kowa komai ba.
Mikewa Mummy ta yi ta bi bayanshi, yaran kuma kowacce ta kama sabgar gabanta cike da farin ciki. Aalimah ta mike za ta shiga kitchen suka hada ido da Abulkhair da ke zaune a kan daya daga cikin kujerun dining table ya zuba mata ido. Wani irin sonshi da kaunarshi ya kara mamaye ta.
Murmushi ta hau yi masa ba ta san tana yi ba, ya wani dauke kai ya juya mata baya. Sai a lokacin ta tuna ashe fa fushi yake yi da ita ta yi masa laifi. Karasawa ta yi kicin don yin abin da ta nufa, amma sai ta ji duk ta damu, zuciyarta ta yi mata babu dadi da fushin nasa.
Da ta fito daga kicin din kuma ba ta same shi a falon ba ya fice ya bar gidan. Tana jiyo hucin motarsa don ba za ta ce kara ba. Motocin Daddy are not making sounds wato (ba sa kara).
A can dakin iyayen suna can suna tafka ta a tsakaninsu, Daddy ya ce, don me ta dawo masa gida bai neme ta ba? Ta ce, saboda gidan mijina ne, gidan ‘ya’yana, kuma mijina ba sakina ya yi ba. Nan kuma ta kwantar da kai ta shiga ba shi haquri har da kukanta.
Mikewa ya yi zai bar mata dakin ta kamo shi ta kankame, ta shiga rantsuwa tana daukar masa alkawarin wannan karon ta dau laifinta, za ta canza ya ba ta dama, she has no business ( ba ruwanta) da kowa nasa da duk wanda zai kawo gidansa. Cewa ya yi I’m tired(na gaji) da tuban muzurinki.You will never change Zulaihatu, (bazaki taba canzawa ba) mai hali ba ya fasa halinsa, I’m tired of all these, ya kamata mu bai wa juna sarari, har kowannenmu ya je ya yi kwas a kan halin dan uwansa. Na kasa saninki fully har gobe, in na ci gaba da biye miki halaka ni za ki yi…!”
Yadda ta rungume shi cikin jikinta da runguma mai tsananin karfi, jikinta yana rawa da karkarwa da jin kalamansa, shi ya hana shi karasa magana. They missed each other to such an extent… don haka duk wani mai korafi ma a tsakaninsu ya adana korafin nasa a gefe zuwa gaba. Amma ko daga yanayin Zulaiha a yau da yanayin bugun numfashinta ya san ta yi nadama wannan karon, wadda yake fatan Allah ya sa ta dore. In kuma hakan bai yiwu ba, duk son da yake mata wannan karon zai ba ta mamaki ta inda ba ta zata ba. Al’amarin mace da miji sai Allah, cikin daren suka shirya kansu.
A can dakin su Aalimah kuma, kowa ya yi barci ya barta. Wayarta ce a hannunta tana jira ko Abulkhair zai kirata? Ta kasa barci ko kankani. Ganin har karfe sha daya na dare bai kiratan ba bai kuma yi mata sako ba ya tabbatar mata fushin nasa na gaske ne. Ji ta yi duk ta tsani kanta, don me zata batawa mutum mai kyakkyawar zuciya irin Abulkhair? Mai sonka shi yake KISHIN KA, shi ya damu da al’amarinka. To amma don me zai damu kansa da zancen Mahmoud? Ya sa pressure sosai a kan zancensa. Ita ba ta dauki al’amarin Mahmoud da zafi ba, ba ta yi masa alkawarin za ta aure shi ba amma yafi karfin wulakanci a idanunta.
Abin da ta san ta ce da shi shi ne, “We can not runaway from our destinies but she is hoping that destiny tied them together (ba za mu iya gujewa kaddarorinmu ba, amma tana fatan kaddarar ta barsu tare). To kuma ga kaddarar ta yi gardama. Kamata yayi Aboulkhair ya dubi present dinta ba past dinta ba. Damuwa ta yi damuwa a zuciyar Aalimah, ta jefa zuciyarta cikin wani yanayi mara dadi. Ba ta san ta kamu da son Abulkhair har hakaba sai yanzu da ta ke ganin yana kokarin barinta kan abin da bai kai ya kawo ba a ganinta.
Da gaske Mahmoud ya fi kama da aboki fiye da saurayi a zuciyarta. Akwai sabo a tsakaninsu, duk da shi ba hakan ba ne a tashi zuciyar. Amma a halin yanzu ji ta ke zata iya komai don ta samu Abulkhair, farin cikinsa da kwanciyar hankalinsa ya fiye mata komai, hada da wannan karatun da ta ke yi kuwa, za ta iya barinshi in har barin nasa na nufin mallakar Aboulkhair a matsayin miji.
Ba ta da masaniyar cewar Abulkhair ya sanya lambar wayarsa a ciki ya adana, sai ganin wani lafiyayyen french word ta yi yana yawo a fuskar wayarta, mai nuna shigowar kira; Ma cherie, wato My love da harshen faransa. Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki ta yunkura ta mike zaune. Sannan ta hau juyawa damanta da hagunta kamar munafuka tana kallon su Basma don tabbatar da barci suke ko idonsu biyu? Ta tabbatar sun yi nisa a barcinsu sai ta lallaba ta shige toilet da wayar a hannunta.
Zuwa lokacin kiran ya katse wani ya kara shigowa. Zama ta yi a gefen bath tube, sannan ta yi sliding wajen amsa kiran.
“Not asleep like me?”
Ta ji muryarsa cikin damuwa tana tambayarta.
“Ta ya ya zan iya barci kana fushi da ni Yayan Basma?” Muryar da ta yi amfani da ita wajen yin maganar ta nuna zahirin damuwar da ta ke ciki.
Tana jin yadda Abulkhair ya sauke ajiyar zuciya, “Ban san kin damu da ni har haka ba, da ban sa kaina cikin damuwa haka ba. I thought you love him, since you cannot erase him from your memories, you want your relationship to continue…” ( na zaci kina sonsa, tunda bazaki iya goge shi daga tunanin ki ba, kina son alaqarku ta cigaba).
Dan runtse ido ta yi, tone din muryarsa na kassara duk wani sauran kwarin gwiwar da ta ke da shi na yi masa bayanin da zai kwantar da hankalinsa. Da kyar ta iya yafito sauti daga makogaronta.
“He is not in my memories, he is where he is (ba ya cikin tunanina, yana dai inda yake). I feel nothing for him” (bana jin komai akansa).
Abulkhair ya kara nitsewa cikin duvet dinsa. Murmushi yake yi wannan karon, duk wata damuwar da ya sanya kansa ya neme ta ya rasa. Murmushin da ake kira daga kunne zuwa kunne don fadinsa.
“Ni kuma fa? A wane bangare aka sanya nawa feeling din? Tunda na shigo gidan nan na rasa kaina, na zama ba ni ba Aal, duk bugun da zuciyata za ta yi ke ce a cikinsa. Aalimah, I want to say it loud I love you… ba zan taba komawa yadda na zo ba sai na samu amsar bakinki. Ki gaya min komai kankantar kalmar da zan amince ba ni kadai nake wahala ba. Amma in kin fi son wancan mutumin don Allah kada ki gaya min, it will go away with my last breadth (zai tafi da numfashina na karshe)”.
Tun da ya fara magana AAlimah ke jin wasu bululluka da suka danne zuciyarta na rugurguzowa suna kara dasa shi a zuciyarta. Zuciyar ta zama ‘yar shafal babu sauran damuwa a cikinta. Lumshe idonta ta yi ita kadai ta ke blushing tana rufe ido tana budewa. Ci gaba ya yi da gaya mata duk abubuwan da yake fama da su cikin zuciyarsa a kanta yana kuma rokon mafi kankantar kalma daga gareta mai nuna kauana ko yaya a gareshi. Kwalla ta ji ta taru a idonta, ta so da kaunar Abulkhair da kuma tausayinsa duka a lokaci daya.
Ta samu kanta a mai tambayar kanta me ta ke da shi da har dan gata irin Abulkhair zai mace a soyayyarta haka? Yaya Aboubacar ya sha cewa she’s the ugliest of their house (itace mafi muni a gidansu). Hancinta kamar an dosana mata shi, idonta kamar kwan zabo, bakinta kamar gidan tsutsa. Ta tuno suffa da kira mai zati irin na Aboulkhair, amma duk bai duba wannan ba a haka yake sonta.
Abulkhair ya fidda ran samun raddi daga Aalimah, yana shirin kashewa ya san yadda zai yi ya yi jinyar zuciyarsa ya jiyo ta tana cewa.
“Ina jin fiyeda abinda kake ji, na fara son ka daga lokacin da na dora idona a kanka. Na kasa barci sabida tunanin kana fushi da ni. Ban taba soyayyya ba sai a kan ka. I love you ABOULKHAIR!”. .
This is the beginning,kuma farkon kaddarorin rayuwar Aalimah.
******
Washegari Mummy ta koma aiki, tsakaninta da Aalimah kadaran-kadahan, babu tsana babu hantara, amma babu soyayyah. Duk hidimominta da ‘ya’yanta ta ke yi ba ta sanya ta. Ba ta sanya ta a shirginta balle ta dame ta, sabgogin gabanta kawai ta ke yi. Aalimah, ba ta sanya hakan a ranta ba balle ya dame ta, sai ma wani ladabi na musamman da ta ke yi wa Mummyn kamar uwar da ta haife ta, ko da Mummyn ba za ta nuna appreciation ba.
Ta dora wa kanta gyaran komai na Mummyn wanda Easther ke yi kamar gyaran kayan sanyawarta, shirya mata takardun office in ta hargitse, rike mata jaka zuwa mota, gaisuwa da tsugunno har kasa. Taya ta hidimar gida, da kula da Yesmin saboda ita kanta Easther ayyukan gidan wani lokacin suna fin karfinta kasancewar ita kadai ta ke komai da komai, Mummy ba ta son yawan ‘yan aiki kada su cika mata gida, don haka Aalimah ta karbi rabin hidimar gidan in dai tana gida ko ba ta da lacca ko a karshen sati dan abin da su Basma ke yi a gidan bai taka kara ba balle ya karya. A ganin Aalimah, a yanzu kam she can do anything for Mummy in dai za ta barta ta rayu da danta. Wanda ranshi ne kawai ba ya cirowa ya bata saboda so da kauna.
Ya ci gaba da kai su makaranta da dauko su da komawa wajen Aalimah su sha hirar soyayyarsu a dukkan intervals dinta, in dare ya yi kuwa lokacin bude ofishin soyayyarsu kenan a waya, yadda suke son junansu ba sa son karatun da suke yi. Tun Basma ba ta ba su hankalinta don ta dauka haduwar jini ce, har ta soma disa wa alakarsu dindimemiyar ayar tambaya.
Mummy kam ba ta fahimci komai ba, har gobe. Don hasashenta da hankalinta bai taba hasaso mata hakan za ta iya kasancewa ba. Khaleesat kam babu harkar kowa a gabanta balle ta damu da sanin me wani nata yake ciki. She’s always busy with her text books and islamic lesson. Basma ta sha kama Aalimah na yin night call a toilet, sai dai ba ta san da wa ta ke yi ba, ta ma fi zaton wannan nataccen saurayin nata na Nigeria ne. Abin da ya fara cika mata idanu shi ne kusan kullum, Monsieur Abulkhair dinsu na makarantarsu, kuma duk sanda ta zo neman Aalimah za ta gansu tare. Mafiyawan lokuta karatu suke yiyana koyar da Aalimah lissafi da sauran abin da ya shige mata duhu, sai dai idanunsu kadai za ka kalla ka hango wani kwantaccen al’amari da suke dauke da shi ga junansu. Kasa boye tambayoyinta ta yi rannan ta tambayi Aalimah a kan hanyarsu ta isa ga inda Abulkhair ya yi parking domin su tafi gida.
“Is Monsieur Abulkhair in love with you?” Ta yi tambayar ne don shakuwar da ta ke gani a tsakaninsu ta wuce hankalinta, amma ba wai don akwai wani abu a ranta game da hakan ba, so ta ke ta tabbatar da abin da zuciyarta ke gaya mata.
Hararar da Aalimah ke jifanta da shi, ta kuma ki ba ta amsa ya tabbatar mata da zarginta. Dariya ta yi, sannan ta kai wa Aalimah dundu a baya.
“Ke da shi din kun dace, saboda dukkaninku halinku daya, charming, cheerfuland compossionate personality. Sai dai zan so in tuna miki rules din Daddy kafin shigowarmu makaranta, duk wadda ta sake ta yi saurayi, AURE!”.
A yadda Aalimah ke jin Abulkhair a ranta, she can give him the life itself(zata iaya bashi rayuwarta dungurungum) idan za ta iya, ba karatu kadai ba. Abulkhair, ba ya son tunowa cewa hutunsa ya zo karshe, zai koma Baton Rouge (Louisiana) kwanaki biyu masu zuwa.
Sosai Aalimah ke rokon Basma kada ta gaya wa Mummy komai a kansu. Da Basma ta tambayi dalili, sai ta ce, “Mummy ta fara sona Basma, mun fara samun fahimtar juna, I don’t want to lose this love from her, (bana son rasa wannan soyayyar daga gareta) tunda ban san yadda za ta karbi al’amarin ba”.
Basma ta yarda da uzurinta, amma zuwa can sai ta ce, “But she must know (dole ta sani) tunda karewa ma jikoki za ki kawo mata!”.
“Sai ki bari in jikokin sun zo sai su fada mata da kansu”.
******
Yau asabar, ta kama da yammacin yau din Abulkhair zai bi jirgin kasa zuwa inda ya fito. Tun safe yake dacin rai, Aalimah ta shirya masa tun bai kifar ba. Gefe ta koma ta langabe kai abin tausayi, sai dai fa duk fadan nan da yake yi ya ki yarda ya kalli kwayar idanunta.
Mummy da ke kan dining din tana cin nata ta dube shi cikin jin haushi, “Amma me ye laifinta, ta bata lokacinta ta shirya maka ba tare da kowa ya sanya ta ba? Besides, the cooking is good, as far as I know, you love chips so much”.
“To yau na daina sonshi. Ni ban ce muku ma zan ci abinci ba, I’m not hungry”.
Aalimah na gefe tana kallon sakarci, uwar ta bi duk ta damu, sai lallaba shi ta ke kan ya ci, yana dada botsarewa.
Daddy ya shigo falon daga jogging din da ya je waje, ya tadda su a haka. Yana shigowa Mummy cikin damuwa ta soma gaya masa yadda aka yi.
“Idan aka kyale shi haka zai kama hanya ya tafi ciki ba komai”.
Ya ce, “Wa ya yi girkin?”
Ta ce, “Aalimah ce”.
“Kuma ya ce ba zai ci ba?”
Abulkhair ya sunkuyar da kai sai cika yake shi kadai. Daddy kwafa ya yi ya iso har gabansa ya ce, “Gara ma ka ci, ka ci na bankwana sai bayan wata ukku. Idan kuma ka sake ka kara ko kwana daya kan hutun nan I know how to deal with you. I will cancel even the phone calls”.
Da sauri ya dago ya dubi mahaifinsa, with shock in his eyes.
Ya ce, “Yes, I mean it”.
Aalimah ta sunkuyar da kai kamar ta ce, kasar ta tsage ta shige. Wato maganar da ya taba gaya mata na cewa, Daddy ya san da zancensu da gaske yake yi? Yau ina za ta sa kanta da kunyar kawunta? Mummy ta ce,
“Wane phone-call za a yi cancelling?”
Daddy bai ba ta amsa ba ya yi wucewarsa.
Basma ta shiga boye bakinta tana dariya, ganin yadda Monsieur ya kwalalo ido an ce za a hana shi waya da Aalimahrsa. Mummy dai ta kasa gane me suke ciki, ta tashi ta bar wajen.
Aalimah ta daga kafa za ta bi bayanta, ya sha gabanta. Ta dago idanunta da suka yi rauni ta dube shi, ta fi shi shiga damuwa a kan tafiyarsa. Ta fi shi shiga taraddadin yadda za ta iya ci gaba da rayuwa cikin Massachusetts babu shi, kanta ya bude da calculus da sauran danginsa, yanzun ba ta shayinsu. He made all her courses very clear and simple to her ta yadda ba ta bukatar taimakon kowanne namiji a Boston yanzu. Ya taka rawar mutane guda hudu a dan zaman da suka yi tare; dan uwa, aboki, malami kuma masoyi. Ya koyar da ita karatu ya koyar da ita yadda za ta so shi. Ba ta son ta soma tunanin ta yadda za ta fara kewarsa…!!!
“Is that the kind of adios we are going to do? (wannan ce irin sallamar da za mu yi?)” Cikin zuciyarta ta ce, “Kai zan tambaya. Ka zo kana ta dagawa iyayenka hankali for no reason (babu dalili) don kawai sun ce ka koma makaranta”.
Zancen zuci ta ke, ba ta san cewa a fili ta ke yi ba.
Yatsun hannunsa ya tura cikin tarin sumar kansa, yanayin fuskarsa kadai ya nuna tsantsar damuwar da yake ciki. “na rasa hanyar da zan nuna musu bana son komawashi ya sa na ce bari in ki cin abinci, watakila su gane zuciya ta, ba ta da lafiya su barni in zauna, amma ki ji abin da ya ce he will cancel even the phone call”.
Ya fada yana bata fuska kamar mai fadar wani mummunan abu.
Dariya Aalimah ta yi, ya bata rai sosai, “Au dariya ma ki ke mini? Ba komai, it’s all a matter of time. I will wait, as he insist, I know it is not easy to possessed a diamond, but when one have it, he will dowhat he wants with it (Zan jira, kamar yada ya dage sai na jira. Nasan ba abu ne mai sauki ba mallakar lu’u’lu’u(dutsen yakutu), amma idan mutum ya mallake shi zai yi abinda ya ga dama da shi”.
Wannan ita ce sallamar Aalimah da Abulkhair. Da yamma ya bi motar haya zuwa birnin Baton Rouge daga Boston inda Louisiana State University ta ke. Tafiya ce ta one hour kacal a tsakaninsu.
Yana zaune a seat dinsa yana ta juya wayar hannunsa. Daddy ya ce bai yarda ya kira Aalimah ba ko ya yi mata sako, sai a karshen mako kadai. Idan kuma ya ketare zai zare hannunsa ya barshi da dabararsa. Hukuncin is so painful so much unbearable… To amma ya zai yi? Yana son mallakar Aalimah kuma Daddy ya yi na’am, alfarma daya yake so ya yi masa kada ya hana ta karatu da soyayyah, don ya fita kunyar iyayenta. Shi kuma zai yi duk iya kokarinsa na samar da ita gare shi. Ya san jiran zai zamanto kamar jiran zuwan ranar tashin kiyama (seem like endless), amma ya amincewith time and Allah’s will da kuma tsawon numfashi komai mai tabbatuwane. .
Da tunani ya cika masa kwanya sai ya kira Yayansa Mu’az, shi kadai ne zai iya mantar da shi duk wani hali da yake ciki da salon tashi kaunar ta dan uwa which is exceptional. Mu’az na dagawa abin da ya fara cewa shi ne.
“Something or someone snatched away my brother from me. What is it? Or who is she?(Wani abu ko wani mutum ya janye min dan uwana daga gareni, menene wannan abun ko wacece ita?)”
Ajiyar zuciya Aboulkhair ya yi, wasu lokutan Mu’azzam kamar yana karantar shafukan zuciyarsa. Duk abin da yake ciki kafin ya gaya masa yake ganewa. Shi ne dai har gobe ya kasa gama sanin Mu’azzam. He is like a magician when it comes to reading minds (kamar wani mai sihiri yake in aka zo batun karantar zuciyar mutane, musamman shi Abulkhair). He care for him too much fiye da sauran kannensa. Tare suka yi duk wata dabdala ta kuruciya a birnin Washington kafin kaddara ta dawo da su zama a Boston (Massachusetts). Haka duk kaddarorin rayuwar Mu’az sun faru ne a kan idonsa. Wani abu da ya dasa wata irin kauna da jin kai a zuciyarsa. Ba don Mu’az ya fi son rayuwa shi kadai a inda yake ba, da zai iya hakura da karatu a Baton Rouge ya zauna tare da shi, ya ba shi dukkanin farin cikin da dan uwa zai iya bai wa dan uwansa duk da ya san hakan ba zai fidda shi daga halin da yake ciki ba.
‘Kwalla’ abu ce mai sauki daga idanun Abulkhair when it comes to MU’AZZAM. A yanzun ma kwallar ce ta cicciko idanunsa. Ya canza position din rikon wayar daga kunnen dama zuwa na hagu, amma bai yi magana ba. Mu’az a tausashe ya ce, “Na ce mene ne ya dauke hankalinka daga gare ni, ko WACE CE?”
With a very low tone ya ce, “AALIMAH”.
Dariya Mu’azzam ya yi irin dariyarshi mai tafe da gentleness tune.Wai yau Abulkhair ne da soyayyah! Abulkhair din da ya sha cewa, tunda ba zai yi aure ba, shi ma ba zai yi ba, yau shi ne da dakon soyayyah tun kan a kai ga zama Doctor din kula da shi da aka ci wa alwashi. Lallai ko wace ce wannan Aalimah ta ciri tuta, kuma zai so ya ganta. Dariyar Mu’az ta sanya Abulkhair rufe fuskarsa da tafin hannunsa, kamar Mu’az din na ganinsa. Wai shi ya ji kunya.
Mu’az ya ce,
“Then where will I find my psychiatric Doctor?”
Cikin tsokana ya yi maganar, kamar yana magana da karamin yaro.
Dariyar da Abulkhair yake yi ta mantar da shi duk wasu damuwoyinsa,
“They boy will keep striving to be what he promised to be. This is a promise!”.
(Yaron zai cigaba da kokari har sai ya zama abinda yayi alkawarin zama. Wannan alkawari ne)”.
Da wannan suka yi sallama.
******
Wani dare mai wuyar barci ga Aalimah. Ji ta ke kamar wani sashe na jikinta ba ya tare da ita. Abulkhair ya shigo rayuwarta da karfi, ya zauna da muhimmanci. Ta kasa barci sai juyi a kan gadonsu. Duk kuma juyin da ta yi sai ta ji amsa kuwwar dadadan kalamansa cikin kunnuwanta. Sai ta ga gilmawar kyakkyawar fuskarsa a idanunta. Idan wannan ita ce soyayyah, to ba ta yi mata kamun sauki ba, sannan aba ce mai wahala cikin zuciya da kwakwalwar dan Adam.
Da safe ta sha tsokana a wajen Basma, ganin yadda ta yi cooling ta rasa duk wani karsashinta, Basma ta ce, “Ko Baton Rouge za mu koma da karatu ne?”
Harararta ta yi ta sauka kasa, don taimaka wa Mummy a kitchen kafin zuwan Easther.
Daddy shi ya kai su makaranta ranar litinin, kamun Laraba kuma ya samar musu direba. Bakar fata ne dan kasar Cameroon. Sunansa Joseph, suka ci gaba da karatunsu cikin kwanciyar hankali. Tsakaninta da Mummy yana nan yadda yake, babu soyayya, amma babu kiyayyah. Kowa yana zaman kansa, zaman wanda ya ajiye shi. Sai dai ita kanta Mummy tana yabawa da dabi’un Aalimah a zuciyarta, furtawa ne ba za ta yi ba. Tana yabawa da kulawarta a kan yaranta da yadda suke canza dabi’u gradually ta hanyar koyi da ‘yar uwar tasu. Khaleesat har koyon daurin zani ta ke, tana kuma daukan karatun alkur’ani daga Aalimah da sauran al’adunmu na gargajiya, al’adun da ta ke wa kallon kauyanci, amma can a karkashin zuciyarta ta san wannan shi ne daidai, kuma ita ma ba sonta ba ne yaranta su lalace ba, tun a kan Mu’azzam ta yi sanyi da daukan dabi’un Turawa da tsanani, duk da cewa sun yi babban tasiri cikin rayuwarta. Ta manta da yawa daga nata al’adun da hukunce-hukuncen addini.
Zamanta da Aalimah da kasancewarta cikin ‘ya’yanta sai ya zamanto kamar ana tuna mata wasu abubuwa da ta manta. Ta kuma fara sassauta wa kanta kin yarinyar, ta yarda mutum rahma ne, amma jure zama da shi shi ne abin da yake mata wuya. Sai dai in ka yi katari da na kirki irin Aalimah ya fi ruwan sha saukin sha.
Babban abin da ke burge ta da Aalimah rashin kiwa, ba ta da son jikinta ko kankani, ga nutsuwa da rashin rawar kai, ga tsafta da kula da tsaftar jikinta. Ko fensir Yesmin ta yasar Aalimah ba za ta barshi ba sai ta dauke ta adana mata shi cikin jakar makarantarta. Sannan ba ta da rayuwa mai zafi irin ta Basma, ita kam Basma komai nata tana so ya zama na musamman. Kayayyakinta, abubuwan amfaninta sai ta tabbatar fitacce ne (designer) ne ko latest fashion. Zamanta da Basma da shakuwar da ke tsakaninsu bai sa ta yi adopting nata dabi’un ba, ita Basman ce ke tsintar nata tana hadawa da nata.
Abulkhair ya yi kokari sosai wajen maida hankali a kan karatunsa kamar yadda mahaifinsa da Yayansa ke so. Sun yi masa alkawarin tsaya masa a kan komai idan ya jajirce ya fiddo kwalin likitancinsa. Ba Aalimah kadai ba, har da karin guda uku bayan ita in yana so. Dakatar da su yake in sun fadi hakan, “She’s okey for me till eternity (ta ishe ni har abada)”.
Asabar na zagayowa ba ya iya hakurin yamma ko dare zai fara kiran waya kamar Allah ya aiko shi. Tana zama unease idan kiranshi ya shigo tana tare da kannensa ko iyayensa ba ta iya amsawa. Don haka duk sabar ta ke maida wayarta a vibrating ta soke ta a jikinta, da ta ji shigowar kiran Abulkhair za ta tsallake ko mene ne ta fita compound na lodge dinsu su sha hirarsu kamar sun hadiye juna, duk rabin hirar Abulkhair yana gaya mata yadda yake kewarta ne da yadda zuciyarsa ta makance a kaunarta. Yadda yake managing kafin zagayowar sati ya yi magana da ita. Hakuri ta ke ba shi ta karfafa masa gwiwa kan bin maganar Daddy. Tana tunatar da shi cewa abu mai kyau yake nufinsu da shi (good future). Ya ci gaba da rokon Allah ya barsu da rai da lafiya, shekaru hudu kamar yau ne. Sun fi yin magana a vedio call, yadda za su dinga ganin zahirin abin da ke zuciyar junansu cikin kwayan idanunsu. Ba ya kiranta da daddare, yana barinta ta yi barci isasshe. Wannan ya kara kauda hankalin kowa a kansu cikin gidan, ban da Basma da Daddy ba wanda ya san me suke ciki.
Sun yi jarrabawar karshen zangonsu lafiya, suka samu hutu na sati biyu. Ba da sanin kowannensu ba daddy ya gama yi musu shirin tafiya Nijar. Bai gaya musu ba, sai ana saura kwana biyu tashinsu. Yaran sai murna suke yi, don sun dade ba su je Nijar ba. Sai dai daddy ya ce da Aalimah ta rage murnarta, ba za su karasa Nigeria ba, sai a hutun karshen shekara zai shirya mata zuwan ita kadai. Murmushi kawai ta yi, daga Nijar har Kano duk gida ne a wurinta.
Mummy dai ta bada uzuri da office dinta. Kuma da gaske hakan ne, ba za su barta ba. Sai dai fa gaskiyar magana ko babu office ba za ta yarda ta bi su ba. Ta riga ta sa wa ranta dangin Ishaq ba sa sonta, don haka babu wata alaka tsakaninta da su. Ta yi kokari kwarai wajen dauke hankalinsa daga kansu da nuna wa ‘ya’yanta su manta da wanzuwarsu a doron kasa ba masoyansu ba ne.
Yau rana daya ya zo ya ce zai tafi Nijar da ‘ya’yansa bayan ‘yarsu da ya dauko ya kawo mata, har ya kore ta daga gidan a kanta! Ba ta san me yake ta canza mata Ishaq haka ba, ga shi duk wani karfi da ta ke da shi a idonsa ya yi sanyi, yanzu ba ta isa ya yi abu wanda bai gamshe ta ba ta ce da shi don me? Wani sabon Ishaq ne wannan ba wanda ta sani tun kuruciyarsu ba.
******
Jirgin Ethiopian Air ya sauke iyalin Ishaq Raazee a filin jiragen saman Diori Hamani International Airport da misalin karfe goma na safiyar lahadi agogonsu na can. Sun samu Hamoud babban dan Uncle Oussama yana jiran saukarsu, shi da Balkisa ‘yar Uncle Edrissa babbar kawa ga Aalimah kenan kaf dangi. Iyalin Ishaq sun zamo kamar wasu taurari sha kallo a cikin gidan Malam Ibrahim Raazee a yau saboda murjewa da kyan fatarsu, duk da cewa kowa a gidan fari ne kal! Amma nasu ya sha bamban da na kowa. Kan ka ce meye wannan? Gida da makwabta ya kacame da murnar zuwansu, aka shiga aiko da akussan abinci daga kowanne bangare. Inna Kasisi kam ko a launin fuska babu wani alamu da zai nuna maka ta yi farin ciki da zuwan nasu, sabgogin gabanta kawai ta ke na dora sanwar abincin rana na gidan bakidaya, kasancewar abincin gandu ake yi a gidan.
Inna Bintou ce ke ta hidima da su tun shigowarsu da ‘yammatan gidan (jikoki) sa’anninsu. Daddy Ishaq kasa yi wa Inna Bintou alkunya ya yi irin wadda ya saba, wato fara shiga sassanta, dakin mahaifiyarsa ya shiga kansa a duke yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Ta kara tsufa mai nuna alamun girma a tare da ita tsayin shekaru shidda da ya kwashe bai sako kafarsa a gidan iyayensa ba. Zama ya yi a kan kilishi ya tankwashe kafafunsa, zuciyarsa ta yi nauyi mai cakude da matsananciyar nadama. Sam ta ki yarda ta zauna a dakin, sai dai ta shigo ta dauki abu ta fita ba tare da ta dubi bigiren da yake ba.
Ko da ta gama girkinta ba ta zubo masa ba, amma ta zuba wa su Aalimah. Shinkafa fara tas! Da miyar dage-dage wadda ta ji fala-falan ganyen kabeji da naman rakumi zuku-zuku. Abincin ya yi masa kyau a ido, ya kuma ba shi sha’awa. Ya shiga tunano yadda suke santin abincin Innar shi da yayyensa Oussama, Edrissa da kaninsa Mansour da sauran kannensu ‘ya’yan Inna Bintou. Da yake a faranti guda ake zuba musu, in an cinye a yi kari, kafin a zo karshe a yi wawa a rikice da kokawa. Kwalla ta ciko idanunsa, amma bai bari ta gangaro ba.
Reaction din Inna ya nuna masa Inna tana fushi da shi, duka tsayin wannan lokacin tana kullace da shi a kan banzatar da ita din da ya yi, ya shiga tambayar kansa me ya shiga kansa? All these while da ya manta da iyayensa, ya manta da girman hakkinsu a kanshi da kulawar da Allah ya ce ya ba su.
A lokacin ne Malam ya dawo daga rangadin da ya tafi wajen rakumansa a can wani kebantaccen muhalli. Tsufa ya bayyana sosai a tare da shi. Inna Bintou ce ta je ta sanar da shi zuwansu. Ko abinci kasa ci ya yi sai da aka kira mishi jikokin nashi, tare suka ci abinci a kwano guda yana tambayar Aalimah yanayin karatunta. Ta gaya masa komai lafiya, sannan ya ce da Basma, “Ina Mu’azzam? Ina kuma Abulkhair?” Cikin harshen buzanci.
Daddy yana yi musu sosai don haka suna ji sama-sama, sai ta juya nata harshen ta soma ba shi amsa cikin yaren Faransa.
“Monsiuer Abulkhair ya koma makaranta, bai ma san za mu zo nan ba, na tabbatar maka da sai ya ajiye jarrabawar da yake yi ya zo. Mu’az kuma yana nan yadda yake, annoying kamar koyaushe. Ya fi son rayuwa a LAS VEGAS fiye da ko’ina a duniya. Ba ya zuwa gidanmu don wai muna yi masa hayaniya. Mum and Dad, su suke zuwa wajen Mu’azzam. Grand-pere (kakanmu) Mu’az ba ya son mu ko kadan, Monsiuer Abulkhair kadai yake so a cikinmu. Ba dama mu yi magana in yana zaune he will throw a tantrum (zai yi masifa). He is the most annoying person in the world (ya fi kowa ban haushi a duniya), watakila shi ya sa ya kasa samun mata”. Ta karasa cikin dariya.
Tunda ta fara kakan yake sauraronta, yana duba maganganunta filla-filla. Shi kuma a wurinsa Mu’azzam is a nice person fiye da dukkan jikokinsa. Duk sanda ya tambaye shi me ya hana shi aure, sai dukkan walwalar fuskarsa ta canza, idan ya takura da tambayar sai ya ce,
“Idan ba ka daina yi min zancen aure ba Mallam zan daina kiranka a waya, ba kun yi min auren ba? Me na tsinta a cikinsa?”
“Mu’azzam, ba mu muka yi maka aure ba, Babarka ce ta yi maka, babu saninmu, babu hannunmu. Babanka ya zo bagatatan ya ce za a daura maka aure don a ceci rayuwarka ba ka da lafiya, shi ya sa na amince wa Oussama ya je aka daura, amma ba mu san komai a kai ba”.
Dattijo Ibrahim Raazee ya yi ajiyar zuciya. Ya dubi jikokinsa biyar da ke zaune a wajen ciki har da Aalimah. Sannan ya kai dubansa ga Basma wadda ta fi kowa kaifin baki cikin jikokinsa. Ya ce da ita cikin auzinanci,
“He is not annoying, he is compassionate”.
Ta daga manyan idanunta irin nasa da suka gado, ta dube shi, “Non Grand pere (a’ah Kaka), he’s annoying, and he don’t like us”.
Sai ya yi murmushi ya kyale ta suka shiga wata hirar. Ya fahimci babu wanda zai kankare wannan belief din daga zuciyar Basma, na cewa, Yayanta mutum ne mai ban haushi, mara dadin mu’amala, sannan ba ya sonsu.
A can dakin Inna kasisi ta gama duk sabgoginta ba abin da ya rage mata a tsakar gidan, dole ta koma dakinta ta yi alwala ta tada sallah. Duk Daddyn Basma yana zaune sunkuye da kai ya kasa cin nau’ikan abincin da aka tara masa a gaba. Sai da ta idar ta yi addu’a ta shafa, sai ta ci gaba da zama a kan sallayarta. Ya ga cewa wannan ita ce damarsa ta karshe, kada ta sake ficewa a dakin.
Ya shiga rarrafawa a kan gwiwoyinsa har ya tadda ita. Hannayenta biyu ya kama ya rike cikin nashi, sai kuma ya kwantar da kai a cinyoyinta ya fashe da kuka.
Cikin kukan yake rokonta ta yafe masa, ya gane dukkan kurakuran da ya tafka da kansa, ya yi nadama ya dauki niyyar gyarawa, in ma cewa ta yi ya baro kasar Amurka ya dawo gida zai yi mata wannan biyayyar. Tun zuciyarta na tururi har ta soma karyewa. Shi din ba karamin yaro ba ne ya ba wa hamsin baya, har da furfurarsa. Amma ga shi yana kuka cikin tsananin nadama, ta gode wa Allah da hakan ta faru da sauran numfashinta. Ta san kaidi irin na mace balle annamimai irin Zulaiha, a kwayar idanunta babu soyayyar kowa sai kanta da ‘ya’yanta. Irinsu ne matan da ke kai mazajensu jahannama a dalilin fushin iyaye.
Lokaci ya yi da ita ma za ta nuna wa Zulaiha matsayinta na UWA mai cikakken iko a kan danta, ba ita da ba ta da ikon komai a kansa ba, shi ne ma yake da shi a kanta.
“Mon pils”. Ya ji ta ambata ayayin da ta kai hannunta cikin tarin sumar kansa. Mon pils na nufin DANA.
“Na yafe maka duniya da lahira. Ka je wajen mahaifinka ya dawo tun dazun”.
Dagowa ya yi idanunsa sharkaf da hawaye yana yi mata godiya. A yadda ya san taurin rai irin na Innarsa bai zaci wannan yafiyar ta gaggawa ba. Allah kadai ya san shekarun da ta kwashe tana kwankwadar damuwa da bacin rai a kansa.
Dakin Malam ya nufa, nan ya tadda su Aalimah suna ta shan hira da kakansu. Kana jin tashin muryar kowaccensu tun daga bakin kofa ana ta auzinanci mai cakude da faransanci, amma ban da ta Aalimah. Da ya yi sallama ya shigo duk suka yo kansa da magana, Aalimah tana daga gefen daman kakan tana danna wayar hannunta, nutsuwar yarinyar da rashin hayaniyarta na burge shi. Sai ta tuna masa da dansa Mu’azzam, haka yake shi ma, in za ka ji muryar mutum goma a wuri ba za ka ji tashi ba. Wani tsananin tausayin Mu’azzam ya kara lullube shi.
To shi Mu’az haka zai karasa rayuwarshi babu farin ciki babu future kawai don Allah ya dora masa lalura? Hawaye ya ji sun ciko idonsa, ya yi sauri ya dauke su da yatsun hannunshi, duk a kan idon mahaifinsa. Duban yaran ya yi, ya ce duk su je su yi sallar la’asar lokaci ya yi. Ya rage daga shi sai Babansa.
Sun gaisa sosai, da tambayar iyali da hidimomin rayuwa. Ya ba wa Malam hakurin tsawon lokacin da ya dauka bai zo gida ba. Ya roke shi ya taya shi kara bai wa Inna hakuri. Ya yi alkawarin canza tsarin rayuwarsa. Ya gane mutum komin matsayinsa a duniya shi ba komai ba ne in babu albarkar iyaye a tare da shi. Duk tsayin shekarun nan ba wai dadi ne ya boye shi ba, ko kwanciyar hankali. Sam ma zai iya cewa tun shekarunsa biyu a American rabonsa da kwanciyar hankali, wato tun haihuwar Abulkhair. Matsalar rashin lafiyar Mu’azzam bai taba barinsa cikin kwanciyar hankali ba, bai barshi ya tara komai ba, kawai dai ya fi karfin abin da iyalinsa za su ci da bukatocinsu, sai gidan da ya mallaka da abin hawa. Shi ma wani babban mai mulki a siyasar kasar da yake aiki a karkashinsa ne ya mallaka masa su.
Komai na rayuwarsa a American da iyalinsa ya fede wa mahaifinsa, amma ya zaftare duk wani abu da ya shafi rayuwar Mu’azzam, saboda shi kansa ba ya son tunawa, kuma ba zai iya tattauna wannan al’amarin da kowa ba ban da Abulkhair, Zulaiha kuwa ba don rashin yafiyarsa gare ta da yin Allah ya isa gare ta a kansa zai kare ba, da sai ya yi mata.
Hira ce aka yi tsakanin uba da Da irin wacce ba a taba yi ba. Malam ya fahimci rayuwar dan nasa sosai, ba wai daular duniya ta boye shi ba, shi ma a can inda yaken matsaloli ne dankare tare da shi. Ba za a sanya Ishaq Raazee matsayin attajirai a Amurka ba, amma yana da rufin asirinsa irin na diaspora.
Kyakkyawan lodge da rantsattsun motocin hawa guda uku. Ga parmanent aikinsa a hannu. Sannan matarsa da ke aiki da babban bankin kasar Amurka ta fi shi tara abin duniya. Aikin Mu’azzam da kamfanin man fetur na CHEVRON CORPORATION ya kara taimakawa wajen rufuwar asirinsu. Kasancewar Mu’az din wani mutum da bai san dadin abun hannunsa ba, saboda ba shi da buri, ba shi da future planning a kan komai. Aikin ma yana yinsa ne don kar ya zauna ba ya komai, yana kuma biyan kudin hayar mansion din da yake ciki.
Shi yake biyan kudin makarantar Abulkhair bakidaya, duk da cewa abin da yake biya din babu yawa kasancewar Abulkhair dan kasa ne, a can aka haife shi, duk cikinsu shi kadai ne mai nationality din Nijar, ba zai iya manta wahalar da Daddy ya ci a kan nasa karatun ba lokacin yana consulate officer karkashin ofishin jakadanci na kasar Nijar a kasar Amurka, lokacin Daddyn ba shi da hanyar samu mai yawa. Don haka zai iya cewa yana da buri a kan DADDY, ya kasance cikin wadata shi da wadanda suka shafe shi da kannenshi. Bayan wannan ba shi da wani solemn buri a rayuwarsa. Daga sanda ya fara aiki da Chevronya dauke wa Daddy hidimar lafiyarsa.
Sai da suka gama hirar suka soma labarin ‘yan uwa na nan kasar da Mansour da ke Nigeria. Mahaifin nasu ya tambaye shi ko shi ne ya sanya Mansour ya ba shi rikon Aalimah? Nan ya yi masa bayanin yadda komai ya kasance. Cewa, Mansour din a kan-kansa shi da maidakinsa suna da burin Aalimah ta yi karatun a Boston jami’ar da mahaifin maidakinsa ya yi ce. Ya gaya masa tun kafin hakan ya sha rokon Mansour ya ba shi yaran guda biyu (Aalimah da Aboubacar), amma ya ki. Sai kuma ga shi shi da kansa ya neme shi ya gaya masa ya samo mata scholarship a garin da yake. Malam ya jinjina son boko irin na Mansour a wasu lokutan har ya fi Ishaq muhimmanta ilimin boko. Kamar daga sama mahaifin nasa ya jefo masa tambayar da ta birkita shi.
“Me ke damun takwarana Mu’azzamu? Kun dade kuna ce da ni ba shi da lafiya, amma daidai da rana daya daga kai har shi ba wanda ya taba bude baki ya gaya min hakikanin me ke damunsa. Ban taba ganinsa da wasu kamanni ko alamomi na mara lafiya ba. Karewa ma duk ya fi ku kyakkyawan tunani da tsinkaye. Ya fi ku son zumunci da muhimmanta shi. Rashin lafiyar me ku ke cewa yana yi da har ya sanya ku yi masa wani irin aure da har gobe ba mu ji karshensa ba? Sannan me ya hana shi yin aure a halin yanzu a wannan gabar ta rayuwarsa?”
Gumi (zufa) Daddy Ishaq ya shiga tsattsafarwa daga kowanne sashe na jikinsa, ya kuma kasa amsa tambayoyin mahaifinsa. Malam din ya tsura masa ido, ya kuma fahimci halin rudanin da maganganunsa suka jefa dan nasa. Take wasu tunaninnika marasa dadi suka shiga darsuwa a ransa. Ya kaurara murya ya ce, “ISHAQA!”
Ya dago a hankali ya dubi mahaifinsa.
“Mu’azzamu kanjamau gare shi ko (yana nufin acquired immune deficiency syndrom)?”
A firgice Ishaq Raazee ya ce,
“A’ah, non, quite non, pere”.
Yana ganin yadda mahaifin nasa ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciya, ya lumshe idonsa irin na samun kubuta daga tunanin da ya dade yana wahalar da mutum. Sannan ya ce,
“Gaya min gaskiya, shi ba namiji ba ne to?”
Cikin yamutsa fuska da rashin fahimtar hausar ya ce, “Malam, kamar ya ya shi ba namiji ba ne?”
Sai Malam din ya sauya harshe, ya yi masa bayani yadda zai gane da abzinanci. Yana nufin wanda ba zai iya biyan bukatar auratayya ba. Ya fada masa gaskiya, in wannan ce matsalar Mu’azzam ba wani abu ba ne, babu irin maganin da bai sani ba a rayuwarsa, in ma shi bai sani ba, to ya san inda zai kai shi a yi masa maganin lalurar a Tessoua. Daddy ya rasa yadda zai yi. Bai san wane bayani zai masa ya fahimta ba. Lalura ce irin wadda bai taba sani ba a duniyarsa, kuma za ta yi masa wuyar fahimta. Nan dai ya tabbatar masa wannan ba ita ce matsalar Mu’azzam ba, sannan ya yi ta kame-kame. A karshe ya ce, likitoci suna kan bincike da sun fadi sakamako zai gaya amsa. Amma ya tabbatar masa ya kwantar da hankalinsa, Mu’azzam ba ya tare da ko daya daga cututtukan da ya ambata a sama.
Suna haka sauran ‘ya’yan Malam suka soma shigowa shigifar daya-bayan-daya daga gidajensu, daga unguwanni daban-daban da suke zaune a nan Niamey (Yamai). Daga ‘yan cikin Innarshi zuwa na Inna Bintou abokiyar zamanta. Kai ka ce Larabawan Kuwait ke shigowa suna zazzaunawa. Musabiha ce ta rika gudana tsakanin Ishaq da ‘yan uwansa, sai tambaye-tambayen lafiya da iyalin juna. Su goma sha tara cif! Sauran shidan mata ne a gidajen aurensu. Mansour da ke Nigeria ne kawai babu a cikinsu yau.
Cikin su mutum biyu ne suka girmi Ishaq, Uncle Edrissa da Uncle Oussama, wadanda suka kasance sun fito ne daga ciki daya, ragowar duka kannensu ne. a mazan akwai wadanda ba su kai ga yin auren fari ba suna karatu, sun biyo Ishaq da Mansour. Amma a nan jami’ar Abdou-moumoun babbar jami’ar kasar Nijar.
Ranar ta zamo wata ranar reunion ta iyalin RAAZEE. Matan ma da ke gidan aure duk sun zo wajen Yayan nasu da suka dade ba su gani ba, da kyawawan ‘ya’yansa wadanda suka dauko gida a kamanninsa.
Da daddare bayan kowa ya koma gidansa dakin Inna Kasisi ya koma. Ya ce, shi ba abincin wanda zai ci sai nata. Murmushi ta yi da ta tuna wani abu, ya fi kowa son girkinta. Har satar dumame yake mata tana barci, in kuma Mansour ya cinye masa abinci kafin ya dawo yana cin uban duka. Bai sani ba tun tafiyarsa dakin Malam ta shiga kicin ta shirya masa lafiyayyen abincin abzinawa na asali. Ya ci ya yi hani’an kamar mai yin cin biyan bashi.
Washegari ya gaya wa Yayansa Uncle Oussama yana so zai je Tessoua da Zinder son samu har Arlit ya kai yara su ga asalinsa da dangin Inna da ke can, da na Malam. Uncle Oussama ya bada mota Hilux da suke shiga sahara da ita, da kuma dansa Hamoud ya tuka su, ya fi kowa iya tukin mota a gidan, kuma ya saba shiga garuruwa da sahara tare da Malam.
Tun suna tafe kan kwalta har ta soma bacewa ganinsu. Tafiya ce suke ta yi cikin rairayin sahara. Aalimah na kallon yanki da bigire na tsatson mahaifinta tana jin wani shauki a zuciyarta. Tafiya ce mai dadi da ta sanya nishadi a zukatansu. Ga guzurin abinciccika kala-kala a warmers da ababen sha masu sanyi a coolers Inna Kasisi ta yo musu. Duk wanda ya ji yunwa zai bude ya diba ya ci ya sha. Tafiya aka ce yankin azaba, kuma mabudin ilmi. Tsananin ranar kasar Nijar da zafin rairayin sahara ya sanya ita kanta A.C din motar ta daina bada wani sanyi mai karfi. Ba abin da Aalimah ke so a wannan tafiya irin kallon rakuma da makiyayansu, Daddy na ba su labarin kuruciyarsu da yadda suke taya mahaifinsu kiwon nashi rakuman a Tessoua, garin da za su je.
Tafiyar awanni masu yawa ta kawo su birnin Tessoua.Tessoua na daya daga cikin manyan birane goma da kasar Niger ke ji da su. Hamoud ya dauke kan motar ya shiga unguwar da za su, har kofar wani gidan laka mai cike da yawan dabbobi da almajirai fal! A kofar gidan Mazaje ne suna daukar karatu tare da wani dattijo. Wannan shi ne ainahin gidan kakannin su Daddy, wato gidan iyayen Malam Raazee. Dattijon da ke bada karatun shi ke amsa sunan Malam Yahyya, kani yake ga Malam, shi ke zaune a gidan yanzu da iyalansa, sai sauran ‘yan uwan Malam da iyalansu duk a gidan suke kasancewarsa babban gida na gado.
Sun samu kyakkyawar tarba daga jama’ar gidan, abinci kala-kala na abzin, rago guda aka gashe musu don Malam Yahya ya san da zuwansu. Har gonar kiwon kakansu an raka su. Su Basma ‘yan Massachusetts yau an yi kwanan gadon alawayyo. Sauro ya ci rabonsa ya more. Sun ga dangi-dangi sun gansu. Washegari da safe Hamoud ya cika tankin motarsu da mai tatul suka kama hanyar Zinder.
Tafiyar sai ta zame musu tamkar ta yawon bude ido, ga Hamoud da ke yi musu bayanin ko’ina. Basma da Khaleesat, sai suka bude wayoyinsu suka shiga recording abubuwan da suka burge su. Zinder babban gari ne, kuma jiha mai tarin al’umma masu ethnic group daban-daban.
A gidan iyayen Inna Kasisi suka sauka, nan ma an musu tarba ta musamman duk da ba su san da zuwansu ba. Daddy ya bi ‘yan uwa lungu-lungu ya yi musu alheri mai yawa, kamar yadda ya yi a Tessoua. Kwana biyu suka yi harama suka dauki hanyar Arlit. Awanni masu yawa a tsakani suka isa. Arlit nan ne tushen su Inna Bintou kishiyar uwa, wadda ta zame musu babu maraba da uwa mahaifiya. Ta ba su kulawar da ba su samu daga mahaifiyarsu ba, don haka tana da matsayi sosai a wurin ‘ya’yan Inna kasisi. Nan ma Daddy ya yi alheri sosai, don duka dangin nasu tun daga na Tessoua, na Zinder har nan na Arlit suna cikin yanayin rayuwa, abin sai godiyar Allah. Daddy yana shan mamaki in yana jin sunan Mu’azzam a bakin danginshi sosai, ba wanda bai sanshi ba, ba wanda ba ya yi masa addu’ar alheri saboda taimakon da yake musu, wanda Daddyn ba shi da masaniya sam. Jinjina kai yake yana sanya mishi albarka cikin zuciyarsa.
Sun baro garuruwan bayan Hilux dinsu cike da tsarabobi kala-kala na abubuwan amfani, irin nasu. Da suka dawo Niamey ma ba su huta ba, zagaye suke na gidajen ‘yan uwa.
A can kasar America kuma Abulkhair ya kira wayar Aalimah a karshen satin kamar yadda ya saba, inda gidan wayar Verizon wareless suka tabbatar masa ba’a amfani da layin, ya kira na Basma shi ma haka, sannan na Khaleesat, shi din ma dai babu. Tsoro da fargaba har ma da mamaki suka kama shi, musamman da ya gwada na Daddy shi ma haka. Wuninsa guda yana abu daya, amma ya kasa samun kowannensu. A karshe ya gwada na Mummy. Cikin sa’a sai ya same ta. Ya tambaye ta ko me ya samu wayoyin Daddy da na su Basma ya kasa samunsu? Nan take gaya masa ai suna Nijar yau satinsu daya. Ya ce ta ba sh lambar da ta ke magana da su.
Tsaki ta yi, ta ce, ita tunda suka tafi ba su yi waya ba, ba ta da lokacinsu. Ya san halin Mamanshi sarai in ya ci gaba da damunta, za su yi ta ba dadi, dole ya hakura, a kalla hankalinsa ya kwanta tunda lafiyarsu kalau. Ya ci gaba da rubuta jarrabawarsa cikin nutsuwa. Sai dai fa Aalimah na ciki kowanne bugun numfashinsa, tafiyar tasu ta tabbatar masa Daddy (takes the first step) ga gyaran rayuwarsa da iyaye da ‘yan uwansa.
Ana saura kwana uku su tafi Inna Kasisi ta kira manyan ‘ya’yanta da na Bintou maza, da shi Daddyn a babban falon Malam Raazee, shi ma Malam din yana zaune. Cewa ta yi Malam ya bude taron da addu’a, akwai damuwa a fuskar Daddy Ishaq don har zuwa lokacin Innar ba ta gama sake masa sosai ba. Kuka Inna Kasisi ta saka wani abu da ta dade ba ta yi shi ba, mace ce mai taurin zuciya kwarai da nuna ba ta da damuwa a kan komai, ko da tana da damuwar. Hankalin manyan ‘ya’yanta ciki har da Daddy ya yi matukar tashi. Lallashinta suka shiga yi suna rokon ta fada musu damuwarta, sun yi alkawarin magance mata ita muddin ba ta fi karfinsu ba. Sai da ta yi mai isarta, sannan ta ce, ba ta yarda Ishaq ya koma Amurka ba, ko dai ya kara aure ya bar matar a nan tare da su, shi ya koma din inyaso ya dinga zuwa in ya samu sarari, ko ya baro Amurka bakidaya ya zo ya zauna cikin ‘yan uwansa tare da iyalinsa.
Zufa ce kawai ta lullube Daddy, saboda cikin zabin nata duka babu mai sauki. He has a life where he live, a career, a family and everything. Ko zai baro Amurka ba lokaci daya ba. Zabinta na biyu kuma karin aure wani karin nauyi ne a gare shi da bai san yadda zai yi ya dinga sauke shi ba.
Bai ma taba hasaso wa kanshi irin wannan rayuwar ba (polygamy), duk da ita ya taso ya tarar a gidansu. Shirunsa ya sanya kowa da ke dakin ma ya yi shiru, ita kuma Inna ta ci gaba da sharbe. Malam ya yi gyaran murya don katse shirun, ya ce,
“To Ishaqu ka ji bukatar mahaifiyarka a kanka, wannan karon ina bayanta, kullum na kasance cikin bin ra’ayinku in dai bai saba wa addini ba, ina hana ta nata hakkin na uwa. Ka kara aure matar ta zauna da mu, ko ka dawo gida”.
Da kyar Daddy ya iya hadiyar miyau, sannan ya muskuta, “Malam da Inna na ji batunku. Da man kowanne bakon haure a kasashen ketare dole watarana zai dawo gida. Ina da wannan niyyar ko Inna ba ta furta ba, amma ba zai yiwu a lokaci daya ba. Duka yaran karatu suke yi ba su gama ba, Mu’azzam ne kadai ya tsaya da kafafunsa.
Ni kuma sai ya kasance ina da abin yi a nan din kafin in dawo, don ba zai yiwu in zo in zame muku lalura ba. Magana ce ta WATARANA da babu wanda ya san wace rana ce. Maganar karin aure kuma Inna ni yanzu tsofai-tsofai da ni wane aure zan kara?
Gidana babu ko dakin ajiye mace, in kuma na ce a nan zan ajiye ta yanayin aikina ba zai bari in dinga zuwa akai-akai ba, zai zama akwai zalunci a ciki ta fannin matar. Inna ko za ki fadi wata alfarmar in yi miki bayan wannan?” Ya fada cikin taushin murya mai cike da ladabi da kwantar da kai, hadi da lallashi.
Amma budar bakin Inna kasisi sai cewa ta yi, ita ta riga ta gama magana, har ta tanadar masa matar, ta ji ta yarda ba zai iya dawowa Niamey yanzu ba, amma dole ya auri GUMSU!
Wata sabuwa inji ‘yan caca, shuka tsakiyar rani!
Mu je ga littafi na biyu.
Taku har kullum.
Sumayyah Abdulkadir
(Takori)