Book 3 (End)
by @takori
Aalimah ta yi wani dan juyi cike da jin dadin barcinta jin sanyi na shigarta tun daga tafin kafa, sakamakon dan janye bargon da Mu’azzam yayi daga jikin ta. Jikinta ne ya ba ta akwai mutum tsaye a kanta. Da sauri ta bude ido, wadanda suka kada suka yi jajir sabida nauyin barci, sai suka rikide suka bada wani irin yanayi mai motsa zuciya, bata yi aune ba sai samun idanun ta tayi kane-kane cikin na Engnr. Mu’azzam Ishaq Raazee, wanda ke tsaye saitin kanta ya zuba mata ido. Da mugun sauri ta yayibi zanin gadon ta rufe jikinta gaba daya. Juyawa ya yi yana mai sakin tsaki ya bar dakin yana mai ce da ita da murya ciki-ciki,
“Ki zo Mummy na kiranki a kasa”.
Dakinsa ya karasa cikin takunsa na nutsuwa da kasaita, lokar jikin gadonsa ya bude. Lokacin shan maganin sa har ya wuce yana can yana yawo a titi duk don kar ya hadu da Aalimah, gashi ya tashi a banza tunda Mummy sai da ta san yadda tayi ta hada su. Magunguna ne ga su nan birjik! Wadanda aka rubuta mood stabilizers su ya cira ya dauko gorar ruwa cikin karamin firjin da ke gefen gadonsa, ya watsa su cikin bakinsa, ya bi su da ruwa. A hankali ya kwanta bisa gadonsa yana maida numfashi a sannu. Saukowar da bai kara yi ba kenan sai asubahin wayewar gari. Shi da kansa ya tuka Mummy zuwa airport bai hada ta da Harrison ba.
Har da Aalimah aka tafi kai Mummy airport, don haka a hanyarsu ta dawowa daga shi sai Aalimah cikin motar an rasa mai yin ko motsin kirki a tsakaninsu. Aalimah ko numfashi za ta fitar sai ta tabbatar ta sake shi a hankali, yadda ba zai zama takura ga Mu’azzam ba. Ta san halinsa sarai, ba yau ta sanshi ba.
Suna isowa gida ta bude motar a hankali ta fita, haka nan a hankali ta rufe ta silently. Ta juya cikin takun nutsuwa ta shige cikin gida, ko kofa za ta bude a hankali ta ke yi, don sanin cewa Mu’azzam ya biyo bayanta.
******
Tafiyar su Mummy sai ya mayarwa da Aalimah gidan kamar maqabarta. Har zuwa washegarin ranar bata kara sanya Mu’azzam a idanunta ba. Ko motsinsa bata ji ba duk da cewa dakunansu na daura dana juna. A washegari Mu’azzam sammako yayi ya fice office ko karyawa bai yi ba, tana iya jiyo fitar motarsa daga gidan. Tana daga kwance a gadonta tayi ajiyar zuciya. A lokacin zuciyarta tayi zurfi cikin tunani mai dimbin yawa. Shikenan rayuwarta da Aboulkhair ta zama tarihi? Mu’azzam ne zai maye duk wani gurbi da Aboulkhair ke kai a baya? Ta yaya hakan zai kasance?
Bata taba yiwa Mu’azzam wani kallo bayan na Yayan su ba, ko ta ce Yayan mijinta. Rayuwar shi da tata ba iri daya bace; ratar dake a tsakani mai tsananin fadi da girma ce. Ga matsalar da yake ciki wadda bata san ranar warkewar ta ba. Saidai tana da tabbacin aggressiveness dinsa bazai shafe ta da komai ba. Zata iya yin nisa da shi a duk lokacin da taga alamun yana kokarin shiga cikin sa. Tunda Aboulkhair ya gaya mata yadda yake. Wanda ana daukan shekaru ma hakan bai faru ba. To amma babbar lalurar fa?
Aalimah ta nisa, ta aje gwauron numfashi.
Ko lokacin da take tare da Aboulkhair ita ba mai son yawan auratayya bace, wancan ma kenan da ya kasance soyayya ce mai tsanani a tsakani balle wannan da ya zamo hadin iyaye, ba da son ran ko dayansu ba.
Tana matukar ganin girman Mu’azzam da ganin kimar sa cikin idanunta, bata fatan zuwan ranar da zama irin na auratayya zai kasance tsakanin su. Koma dai yaya ne, tasa a ranta zaman iyayensu zata yi a gidan nan ba zaman Mu’azzam ba, wanda take da tabbacin shima ba son auren yake yi ba koda ace bai bude baki ya furta ba. Alamu duk sun gama bayyana kansu.
Data gaji da tunanin wanda ta amince bazai kawo mata mafita ba cikin tarin kalubalen dake gabanta, sai ta tattara komai ta mikawa Ubangiji. Ta tashi ta dauro alwala ta shiga gabatar da nafilfili.
Lokacin gari yayi haske, ta yunkura ta mike daga kwanciyar bayan ta ture bargon rufarta. Kai tsaye toilet ta fada tayi wanka tayi brushing bakinta ta dauro towell ta fito. Ta bude closet dinta ta soma ruwan idon kayan sanyawa. Ba Mu’azzam take da niyyar yiwa kwalliya ba kawai ta samu kanta yau cikin sukunin zuciya irin wanda bata taba samu ba tun rasuwar Aboulkhair. Lallai ne da ake ce aure rahma ne, kuma gidan miji ‘yanci ne ga diya mace koda wane iri ne kuwa.
Ruwan idonta ya tsaya akan wata doguwar riga ‘dark blue’ wadda nauyin duwatsun jikinta yafi yadin rigar nauyi, ta cirota ta zura a jikinta sannan ta zauna kan stool gaban dressing mirrow tana gyara dogon sassalkan gashin kanta wanda saida dabara take iya tazarsa.
Wayarta dake kan bed-side tayi kara da kiran sallah wanda shine ringing tone dinta. Mikewa tayi ta isa ga wayar ta dauka. Ganin sunan mai kiran sai ta zauna a gefen gadonta cike da farinciki tana amsawa.
Mama ce.
Bayan sun gaisa cike da shauki irin na Da da mahaifi ta tambayi lafiyar kowa na gida, Mama ta tabbatar mata kowa lafiya, ashe Daddy na kusa, don Mama mikawa Daddy wayar tayi tace shi ke son magana da ita. Aalimah ta gaisheshi shi kuma ya dinga zuba mata albarka akan biyayyar data yi masa, ko daga sautin muryarta ya fahimci ta kwantar da hankalinta yanzu ta kuma rungumi kaddararta da hannu bibbiyu.
Dr. Mansur yace “Aalimah kinsan dai ni na haifeki ko?” Ta gyada kai cikin tabbatarwa kamar yana ganin ta. Yace “to ki yarda bazan taba yin abinda zai cutar da ke ba. Kada rashin lafiyar Mu’azzam yasa kiyi tunanin don bazai samu matar aure bane yasa muka aurar dake gareshi, ko kadan, Ko ‘yar wa Mu’azzam yake so a fadin kasar Nijar zai aura mun dai ga bashi da niyya ne. Bari in gaya miki wani abu wanda ko uban Mu’azzam da ya haifeshi bai sani ba.
Rana ta karshe dana gana da Aboulkhair a dakina, munyi maganganu masu yawa akan Mu’azzam, kin san dai fannin rashin lafiyar Mu’azzam ya karanta har matakin consultant, kuma yake kan cigaba da zurfafa ilmi akai a jami’ar Johns Hopkins, ya gaya min bincike na karshe da suke kan yi of recent research ya nuna Mu’azzam zai iya warkewa gabadaya, zai koma normal sexual life bayan shekaru kamar goma in dai an kula da bashi treatment. Ya gaya min yana so ya gayawa Mu’azzam amma ya fasa don kada yace sai ya warke zai yi aure, amma ko likitansa Nebrass yasan Mu’azzam zai iya warkewa daga yanzu zuwa kowanne lokaci in aka kidaya yawan shekarun da ya kwashe cikin lalurar karkashin kyakkyawar kulawa kuma zai iya rayuwar aure yanzu haka (under treatment).
Shine dai yake tsaurarawa kansa damuwa da ganin cewa rayuwar sa ta gama amfani. Amma babu cutar da Allah ya saukar a duniya ba tare da ya saukar da ita tare da maganin ta ba. Ki yi tawakkali ki tattara komai ki barwa Allah. Kiyi addu’a kan Allah ya hada kanku da kuma zukatanku wuri guda, ki zubawa sarautarsa ido.
Ni Mansur Sarhamu Raazee na tabbatar miki sai kinyi alfahari da wannan auren watarana kuma sai kin zo kin gode mini. Soyayyata gareki ce tasa nayi miki wannan zabin. Zabin da duk cikin family din RAAZEE babu mai kamar naki. Ki kwantar da hankalinki a gidanki kinji Aalimah? Ki kuma yi hakuri da halin Mu’azzam mutum ne mai wuyar sha’ani. A matsayin ki na mace, zaki iya canza shi zuwa duk irin yadda kikeso ya koma. Mu’azzam is a nice person kuma idan kinyi hakuri zaki ci riba watarana”.
Aalimah hawaye take yi tana sharewa da bayan hannunta. Ta san Daddy na sonta amma zata iya bayar da shaidar son da yake yiwa Mu’azzam ya nunka nata sau goma. Zuciyarta na mai amanna da kowacce kalma dake fita daga bakinsa.
Cikin rishin kuka Aalimah take fadin.
“Don Allah Daddy ka yafe mun gardamar dana yi maka a baya. Na rasa nutsuwa ta ne a lokacin. Ba kiyayya nake yiwa Mu’azzam ba, sannan ba rashin lafiyar sa ke damuna ba, ina dai duba kusancinsa da Aboulkhair ne. Amma daga yau na yi maka alkawarin cire komai daga raina insha Allahu, na yarda haka Allah ya rubuto mana bakidayan mu. Na san aure a tsakaninmu halastacce ne. Na yarda da duk abinda ka fada, ko Mu’azzam ba zai warke ba zan zauna dashi insha Allahu har karshen rayuwata. Ka taya ni addu’a Allah yasa nima ya so ni irin yadda Aboulkhair ke so na......!”.
Sai kukan ya kwace mata bakidaya.
Daddy yace “is OK, is ok my dear. Na fahimta ki daina kukan. Na yafe miki duniya da lahira. Allah yayi muku albarka bakidaya”.
Bayan sunyi sallama ya mikawa Mama, ta share hawaye suka cigaba da hirarsu, tace a bata su Sultana su gaisa. Mama tasa murya ta kira su dukkansu su ukun. Ta mikawa babbarsu wato Sultana wayar. Nan kokawa ta fara, kowacce na fadin ita zata fara magana da Yaya Aalimah. Kaunar da suke yiwa Yayar nan tasu ba ‘yar kadan bace. Murmushin kauna ya subuce a siririyar fatar bakinta, tace “shikenan a yi video call. Ina ganinku kuna ganina”. Nan suka bata lokaci har wajen azahar saida Mama ta kwace wayarta ta kashe.
Aalimah ta koma jikin pillow ta jingina tana murmushin samun nutsuwa a ranta da jin muryar kowa nata data yi, da kuma muhimman maganganun da suka yi da Babanta. A lokacin ta kira Basma don jin yadda suka sauka, sun dade suna hira tasa mata kukan twins suka yi ta dariya. Ta tambayeta Yaya Aboubacar tace yana office sannan suka yi sallama. Taso ta kira aunty Gumsu taga lokacin sallar azahar yayi, ga hirar Gumsu bata karewa, dole ta hakura da niyyar da daddare kafin ta kwanta zata kirata.
Bayan tayi sallar azuhur ta sauko kasa, kitchen ta shiga don samawa cikinta abinda zata ci, bata yi tunanin girka komai ba don dai tasan ita kadai ce a cikin gidan ba kuma yanzu mamallakin gidan zai dawo ba, ta san sai dare ya nausa, watakila har sai ta yi barci, duk don kada ya hadu da ita, ita da baya son gani, itama bata sa aka ba, kowa yayi rayuwar da yake so cikin gidan.
Garin quaker oat ta farke cikin gongoninsa ta dama da madara ta zauna cikin kitchen din tana sha. Data gama ta fito falon gidan na kasa, a yau lungu-lungu sako-sako na gidan Mu’azzam saida ta shiga, dakin dasu Mummy suka tafi suka bari ta shiga ta gyara shi tsaf. Yau bata san mai yasa yaron gidan bai zo ba wanda ta ji su Mummy na kira Jacob, shi yake yiwa Mu’azzam duk wasu aikace-aikacen cikin gida da kula da furanni yayin da Harrison ke yin direba da kula da motoci da sauran abubuwan da ba’a rasa ba.
Gidan Mu’az ya burgeta matuka domin gidane da aka yi amfani da hikima da fasahar bature wajen gininsa, tun zuwanta gidan bata shiga ko’ina ba kullum tana daki, sanda suke zuwa ita da Aboulkhair kuma iyakacin ta falon kasa. Idan ka hau sama tun daga steps din benen zaka soma shaqar sassanyar kamshin turaren Mu’azzam wanda duk sanin da tayi wa turare ta kasa tantance wanne ne turaren Mu’azzam. Sannan ta fahimci his favourite colour is white daga fentin gidan, labulaye (curtains), furnitures, kujeru har tiles din gidan farare ne kal suna masu kayatar da idanun mai kallon su, haka motarsa da yake hawa Acura fara ce sol, sai surki da baki cikin gidan jefi-jefi.
Data gaji dakinta ta koma ta rasa abin yi, saboda ita bata saba zama cikin kadaici ba, a Yamai kullum cikin ayyukan gida suke itada su Balkissa, ko taya Kakannin su girki da sauran abubuwan debewa mutum kewa. Tana matukar kewar Balkissa da Rumana. Gashi ita ba gwanar kallon talbijin bace. Don haka duk ta zama unease. Kamar daga sama taji motsin ana taba kofa.
Koda ta saurara sai taji kofar dakin Mu’azzam ake budewa, ko da bata fito ba ta san shine. Saidai tayi mamakin dawowarsa a daidai wannan lokacin. Abinda bata sani ba shine mantuwa yayi, wasu takardun ofis ya dawo ya dauka, bata yi gigin fitowa ba har ya dauki abinda zai dauka ya fice ya koma ofis.
Ajiyar zuciya tayi tana tambayar kanta shin wace irin rayuwa ce haka zasu yi da mutumin da ke amsa sunan mijinta a yanzu, amma bai dauketa matsayin mutum ba a cikin gidansa? Ta kwana ta tashi cikin gidansa amma ko gaisuwa babu tsakanin su? Su kwana su tashi gida daya ga daki ga daki amma bazai iya bincikar halin data tashi ciki ba? Ba haka tsohon mijinta ya sabar mata ba, ko yadda yake tashin ta daga barci daban ne, mutuwa mai tonon asiri! A yanzu ta tabbata tayi rashin da bazata taba mayarwa ba. Sha’anin Mu’azzam hali ne ke taka muhimmiyar rawa kafin rashin lafiya. He’s a total opposite of Aboulkhair. Iyaye daya suka haifesu amma personality dinsu daban-daban ne. Amma data tuno da nasihohin mahaifinta sai ta mika wuya ga duk abinda zata gani a tare da Mu’azzam tare da zubawa sarautar Allah ido.
Haka tafiyar tasu tayi ta mikawa har tsayin wata guda. Aalimah bata sanya Mu’azzam a idanunta saidai taji fitar motarsa da kuma dawowarsa. Ya bar komai na gidansa a hannun Harrison da Jacob. Har ta saba da Harrison baturen Mexico ne mai matukar kirki, as for Jacob ba mutum a idonsa sai Mu’azzam ba ruwansa da ita gaisheta kawai yake yi idan yazo sharar kitchen ya tadda ta, sau daya suka taba yin magana mai dan tsayi da shi ranar da ya kawo mata menu daga WALDORF ASTORIA bayan tafiyar su Mummy yace maigidansu yace ta dinga zaba yana karbowa yana kawo mata kullum sau uku a rana. Aalimah sai tayi murmushi tace masa ya koma yace da ubangidansa ita mace ce agidan mijinta. A al’adarsu ta Abzinawa mace ce ke dawainiyar abincin gidanta. Ya je ya gayawa Ubangidansa a dinga yi mata cefane kawai bata bukatar abincin WALDORF.
Koda sakon ya riski Mu’azzam kada kafada yayi irin na bashi da damuwa, yace a ransa kiyi abinda kike so. A fili kuma yace Harrison ya gaya mata ta rubuta duk abinda take so na cefanen ya je ya kawo mata.
Mafari kenan da Jacob ya ke yo mata cefane na duk abinda take bukata.
Ofis din su Mu’azzam ya turasu su biyar su wakilci (Chevron) halartar taron seminar ta kwana biyar domin bunkasa refineries din man petir na kasar Amurka a jihar Atlanta. Ya rasa yadda zai yi ya gaya mata zai yi tafiya. Ya amince bai kamata ya tafi batare da saninta ba. Wani bangaren na zuciyarsa na yawan gaya masa rayuwar da yake yi da ita cikin gidan bata kamata ba, ko babu aure ita din ‘yar uwarsa ce jininsa, diyar Kawunsa Mansur mai yawan kyautayi a gareshi. Amma ko lafiyarta baya bincika. Ga ta iyalin Dan uwansa da bashi da ya shi a duniya abin kaunarsa Aboulkhair wanda ko babu aure tsakaninsu hakkinsa ne ya kula da ita da rayuwarta.
A lokacin da take iyalin dan uwansa ita kullum cikin girmama shi take, hidimta masa take, mutumta shi take, ya kamata yayi maintaining wannan girman dake idanunta ya dinga kula da rayuwarta da iyayensu da kakanninsu suka dora a wuyansa. Idan Kawu Mansur ko Mallam Raazee suka ji cewa tunda ta zo sau daya yaga fuskarta bai san da wane kalami zai kare kansa ba. To al’amarin ne shima yafi karfinsa har yanzu ya kasa daina yi mata kallon matar Aboulkhair.
A yau dai ya karfafi zuciyarsa ta yarda da cewa kafin ya tafi zuwa Atlanta zai ganta ko na minti biyar ne, zai binciki halin data ke ciki da lafiyarta. Wannan auren nasu wanda bashi da focus ya san ba mai karewa bane. Idan akwai abinda yafi mutu ka raba takalmin kaza to sunansa kenan. Tunda kuwa diyar Kawu Mansour ce kalmar ‘saki’ bazata taba giftawa tsakaninsu ba ko babu kandagarkin mahaifinsa. Saidai shi kansa bai san yaya auren zai kasance a gaba ba, ya san dai wani nauyi ne maigirma aka dora masa wanda bashi da yadda zai yi da shi. Ko babu iyayensu a raye shine Ahaqqu daya riketa tunda kuwa iyalin Aboulkhair ce, kuma diya ga wanda ubansa ya sha nono ya saki nasa ya kama.
Abinda ya sani shine baya bukatar auren cikin rayuwarsa. Yana jin dadin rayuwarsa a haka, baya son duk wani motsi da zai kawo sauyi a cikin ta. Hausawa suka ce “Da muguwar rawa........ gwamma kin tashi. Kuma baya bukatar kowa a kusa dashi.
Mu’azzam ya ja gwauron numfashi, “su kuma sun kawo ta sun ajiye mai a gida, so suke ya daina shan magani ya kusanceta rayuwarsa ta canza.....A zo ana masa terere da bankada irin wanda Halima tayi masa. Shi tun daga kan Halima bai kara sha’awar aure ba! Da likitoci suka tabbatar masa zai iya rayuwarsa lafiya batare da sha’awar auratayya ba ta hanyar taking kwayoyin “anti-androgens” masu kashe tasirin ‘sex hormones’ a jikin dan adam yayi farin-ciki da hakan. Yana cin ribar rayuwarsa a hakan, aikinsa na tafiya yadda ya kamata har mantawa yake yana da disorder.
Rana daya ba tare da yin shawara da shi ba sun sake yi masa aure a karo na biyu, bayan ya roki Daddy kada ya kara yi masa aure ba da saninsa ba tun a wancan lokacin kafin ya yarda ya saki Halima, kuma kafin su yi, sai da suka duba suka hanga suka zabo wadda suka tabbatar bazai iya saki ba, bazai iya wulakantawa ba! Diyar Oncle Mansour.... kuma widow din Aboulkhair! Wadda ko babu aure shine dolenta! Amma hakika da ba ita bace saidai su Daddy suyi hakuri amma ko wacece sakin auren zai yi, da dai ya zauna da nauyinsa yana daukar alhaki irin haka.
Tsaki ya aje mai matukar tsayi, wani zubin iyaye babu yadda zakayi dasu, suna amfani da power din da Allah ya basu a kanka su takurawa rayuwar ka. Ko da Daddy yace yayi furnishing din daki da gidansa gabadaya bai taba kawowa ransa aure zai karba mai ba tunda ya san cewa Daddyn ya fi kowa sanin halin da yake ciki, da tun a lokacin yayi duk kokarin da zai iya wajen dakile afkuwar al’amarin tare da taka masa burki ta duk hanyar da zai iya. Sake-saken da Mu’azzam ya wuni yi kenan a tsayin ranar yau bakidayanta da ya yanke shawarar zai ga Aalimah.
Koda ya dawo gida a daren yau ya janyo trolley din da zai yi tafiyar da ita ya soma diban kayan amfaninsa yana zubawa. Motsin rufe kofar dakinta ya ji saidai bai sani ba cewa fitowa tayi ko komawa tayi. Daure zuciyarsa yayi ya bar abinda yake yi ya fito zuwa dakin nata.
Aalimah kasa ta sauka ta hado ‘tea’ mai kauri da ‘cup cakes’ din data yi da safe wanda ta mayar abincin darenta kasancewar bata cin abu mai nauyi da daddare, tana hawowa steps din benen da dan gudunta irin tafiyar Aboulkhair akan bene (hada steps biyu-biyu uku-uku). Tana sako kai dakin ta ji atmosphere na dakin ya canza mata da wannan daddadan kamshin na Mu’azzam wanda ta dade da gane na mamallakin gidan ne shi kadai. Tana karasa shigowa tayi arba dashi zaune a gefen gadonta. Ya mike kafafunsa tare da harde su. Turus! Ta ja ta tsaya a bakin kofar ita bata shigo ba ita bata koma ba. Sanye yake da pajamas ruwan toka masu dan kauri samfurin ‘balanciaga’. Duk dakin ta ya gauraye da sassanyan kamshin na mayataccen turaren Mu’azzam har ta samu kanta da dan lumshe ido wajen shaqar iskar dakin data canza bakidaya. Ya cure hannayensa biyu ya mikar dasu akan gwaiwarsa ya dora habarsa a kan su.
Idonsa na hanyar shigowarta dakin. Koda ta shigo sai ta ci burki a bakin kofa tana masa kallon da ya kasa fassarawa, shi ba na tsoro ba shi ba na maraba ba. A zuciyar ta tafi zaton batan kai yayi. Tunda kuwa yau kwananta sittin a gidansa ko inuwarsa bata taba gani cikin dakin nata ba. Sai dai ta hangoshi yana fitowa ko yana shiga mota daga tagar dakinta.
Mu’azzam haushi ta bashi da wannan birkin data ja ta tsaya daga bakin kofa. Kamar wadda ta ga aljani. Ya sauke hannayensa daga habarsa a dan harzuke yace,
“Are you ready to listen to me ko komawa zakiyi?”
Jiki a sanyaye ta saki murfin kofar ta cira kafa da kyar tana shigowa dakin kamar mai tausayin kasa har ta tadda stool din mudubi ta zauna, ta ajiye kofin hannunta kan mudubin yana ta tururi, kanta ta sunkuyar tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta sabida fahimta data yi idanuwan Mu’azzam bakidaya akan ta suke. Ko kallon me yake mata haka oho. Sai da ya ja fasali son ransa ya ce.
“I’m going to Atlanta tomorrow for a 5-day seminar. Sai nayi kwanaki biyar zan dawo, ina son sanin bukatunki da kuma bincikar lafiyarki?”
Shiru tayi masa tamkar da dutse yake magana. Wani irin haushinsa take ji a ranta. Yau ne da zai yi tafiya ya san tana cikin gidan? An kawota gidansa mai kama da kurkuku an garkameta tsayin watanni biyu maigidan bai taba nemanta ba. A yanzu kuma yazo yana gaya mata zai bar mata gidan ma bakidayansa. Duk abinda zai cinyeta ya cinyeta, ba sai yayi haka ne zata fahimci baya maraba da ita cikin rayuwarsa ba already ta dade da sani. Itama fin karfinta aka yi amma aurensa shine abu mafi tashin hankali a gareta, tana rokon Allah ya bata mafita a cikinsa da gaggawa, idan kuma a cikinsa zata mutu, to tana addu’ar neman dacewa.....
Mu’azzam bai yi aune ba sai gani yayi tana sharar hawaye, hawayen da bai san dalilin zubarsu ba, cikin kalamansa bai ji mai taba rai ba, kawai ce mata yayi zaiyi tafiya.
..... Sai yaji duk bai ji dadi ba, he hates to offend someone amma sau da dama yana batawa mutane batare da ya sani ba, ya gane hakan ne akan mahaifiyarsa.
Ya dauki wayarta daya gani a gefensa ya hau danne-danne, lambobin sa ya zuba mata tare da na Harrison, da lambobin katin banki, ya ajiye mata wayar tare da daya daga cikin atm cards dinsa ya ce “duk abinda kikeso ki kira Harrison ki aike shi, na kuma saka miki lambobin wayata, you are free to call me anytime, ni zan tafi, sai Allah ya dawo dani.
I’m sorry if i offend you, it’s not intended”.
Ya mike zai fita. Har ya bar dakin bata ce masa komai ba. Ya fita yana mamakinta.
Ashe ba shikadai ne bai son auren ba, itama bata so? Amma shi ai duk da rashin son auren ya danne komai yayiwa komai hujja da uzuri ya bita har dakin ta ya kula ta, ya sauke nauyinta dake kansa? Saidai da sauri zuciyarsa ta halarto da amsa; a irin soyayyar data yi da mijinta akan idonsa, mawuyaci ne ta karbi wani aure a bayansa koda kuwa na (Prime minister) ne balle auren maridi (mara lafiya) irinsa. (A tunaninsa fa).
Wanda yake da tabbacin Aboulkhair bazai kasa gaya mata matsalolinsa ba idan aka yi la’akari da irin shaquwar su. Murmushi yayi mai sauti, ko babu lalura ita ba irin matar da yake so bace, wadda zuciyarta baki daya ta riga ta mace akan wani ba shi ba. Ta kwantar da hankalinta shi ba bakon zafi bane he have a lot to do. Abinda take kin auren a kansa bazai faru ba insha Allahu.
******
Bayan tafiyar Mu’azzam Atlanta, duk da cewa sanda yake nan din ba wani haduwa suke yi ba sai ta ji gidan yayi mata mugun fadi. Akalla sanda yake nan ta san cewa ba ita kadai ce cikin gidan ba, ta kan ji motsinsa in ya shigo, da kuma in zai fita. Sannan kamshin turarensa na tabbatar da presence dinsa cikin gidan amma yanzu duk babu ko daya. Bata son yarda da abinda zuciyarta ke fadi na cewa “gara sanda yake nan, akan sanda baya nan”.
A kokarin ta na nemawa kanta abin debe kewa sai ta maida buge-bugen waya ga ‘yan uwa da iyaye abin yin ta. Rannan Basma ta gaji da wayar Aalimah take cewa “Aal, wai mijinki baya kusa ne? Ni fa kina damuna, da wayarki zan ji safe da dare ko da rainon ‘ya’yanki koda hidimar wannan Yayan naki marar daga kafa? Kin san shi gwauro nan da nan ake gane shi”.
Tana so ta gayawa Basma cewa ko yana nan ba haduwa suke ba, ba shiga sabgar juna suke ba. Kowa rayuwar sa yake yi cikin gidan. Wata zuciyar na hana ta kada Basma taji haushinta ko tayi mata kallon mara kirki. Ita akan karan-kanta ta san bata kyautawa a cikin zamansu, koda Mu’azzam baya kula ta baya shiga sha’aninta ya kamata ita ta biye masa su dinga zaman gaba kamar wasu kafurai? Ai shine gaba da ita, kuma halinsa ba bakonta bane, ita ya kamata ta kwantar da zuciyar ta su yi zama na muslunci koda babu soyayya tunda jinin junansu na yawo a jikinsu. Kuma a sanin halinsa data yi, hakan da yake yi ba komai bane shi a wajensa.
Ta tuno kalamansa ranar da zai tafi, da biyota har dakin ta da ya yi amma taki kula shi…yace da ita “….I’m sorry if I offend you, it’s not intended”. Wanda ke nufin bai san abinda yake yi wanda ya bata mata rai ba, da har ya kaita ga zub da hawaye a gabansa.
Gara ta ja bakinta tayi shiru. Don haka a fili tace da Basma “Mu’azzam yayi tafiya”. Basma tace ta roke shi ta koma aikinta na pharmacy zai fiye mata zaman kadaicin data ke yi. Sosai taji dadin wannan shawara ta ‘yar uwarta Basma.
Sun yi waya da Khaleesat a washegarin ranar take tsokanarta wai an bar musu gidansu su kadai yadda suke so, don Mummy ta gaya mata Dr. Nebrass ne ya kore ta. Aalimah tace.
“Kayya! Nima in za’a korenin ai haka yake so Khalisat. Ko sauro baya so ya gifta ta gabansa”. Dariya Khaleesat tayi tace “he’s very ANNOYING......ki yi manage dashi a haka. That was what we have been telling you......”.
A zuciyarta ta yarda yanzu, he’s annoying din kamar yadda kannen sa ke cewa, sabanin da data ke masa uzuri kala-kala. Ashe don bata shigo jikinsa sosai bane. A ganinta Aboulkhair kadai ke jin dadin Mu’azzam. Shi kadai ke ganin fuskarsa da walwalarsa, far’arsa da murmushinsa, haka zalika shi kadai zai iya sakewa da shi. Amma wani bangaren na zuciyarta yana gaya mata; bata yi yunkurin da zai bata matsayin da Aboulkhair ke da shi ba, ai ko Aboulkhair shi yake kula shi, shi yake fara yi masa magana ba, sai ya fadi goma bai amsa masa biyar ba.
Ya kamata ko yaya ne ta dinga sauke nauyin da addini ya dora akanta koda kuwa Mu’azzam bazai kula ta ba. Tayi koyi da al’adar zaman aure irin na iyaye da kakannin ta, inda mace ce ke dauke da duk wani nauyi na ci da sha, kulawa da walwalar maigida. Ba ruwan Ubangiji da kusancin dake tsakanin Mu’azzam da Aboulkhair, auren Mu’azzam da ke wuyanta shine abinda Ubangiji ya sani kuma zai yi hujjah da shi ranar gobe kiyama.
Duk da ta san abune mai matukar wuya ta iya yin rayuwar data yi da Aboulkhair da Mu’azzam amma akalla zata kwatanta sauke nauyin da ya hau kanta iyakar iyawarta. Sauran kuma zata fawwalawa Allah kamar yadda Daddy dinta ya ce.
******
Cikin dare ana tafka ruwan sama harda kankara Mu’azzam ya dawo, tana kwance tana tilawar Alqur’ani da dan karamin Alqur’aninta a hannu, ta lullube jikinta ruf da duvet sabida tsananin sanyi, taji shigowar mota harabar gidan cikin wannan ruwa mai tsananin karfi. Daidai lokacin data kai (Suratul Tahrim) ta karanta fatiha tayi sadaqallah ta shafa ta kuma rufe Alqur’anin ta maida shi mazauninsa. Mikewa ta yi sannu a hankali ta isa ga tagar dakinta wadda ke fuskantar harabar gidan. Tasa hannu ta yaye curtains din.
Mu’azzam ta gani ya fito daga mota, har ya dauko jakarsa kuma ya mayar sabida yadda ruwan ya kara karfi. Ya rufe booth din motor da hanzari. Da sassarfa yake takowa amma kafin ya shigo falon kasa ruwan ya gama yi masa duka. Ta tuna Aboulkhair ko yaya ruwan sama ya same shi sai yayi zazzabi.
Ta runtse idonta a hankali kewar Aboulkhair mai yawa ta ziyarceta, da shine ya dawo cikin ruwannan da yanzu ya janyeta cikin bargo yayi cuddling dinta yace sai sun raba sanyin nan da ya kwaso tare. Ba tayi aune ba taji hawaye masu dumi akan kundukukinta.
Meyasa mutuwa bata da adalci ne? Me yasa in ta tashi raba masoya bata la’akari da halin da abokin rayuwar zai fada a bayansa? Yaya zata yi da Mu’azzam? Ta ina zata bullowa wadannan baudaddun halayen nasa? Ta tabbata tayi rashin masoyi wanda har kasa ta nade bazata maida makwafinsa ba. Aboulkhair bai taba raba makwanci da ita ba, kullum nan-nan yake da ita, soyayya yake gwada mata kamar ya hadiye ta. Yau ga inda rayuwa a bayansa ta jefo ta.
Inda ba’a damu da wanzuwarta ba, ba’a damu da kowanne hali take ciki ba. Don duk da ya zuba lambobinsa a wayarta, ko sau daya bai kirata ba har zuwa yau da ya dawo. Bata da tabbacin ma ya dauki tata lambar. Haka ta koma gado ta nannade ta shaqi kukanta sosai ta godewa Allah.
******
Washegari ya kama litinin, amma har karfe tara na safe bata ji motsin fitar Mu’azzam ba kamar yadda saba, Monday sammako na musamman yake mata, amma yau ko motsin sa babu. Zuwa karfe tara da rabi taji ana danna musu kararrawa alamar akwai bako mai son shigowa a kofarsu, koda ta sauko ta bude wani farin mutum kamar balarabe mai tarin shekaru da cikar kamala ta gani tareda Harrison. Inda Harrison ke gaya mata tayi masa jagora zai shiga ya duba Mu’azzam, Dr. Nebrass ne ya turo shi sabida baya gari, Mu’azzam dinne ya kira shi a waya.
Likitan yace taje tayi masa iso zai shigo ya duba shi. Aalimah ta daburce, bata taba dosar dakin Mu’azzam ba koda kuskure, bata son yin abinda zai zama tayi masa ba daidai ba tunda bai taba yi mata umarnin shiga dakin nasa ba. Hankalinta ya tashi jin cewa bashi da lafiya shiyasa ashe ya kasa fitowa. Ashe jikinsa irin na Aboulkhair ne baya daukan dukan ruwan sama. Ta rasa abinda zata ce musu.
A karshe dole ta juya ta koma saman ta isa ga kofar dakin Mu’azzam kirjinta na harbawa. Ba karamin daurewa tayi ba ta soma dan kwankwasa masa tare da hadawa da sallama.
Muryarsa ko fita bata yi yace mata daga can kasan makoshinsa “let him in”. Komawa tayi ta fadawa likitan suka taho tare, bude masa kofar tayi ya shiga amma ita sai ta zame ta koma dakinta.
Tagumi tayi da hannu bibbiyu a gefen gado tana jin babu dadi. Likitan ya kwashi wajen mintuna ashirin tare da shi kafin ya fito. Kamar wacce aka tsikara haka ta tashi ta biyo bayansa. A falon kasa suka hadu, kallon fuskarta kawai yayi ya hango damuwa da tambayoyin da take son yi masa. Murmushi yayi mata yace “he will soon be alright da zarar ya sha magungunan da za’a kawo masa yanzu, cold ne ya kama shi da zazzabi, ta kula da shan magungunan sa kan lokaci kuma ta tabbatar room-heater na aiki ko yaushe cikin dakin.
Bai dade da fita ba Harrison ya kawo mata magungunan da bayanin shansu rubuce jikin kowanne yayi mata sallama ya fita. Aalimah ta rasa inda zata sanya kanta, ta dade rike da ledar magungunan a dakinta tana safah da marwa.
Shine mutum mafi girman daraja cikin idanunta bayan iyayenta kasancewarsa Yayan mijinta kuma babban Yaya a garesu su duka. Bata shiryawa ginuwar mu’amala ko yaya a tsakaninsu ba, har yanzu ita kanta ta rasa dalili duk da fadan da zuciyarta ke yi mata kullum. Gashi Dr. Na nufin ita zata yi jinyarsa ma bakidaya.
Tana cikin wannan halin Harrison ya sake danna mata kararrawa, zuwa tayi ta bude masa, sai ya mika mata karamin kwandon abincin dake hannunsa. Breakfast din da Mu’azzam yayi order ne daga Waldorf Astoria. Karba tayi jiki a sanyaye, tana mai jin kanta a sakarya, useless din mace a gidan miji.
Haka ta hada ledar magungunan da kwandon abincin ta doshi dakin Mu’azzam kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, bakinta dauke da sunan Allah cikin neman agajinsa, tana rokonsa ya bata karfin gwiwar fuskantar Mu’azzam ya yaye mata dabaibayin dake dabaibaye zuciyarta akansa; wani kwayan mutum guda daya data ke matukar jin nauyi a rayuwarta. Zuciyarta tafi bashi matsayin babban Yayan da ake matukar girmamawa, ta ki ta bashi matsayin miji ko yaya ne. Kwarai hankalinta ya tashi da rashin lafiyar data same shi a daren jiya don in har irin na Aboulkhair ne to haqiqa sai ya ji jiki. Yana dadewa bai yi ciwo ba, amma in ruwa ya bugeshi zai yi, kuma ba dan kadan ba.
Haka ta daure da taimakon addu’o’in bakinta ta sanya kai dakin Mu’azzam bakinta dauke da sallamar da bata jira ya amsa mata ba. Jikinta na shaking kadan-kadan na tsoro da rashin sabo.
Kwance ta same shi a makeken gadonsa ya dukunkune a cikin quilt. Ya ji shigowarta amma bai dago ya dubeta ba. Saidai cikin zuciyarsa ya amsa sallamarta. Ta tako har gaban gadon ta zauna a bedside ta barin damansa. Cikin kankanuwar muryar data dade tana saitawa ta soma magana.
Yaya Mu’azzam sannu da jiki, ga magungunan da abincinka an kawo. Amma Dr. Ya ce sai ka fara cin abincin sannan zaka sha maganin”. Ta soma fiddo komai daga maganin har abincin. An jera abincin cikin tsari a wani kyakkyawan kwando (food basket). Hatta ruwan shayin da zai sha yana ciki cikin karamin tea flask. Ba wani abu ne abincin ba chips ne da soyayyen kwai, sai wata hanta da aka yiwa wata irin dahuwa cikin albasa da koren tattasai. Mu’azzam yunwa yake ji sosai don rabonsa da abinci tun a Atlanta. Kokari yayi ya tashi zaune ya zuro kafafunsa kasan gadon ya zauna sosai idanunsa a runtse fuskarsa kuma ya sanyata cikin tafukansa.
Yana sanye da rigar sanyi mai kauri wadda keda dogon wuya ‘dark brown’, wandon jikinsa bai karasa idon sawunsa ba kuma ya dan kama jikinsa sosai. Kallo daya tayi masa ta sunkuyar da kanta tana juye masa abincin akan faranti sakamakon kwarjinin da yayi mata, wani irin kyau taga ya yi mata saida gabanta ya doka zuciyarta ta hau rawa.
Ta zuba tea ta hau firfitawa da daya kofin yaji coffee yayi kauri yadda Mu’azzam ke so. Kallonta yayi yace “barshi haka, da zafi nake so”. Mika masa tayi ya soma sha kamar baya so. Ta wani karkace kai tace “kaci abincin ko kadan ne don ka sha magani”. Yana so ya harareta amma idanunsa ko buduwa basa yi don azabar zazzabi.
Saida ya shanye ruwan shayin sannan ya yarda yaci hantar da dankalin kadan ya tura mata ragowar ya sanya hannayensa biyu ya dafe kansa dake bala’in sara masa.
Ballo magungunan tayi bayan ta karanta prescription din kowanne, mika masa tayi tareda gorar ruwa mara sanyi. Yi yayi kamar bazai karba ba sabida azabar ciwon da kansa ke masa, ita kuma bata dameshi da nacin magana ba har saida aka kwashi wajen mintuna biyar sannan ya mika mata hannu ta zuba masa kwayoyin maganin a tafin hannunsa tare da sake mika masa ruwan. Data tabbatar ya shanye sai ta hau kintsa wajen ta adana ledar magungunan akan bedside ta mike da zummar barin dakin.
Ta dora hannunta akan marikin kofar kenan ta tsinkayi muryarsa can saman kanta yana fadin “thank you”. Murmushi tayi ba tareda ta juyo ba ta fita ta rufo masa kofar silently.
Haka ta maida hankali wajen ganin cewa yana shan magani akan lokaci kuma dakin na kasancewa cikin dumi kodayaushe kamar yadda likita ya umarceta.
Kwana uku ya kwashe yana jinya, jinyar da ta kwashe tsoro da fargabar da take fama dashi idan ta tunkareshi, a yanzu tana iya zama gabansa batare da ta ji ko darr ba. Duk da ba magana ce mai yawa take gudana a tsakaninsu ba. Har yanzu kuma bai bar yo odar abinda zai ci daga Waldorf ba. Abinda ke matukar ci mata rai ta kuma rasa yadda zatayi ta gaya masa ya daina zata dauki nauyin abincinsa. Kwarjini yake mata sosai, gani take in ta fadi hakan kamar tana neman kusanci da shi ne.
Ranar ta kasance Asabar ya samu lafiya sosai ba zai je office ba har sai Monday sun bashi leave na sati guda, haka kawai zuciyarsa ta ce da shi yau ya gwada zaman gida, kada yaje ko’ina tunda dama in ya fitan bashi da wani takamaiman wajen zuwa, yawo kawai yake yi a titi saboda kada ya zauna tare da ita, bari yau ya zauna a gida, ita kuma ya ga irin kalar tata hayaniyar.
A kwanakin nan biyar da ya kwanta masassara da zazzabi, ta kuma kasance koyaushe tare da shi sai yaji bata gundureshi ba kamar yadda yake tsammani a baya, tana da nutsuwa sosai ga taka-tsan-tsan akan duk motsin da zata yi a gabansa.
Yana nan kwance cikin sofa dake falon kasa Aalimah ta sauko cikin kyakkyawar shiga ta shaddar matan Agadez ruwan hoda mai turuwa (dark pink) ta sha aiki da zaren silver daga sama har kasa sai zuba kamshi take yi na turarenta Nude (By Rihanna), kai tsaye ta fada kicin. Tasa a ranta daga yau zata raba Mu’azzam da cin abincin restaurant ko yana so ko baya so.
Shawarwarin Gumsu ta dauko daya bayan daya tana son practicing dinsu yanzu. Ta yarda zaman da suke yi sam bashi da ma’ana kuma 80% laifin ta ne. Zama da Mu’azzam iyayensu basu kulla shi don watarana su kwance ba, to ina amfanin kuntatawa kai da cutar da juna? Bai san abin da ta ke yi ba cikin kitchen din tun shigarta, amma zai yi rantsuwa da Allah har barci ya yi ya farka she does not make sound.
A nata bangaren tana kokarin yin komai ne a hankali, musamman da ta ganshi kwance a falon. Wani abu da bai taba yi ba tun zuwanta. Da ya farka yunwa ce ta tashe shi misalin karfe daya da rabi na rana agogonsu na can, lokacin yin lunch dinsa kenan, ya dauko waya da nufin yin order ya ganta ta taho daga madafi rike da tray kuma gurinshi ta nufo kanta tsaye. Ta jawo side-table ta dora tray din a gabansa. Uffan ba ta ce ba ta koma kitchen din ta dauki nata ta yi sama.
A hankali ya yunkura ya tashi zaune, ya bude kananun warmers din data aje. Wani lafiyayyen kamshin farfesun kayan ciki da suka sha kayan hadi ya doki hancinsa. A daya warmer din fried macaroni tayi masa wadda taji kayan lambu suka fito shar a cikinta, ya bude foil paper data nannade saman wani faranti in da ya tadda gasashshen katon kifi daya ji kayan kashe karni da spices, ya sha adon kayan lambu yankakku a samansa. Mu’azzam ji ya yi yunwar da yake ji ta nunku, ya sa fork ya soma cin kifin bayan ya zuba lemon tatacciyar abarba a tambulan mai garai-garai. Order din da bai yi ba kenan.
******
Tun daga wannan ranar Aalimah ta kwace ragamar cikin Mu’azzam daga WALDORF ASTORIA. Ya yarda babu wanda ya kai matan abzinawa iya sarrafa girki. Ko bai bude baki ya fada ba cikin ransa yana maraba da wannan sauyin kuma yana jinjina mata a wannan fannin. Ba tun yau ya san ita kwararriya ce a girki ba, ya san wannan tun sanda Aboulkhair ke raye. Amma kasaitarsa da miskilancinsa sun hana ya nuna appreciation din, sai dai ya bude ciki ya zage yayi ta cinyewa ko kalmar sannu bata samu. Amma fa ya kara bude bakin aljihu sosai ga cefanen gidansa, har abinda bata ce tana so ba indai ya shafi girki sai ya sa Harrison ya kawo mata.
A wani yammacin Lahadi ya fita harabar gidansa don shan iska kamar yadda ya saba a kowanne karshen mako, tun daga sanda ya yarda ita ba ta da hayaniya sosai ya sake a gidansa, ya daina yawon kan titi, ko kofar gidansa yau bai leka ba. Haka nan ba ta saukowa idan ba girki za ta yi ba. Yana kwance cikin sofa dinkin (kaba) da jaridar ‘Los Angeles Times’ a hannunsa yana karanta labarai ya hango fitowarta cikin takun nutsuwa. Ta sha adonta kamar yadda ta saba cikin shigar matan abzinawa. Aalimah, na jin dadin yin shigar matan Niger da Mali fiye da kowacce shiga. Tana alfahari da kabilar data fito. Ya lura da irin tafiyar ta kenan (cat-walk) kamar mai taku a fashion parade, gata doguwa sambaleliya masha Allah son kowa....., kin wanda bai samu ba. Jikin Inna Kasisi ta debo bakidayanta, ga tsayi ga zati, ga kyawun sura ga kyawun zuciya, ya samu kansa da kasa dauke ido daga gareta, kai tsaye inda yake kwance ta nufo, ta russuna ta ajiye abin dake hannunta.
Ba kuma tare da ta ce masa komai ba ta juya akan takun ta ta koma inda ta fito, don ba ta sani ba ko gaisuwa ma zai ce takura ce a gare shi, shi ya sa ba ta fiya wani gaishe shi ba sai ta kama. Ta zame masa kamar wata kurma a cikin gidan, in ka ji tashin sautinta to waya take yi daga cikin dakinta.
Mu’azzam ya yunkura ya dauki abin da ta ajiye, don tsakani da Allah yunwar yake ji, awanni hudu tsakaninsa da abinci, tun lokacin da ta ba shi na rana. Dambun naman kaza ne da snacks (samosa, spring rolls da Meat pie) ta ajiye masa cikin wani faffadan faranti data rufe da foil paper. Ya jefar da jaridar ya zauna ya soma ci, ga sassanyan lemon zobo wanda ya ji danyar citta ta ajiye a gefe cikin jug.
Hidimar da Aalimah ke ta yi da cikin mijinta Mu’azzam kenan, ta hana shi yin order din abinci kamar yadda ya saba. Ga mamakin Mu’azzam ya fi gamsuwa da natan a kan na Waldorf Astoria da ya kwashe shekaru yana zabga kudi yana ci. Ga satisfaction ga rashin kashe kudi. Duk da ko kalmar ‘Nagode’, ba kullum take giftawa tsakaninsu ba sai ranar da ya bushi iska, in ya ce ba ya godewar shi kansa ya san ya yi babbar karya.
Idan ya je ofis kullum Allah-Allah yake ya dawo gida don kawai ya ci girkin Aalimah. Kamar wani maganadisu ne a cikin hannun nata data ke sarrafa abincin da shi. Har wata ‘yar kiba ya aje a kwanakin nan ya murje yayi fresh da shi.
Za ki yi mamaki in na ce miki kalmar ‘sannu da gida’, ko ‘ya office’ ba ta giftawa tsakaninsu. Saidai a hada ido kowa ya dauke kai cikin basarwa. Sosai ta ke kiyaye wannan hayaniyar da ta san ba ya so, har fiye da kima, ta yadda har ta ke tunanin gaishe shi ma zai ce hayaniya ce don a zauna lafiya.
Bayan haka akwai wannnan girma na musamman da tuntuni Mu’azzam ke da shi a cikin idanunta, tana kiyaye wannan girman har gobe, musamman in ta tuna yadda Aboulkhair ke respecting dinsa da karrama duk wani al’amarinsa. A yanzu ma komai ta ke yi tana danganta shi da albarkacin Aboulkhair da kulawar da Mu’azzam din ya bata a matsayinta na matar kaninsa a lokacin da ta ke auren Aboulkhair, ita ba butulu ba ce, ba ta manta alkhairi komai kankantarsa, balle kuma ALHERI irin na Mu’azzam abin kwatance ne. Shi yasa wadannan halayen nasa masu ban haushi basu cika damunta ba. Ta yarda he’s annoying din da gaske ta bakin su Basma, sai ka zauna da shi zama na sosai zaka gane hakan ba zaman bakunta ba.
Zaman haka ba ta komai sai girki ya soma damunta. Ba ta saba da zaman waje daya ba, zaman kashe zani, idan ba ta yi karya ba sai ta ce kiba ta ke yi sannu a hankali. Kamar yadda ta lura shima Mu’azzam kiba yake yi. Amma shi tasa ta san bata zaman waje daya bace ta kwanciyar hankali ce da samun abinci mai gina jiki akan-kari. Don haka ta soma tunanin abin yi, kamar yadda Basma ta shawarce ta, wanda ba za ta samu ba in ba da taimakon Mu’azzam ba.
Aalimah ta mike ta isa ga bakin tagar dakinta tana hango dogayen gine-ginen birnin Las Vegas, da kayatattun tituna da motoci da ke gudu a kansu. Ta tuna lokutta na farko da ta ke jin sunan birnin; a bakin su Basma ne and her fellow Boston students.. Ta tuno wata hatsaniyarsu da Mummy a da can, abin da ta ce da Basma a wancan lokacin....., “I’m not here to bring ‘anarchy’ between your parents.......”. Da nata tunanin da ya dade yana yawo a kanta; “....There is something STRANGE associated with her life and this city…”. Ashe Allah ya riga ya rubuta “aure ne”. Za ta auri MU’AZZAM ne komai daren dadewa, ta zauna tare da shi a wannan gari da sunansa ya zauna mata a zuciya.
Ta kai tunaninta ga mijinta a yanzu...Engnr. Mu’azzam Ishaq Raazee da yanayin rayuwarshi, in ta ce ba ta takura hakika ta yi karya. Tun halayen nasa basa damunta har sun fara kaita bango. Rayuwar Mu’azzam shi kadai yake jin dadin abarsa, ta wace hanya za ta bi ta nuna masa akwai rayuwa mai focus, inganci, dadi da ma’ana bayan wannan ta kadaicin da yake yi din???
Ta baro jikin tagar da sauri a lokacin da ta hango shi kwance cikin garden dinsa, wandon da ke jikinsa bai karasa idon sawunsa ba, rigar jikinsa short sleeved ‘yar gidan marks&spencer ta dan kama jikinsa ta fiddo zahirin kirar jikinsa ta ingarman matashi. Lemo ne a hannunsa pepsi na gongoni yana sha da magazine (Las Vegas Times) a hannunsa. Ba wani abu ne ya sa ta yi saurin barin tagar ba, sai don cewa ji tayi ba za ta iya jurar ci gaba da kallonsa cikin wannan yanayin data samu kanta a ciki ba. Wani abu cikin gangar jikinta ke circulating, yana tuna mata rabonta da samun wani muhimmin abu da ya manta da shi a can baya.
Kai tsaye shower ta je ta sakarwa kanta. Ta fi rabin awa a haka don nema wa kanta sauki har ta samu ya lafa, ta sanya kayan wanka ta fito daidai lokacin da ta ji an murda kofar dakinta, wanda ta guda din ne ya biyo ta har inda ta ke.
Tsayawa yayi daga bakin kofa yana kallonta cikin kayan wankan ruwa na yarari a jikinta. Dogon bakin gashin kanta ya jike sharkaf ya manne a wuya da gadon bayan ta. Wani ya zubo ta gaban fuskarta sai disar ruwa yake. “She’s very beautiful, very beautiful”. Abinda Mu’azzam ya ayyana a ransa kenan. Ko a cikin kyawawa ya dade bai ga mai kyawun surarta ba. Babban abinda ke burgeshi da ita; rashin hayaniyarta da sanyin ranta. Inama yana da lafiyar da zai iya nagartacciyar rayuwar aure da ita! Inama yana da gurbin da zai sanyata a zuciyarsa!! Inama yana da feeling din da zai iya rabawa tare da ita!!! Da sauri ya kawar da wannan tunanin mara ma’ana a ganinsa, ya gaya mata abinda ya kawo shi.
“Tea nake so in ban takura ki ba, please”.
Bakinta da jikinta na rawa ta ce,
“Ka je za’a kawo”.
Har ya juya din sai kuma ya dawo. Sake tsayawa ya yi yana nazarinta, yana son sanin abin da ya birkitata haka. Bai fahimci komai ba, don bakidaya ma sai ta koma toilet din ta rufe kanta. Dariya ta bashi sosai, ta baya ta rago kenan, bayan ya riga ya gama kare mata kallon, ya koma ya rufo mata dakin.
Bayan shower da ta sake sakar wa kanta har da durkushewa a kan gwiwoyinta. Al’amarin na ci gaba da kamari a tare da ita. Ta tuno mijinta Aboulkhairi, ta tuno soyayyar da ya wanzar da rayuwarshi nuna mata, yau ga halin da rayuwa a rashinsa ta jefa ta.
A daddafe ta fito, ta nemi doguwar riga ta sanya. Kasa ta sauka ta dafa masa ruwan shayin da ya bukata, sannan ta bi shi da shi dakinsa don ba ta ganshi a falon ba, ta duba harabar gidan ma in da ta hange shi dazu ba ya nan, sai jaridunsa da magazines da gwangwanin lemun pepsi da ya sha.
Sallama ta yi a kofar dakin barcinsa, ya dan jima kafin ya zo ya bude, shima da alama wanka ya fito, sabida kayan wanka ne a jikinsa, yana kuma tazar jikakkiyar sumar kanshi ta abzinawan usli, koda yake tashin farko shi bazaka kirashi Ba-abzine ba, don kalar fatar mamanshi ta rinjayi ta Daddy sosai a jikinshi, sai ya zamana kallo daya zaka yi masa ka kira shi half-caste, kamshin ‘bath-robb’ din shi na desire-dunhill ya bakunci hancinta, ya karbi shayin ya ce,
“Na gode”.
Rana ta biyar kenan da kalmar godiya ta gifta a tsakaninsu.
Har zai rufe kofar ya ga ba ta da niyyar barin wajen. Alamu sun nuna kammar tana son yin magana da shi ne.
Hanya ya ba ta ta wuce ciki, ta samu inda ya dace ta zauna, wato gefen drawer din jikin gadonsa, rufe kofar ya yi ya nufi gefen gadonsa shi ma ya zauna. Zuba shayin ya yi a tambulan ya soma shan abinsa ba tare da ya saisaita zafinsa ba, kamar ya manta da cewa akwai mutum a dakin.
Hawaye suka zubo daga idanun Aalimah, ba haka tsohon mijinta ya sabar mata ba; she is treated like a queen’, ko me yake yi in ta zo da magana zai bari, ya bata dukkan hankalinsa, yau ga ta a gaban wanda da ita da babu duk daya.
Ta daure ta cije ta hadiye bakin cikinta ta ce,
“Yaya Mu’azzam aiki nake so ka samar min, ko masters in dora karatuna, zaman haka bana komai yana damuna”.
Ya ci gaba da shan tea dinsa, kamar bai ji ba, kamar bai fahimce ta ba, sai da ta sake maimaitawa, a takaice ya jumlace maganar ya ce.
“Ba yanzu ba”.
“Saboda me?”
Aalimah ta tambaya cikin hadiye bacin rai.
(Amsar da ya bata bata yi tsammanin jin ta daga gareshi ba).
“Saboda auren namu bai gama ginuwa ba tukunna”.
“Kamar ya ya?”
Ta tambaya cikin mamaki.
Ya ajiye kofin hannunsa a kan karamin farantin silver da ta kawo shi. Ya ce yana duban tsakiyar idanunta.
“Do you really want to know? I’m afraid of letting you out (ina tsoron barinki fita waje) sai ranar da ki ka shirya zama cikakakkiyar matar aure”.
Da dumbin mamaki Aalimah ta ke kallonsa. Wanda ka ke so ai shi ka ke kishi! Aboulkhair ya gaya mata Mu’azzam ba zai iya gina komai a zuciyarsa ba (he cannot develop emotion). Wannan na nufin…. shi ya karbi auren kenan? Ya mika wuya ga kaddarar da ta same su?? Har yana ma auren kyakkyawan fatan ginuwa a can gaba???
Shayinsa ya ci gaba da sha cikin nutsuwa kamar ba daga bakinsa maganganun suka fito ba, ya barta a zaune gefe kamar mutum-mutuma tana ta karanta wasikar jaki. Shi da aka ce bai da emotion ya akai ya gina kishin iyali a zuciyarsa? Da za ta iya, cewa za ta yi da shi; ita a yanzu ma ta shirya, ta dade da shirya karbar aurensu da hannu bibbiyu, tun daga lokacin da ta fahimci iyayensu basu kulla shi don wata rana su kwance ba. Su kadai suke wahalar da kansu, gashi har ta fara shiga wani hali wanda daga ita sai ubangijinta suka sani. Kawai tsoron abin da zai je ya zo ta ke yi a yadda Aboulkhair ya bata labarin situation din Mu’azzam na farko da Halima.
Tana da yakinin in ita ce za ta rufa sirrin aurenta, ta rungumi Mu’azzam cikin kowanne yanayin lafiya yake ciki, ko da hakan shi ne hanyar tafiyar ta lahira, ba kamar Halima ba.
Ta fahinci a cikin abubuwan da suka taka rawa wajen hana Mu’azzam aure a baya, har da bakin cikin tereren da Halima tayi masa.
To ba za ta iya ba, don haka salin’alin sawunta a likkafa ta fice ta rufo masa dakin.