Book 2 (Karshe)
by @takori
Dawowar shi kenan daga sallar jumaa ya shigo falon Farida babu kowa, Sabuwa ta koma gidan Hajiya tun bayan tafiyar Sakinah.
Ya duba dining babu wani abincin kirki da aka ajiye, sai wata dankararriyar taliyar Indomie fara sol. Ya yi tsaki ya rufe, matsalar Farida ke nan, shegiyar kiwa da lalaci.
Ba ya jin wannan farar taliyar za ta iya quenching wannan gigitacciyar yunwa da yake ji. Don tun safe haka ya fita ya barta tana barci ko karin kumallo ba ta ba shi ba.
Sannan Hajiya ta ce kada ya sake ya kara zuwa wajenta neman abinci, ta kuma gargaxi masu aikinta kada wanda ya ba shi, ya je ya soya Faridar ya cinye, amma babu ruwanta.
Ya shiga kicin ya bude firij babu komi ciki, sai xoyin ruvavven nama, ga tulin wanke-wanke ba a yi ba.
A store din da ke cikin kicin din kayan miya ne fal da potatoes duk sun ruve, sai wari suke. Cike da bakin ciki ya nufo dakin Farida don ya sauke mata balain da ke cin zuciyarshi, ya dora hannu akan marikin kofar dakinta ke nan ya jiyo dariyarta, da alama ba ita kadai ba ce.
Ta ce, Duk magungunan da na karba na yi amfani dasu yadda ya dace, zancen nan da nake miki Mama, yanzu ba ta gidan nan, shi kansa bai san inda take ba. Kuma ya tabbatar min ta tafi ke nan, don ta bi mahaifiyarta kasar su.
Aikin na Bakin-Kogi ya fi na dan Tsuburau, don na ga yakini, tunda na hada na gashin gaba, gashin hammata da gashin kaina da aladata na qona na zuba mishi a juicy shi ke nan bai kara tunata ba tsayin watannin nan, sai da uwar ta bude mishi wuta.
Duk da haka ya ce sai dai in tare zamu je, amma in ba haka ba to ba zai zo ba. Ni kuma gudun bacin ran iyayen ya sa na ce da shi ya yi hakuri mu zo don na lura ba tun yau ba Hajiyar ba ta sona, Balarabiyar take so.
Sannan na hana shi haihuwa da ita kuma ya amince, har ya kaita an sa mata abin hana daukar ciki da yake yarinya ce ba ta san komai ba. Ni yanzu hankalina kwance yake ya tsumma a randa, don haka na fasa fitowa in komawa Alh. Garba, don ba zai shayar dani soyayyar da Abdulhakim ke shayar dani ba. Saidai ya bani kudi.
In kuma don naira ne ga inda nairar ta zauna da gindinta nan. Ada kam ban san yaya aljihun Abdulhakim yake ba, shi ya sa naki aurensa na yarda da auren Alh. Garba......
Ji ya yi numfashinsa na shixewa, ya juya baya ya jingina da kofar don ta dauki nauyin gangar jikinshi.
Uwar ta ce, Kina nufin bai san kin taba aure ba? Kada fa watarana ya binciko liki ya valle?
Ta ce, Ni mahaukaciyar ina ce zan gaya mishi na taba auren? Ai duniyar nan Mama yanzu kawai ZUCIYAR MUTUM..........BIRNIN SA, wallahi da ya ji da ba zai aure ni ba yadda yake da masifaffen kishin nan.
Dinki na je aka yi min kuma bai gane ba, don har yau bai taba tada zancen ba. Yanzu abin da ya rage min shi ne, ina jiran aikin da na bakin kogi yake hadamin wanda zai bita da takardarta har dakin uwarta..........
Sai ya bude kofar, hawaye na tsiyaya daga idanunsa ya ce, Kafin in bita da takardar har dakin uwarta.......ke ga taki a gaban taki uwar. Ki je ki komawa mai kudi tsohon mijinki, amma ni bani da kudin da kike zato.
Ni maaikaci ni wanda zai iya ciyar da Sakinah kadai, ki je na sake ki saki uku! Ko a yanzu haila kike, babu jinina a tare da ke.
Cutar da kika yi min kika kika rabani da mai kaunata kika hadani da iyayena ki je na yafe miki.
Ya juya ya fita ya barsu tsuru-tsuru an rasa mai karfin gwiwar yin wani motsin kirki a tsakaninsu.
Ya dawo da takarda cikin ambulan ya dora mata a kan cinya ya juya ya fita yana cewa.
Ina da bukatar muhallina, don haka na baki kwana daya ko allurarki kada in gani a gidana. Idan hakan ta faru to za ki kwashe su a waje. Na gaya miki na kara gaya miki, kwana daya rak na baki ki bani muhallina.
Ya fita yana hawaye ya nufi gidan Hajiya. Yadda ya shigo ma Hajiya Laila sai da gabanta ya fadi.
Ya zauna cikin kujera idanuwanshi jazur, jijiyoyin kansa sun fito raxo-raxo, ya dafe kanshi da hannuwa bibbiyu hawayenshi na zuba.
Ta ce, Kai lafiya? Ko wani ya mutu?
Ya girgiza kai, ya ce, Ki yafeni Hajiya......tabbas duk wanda ya ki bin mahaifiyarshi yana tare da nadama......
Ya kwashe duk abin da kunnuwanshi suka jiye mishi tsakanin Farida da mahaifiyarta ya fada mata. Da kuma matakin da ya dauka. Ta ce, Kash!
Ka yi mummunan saki wanda Allah ba ya so. Sannan saurin saki ba xabia ce mai kyau ba.
Ni din nan ba abin da ban yiwa mahaifinka ba,don kada ya kara aure, don haka don anyi maka ba zai zamo abin mamaki ba, tunda an ce duk abin da ka yi, sai an yi maka, ko a yiwa naka.
Amma yanzu na gane kuskurena, na tuba ga Allah na nemi afuwar mahaifinka, kuma ya yi afuwa a gareni.
Sannan don ta taba yin aure ai ba wani abu bane, tunda ba cikin shege ta yi ba. Sannan akasarin mata da suke bin wannan hanyar don soyayyar da suke yiwa mazajensu ne ta yadda har basa son wata ta rabe su......
Ya girgiza kai ya ce, Duk soyayyar da aka ginata bisa karya da yaudara Hajiya ba soyayyar gaskiya ba ce, don wanda ke son wani da sharri, shi da alheri, to zuciyarshi ba mai kyau ba ce.
Farida ta sire min Hajiya, don ba sona take ba, kanta kawai take so da amfanin kanta. Ba zan kuma amince mata ba, domin a da na yarda da ita, nayi mata shaidar alheri, amma ashe ZUCIYAR MUTUM .BIRNIN SA! Ba zan kuma iya ci gaba da zama da ita ba.
Ina da kishi Hajiya, ba zan iya sake hada jiki da sauran wani ba. Ta je ta koma gidan mijinta, dama tausayinta ne ya ribace ni da tunanin soyayyar da take yi min ce ta hanata yin aure. Don haka tunda ita mayaudariya ce, to ta je ta ci gaba da yaudarar wasu ba ni ba”.
Hajiya ta girgiza kai ta ce, Allah shi kyauta.
Ya ci gaba da zama bai tashi ba, yana so Hajiya ta yi mishi zancen Sakinah, amma ba ta yi ba. Ya kara sunkuyar da kai ya ce, Don Allah Hajiya ki taimake ni ku dawo min da Sakinah........Daddy da Abban Sakinah sun ki saurarata.
Wallahi Hajiya bani da wani nufi a kan Sakinah sai na soyayya, amana da alheri........illa na samu kaina cikin gudun bacin ran Farida da tsoronta. Hajiya a yanzu Allah ya yaye min, ji nake kamar an sauke min wasu kaya masu nauyi daga kaina.
Hararar shi Hajiya ta yi, kafin ta yi murmushi ta ce, Sanda kuke kulla mata mugun nufi kai da matar da kake son ka tuna dani? Sai yanzu da ta kwave maka za ka san dani? To babu ruwana, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Cewa nake ka san inda take, sai ka je can ka nemo ta.
Kamar ya yi kuka ya ce, Don Allah don Annabi Hajiya ki yi hakuri, kuskure ne babu wanda ya wuce shi. Na kuma amsa cewa na yi kuskuren, na tuba na bi Allah na biki...........don Allah Hajiyata.
Abinki da UWA, nan da nan zuciyarta ta soma sanyi, ganin Abdulhakim yau yana yi mata kuka da girmanshi da komai, abin da ba ta taba gani ba a girmansa.
Sannan Abdulhakim din shi kadai Allah ya bata duk fadin duniyar nan, kaunar da ta ke mishi ba kadan ba ce. Sai dai ya vata mata rai ba kadan ba, tunda ya vatawa Sakinarta.
Ya sauka daga kujerar ya kama kafafunta yana kuka sosai. Ba ta san sanda ta kai hannunta tana share mai hawaye ba.
Ta ce, Ya isa haka Abdulhakim, Sakinah da Abbanta basa nan suna kasar Libya wajen mahaifiyarta. Ban san kuma ranar da za su dawo ba, ka je ka nemi afuwar Daddy in ya ga dama sai ya baka adires ka same su a can ko ya rakaka tunda ya san inda suke.
Ranshi ya yi sanyi, tunda a qalla Hajiya ta yafe mishi. Sai dai yana tsoron karon shi da Daddy.
Kwanan shi uku yana bin Daddy da magiya da ban hakuri kamin ya samu Daddyn ya sauko, amma ya yi masa fada sosai, ya kuma hada da nasiha.
Sannan shi ma bai ji dadin sakin rashin tausayi da ya yiwa Farida ba. Duk Abdulhakim ya karba ya kuma ba da hakuri, sannan ne Daddyn ya ce ya soma yi musu shirin tafiya kasar Libya.
****
Kwananmu bakwai a Libya, Abbana da Sakinah kullum suna tare, tsumin tsohuwar soyayya na tashi. Daga karshe suka sasanta kansu, na cewa sun yarda za su kara zama karkashin inuwar aure a karo na biyu.
Sai dai ta ce ba za ta kuma zama da Lami ba, ya amince kuma zai ware mata gidanta daban, ya kuma dauki alqawarin rikle mata yayanta Tananni da Musab su zauna tare da ita.
Ya yi waya da Kawu Tasiu ya sa shi ya yi musu shirin tahowa kasar Libya shi da Baffa Sule zai aiko musu da tikiti.
Ranar litinin suka iso Libya, washegari aka mai da auren Abbana da mahaifiyata a masallacin da ke maqwabtaka dasu.
A ranar ne kuma Abdulhakim da Daddyn shi suka iso Tripoli, suka samu walimar daurin auren. Karramawa ta musamman Gaddafi ya yiwa su Daddy jin cewa surukinshi ne.
Abba da Daddy suka zaunar da shi suna ta nasiha, wani zubin su hada da fada. Duk Mijin-Sakinah ya amsa cewa ya yi laifi.
Sakinah kawai yake so in dai za su ba shi a karo na biyu, to zai jure duk wani punishment da za su ba shi.
Waya ta samu Abba cewa Mami babu lafiya ta samu ciwon iska, yanzu haka tana Psychiatrist na National Hospital. Nan aka soma shirin tahowa.
Ranar jumaa muka sauka a filin jirgin saman Abuja, kai tsaye asibitin muka wuce. Abun babu kyawun gani, Mami sai addua domin hauka tuburan take tana tonawa kanta asiri tana cizgar gashin kanta, na gabanta dana hammatarta, na duk irin abubuwan da ta yiwa matan da Daddy yake aure yana saki, da abubuwan da ta yiwa Sakinah.
Sakinah ta kama hannunta ta ce, Na yafe miki Lami duniya da lahira na yafe miki. Amma ba ta fasa surutanta ba. Sai likitocin sun zurmuqa mata allura sannan ake samu ta yi barci.
Hajiya Laila ita ma ta dinga kuka tana cewa, Da ban tuba ba nima da na san makomata ke nan, Alhaji ka yafe mini, duk tare muke yin komai, ko mata dari kake so ka aura wallahi na amince maka.
Dariya ta kama Daddy, ya ce, Aa, ki bar casain da shidan na bar miki, guda ukun dai zan kara tambaxaxxu masu ja da abin da ya halarta.
Kwanan Mami goma sha hudu sannan ta samu sauki, suka sallame ta da magungunan da za ta dinga sha. Gaba daya Mami ta yi sanyi, tana ji kuma tana ganin Sakinah da M.T Liman matsayin mata da miji a karo na biyu. Ta yi ladaf ta zama kamar idan ka sanya mata yatsa a baka ba za ta ciza ba.
Gidan da Abba ya sayawa Mamana yana nan a Kubuwa, kwanan su Uncle Gadaffi uku a Abuja suka koma Libya.
Babu abin da babu a gidan na jin dadin rayuwa. Duk yadda Abdulhakim ya yi don ya ganni a wannan dan tsukin bai samu ba, Mamana ta boye ni, tana ta gyareni, gyara irin na Larabawan asali.
Jikina ya yi kyau, zuciyata sarai. Da kanta ta kaini asibiti aka cire min loops din. Sati hudu ke nan rabona da Mijin-Sakinah, ni kaina na san na yi kewarsa, yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Na yi kewar soyayya da kyautayinsa, na kuma tabbata ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba.
Kwance nake a cinyar Mamana tana gyara min gashina da man (Bergamot), sallamar Abdallah ta tsinkayi kunnuwanmu, Abdulhakim na bayansa, wasu irin zaratan matasa masu kwarjini na daukar hankali, ilhama da cikar zati.
Mijin-Sakinah ya rame fiye da tsammanina, ya riga ya ganni, don haka babu damar gudu. Ko da damar gudun ba zan iya gudun ba, don kwarjinin shi ya cika ko ina.
Na tashi daga kwanciyar da na yi, na nemi dankwalina na daura. Tunda suka shigo Tananni ta zura daki da gudu sbaoda yadda tun a Libya Abdulhakim ke tsokanarta da kiranta Zaujatee. Wato matarsa.
Sakinah ta shiga marhaban dasu, cikin dan lokaci an cikasu da cima kala-kala. Mijin Sakinah kokari yake mu hada idanu amma na ki.
Abba ya yi sallama ya shigo yana murmushi, ya ce, Manyan baki garemu a gidan? Da kun yi zamanku yau zamu kawo muku matarku. Ke Sakinah dauko mayafinki ku tafi bana son wata tashin-tashina, komai ya wuce Allah ya baku hakurin zama da juna.
Idanuna suka cicciko zan yi kuka, Abba ya ce, Aa, kar ki yarda mu yi haka dake Sakinah.
Shi auren baki dayansa jigonsa shi ne hakuri, Abdulhakim ya yi laifi, amma ya gane da kansa bai kyauta ba, ki zamo mai afuwa ga wanda ya sava miki, amma bana son kullaci da sanya abu a rai fiye da kima, maza tashi kuje Allah ya yi muku albarka.
Har mota suka rakomu ina ta kuka, Mamana rungume dani tana lallashina. Tunanina shi ne yadda zan ci gaba da rayuwa da Farida, tunda na gane ba ta sona da alheri.
Abdulhakim na tuki yana murmushi, Abdallah sai zuba min hira yake, amma na ki in kula shi. Ya ce, Haba Sakinah, dan wannan abu da bai kai ya kawo ba sai ki zo ki gayawa Abba? Maimakon ki neme ni ki gaya mini mu ci mu binne abinmu ba tare da kowa ya ji ba. Na raina wayonki, nan gaba kar ki sake yin haka, wannan rashin wayo ne, kin ji na gaya miki.
Ko amsa ban ba shi ba ya gaji da babatunshi ya yi shiru. Abdulhakim bai tofa mana ba, tukin shi yake cikin kwarewa da sukuni.
Gidan Hajiya muka fara shiga don ta san na dawo, Hajiya kamar ta goyani saboda lallashi da nuna kauna.
Sabuwa bakinta har kunne, tana “sannu da zuwa uwar dakina”. Daddy ya kawo kudi masu yawa ya bani.
Abdallah ya wuce gidanshi, mu kuma muka nufo namu gidan. Sabuwa ta sa mukulli ta bude, ko ina fes kamar ba a je ko ina ba.
Sabuwa na ba da baya ya sunkuce ni yana juyi dani a tsakar falon yana cewa, Yarinyar nan kin wana ni da yawa ... Daga nan muka rankaya ga dakin barcin mu, cikin wata irin soyayyah mai wuyar bayyanawa.
Gyaran Mamana yayi aiki sosai, lallai gata sai uwar data haifeka. Babban goro sai magogin karfe .(sunan littafin TAKORI mai zuwa). Duk yadda Abdulhakim zai yi ya wanke laifinsa cikin hikima da soyayya ya sani. Na ji babu abin da nake so nake kuma kishi a wannan duniyar irin mijina Abdulhakim Khalil Ribadu. Daya tamkar da dubu, abin alfaharina, farin cikin rayuwata. Bani da zabi ban da nima in mallaka mishi soyayyata mu raya daren cikin farantawa juna rai.
Na kalubalanci kaina da tunanina na baya cewa zan iya rayuwa babu Abdulhakim a cikinta.
Kwana uku kwarara Abdulhakim bai je ofis ba, amarci sosai muke gudanarwa wanda a baya bamu taba yi ba.
Na sha mamaki da har kwana uku ban ga Farida ba, ban ji ya yi zancenta ba. Ni kuma ban tambaye shi ba.
Sabuwa ke kyankyasa min tana jin Abdulhakim ya saki Farida, don taga sanda ake kwashe kayanta.
Na dade ina tunanin alamarin, daga baya na watsar na shiga harkokina. Shi da kansa yake gaya min Farida tana gidansu, sun rabu.
Bayan wannan bai kara komi a kai ba. Na ji tausayin Farida, domin dai duk wacce ta yi rashin gwarzon miji irin Mijin-Sakina, dole a jajanta mata. Sannan ciwon ya mace na ya mace ne.
Sati hudun da na yi ba tare da Abdulhakim ba, ni kadai na san irin halin da na shiga. Na yi mana addua dukkanmu cewa, Allah ya sa hakan shi ne alherinmu.
Jarrabawarmu ta fito, daidai sanda Abdulhakim zai tafi qaro karatu (in-service) zuwa jamiar (Waterloo, Canada).Ya yi cuku-cukun da nima na samu gurbi a can, inda zan yi karatu a kan tsimi da tanadi, wanda aka fi sani da tattalin arzikin kasa (economics).
Ranar litinin jirginmu ya daga zuwa kasar Canada, birnin Vancouver. Rayuwa ta mika mana cike da ci gaba da buxi ta kowanne bangare. Da albarkar iyaye lullube da mu. A Canada na haifi Abdulhakim (Daddy), Ibrahim Khalil, da Mukhtar. Iyayenmu kullum cikin sanya mana albarka suke, kuma albarkar muke ta gani har gobe, don kuwa kullum cikin niimomin Ubangiji muke. Tabbas duk wanda ya yi biyayya ga iyayenshi zai ga da kyau a rayuwarshi ta duniya da lahira.
Masha Allahu la-quwwata illa billah!