AALIMAH

Book 2 (End)

by @takori

Shekaru guda biyu kwarara kenan da wannan aure mai dumbin albarka, wanda ya zamo wani tubali na hadin kan iyalin Malam Ibrahim Raazee bakidaya. Ya kawo alheri mai yawa ga kowannensu. Duk weekend Aalimah da Basma na rike da juna a kan waya, sabida a weekend din kadai ta ke samun lokacin gaisawa da ‘yan uwa da iyayenta, saboda yanayin aikinta da hidimar Aboulkhair da ba ta karewa. Shagwababbe, cingam, super glue din Aalimah, dan gatan Engnr. Mu’azzam Raazee. A karshen shekarar Aboulkhair ya koma John Hopkins University ya zana jarrabawar part 2 dinsa. Ba da jimawa ba sakamako ya fito, ya cinye komai da wata irin madaukakiyar nasara, ya dawo asibitinsu inda aka canza masa ofis a matsayinsa na cikakken consultant (Neuro-Psychiatrist) a halin yanzu.

A wannan lokacin ne Dr. Nebrass likitan Mu’azzam na shekaru masu yawa da suka gabata ya danka wa Dr. Aboulkhair Raazee kulawar dan uwansa Mu’azzam bakidaya, ta hanyar damka masa file dinsa sabida shi kansa jinjinawa kwarewa da fasahar Aboulkhair yake yi, kamar wanda ya shekara goma yana practicing. Bai sani ba, hakan na da alaka ne da zuciyar ‘yan uwantaka da shakuwa wadda aka gina karatun kacokam a kanta, sannan shi din shekarunsa na komawa gida ya huta (retire) sun cika.

Zuwa wannan lokacin Daddy Ishaq ya gama komai na shirin komawarsa gida Niger da iyalinsa mata bakidaya. Abu daya yake jira su ajiye ayyukansu su koma (takardar daukarsa aiki da ministere des affaires etrangeres), wato ministry of foreign affairs, hukumar hulda da kasashen waje ta kasar Niger mai location a babban birni Niamey, wadda wani tsohon abokinsa ma’aikaci a wurin da suka yi aiki tare tun a Niger Consulate America yake ta kokarin nema masa.

Sun hadu ita da su Mummy a Massachusetts sun je wa Aboulkhair jami’ar John Hopkins har can garin Baltimore  (Maryland) ranar da ya karbi shaidarsa ta zama consultant, tare da shi suka taho Boston. Kwanansu biyu da iyayen nasu da kannensu su Khaleesat wadda ta gama karatunta ita ma a wannan shekarar, suka koma gidansu.

Kafin su shiga gida ya ce, lallai wannan karon sai sun je ta gaida Mu’azzam. Zuwanta daya a kulliyar zamanta cikin garin da yake, sai dai in suna waya da Aboulkhair yakan ba ta su gaisa a gajarce. Ita girmansa da respect dinta gare shi ke hana ta sakewa da shi, a wani bangaren kuma tausayinsa bakidaya. Yayin da shi kuma a nasa bangaren da ma ba ya sakewa da kowa sai Aboulkhair, sai kuma Daddy da kaninsa Mansour Raazee, da kuma kakansa mai ran karfe. Ko Mummy ba ruwanta da rayuwarsa. In ka ji suna magana mai tsawo, to nata matsalolin ne da ta ke neman ya taimaka mata ta fita daga cikinsu. Da shawarwarin Mu’azzam ne ta tabbatar a yanzu ta zauna lafiya cikin sukunin zuciya da kyakkyawar mu’amala da kishiya da dangin mijinta, mutuncinta ya dawo cikin idanunsu.

A halin yanzu ma ta neme shi kan babban kalubalenta na yanzu (barin aiki da Daddy ke so ta yi su koma gida). Tana cikin damuwa da hakan matuka. Abin da Mu’azzam ya ce da ita shi ne, “Mummy me kuma ki ke nema a rayuwa? Kin aurar da duka manyan ‘ya’yanki bayan kin ba su wadataccen ilmi, nan da shekara daya za ki aurar da wadda ta saura. Kudin da ki ka tara shekaru masu yawa ki ka ba ni, ki ka ce in sayi gida in bar rent, gaya miki ne ban yi ba, hannayen jari na siya miki da su a manyan bankunan Nigeria da Niger. A yanzu haka gidan nan da nake ciki mallakina ne, na dade ina biya da kadan da kadan na kuma hada da wani kaso kadan daga wanda ki ka ba ni. Don haka don Allah Mummy ki yi wa mijinki biyayya kamar yadda ki ka saba, ke ma ki zauna waje daya ki huta kamar kowacce matar aure ki fara rainon jikoki da tarbiyyarsu. Aboulkhair ya gaya min Basma ta kusa haihuwa, shi ma tashi matar ta samu yanzu, ga Khaleesat za ta shiga daga ciki ita ma. Mummy you are blessed ki kara gode wa Allah, ki koma neman lahira. Na yi miki alkawarin 40% na albashina duk wata”.

Kuka Mummy Zulaiha ta saka, abin da Mu’azzam ba ya so daga gare ta.

“Mu’azzam ban san da wane harshe zan daina cewa ni na jawo rushewar farin ciki da cikar rayuwarka ba. Ba zan iya daina cewa ka yafe min ba! Ka ambaci kowa zai haihu ban da kai, Mu’azzam naka na fi son gani. Mu’azzam ka taimaka min in sake yi maka aure ko me zai faru. Ni ban yarda da kafiran nan ba, namu addinin ya ce kowacce cuta tana da magani, Malam Raazee da kawunka Edrissa sun ce za su nemo magani…”

Ta ci gaba da kuka sadidan fiye da wanda ta ke yi a baya.

Mu’azzam ya dafe kansa da hannun damansa, jijiyoyin kansa na sarawa. Da kyar ya ce, “Mummy ki daina maganar nan don Allah. Na riga na karbi kaddarata da hannu bibbiyu. Mummy I don’t have a feeling to give to a woman. Mummy aure is not about having sex and children only, there’s a matter of LOVE and AFFECTION. And Mu’azzam don’t have any, not even a remnant. Ki sa a ranki ‘ya’yan Aboulkhair da Basma ‘ya’yana ne da na haifa tunda in an tsaga jikinsu za a ga jinina. Mummy please..... ki daina kukan nan, kina tayar min da hankali. In Aboulkhair ya san abin da ki ke gaya min zai hana ni yin waya da ke…”.

Alamun zaman mutum ya ji a kusa da shi, ya daga idanunsa da suka rine da sauri ya dube shi, Aboulkhair ne.

Gabadaya yanayinsa ya canza, bacin rai da tashin hankali sun bayyana karara a kyakkyawar fuskarsa. Idanunsa sun kada sun yi jazir. Mummy ba ta kyauta masa ba. Yana tufka tana warwara, maimakon ta shanye damuwarta ita kadai, ko shi ta kira shi ta yi masa. Me Mu’azzam zai maganta mata ban da ta kara masa damuwa, yana fama da jinyar tashi zuciyar da kwakwalwar? Mu’azzam din ya kamata ta gaya wa halin da ta ke ciki a kansa?

Mikewa ya yi zai fita, Mu’azzam ya rike shi yana daga zaune. Bai iya ya juyo sun hada ido ba saboda idanunsa da suka cicciko da hawaye. Murmushi Mu’azzam din ya yi duk da idanunsa sun kada, ya ce, “Ina ruwanka da hirata da uwata? Wato labe ka koma? Kuma meye laifi don ta yi sharing damuwar zuciyarta da ni?”

Ba tare da ya juyo ba ya ce, “I’m your doctor. Not a brother. I’m responsible for all the progress and the downfall of your health. Da ni ya kamata ta tattauna abin da ta ke tattaunawa da kai. Mummy ba ta kyauta min ba! Damuwa da tunani suna hana mood stabilizers aiki yadda ya kamata. Kuma na san abin da zan yi”.

Ya kwace hannunsa zai fita. Mu’azzam ya daga murya ya ce, “Aboulkhair uwata ce fa! Za ka hana ni magana da ita ne? Ka shiga hankalinka kai da likitancin naka. Rayuwa da ciwo duka a hannun Allah suke. Idan Allah ya ce ma mutuwa zan yi dukkaninku ba abin da za ku iya. Ni gara ma in mutu in huta da wannan rayuwar…!”

Da gudu Aboulkhair ya dawo ya rungume shi. Hawaye ya soma yana fadin, “Insha Allahu kai za ka binne ni, ba dai ni in ga kabarinka ba Mu’az, ba zan iya jura ba. Zan yi abin da ya fi hauka, ba zan iya rayuwa ba, na roke ka kada ka kara yi min wannan fatan”.

Ya dago shi ya zaunar kusa da shi, yana bubbuga bayansa.

“Na ji ba zan kara ba. Amma kada ka kara fadin in ba ni ba za ka iya rayuwa ba. kowanne rai sai ya dandani mutuwa Aboulkhair. Abin fatan shi ne mu cika da kyau da imani. Ka yi wa Mummy uzuri kada ka ce mata komai a kaina.

 Ta hanyar expressing griefs and sorrows dinta (bakin cikinta) a kaina ne kadai za ta samu sassaucin tata zuciyar. Ni ne mai ciwo Aboulkhair, amma UWA ta fi ni ji a jikinta. Yanzu tashi mu je kasa in ba ka Sangria Mocktail (Non-Alcoholic fruit drink) ka sha, ka kai wa matarka ita ma. Dazu na yi order dinsa”.

Murmushi Aboulkhair ya yi, kaunar Yayan nasa na kara keta zuciyarsa. Ya san so yake ya gusar masa da bacin ransa. Sai a lokacin ya tuna tare da Aalimah yake ya barta a falon kasa.

“Tare ma muke da ita, mu je ka bata da kanka”.

Suka sauko tare.

Tun daga nesa ta hango su don haka ta kara nutsuwa ta ajiye littafin da ta dauka na Mu’azzam, wanda ta fahimci dubawa yake yi ya ajiye ya tashi, ‘The Danger Of Hypersexual Disorder (By Dr. Martin Kafka, 4thEdition)’.

Da sauri ta ajiye ba tare da kowannensu ya lura ba. Aboulkhair ya zauna a kusa da ita, Mu’azzam ya wuce firjinsa ya zuba mocktail din a manyan kofunan glass guda biyu, ya sanya straw a kowanne ya iso gare su. Aalimah ta sa hannu tana ture Aboulkhair daga kusa da ita, shi kuma ya ki turuwa har Mu’azzam ya iso. Karshe ita ta tashi ta matsa gefe, Aboulkhair ya bi ta da harara.

“Koma wajenki ki zauna”. In ji Mu’azzam da muryar manyantaka irin tashi in yana magana da ita, wadda ta dade da lura ba da irinta yake yi wa Aboulkhair magana ba.

Aalimah ta sunkuyar da kai tana murmushi, a kunyace ta ce, “Shi ya ce in mun zo gidan nan kada in zauna kusa da shi”.

Aboulkhair ya hangame baki, ya ce,

“Yaushe aka yi haka???”

Mu’azzam ya mika mata kofin, hannu biyu tasa ta karba ta yi godiya ya samu kujera mai fuskantarsu ya zauna. Ya dubi Aalimah ya ce,

 “Kin ga kuma ni din, sanda ya fara sonki sai da na yi da gaske ya tsaya ya yi karatu. Sai da na ce zan aura masa mata hudu in ya dage ya zama Psychiatric dina. Yanzu haka yana min tunin ukun da suka yi saura ne a sama kafin mu sauko”.

Aboulkhair ya sake kwalalo idanu ya sake hangame baki, ya ce, “Yaushe aka yi haka???”

“To mu duka ka mana tambaya iri daya, wadda ke nufin dukkanmu kana nufin mun yi maka karya”.

Mutsu-mutsu ya hau yi da baki yana rokon Mu’azzam da ido ya warware masa gadar zaren da ya kulla masa ba tare da ya ce da ita ya yi karya ba.

Aalimah ta fahimci halin da Mu’azzam ya jefa mijinta, har gumi yake yi, duk da sanyin garin Las Vegas, ta ce, “Yaya Mu’azzam ai addini ya bashi dama”.

Mu’azzam ya zuba mata ido na ‘yan dakiku, ba tun yau ba ya fahimci yarinyar tana da hankali, ga nutsuwa da girmama na gaba. Ya ce,

 “Haka ne Aalimah! To amma me ya sa ya ce kada ki zauna a kusa da shi a gidana?”

Da sauri Aboulkhair ya ce, “Ni fa ban san an yi ba Aalimah, ban sanki da karya ba!”.

Dariya ta yi har fararen hakoranta suka bayyana, ta ce, “Yaya Mu’azzam ka san ko zan yi karya kai ba zan yi maka ba. Wai kunyarka yake ji”.

Murmushi Mu’azzam ya yi, murmushin nan nasa ingentleness,ya juya yana kallon Aboulkhair da kyawawan idanunsa cike da kauna, bai ce komai ba. Duba agogo ya hau yi, Aalimah ta ce a ranta, “Mun shiga lokacinsa”.

Tun kafin ya ce, “Ku je na sallame ku”. Dinsa tayi buzut ta mike ta ce,

“Mun tafi Yaya Mu’azzam, sai mun sake shigowa”.

Yana mai kara yaba hankalinta ya ce, “Tun ban sallame ku ba? To na gode, kuma ki je ATM.I’ve nothing to give you”.

Murmushi ta yi ta ce, “Muna godiya ni da wadanda nake aikawa kudin. Allah Ya kara budi”.

Juyawa ya yi ya haye upstairs dinsa.

Suna tafe a hanyarsu ta zuwa gida, Aboulkhair ya ce, “Me ya sa ki ka gaya masa ba kya amfani da kudin da yake ba ki? Ai ba zai ji dadi ba”.

Ta gyara zamanta da lullubin kanta, ta ce, “Saboda ya san ba ni da matsala ni, kada in zamo mai hadama. Ga aiki ya sama min ana biyana albashi mai tsoka, kuma yana bina da kudi kusan kamarsu duk wata, ai na zama mara godiyar Allah. Zai yi tunanin me nake yi da su, ga mijina bai rage ni da komai ba”.

Girgiza kai kawai Aboulkhair ya yi, har yau Aalimah ba ta san Mu’azzam ba. Bai kuma san irin bayanin da zai mata ta fahimce shi ba. Ba ruwanshi da abin da kowa ke ciki ko me wani ke gudanarwa a rayuwarsa. Shi kansa bai damu da rayuwar da yake ciki ba. Ba komai cikin ransa sai kwarewa da aikinsa na hakowa da tace man fetur (Exploration and refining petroleum). Tana wahalar da kanta wajen son ya fahimci me ta ke ciki, ba fahimta zai yi ba. Wani saint (waliyyi) ne shi a cikin turawa, kowa ya je ya yi abin da ke gabansa.

 

A karshen sabuwar shekarar da ake ciki sun yi shawarar za su dauki hutu lokaci daya saboda su samu zuwa Nigeria daidai lokacin haihuwar Basma. Kuma watan haihuwarta ne watan bikin Khaleesat. Duk da rashin wadatacciyar lafiyar ita Aalimahr ita ma tana fama da laulayin ciki wata hudu, boye rashin karfin jikin nata ta ke ga Aboulkhair tana kwarara kanta a gabansa, don kada ya hana ta zuwa. She missed Basma so much yadda ba za ta iya bayyanawa ba duk da suna waya a kowanne karshen sati, ga dokin ganin abin da za ta haifa mata tunda kuwa dan Yaya Aboubacar ita za a haifa mawa halak-malak. Fatanta ma a nan gaba in za su amince su bata ta hada da wanda za ta haifa ta rike a nan Las Vegas.

Mu’azzam ya samu karin ‘yan uwa masu kula da walwalarsa, ta san in ya hana kowa damunsa ba zai hana ‘ya’yansa ba. Tun daga lokacin da ta san wanene shi, ta damu da al’amarinsa sosai.

 

KANO-NIGERIA

Sun sauka a birnin Kano ranar alhamis. Ba matar ba, ba mijin ba, kowannensu ya yi ‘yar kyakkyawar kiba kib-kib ga kumatu luwai-luwai a fuskar Aalimah wanda a da ba ta da shi. Yaya Aboubacar ne ya zuba su Sabrina a mota suka je filin jirgin saman Malam Aminu Kano suka dauko su.

Basma na ta kiran waya tana ita a wuto mata da Aalimah ba ta yarda ta fara zuwa sultan road a bata mata lokacin ganinta ba. Aalimah na ba ta hakuri tana gaya mata ba za ta iya kara minti goma ba ta ga Mama ba alhalin tana cikin Kano, ta mata alkawarin har kwana za ta yi a gidanta in ta huta, saboda an hana basma fita saboda ta shiga EDD ga cikin mai wani irin girma.

Sun yi waya da su Mummy su sai bikin Khaleesat saura sati daya za su samu tahowa, yau kuma saura sati biyu.

Mama ta fito kofar shiga falo tana kallon Aalimah na fitowa daga mota da dan matashin cikinta tsab da ita cikin wata irin shiga ta doguwar riga ruwan hanta kirar Abu-Dhabi, takalminta ma kalarsa kenan marasa tsayin dunduniya dan kasar Italy. Ta yi wani irin haske mai nuna yanayin rayuwar da ta ke ciki wanke hannu ka taba. Aboulkhair da Aboubacar suna cikin motar ba su fito ba, suna maganar da ba ta san ta mece ce ba (zancen tafiyarsu Nijar suke daga Kano don fara shirin auren kannen su Hamoud da Khaleesat sati mai zuwa idan su Daddy sun iso). Su Suhaima sun rirriko hannayenta kamar sa cinye ta don murna. Shi kansa Aboulkhair din da ta hango ta cikin glass ya yi kyau da kibar da da gani ka san na zaunuwar wadata da kwanciyar hankali ne, fiye da lokacin da yake neman auren Aalimah. Godiya ta shiga yi wa ubangiji a fili tare da binsu da addu’a iri-iri a zuciyarta.

Daidai lokacin da ta ji Aalimah da tattausan jikinta da kamshin jikinta sun rungume ta. Dariya ta yi ita ma ta yi mata kyakkyawar runguma. A yadda Aalimah ta zama matar Neuro-psychiatrist da yawan tu’ammali da patients din Aboulkhair ko duba su da yake tana zaune, da yawan tattaunawa da suke kan cututtukan, ita kanta tana da experience mai dumbin yawa a kan mental health illnesses. Ta fahimci akwai ci gaba sosai da stable treatment a tare da Mamanta fiye da baya.

Shi kansa Daddy da ya dawo nan-nan yake ta yi da Aalimah da maigidanta. Ya rasa ina yaka saka-ina-yaka-aje da su. Kowa ya yi kewar kowa. Shekaru uku cif kenan ba su ga juna ba. Baban da Aboulkhair suna labari, Aalimah da Mamanta da kannenta na yin nasu a daki. Hirar Baban su Aalimah da surukinsa Aboulkhair yawanci kuma kaso tamatin cikin dari ta Mu’azzam ce. Yau Dr. Mansour Raazee ya kara sanin abubuwa masu yawa dangane da Mu’azzam har da wadanda Daddyn su Aboulkhair ya cire a nasa labarin da ya basu a Nijar. Kamar cewa Clearson ya koya wa Mu’azzam kallon fina-finan batsa tun kafin shekarun balaga wadanda su ma suna cikin causes na hypersexuality disorder a shekarun girma. Daddy gefe ya koma yana share hawaye da hankalinsa, ya ce da Aboulkhair wa ya sani ma ko har kwayoyi ya banka masa? Wa ya sani ko ya koya masa ma wata lalatar bayan wannan?

Aboulkhair ya yi murmushi, ya ce, “Daddy ka daina kuka, abin da ya wuce ya wuce. Kuma ni ina tare da su a lokacin na san komai. Na san abin da suke yi da wanda ba su yi ba, duk da karancin shekaruna. Ka ga Clearson bai taba neman Mu’azzam ta wata hanya ba saboda ‘yan wani addini ne wai shi Rastafari, wanda ya haramta musu neman jinsi, sannan ban taba ganin wata yarinya mace ta shiga gidan su Clerson ba, shi kadai ne kwal a wurin iyayensa ya tsoka daya a miya, sannan a shekarun Clearson a lokacin ya san rape shi ne mistake na karshe a kasar Turai, musamman ga su bakin haure. Ya fito ne daga wata kasa Portugal shi da iyayensa. Kwayoyi kuma ba zan iya cewa ba su sha ba, tunda wanda ya sha giya sanda zai sha kwaya ma ba zai sani ba”.

Daddy sai kuka kamar wani karamin yaro, ya ce da Aboulkhair, yanzu ba don magungunan da yake sha ba, ci gaba zai yi da alcoholic consumption?

Aboulkhair ya girgiza kai, “Daga shekaru goma sha tara Mu’azzam ya san cewa, Clearson ya illata masa rayuwa. Daga wadannan shekarun shi da kansa ya daina sha’awar giya. Daga lokacin da ya tabbatar wannan aggressiveness din nasa da ke sa shi ya illata lafiyarsa ya ji wa kansa ciwo, ya yi wa Daddy asarar komai na gidansa giyar da ya sha ce sanadi, ko a boye bai kara kallonta ba. Daddy ya dauke Mu’azzam daga America tsayin shekaru uku ba tare da yardar Mummy ba, bayan mun bar garin da Clearson yake babu wanda ya san inda ya kai shi sai ni, har gobe. Kuma na tabbata kuma bai gaya muku ba. Daddy you are Mu’az’s father also, ina gaya maka Wadannan sirrukan na Mu’azzam ne saboda haka kawai jikina ke gaya mini watarana za ka taimaka masa sabida dumbin kaunarka gare shi. Ina raye ko ba na raye, and Daddy will not tell anybody wasu muhimman abubuwa irin wadannan da suka shafi Mu’azzam saboda daga shi har Mu’azzam din yanzu ba sa son tunawa.

Ya kai shi birnin Medinah shekaru uku a wani gari wai shi YAMBOU hannun wani shehin malami dan asalin Hijaz (Madinah) ya sanya shi a wata makarantar mmalamin a wani kauye Yambou. A can ya yi sauka, ya yi hadda ya manta da rayuwar da ke cikin America bakidaya da zaman da ya yi da Clearson, yana kuma zuwa duk bayan wasu watanni yana kai masa magungunansa. Bai dawo da shi ba sai da ya ga zai zarce shekarun shiga jami’a. Bayan ya dawo kememe ya ki zama tare da kowa, ya zabi zama nesa da gida, wato birnin Nevada (Las Vegas) inda muke gabadayanmu yanzu”.

Dr. Mansour ya saki baki da kunnuwa yana jin Aboulkhair, ba Mu’azzam kadai ya ji tausayi ba wannan karon, har da dan uwansa (Ishaq), su suna nan suna ta jin haushinsa ba ya kula ‘yan uwa sabida ya samu duniya, shi yana can yana fadi-tashi don gyara rayuwar dansa da aka lalata masa. ko zaryar zuwa Madinah daga America wani hanzari ne mai zaman kansa. Ko a ina ya samo Balaraben da ya kai wa Mu’azzam din? Oho!

Aboulkhair ya ce, “Through internet”.

Sheikh Bahari Limamin babban masallacin Yambou ne. A wata lecture da ya saki a yanar gizo ne ya ce, yana da maganin raba matasa da shan giya da drug addiction komai tsananinsa in dai za a iya yin tattaki a same shi har inda yake. A nan ne Daddy ya samu email dinsa suka tattauna ya taimaka musu da yadda za su samu visa kai tsaye zuwa Yambou ba ta umrah ba. Saboda in ta umrah ce ba za ka iya shiga Yambou ba, ta karatu aka yi wa Mu’azzam. Makarantar kuma mallakinsa ce mai zaune da lasisi daga gwamnatin Saudiyyah. Mu’azzam ya shiga ransa daga ganinsa na farko da shi kuma da bakinsa ya gaya masa yana so ya bari, ba ya son ganinta ba dadinta yake ji ba”.

Daddyn Aalimah sai karin hawaye.

Aboulkhair ya ce, “Wallahi Daddy bayan dawowar Mu’azzam daga Madinah ko sallarsa abin kallo ce, saboda hakkinta da yake ba ta, a wajensa na koyi gyara sallah ta, a wajensa na koyi komai na ibada na gane su kansu Malaman da ke koyar da mu a America duk rabi baragada ce, ilmin musulunci bai wani ratsa su ba”.

Daddy ya girgiza kai ya fyace hanci, ya ce, “To wai ni shi kenan haka zai dauwama? Aure da haihuwa sai dai ya gani wurin kannensa?”

Aboulkhair ya ce, “Daddy mu yi sirri mana ni da kai?”

Murmushi Dr. Mansour ya yi, ya ce, “Mu yi Aboulkhair, ko Ishaq bai isa ya ji ba idan ba kai ka yarda ya ji ba”.

Aboulkhair ya matso jikinsa sosai kamar zai shige jikinsa, ya ce, “Daddy sabida Mu’az na karanci Neuro-Psychiatry, saboda in san wannan lalurar ciki da bai dinta, saboda a yadda na fahimta su kansu likitocin Mu’azzam ba su da magana kwaya daya game da warkewarsa, ko rashin warkewarsa. Bakunansu sun rabu. Na zabi John Hopkins saboda duk duniya ita ce lamba daya a ilmin Psychiatry, Daddy har gobe bincike nake ban fasa ba, ko bayan zamowata consultant. Aalimah shaida ce kan cewa sai in kwana uku a asibiti ba ta gan ni ba, amma ko kusa ba ta damuwa. A gida ma na kan kulle kaina a study room dinmu yini guda in ce ko abinci kada ta ba ni sai na nema da kaina. Ta kan ce ba ta taba ganin mai son dan uwansa irina ba, tana fatan wannan zumuncin ya kai mu aljanna ni da shi bakidaya, saboda ta lura nawa kadan ne a kan nasa. Kowa ya je masa gida damunsa yake ban da ni. Kowa kamar a kansa yake in dai zai masa awanni cikin gida, amma ni in ya yi kwana daya bai gan ni ba sai ya neme ni. Akwai sanda na kashe waya tsayin kwana biyu ina bincike, ta ce fada yake mata kamar zai doke ta kan ta turo masa ni, ba ruwanshi da wani bincike na.

Daddy duk ina gaya maka wannan ne saboda ka gane irin son da nake yi wa Mu’azzam, Daddy dama ni ne wannan lalurar ta ke a kaina… In dai zan ga ‘ya’yan Mu’azzam da fararen hakoransa a waje yana dariya kamar kowa. Ranar da na dauki hutun tahowa na gama wallafa littafina na farko;A Psychometric Investigation Of The Hypersexuality Disorder- Aboulkhair I.R’, kuma har na yi submitting dinsa a sashenmu na Neuropsychiatry a John Hopkins, tsofaffin malamai za su sake duba shi kafin a sake shi a duniya da sauran jami’o’in America. Kuma Proffessors na tsangayarmu bakidaya da tsofaffin likitoci na asibitocinmu daban-daban, da wadanda suka shude kafinsu a fannin sun tabbatar da cewa, wannan shi ne dependent kuma tsaftacciyar magana ta karshe a kan aggressive tendency and Hypersexuality Disorder”.

Dr. Mansour Raazee ya kama hannunsa ya rike tamau cike da fargabar abin da zai fito daga bakinsa… wanda shi ke determining future din rayuwar Mu’azzam, sai dai kafin shi ko Aboulkhair su ce komi Aboubacar da Aalimah sun yi sallama sun fado dakin a hargitse, wai basma Aboubacar ya kai asibiti yanzun nan za ta haihu, kuma haihuwar ta zo da tangarda. Likitoci sun tabbatar musu ba za ta iya haihuwa da kanta ba, ‘yan biyu ne, kuma haihuwar fari, ga shi ba ta exercise duk karfinta ya kare. Ana bukatar ya saka hannu kafin a yi mata aiki, shi ne ya zo su tafi gabadaya.

Fada Daddyn ya hau shi da shi, kan me ya sa ya taho ya baro ta ba tare da ya saka hannun ba? cikinsu wa ya fi dacewa da sanya hannun? Ya kasa ganewa Aboubacar a rude yake ba abin da zai iya kulla wa kansa a wannan lokacin.

Dukkansu suka dunguma zuwa asibitin standard inda a can ne Basma ke awo, Aboulkhair ya taimaka masa ya sanya hannun aka shigar da Basma dakin tiyata.

Aalimah ban da kuka ba abin da ta ke yi. Damuwarta shi ne, ko tozali da juna ba su yi ba. Ba yadda Basma ba ta yi ba kan ta zo ta ganta ko na minti goma ne ta koma, ta ce ita sai gobe. Da ta san haka ce za ta faru da ta je din, ta san Mama ba za ta hana ta ba.

 

******

Suna nan zaune jigum-jigum kowanne da carbi a hannu, ABoubacar sai safah da marwa yake a cikin asibitin. Mama ta koma gidansu don ta dauko kayan haihuwar da gigicewa ba ta bar Aboubacar ya dauko ba.

Aboulkhair ne kadai mai karfin hali, don waya yake yi da Mummy yana gaya mata ta yi wa Basma addu’a tana dakin haihuwa, kuma an ce ‘yan biyu ne. Sai dai bai gaya mata CS ake mata a halin yanzu ba, kada hankalinta ya zarta. Ya san Mummy sarai a kan son ‘ya’yanta.

Suna cikin wannan hali nurses biyu suka nufo su dauke da jarirai biyu cikin fararen shawul. Haba! In ba ka yi ba ni wuri, kowanne da gudu ya riske su tun kafin ya karaso tsakanin Aboubacar da Aalimah da Mama, Aboulkhair na yi musu dariya, don ya san shi kam ba za su ba shi ba. amma Aboubacar sai ya bi su yana tambayarsu lafiyar uwar jariran, murnar tasa rabi-da-rabi ce. Murmushi daya daga cikinsu ta yi masa, ta ce,

“Nan da minti goma sha biyar za ka iya ganinta a dakin aminity”.

Sai da aka gyara Basma aka kai ta daki, sannan aka ba su izinin ganinta. Aalimah ce a gaba, suka yi tozali da juna bayan rabuwar shekaru uku, ga ba damar rungumar juna, Basman na kwance ciki a farke. Sai murmushi ta ke wa Aalimah, ta miko mata hannu ta kama ta matse hannun sosai, sai kuma suka saki dariya dukkansu.

“Welcome to 9ja”. In ji Basma.

Da ‘yar siririyar wahalliyar murya, Aalimahr kuma ta ce,

“I congratulate us for becoming mummies”.

Aboubacar ya karaso da Hussainar ya dora mata a gabanta, Aalimah ta karbo Hassanar daga hannun Aboulkhair ta jera mata a gaban ‘yar uwarta. Basma ba ko kunya aka bude ido ana kallon ‘ya’ya, bakin nan kamar zai tsage don murmushi, ko kunyar Mama da ke gefe.

Aboulkhair ya ce, “Kin ji haushi wollah, mutum ba kawaici ko kadan?”

Mama ta ce, “Kyale ta ta gode wa Allah baiwar da Ya yi mata, kyautar ‘ya’ya mata biyu lokaci daya ma’abota jin kan UWA!”

Aboulkhair ya ce, “Au abin haka ne Mama? Mata na iyayensu mata ne? Ma cherie ba zan yarda ba, in kin zo taki kihaifo biyuamma mace da namiji kowa ya dauki nasa, ko ki haifi namiji daya, daga baya ki haifo takin. Amma wannan ai wayo ne”.

Kowa sai dariya har Aalimahr, duk da ta ji kunya. Haka Aboulkhair yake, very friendly to all. Shi ya sa yake da shiga ran kowa. Ba yadda za a yi ka yi zaman minti goma da shi ba ka nemi kun yi alaka ba. Bai da miskilanci, bai da jin kai. Ba za ka taba zaton da consultant ka ke zaune ba, sai dai saurayi dan makaranta.

Sai da suka kwana uku aka sallami Basma, suna ta ja wa Mama kunne ban da wankan ganye, sai na tawul. Murna a wurin Basma ba a magana, da ma ita wannan wankan ganyen da runhu da Mama ta ce in ta haihu sai ta yi mata ba karamin tayar mata da hankali yake ba.

Nan sultan road suka taho, Aboubacar da Aalimah suka je Hotoron suka dauko mata duk abin da za ta bukata.

Aalimah ta dade tana sai wa basma kayan haihuwa, duk abin da Aboulkhair ya sayo ya kawo ya ce ta ajiye saboda babynsu, sai ta saya wa Basma irinsa. Don haka ba kananan kaya ta tara ta taho mata da su ba. har da laces da tsadaddun materials don fitar biki. Ga wadanda Mama ta saya, ga na Aboubacar maigida kan gida. Ba a maganar wanda Mummy da Gumsu za su kawo nan da kwana hudu in sun iso. Don haka Basma da ‘ya’yanta sun ga gata, kuma suna kan gani, don jin cewa ‘yan biyu ne Mummy da Gumsu aka bazama kasuwa aka yi discarding waccan sayayyar aka ce an bar wa Aalimah, komi bibbiyu suke saye, kuma iri daya, ga shi an san abin da aka haifa.

Kwanan Basma bakwai cif! Da haihuwa wanda ya yi daidai da saura kwana biyar daurin auren Khaleesat saboda su Niger sai an fara daura aure ake shiga shagalin biki. Su Mummy suka iso Nigeria ita da Daddy da amarya Khaleesat da sauran ahalin gidan su Gumsu da kananan ‘ya’yansu Yesmin da Nurat. Kodayake yanzu ba mai kiran Yesmin yarinya, tunda kuwa shekarunta goma sha biyar.

Gida ya kacame da hidima ko ta ina, Mama da Gumsu nata jajircewa wajen kula da maijego da ‘ya’yanta. Sun so su yi taron suna a ranar ba zai yiwu ba, kasancewar duka ‘yan uwansu na nesa daga na Mama har na mahaifansu maza sai ‘yan uwan mummy Zulaiha ne suka zo, da yake su ‘yan Kano ne, su ma ba dukkansu ba saboda ba a gaya musu da wuri ba. Don haka su-ya-su suka yi get-together dinsu. Aka ce in ta yi arba’in ta je Nijar da maid. Amarya Khaleesat ta sha ado, maijego da Aalimah sun yi anko na wani masifaffen leshi baki mai fararen duwatsu da Mummy ta taho musu da shi a dinke. Daga wani kwararren gidan hoto na kano Aboubacar ya dauko mai daukan hoto ya zo ya yi ta daukarsu. Shi da Aboulkhair ma sun shigo an yi hotunan da su, kowanne kuma ya yi da matarsa a falon Daddy kamar wasu sababbin aure a yanayin da suka firfito cikin hotunan.

Basma ga bikin zuwa, amma babu zanen daurawa, wai bikin Khaleesat amma an ce ba ita za a yi saboda kawai ta haihu, kuma yanka ta aka yi. Ta turka kuka da magiya, amma babu wanda ya bi bayanta har Mummy mai gudun bacin ransu. Fada ma ta hau ta da shi tana fadin, ba ta da hankali, wadannan jariran sabuwar haihuwa za ta zuba a mota zuwa wata kasa biki, saboda ba ta da imani? Idan ba ta tausayin kanta, kuma ba ta san muhimmancin lafiyarta ba? Mama saboda ita ta ce ta hakura da bikin. Amma duk ba ta gode ba.

Aalimah ce kadai ta ke rarrashinta, a karshe ta ce, tunda Basma ba za ta ba ita ma ta hakura, da ma aiki zai wa Mama yawa, tunda ita ke kula da su ita kadai, masu aiki aikin gida kawai suke yi, amma har girkin abinci a wuyan Mama yake.

Khaleesat kuma sai ta sa kuka ita ma ba ta yarda ba, aurenta guda babu manyan yayyenta mata ba a yi mata adalci ba.

Karshe Daddy Ishaq ne ya raba wannan rigimar. Ya bai wa Khaleesat hakuri soslai, ya ce ta gode wa Allah da kyautar da ya yi mata ta ‘ya’ya har biyu, ta bar Aalimah ta zauna da ‘yar uwarta. Babu abin da za a fasa, a can Niger ma wasu tarin yayyen na jiranta za su yi mata komai.

Gumsu ta ce, “Ba ga su Balkeesa ba? Kuma ita Aalimah sai ta raka ki har Japan insha-Allah (Khaleesat a kasar Japan za ta zauna inda aka tura Hamoud ya karo wani course duk dai a kan sojancin ruwa kafin ya kammala ya dawo ya yi wa kasarsa Niger Republic aiki na din-din-din)”.

Aka samu Khaleesat ta hakura, sai suka koma tsara yadda tafiyarsu Niger za ta kasance.

Daddy ya ce amarya da su Mummy za su wuce jibi, kwana biyu da suna kenan. Su kuma sai ana i-gobe daurin aure za su yi asubanci. Mu’azzam ma sai ana i-gobe daurin aure zai shiga Niger. Ya yi musu booking Niamey Flight bakidayansu, har kannen Aalimah mata amma dole sai sun je Abuja babu jirgin Niamey daga Kano.

Su Mummy suka tashi zuwa Niamey suka bar masu jego, Aalimah da dukkan zuciyarta da lafiyarta ta ke hidimtawa Basma da jariranta. A gefe ga takurar Aboulkhair wanda kawaicinsa ya fara karewa, zaman ya fara gundurarsa shi da matarsa sai daga nesa. A gidan Aboubacar suke zaune shi da Aboubacar din. Cin abinci kadai ke shigo da su gidan. Har bankin GT Aboulkhair ke bin Aboubacar yana ganin yadda suke gudanar da ayyukansu, inda Aboubacar yake a branch dinsu na Hotoro. System din aikin Nigeria yana ba shi mamaki, ka wuni kana aiki amma albashin bai fi ka kashe shi a sati daya ba. Wai ma banki kenan, bankin ma mai daraja irin Guaranteed Trust.

Aboubacar ya ce, “A wurinka kenan. Mu kam ai mun san yadda muke tattala kayanmu ya kai mu karshen watan. Basma ma a nan ta ke aikin, saboda jami’ar da ta fito da na kawo wa manajanmu takardunta da gudu suka dauke ta ba tare da la’akari da abin da ta karanta ba”.

Irin hirarrakinsu kenan na matasa masu jini a jika, ‘yan uwan da suka san muhimmancin junansu.

Ana i-gobe za su tafi Niger bayan sun zo sun ci abincin dare wanda Aalimah ta dafa ta yi serving dinsu a dining ta koma gefe tana cin nata. Tunda suka zo suka raba plate saboda idon iyaye da sanin ya-kamata. Amma a nasu gidan bayan plate guda ma da one spoon suke amfani. Aboubacar ya riga gamawa ya tashi ya nufi wurin iyalinsa, wadanda suke a dakin Aalimah na gidan. Kamar jira Aboulkhair yake ya tashi, ya ajiye cokalinsa ya mike. Ya juya kofar dakin Mama da alama ta kulle ta ciki duk da dai ya san ba ta yi barci ba. Hannun Aalimah kawai ya kama ya mikar da ita. Za ta yi magana ya dora yatsa a baki, “Zo mu je, sako zan ba ki, yanzu za ki dawo”.

Aalimah ba ta gane Aboulkhair so yake su bar gidan ba, sai da ta ji ta a motar Aboubacar, ya tada motar da gudu, suka harba kan titi.

Kasa magana ta yi har suka iso gidan Basma. Ya shigar da motar cikin gate maigadin ya rufe ya wuce ciki ba tare da ya bari sun hada ido ba. To amma ai ita ta san kan kayanta, a kwayar idanunsa ta ke gano komai nasa. Kuma a yadda ta san halittar mijinta ta san ya yi kokarin da bai taba yi ba tun bayan aurensu. Sai ko komawar saJohn Hopkins yin part two exams dinsa da suka jima ba sa tare. Ranar da suka hadun kuwa, har gobe ba za ta manta yadda ranar ta gudana gare su ba, with a fondest thought!

Girgiza kai ta yi cike da tausayin mijinta, ta fito ta bi bayansa. Tun a falon Basma al’amuransa suka soma ganar da ita kewar tata da ya yi ba ‘yar kadan ba ce. Ba ta hana shi komai ba, karewa ma samun kanta ta yi da ba shi hadin kai da zuciya da gangar jikinta bakidaya fiye da na kowacce rana cikin rayuwar aurensu. Da wani irin feeling a zuciyarta da ruhinta da ba za ta iya kwatantawa ba.

Gare shi jin ranar yau yake kamar ranar da ya bare ta a ledarta, komai nata ya kara canzawa fiye da baya, sakamakon matashin cikin jikinta. Aalimah, na cikin sahun matan da ba sa taba gundurar mazajensu sabida baiwar ni’imar da Allah ya yi musu, wanda ita kanta ba ta sani ba, shi kuma ba shi da bakin furta mata hakan sai dai ta gani practically daga yanayin da yake kasancewa a kullum suke tare, wanda ke kara mata kaunarsa.

Dukkaninsu ba su san sanda wani irin barci ya sure su ba, wanda ba shakka na gajiya ne, saboda dukkaninsu sun taimaki juna ne ta hanyoyi da dama da ba su taba samun kansu a ciki ba.

Karar wayarsa ce ta tashe shi, ya janye Aalimah daga kafadunsa ya ga Aboubacar ke kiransa.

“Ban tambaye ka inda ku ka tafi ba, kawai ku yi zamanku da asubah mu biyo mu dauke ka, ita kuma ta dawo da kanta, ai ta san gari”.

Dariya Aboulkhair ya yi, wadda ta tada Aalimah daga nata daddadan barcin, suka soma shirin barin gidan.

Sanda suka iso karfe goma sha biyu na dare Aboubacar na kofar gida. Kasa fitowa daga motar suka yi dukkansu duk da sanin da suke da shi na cewa Aboubacar zai iya hango su ta glass. Hannunsa ya dora a kan cikinta yana sauraron harbawar jaririn yana lumshe idanu ya ce, “Kin san wani abu?”

Girgiza kai ta yi, haka kawai ta ji ranta ba dadi, kamar su koma gidan Basman su kwana tare. In ya tafi Niger ita da ganinsa sai nan da kwana goma in an gama bikin Khaleesat, sannan ne zai zo su koma. Ba lokaci daya za su tashi da ‘yan Massachusetts ba, su sai nan da sati biyu. Ko dai ta kyale Basma ne ta bi mijinta ga kyawawan ‘yammatan nan na zuri’arsu da ba ta san iyaka wadanda za su kalle mata shi ba? Wani bala’e’en kishi ya turnuke ta irin wanda ba ta taba sanin tana da shi ba. Sabida a inda suke rayuwa ba ruwansu da irin wadannan abubuwan kowa da life-partner dinshi ba mai shiga gonar wani. Ta girgiza kai, ba tare da ya fahimci tunanin da ta ke ba, ya ce, “In namiji ki ka haifa ‘MU’AZZAM zan sa masa, in mace ce, ‘AALIMAH’ (mai ilmi) yadda zan ji dadin gaya mata how sweet and loving her mum is, how helping and generous she is, how much I truly love her and the long time I spend waiting to marry her. Duka zan gaya mata Aalimah, idan kuma namiji ne zan gaya masa yadda na rayu cikin soyayyar dan uwana mai lalura, yadda nake sonsa da burin samun lafiyarsa. Yadda ya kyautata wa rayuwata, ya tsaya min against all odds. Ya mayar da ni abin da nake a yau; Aboulkhair mai rayuwa da tsayayyun kafafu mamallakin Aalimah. Har ga shi za ta samar da Da a gare mu ni da Mu’azzam…”

A lokacin ya ankara Aalimah kuka ta ke yi.

“Mon Amour na fasa zama, tare za mu tafi”.

Dan tsayawa ya yi yana nazarinta gabadaya ta birkice kamar ba ita ba. Nazarin maganganun da ya furta yake yi, ko akwai na tashin hankali a ciki? Iyakar tunaninsa bai gani ba. Kuka ta ke yi shabe-shabe da hawaye da majina. Janyo ta ya yi jikinsa, ya ce, “Aalimah”. Sunanta na hakika.

“Nda’am”. Ta amsa cikin rishin kuka, don rabon da ta ji ya kira ta tun zamanin samartaka (‘yammatancinsu).

“me na fada wanda ya bata miki rai?”

“Babu komai”. Ta amsa da sauri.

“To me ya sa za ki canza shawara cewa sai kin je Niger? You are kidding. Kada ki dauka ban san halin da ki ke ciki ba, ko daga kumburarrun kafafunki. Kina wasa ne ma da ki ke tunanin zan barki ki shiga kujiba-kujibar bikin nan na Niger, ki je kina girkin roti da rawa a wajen cocktail, ki jawo min asarar da ban taba shirya mata ba! Don haka ki saki ranki kawai mu yi rabuwar arziki ko a yi ta tsiya-tsiya”.

Ba ta san sanda murmushi ya kubuce mata ba, ga hawaye face-face a fuskarta. Ba ta yi aune ba ta ji Aboulkhair ya rungume ta, sai saukar harshensa a fuskarta yana dauke hawayen salla-salla daga kan fuskarta. Idanun kuwa har wani side su yake yi.

Aboubacar da ke gefe yana waya da Basma yana jiran Aboulkhair ya sallami Aalimah su tafi, gefen idanunsa ya dan hasko masa abin da ke faruwa. Da sauri ya yi cikin gida yana bai wa Basma labari, ta kai yatsunta ta rufe fuskarta wai tana ji masa kunyar abin da ya gano. Sai jinsa ta yi a nata kumatun yana fadin, “Bari in nuna miki yadda suke yi”.

Aboukhair da Aalimah ba su rabu ba sai karfe daya daidai na dare. Tana tafiya zuwa cikin gida tana waiwayonsa da murmushi, yana tsaye jikin motar Aboubacar shi ma murmushin ya ke mata. In ba ta yi kuskure ba ba ta taba ganin irin wannan kasaitaccen murmushin daga gare shi ba.

 

*****

Daddyn Aalimah, Daddyn Aboulkhair, Aboubacar da Aboulkhair afilin jirgin saman Malam Aminu Kano, fuskokinsu cike da takaici da bacin rai. Wai babu jirgi mai zuwa Niamey a yau sakamakon lalacewar jirgin da suka yi booking din a safiyar yau, yana can Niamey ma bai taso ba ana gyara shi.

Aboubacar ya duba agogon hannunsa, ya ce, “Daddy, da wannan zaman cinye lokacin da muke gara mu je mu bi mota. Tafiyar awanni goma sha biyu cif nan gaba za ta kai mu Niamey. Yanzu karfe takwas na safe, in muka yi sauri muka dauki hanya zuwa tara na safe za mu isa Niamey nan da karfe tara na dare. Za kuma mu samu daurin aure a kan lokaci”.

Duk sun yi na’am da wannan shawarar, Daddyn Aboulkhair ya ce, “Aboulkhair is a very good driver, na tabbata kafin lokacin ma mun isa”.

A gurguje suka dawo gida suka yi wa Mama bayanin canjin da aka samu. Ba su bata lokaci ba suka dauki sabuwar motar Dr. Mansour kirar Jeep 2015 model, Aboulkhair ya tada ita suka shisshigar da kayansu, sannan Aboubacar ya shiga gaba, iyayen suna baya su biyu. Ko su Aalimah ba su san da wannan sauyin da aka samu ba, ba sa gidan dukkaninsu tun sassafe, ta raka Basma asibiti, Hassana (Zulaiha) na fama da mura, Hussainar sunan mama aka sa mata (Aseeya).

Sai da suka shiga gidan mai suka yi full tank, sannan suka dauki hanyar jamhuriyyar Niger.

                      ******

Mummunan hadarin motar ya afku ne kafin a kai boarder din da ta raba iyakar kasar Najeriya da jamhuriyyar Nijar, bayan sun tsallake garin Jibiya sun shiga boarder din kasar Nijar.

Wasu gungun fulani ne makiyaya suka koro shanu a kan titin za su tsallaka. Ga direban Jeep din ya kwararo motar da gudu irin na neman biyan bukata. Burinsa su shiga Niger kawai kafin azahar a kalla ya san suna cikin kasar ainahinta, inyaso su yi sallah su ci abinci su durfafi Niamey ba tare da sun bata lokaci ba.

Shanun sun taho fal da gudunsu, shi ma ya shararo motar, sai ya ga bari ya dauke kan motar da azama tunda daya titin babu mota ko daya, ba tare da lura da cewa wata karamar mota ta taho ita ma a guje ta bayansa ba, kawai ta ga motar a kan nata titin ba tare da ta tsammata ko ta ankara ba. Kafin direban karamar motar ya yi tunanin abin yi, ya yi mugun taho-mu-gama da bakar Jeep din wanda hakan ya sanya duka motocin biyu fara katantanwa a tsakiyar babban titin kafin a karshe su duka biyun su hantsila wani katon rami a gefen titin. Ba ka jin komai sai hailala da salatin mutanen da ke cikin motocin cikin mika wuya ga hukuncin mahaliccinsu.

 

******

Da asubahin ranar Hassana da Hussaina suka ci gaba da ruda gidan da kuka, wanda suka kwana suna yi suna hutawa. Tun daren jiya sun ki karbar nono. Daga Basma har Aalimah babu wacce ta runtsa, suna fama da yaran nan saboda mama na can dakinta kwance babu lafiya, ta ce kuma takamaimai ba ta san inda ke mata ciwo ba, amma ko hannunta ta kasa motsawa balle ta zo ta taimaka musu. Daga kwance ta ce su dinga yin addu’a suna tofa musu.

Basma gefe ta koma ta zuba tagumi, nonuwa sun mata suntum suna ta sukarta suna kuma diga, duk sun jika gaban rigarta. Aalimah na so ta yi sallar asubah don har masallacin kusa da su sun idar, yaran duka biyu suna hannunta tana jijjaga su, ta san in ta ajiye su Basma ko taba su ba za ta yi ba. ta zama dumm! Kamar wadda ta samu ciwon kurumta na lokaci mai tsawo.

Aalimah ta ajiye daya ta goya daya. Rabonta da goyo tun haihuwar Aunty Gumsu. Tunda aka sallamo Basma Mama ke goya su, ta zura hijabi ta tada sallah zuciyarta na harbawa da kukan da yarinyar ke zubawa a bayanta. Ga wadda ta ajiye ita ma ba ta fasa ba. Kawai ita ma sai ta soma kukan tausayin Basma, ta san tsananin damuwa ne ya sa ta daina tabuka komai a kansu. Allah-Allah ta ke ta idar su tafi asibiti, tukin motar da Aboulkhair ya nace ya koya mata duk da ba ta so yau zai yi mata amfani. Da safe ma ita ta kai su asibiti aka duba yarinyar aka ce mura ce kawai, suka sayo magani suka dawo.

Nan Mama ke gaya musu tafiyar su Daddy a mota sakamakon rashin jirgi. Duka addu’ar sauka lafiya suka yi musu, suka ci gaba da hidimar yaran.

Tun bayan maghriba kuma suka bude makogaro suke zunduma kuka. Wanda shi ne har yanzu suke fama. Tana idarwa ta fito goye da Husainar ta je dakin su Sabrina ta rufe su da duka suna barci. A tsorace duk suka tashi suna tambayarta me ya faru? Kuka ta hau yi a gabansu tana fadin, sai barcinsu na tsiya ya jawo musu masifa, uwarsu na kwance babu inda ta ke iya motsawa tun dare suna nan suna barcin asara, duk kukan da ‘yan biyu ke yi ba su san ana yi ba ko me? Rantsuwa suka hau yi mata suna dirgowa daga gado suna fadin, wallahi ba su sani ba, kuma su ba su ji kuka ba. Ta ce su je su kula da Mama ita da Basma za su je asibiti a duba yaran.

Wata na ture wata haka suka fita a gigice, ta bi su da harara da idanunta da suka yi jawur. Lokaci-lokaci gabanta na tsinkewa ya fadi, har sai ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta ta ambaci sunan Allah. Dan cikinta sai wani irin juyi yake kamar ya wuce watanninsa. Ta dawo tana rarrashin Basma, ta canza riga su tafi asibiti, amma ta yi gumm! Kamar ba da ita ta ke ba, gani kawai ta ke rasa yaran za ta yi, don haka ba ta ga amfanin su je wani asibiti ba. ga Aboubacar tun kafin azahar rabonsa da kiranta, ita kuma in ta kira shi wayar ba ta shiga. Dalilin damuwarta kenan.

Aalimah ta yi rarrashin duniyar nan, Basma ta ki tashi, kawai sai ta fashe da kuka mai karfi.

Ta ce, “Basma, ya ki ke so in yi da raina? Kina so na zauce? Ga Mama can ba ta san wanda ke kanta ba, ni ma zuciyata tsinkewa ta ke yi, karfin hali kawai nake yi, su kuma da gani akwai abin da ke damunsu. Jarirai su kwana ba su sha nono ba ki ce haka za mu ci gaba da zama da su muna kallonsu?”

Basma ko gezau! Sai ta rabu da ita ta sanya hijab din sallarta ta dauki mukullin motar Aboubacar da ya bar musu don irin hakan, kamar ya san za su bukace ta. Ta nade Hassanar a shawul mai kauri, ta dauki katinansu na asibiti ta tafi, Suhaima ta biyo ta da gudu ta karbi ta hannunta tana fadin, “Muje na raka ki in ji Mama”.

Da suka je asibitin a sashen sababbin haihuwa aka karbi jariran (Day old), likitoci suka hau bincikarsu. Suka samu wuri ita da Suhaima suka zauna. Sai a lokacin nutsuwa ta soma dawo mata jin ta daina jiyo kukansu. Tunanin Aboulkhair ya fado mata. Ta kira shi bayan sun dawo daga asibiti da safe ya ce mata suna Katsina, “in mun shiga Niger I will call you. Take care of yourself and my baby for me MON AMOUR!”.

Kiran da har yanzu ko kyallinsa ba ta gani ba. Tsabar jiran kiran wuni ta yi rike da wayar a hannunta, in sallah za ta yi a cikinta ta ke soke ta. Da ta gaji da jiran ta yi ta gwadawa ita ya ki shiga. Ta yi tunanin sun shiga sahara sun rasa network, amma har twins suka fara jiniyarsu babu kiran Aboulkhair ko na Aboubacar. Mama ta ce, Daddy ma bai kira ba. A lokacin ya isa a ce ma sun shiga Niamey. To balle yanzu da za a iya cewa sun kwana sun hantse, tunda har ga shi alfijir ya keto.

Ba ta kawo wani mummunan tunani a ranta ba, duk da ta san Aboulkhair yana da layin Niger. Ta sa a ranta bai samu sukunin kiran nata ba ne saboda gajiya duba da cewa, shi ya tuka motar tun daga Nigeria har Niger, har kuma babban birni Niamey. Sai dai wannan tsinkewar na zuciyarta shi yake damunta, saboda ba a son faduwar gaba ga mai ciki. A matsayinta na medical personnel ta san hatsarin hakan, don haka ta koma hailala da salatin Annabi cikin zuciyarta.

Daidai lokacin likitan da ya karbi yaran ya fito. Tambayarta ya yi, ina uwarsu? Ta ce tana gida.

Da mamaki ya dube ta, sai kuma ya basar ya

 ce ta je ta zo da ita za a debi nonon a ba su ta hancinsu, masassara ce ta cika musu makogaro.

Ta ce da Suhaima ta zauna ta je ta zo da Basma, ba za ta jima ba. Har Mama za ta dauko.

Tun daga nesa ta hangi bakar motar ‘yansanda fake a kofar gidansu. Tsinkewar da gabanta ke yi ya fadi da ta samu ya lafa sabida karfin hailala ne ya sake faruwa da ita. ‘Yansanda biyu na tsaye tare da maigadinsu Bilyaminu.

A hankali ta ke rage gudun motar ta wuce su ta nufi gate tana danna wa Bilyaminu horn da nufin ya zo ya bude mata ta shige.

Bilyaminu ya karaso da sauri, maimakon ya bude mata sai ya tsaya yi mata bayanin wai ‘yansandan gidan suka zo. Wani babba a gidan suke son gani. Ba halinta ba ne raina babba ko na kasa da ita, amma ba ta san sanda ta sakar wa Bilyaminu harara ba, “Amma dai ka san daga Daddy har Yaya Aboubacar ba sa nan ko? Don me ba za ka gaya musu ba da za ka tare ni kana gaya min? Ka san uzurin da ke gabana? Tunda ka ga na fita da asubah na dawo yanzu ba sai ka bude min kofa ba ka san ya zaka yi da su ba, tunda ba sata na yi ba?”

Daya daga cikin ‘yan sandan ya karaso ganin ta ki kula su, kuma ta rufe dattijon da fada, “Excuse me Madam!” Ya fada da kyakkyawar siga.

Dole ta yi shiru ta bi shi da ido.

“Muna neman gidan Dr. Mansour Raazee, lecturer a jami’ar Bayero, tsangayar Mass Communication, da gidan Aboubacar Raazee, accounter GTBank Hotoro Branch”. Ya fada cikin harshen turanci.

A sanyaye ta ce, “Nan ne!”.

“Ko za ki turo mana namiji ya bi mu ofishinmu? Akwai bayani a kansu”.

Girgiza kai ta yi, abin gwanin ban tausayi ta ce, “Ni ce babba a gidan, babu namiji bayan su, uwata kuma ba ta da lafiya”.

Tsayawa ya yi yana tunani, bai kamata ya tafi da ita ba ya gaya mata al’amarin da ke tafe da shi, ga ciki yana gani tare da ita, kuma ga dukkan alamu dukkaninsu ‘yan uwanta ne. A hotunan da aka turo musu babu wanda bai yi kama da ita ba.

“Madam, daure ki turo min namiji ko makocinku ne, zan fi son magana da shi a kanki”.

“Ka yi hakuri Officer, ni ma bakuwa ce a unguwar ban san kowa ba. Ka yi hakuri ka bar ni in wuce in ba za ka hanzarta fadar uzurinka ba. Na baro jarirai a asibiti”.

Kawai sai ta soma hawaye a gabansu, zuciyarta ce ta tsinke, jikinta ya gama ba ta wani tafiyayyen labari ne suke tafe da shi, wanda zai kawo karshen duk wani farin cikin rayuwarta. Wanda suke shakkar tattauna shi da ita, ganinta mace, kuma mai ciki.

“Ok, since you insist (tunda kin dage), za ki iya biyo mu ofishinmu?”

Ta zuki numfashi da kyar, amma ta kasa furzo shi waje. Yau ita ce a ofishin ‘yan sanda a kan laifin da ba ta sani ba! Kodayake sun ce abin da suke tafe da shi din ya shafi babanta da yayanta ne. To ko laifi suka yi? Ko kama su aka yi a hanyar Niger din? To su kuma sauran da ba’a ambata ba ina suke?

Ba ta da amsa ko daya, don haka ta share hawayen da suka cika mata fuska ta ce su ba ta minti goma ta fada a gida, ta dauko ‘yar uwarta ta kai ta asibiti, sai ta same su a inda suka ce.

Tana shiga gida ta tarar da wani tashin hankalin. Basma ce a sume, su Sabrina na ta sheka mata ruwa. Duk tsananin da Mama ke ciki ta sa sun tayar da ita sun jinginar a jikin filo. Sabrina ke gaya mata tunda aka yo mata waya daga Niger aka ce su Daddy ba su isa ba tun jiya kuma an kasa samun kowannensu a waya ta ke suma tana farfadowa. Ta dubi Mama a firgice sai Mama ta lumshe ido, ta ce, “Ku hada karfi ku sa ta a mota, ki kai ta asibiti”.

Jikinta na rawa ta ce, “Mama har ke zan kai, wallahi ba zan barki a gida ba. Kuma yanzu zan yi wa Mummy waya har Niger din in gaya mata ga halin da ku ke ciki dukkanku, ni kadai ba zan iya ba, kwakwalwata kamar ta zauce. Yanzu haka ‘yan sanda ne a bakin gate sun zo tafiya da ni. Ba su je Niger ba, ina suka je? Na shiga uku ni Aalimah, ko dai ‘yan fashi ne suka tare su?”

Dukkansu babu wanda ya kawo wani abu a zuciyarsa bayan wannan, Mama ta ce ba za ta iya fita zuwa mota ba. Aalimah na kuka ta ce, “Ko a goye ne sai na kai ki asibiti”.

Ita da kannenta biyu suka ciccibi Mama, rabi kuma da kafarta suke janta a kasa zuwa mota. Suna fitowa harabar gidan Tabawa da Sabira suna shigowa (masu aikin Mama), wadanda ba aikin kwana suke yi ba.

Wata ajiyar zuciya Aalimah ta yi, da hanzari suka taimaka mata ta sa Mama a mota, ta gaya musu saura Basma, Tabawa ita kadai ta ciccibo Basma sabida kakkarfa ce. Gabadayansu suka duru a motar har su Sabrina, su biyu a gaba, ta ja su zuwa asibitin da ta kai su Hassana da Hussaina.

Dukkansu an karbe su ba bata lokaci, da yake asibitin na kudi ne, international. Ta gaya wa Mama za ta je ofishin ‘yan sandan ta dawo, Mama na daga kwance ta ce ba ta yarda ba. Ta kara gwada layin Aboulkhair, in har yanzu ba ta same shi ba, ta kira Uncle Oussama ta gaya masa, ko kofar asibitin ba ta yarda ta taka ba.

Hakan kuwa ta yi, duk da cewa ta so Mama ta barta ta je, don idan reality bai kassara ta ba, fargaba da zullumi dake zuciyarta za su haifar mata da hauhawar jini, wanda shi ma ba’a sonsa ga mai ciki.

Jiya-i-yau. Ba ta samu Aboubacar ko Aboulkhair ko Daddy ba. Don haka tana kuka ta kira Oncle Oussama wadanda ke can zugum-zugum sun kasa daura aure bayan sun tara jama’a makil daga birni da kauye, tunda babu labarin iyayen yaran bayan kowa ya tabbatar da tahowarsu tun jiya.

Kukan da ta ke yi bai hana shi gane me ta ke cewa ba. Duk halin da suke ciki tun jiya ta warware masa. ta gaya amsa yanzu haka duk an ba su gado daga su har jariran kuma Mama ta hana ta zuwa police station din.

“Za mu zo a yau, kada ki sake kije police station dinnan”. Abin da ya ce mata kawai kenan yana mai jin wani irin tsoro da tashin hankali na shigarsa.

Ango Hamoud da ya yi zugum a gefe, da Mu’azzam da ya iso tun jiya ya ja gefe ya ce su je su nema musu ticket yanzu-yanzu mai zuwa Abuja, shi da Edrissa da Mu’azzam da angon da Malam kansa. Bayan wannan bai kara musu bayanin komai ba. Ya karbi sadaki daga hannun kaninsa babban dan Inna Bintou ya daura auren Khaleesat da Hamoud ba cikin dadin rai ba, sai don ba yadda za su yi da jama’ar da suka tara. Tun ba a gama watsewa ba ya ja Malam gefe ya gaya masa duk bayanin da Aalimah ta yi masa a waya, ya kara da cewa, yana tsammanin suna hannun ‘yan sandan da suka je neman wani nasun, ko dai sun yi wani laifin ne an kama su, ko ‘yan fashi ko hadari. Abin da yake zato kenan.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Shi ne abin da Malam Ibraheem Raazee ke ambato, babu kakkautawa. Zufa na keto masa ta ko’ina a jikinsa a lokacin da ya daga kai ya hangi Mu’azzam na fitowa daga mota.

 

 

Su waye suka mutu su waye zasu rayu? Kun yarda rayuwa bata da tabbas? Kun yarda ba abinda yake dorewa banda ikon Allah? Idan kun yarda da hakan to yanzu muka fara labarin Aalimah.!SumayyahAbdulkadir na tafe da cigaban labarin nan ba da jimawa ba!!!