Chapter:1 The Beginning Of Everything
by @jannat57
Bismillahir Rahmanir Rahim.....
In the name of Allah the compassionate the most Merciful...
💍💕"JIRAN__ _MASOYI"💕
💕💍"WAITING_FOR_LOVE"💕💍
Noor! Noor! Noor!
Kwance take a ɗaki akan gado mai 6/6 flat take kwance tana kallon ceiling in ɗakin, she keeps on counting the ceiling, like someone who doesn't have a work to do. tana tsanye cikin plain dogon riga marun,tanajin kiran sunan nata tasan wanda ke kiran nata lumshe idon ta tayi, before she answer the woman...
Yes granny.
motsin buɗe kofan ɗakin taji kakar tane tashigo wanda daka ganta kasan ta manyan ta, tare da kanwar ta Jannat wanda ke biye da kakar a baya.
Granny are you alright?
Lafiya kalau Noor ina,yanzu muka yi waya da Dr khalid yake faɗa min, there is professional lawyer that he talk to him about you my dear, you would went there as an assistant and intern, you would be working together, and the best thing about him is that he has never fail a case...kinga as a growing up young barrister kema zaki zama kamar shi idan kukayi aiki tare...
tana faɗa suna hada ido da Jannat wanda suma da kansu sunsan baza ta yarda da zancen ba saboda sassauran ra'ayi irin nata wataran.......
Granny what did you people mean?? I don't want my success to rely on another person's own, and you both know that...
Sis seriously you didn't understand what me and granny mean....
no, I understand what exactly you both mean, she said and smile at them...
shikenan tunda haka kike nufi inji granny ta juya zata bar dakin.
Oh my God sis granny will be mad at you shikenan.
tashi tayi da gudu taje ta kama ta, ta baya granny na amince....
granny tasan idan ba haka tamata ba,bazata dau maganan da muhimmanci ba.shikenan zai turo miki address in ran monday insha Allah zaki je ki same sa....
toh shikenan granny Allah ya kaimu gobe nema...
Ameen granny tace...
Ayyah na jiran mu muje mu karya inji Jannat...
take suka fita daga dakin sukayi hanyan dining domin yin breakfast nasu wata yar karaman dining ne na katako mai sit shida da tablecloth akai tare da platemats akai..
wata mata wanda baza ta wuce shekara arbain da dan kai bane fara doguwa bata da jiki sosai tafiyan ta a mike take yin sa tana da tsayin fuka da dogon hanci wanda akwai wani babban tawadan Allah akan karan hancin ta,da manyan ido masha Allah ga tsayin gashi baƙi kirin wanda ya ɗan kwanto a saman goshin ta tsanye take da dogon riga mai kamar buba mai kalan red da milk tafito da plate a hannu daga kitchen...
Jannat ce tayi sauri ta karba,Ayyah bari na taya ki,bata tayi taje ta tazauna a kujera daya mai side in mutum ɗaya...
Noor ce tamaso kusa take wa Ayyan nasu sannu tare da sawa kowa pancake nasa a plate nasa ta mika granny flask in shayi da kwan-kwamin madara da bonvita domin tafison ta zuba shayin ta da kanta...
"granny it quite time that your everything is suppose to be sugar free" saboda girman ki yanzu inji Noor...
duk abin danake sha kullum is "sugar free" tunda da dafaffen sugar muke amfani kuma ni da ku ai ba daya bane nasha nono da man shanu...
shikenan kaka Allah ya kara mana lafiya.ameeen...
Suna gama cin abincin Noor da Jannat suka kwashe kayan wanke wa na breakfast in Jannat ce tace wa Noor ta bari zata wanke kasance wan basu da mai aiki su suke komai a gidan, su huɗu ne kawai duka mata a gidan...
Gida ne dede na rufin asiri mai ɗauke da falo ɗaya da three bedroom wanda koh wanne akwai toilet aciki sai kitchen a haɗe da store kana fita sai dining room bedroom in farko a kulle yake kasance wan na yayan su Ayman ne baya nan sai yazo ake buɗe masa a share, Medical Doctor ne a Abuja, sai ɗaya na granny da Noor ɗaya kuma Jannat da maman su daga waje kuma akwai ƙaramin space mai ɗaukan mota biyu amma mota daya ne a pake kirar vibe silver colour wanda yaya Ayman ya siya yasa aka fara koya wa Noor saboda hidimar yau da gobe na gidan nasu, kuma duk ita take zuwa tayi musu komai,wata tsohuwar bak'ar gate ne a gidan wanda ta fara tsatsa ta gefe gefen sa.saboda yau lahadi ne babu mai zuwa koh ina shiyasa duk a gida suke yini. suna cin dinnern su suna hira kaɗan kaɗan, kowa yatashi yayi hanyar ɗaki zasu kwanta...
chan dare kusan karfe ɗaya na dare granny ta tashi shan ruwa sai ta fuskanci Noor bata ɗakin ta duba ban ɗaki ma babu kowa ta zabura ta fita da mamakin me Noor take a waje war haka gashi bata falo tana zuwa baƙin kofan backyard ta same ta zaune a kan dakalin gurin.
Noor me kuma kike a gurin nan war haka?
Granny me ya fito dake na kasa bacci ne kawai sai naji bari na fito nasha iska.
Noor ba sai kin min karya ba, nasan akwai abinda ke damun ki....... ki faɗa min...
Babu komai kawai kinsan gobe monday zanje gurin barrister nan koh wani irin mutum ne oho? granny kuma kinsan koh bature na tsoron mondays...
haka ne Noor ina,toh me abin damuwa bayan kakar ki na tare dake...
hakane kakata takaina tun na buɗe ido na kike tare dani har yau kuma har kullum insha Allah.
hakane Noor yanzu ki tashi muje mu kwanta koh.eh tashi maza.... tashi tayi suka je suka kwanta...
washe gari bayan sallar asuba sun gama adzkar nasu chan gari ya fara waye wa Noor da granny suka koma bacci,Jannat ce ta tashi ta gama shirin ta tsaf ta haɗa complex da madara tasha saboda tana da lectures in safe chan tazo tafiya taji shiru babu motsin yayar ta sai taje duba ta tana buɗe ɗakin granny ta farka...
Good morning granny....
Morning Jannat kin gama shiri ne zaki fita...
Eh kaka nazo duba Noor ne...
toh ai kingan ta tana bacci...
granny kinsan yau zataje office at least ki barni..........
A'a, zan faɗa mata zata kira ki kinsan idan ta tashi shikenan kuma......
Toh shikenan kaka.juya wa tayi tabar mata ɗakin taje kan dining tadau jakan ta da ta ajiye sai ga Ayyah nan ta fito daga daki tazo ta same ta.Jannat yau ba kuɗi kuma zaki tafi?
A'a Ayyah daman yanzu zanzo na karba.toh gashi Jannat tasa hannu a ɗan dur kushe ta karbi kuɗin...
nagode Ayyah...
Menene kuma kike ta faman haɗa rai...
Babu komai Ayyah...
A'a nasani ke da kakar ku....
Eh Ayyah, tahana ni magana da Noor...
Bakomai kije kar kiyi letti Allah yayi miki Albarka Allah ya bada sa'a...
Ameen Ayyah,Jannat zuwa tayi ta rungume Ayyah sai tamata light kiss a goshi kafin ta juya ta tafi.
*****
Daddy! Daddy! Daddy!
Wani ɗan matashi ne wanda be wuce shekara 33 ba Fari ne sol dogo yana da kaurin jiki domin bazaka ce siriri bane yana da manyan muscles both kafaɗa da chest a murde suke, da manly voice, yana da tsayin fuska and he has that colourful eyes da tsayin hanci yana da kyawun gani a faɗa,tsanye yake da ba'ka ken suit na lawyoyi me haɗe da button-down collared shirt da jacket da tie haɗe da navy blue socks da baƙin loafers wanda suka karbi jikin sa, saukowa yake daga saman stairs wanda daka gansa kasan sauri yake yi, yaji kiran da yaran nan suke masa yasa sa tsaya wa tare da amsa musu...
Na'am my children...
da gudu suka zo suka kama sa tsanye suke da pink blouse da checkered skirt uniform mace da namiji ne wanda namijin be wuce shekara bakwai ba macen kuma shida...
A tare suka ce, Good Morning Daddy...
Morning my kids, where is your Mum? I hope you didn't disturb her, and stop her from sleeping...
Yes Daddy she is in the room...
Daddy bazaka kaimu school ba tunda kaima fita zakayi uncle Usman driver baya nan inji Sultan.
No sultan I am in a hurry,next time zan kai ku amma yanzu zansa Fahad ya kai ku sai ya wuce school shima...
Ok thank you Daddy....
Toh bye bye my kids...
Noora! Sultan. Noora kamar uncle Fahad is the one calling us...
Yes mutafi watakil Daddy ya fada masa...
Zuwa sukayi suka dauko jakan su na school Umma Ladi ne tazo da lunch box nasu ta basu sannan suka fita,sun samu ya dauko motan daga parking space...
ƙato ton gida ne mai haɗe da beni bayan yan gidan da masu aiki, haɗe da yaran riƙo, gida ne wanda duk ɗan uwan daya zo is welcome idan yana buƙatan zama kuma duk ɗan gidan da zaiyi aure a gidan zai zauna...
Fahad zuwa yayi ya sauke su ya wuce school 🏫...
Ɓangaren Noor kuwa haryan zu bacci take yi har sha daya tayi bata farka ba,alarm in data saka ma daya buga kashe wa tayi saboda bata sami bacci da wuri ba jiya, kuma idan ta zabura ta tashi toh haka yinin ranan da ciwon kai zatayi,asalima ita ba mai son baccin rana bane gashi yau kuwa sai bacci take yi abin ta,gashi appointment nata 8 akace tazo koh ya zatayi?
Granny ce tashigo dakin domin ta tashe ta taga baccin ta yaƙi kare wa...
zuwa tayi ta ɗan taɓa ta,wake up Noor...
ɗan juyawa tayi tana facing in ceiling tana murza idon ta a hankali...
Me ya faru kuma yanzu Granny?
Granny ne tazo ta ɗaga ta daga kwanciyan da ta...
ha'a yau naga ikon Allah wani dare aka sake miki ne? ki tashi ki duba rana har ta gama fito wa...
Oh my God, tou kaka ai na tashi yanzu...
Naji kije kici abinci,ki ɗan gama ayyukan ki, kiyi wanka kafin azahar lokacin zuwa gurin mutumin nan kinga tunda ƙarfe biyu ne babu African time sai ki fita ƙarfe ɗaya nan da minti talatin kin isa Insha Allah sauran minti talatin in sai ki zauna jiran sa koh yazo yasan kin darraja sa kin zo tun kafin lokacin ya cika...
Shikenan kaka yanzu ƙarfe nawa ne?
Sha ɗaya de zai dan wuce...
What Granny are you serious?
Ni kike tambaya serious?ba ina ta tashin ki ba kina cemin me ya faru dan iskanci...
Kaka wanka kawai zanyi na tafi nayi letti,tana gama faɗin haka tashige ban ɗaki ta rufo kofan...
Granny tana karfe nawa Dr Khalid ya turomiki daya turo address in na zata biyu ne,amma ina Noor koh sauraron ta batayi ba.ta fito zata shafa mai tasa kayan ta kenan taga kanta a mirror kanta duk yayi kamar na mahaukata dole sai ta tsaya ta taje domin lokacin ya riga ya wuce,ga idanun ta duk sunyi zuru zuru,bata da manya ko kananan ido,amma tana da tsayin gashin ido wanda suka ƙara idon nata kyau masha Allah,tagama taje kan nata duk da taje wan na bata wuya domin tana da cika da tsayin gashi baki ne gashin nata sosai ga tsayi sai sheki yake da ta kama sa,ta shafa mai wanda ya ƙara wa farin fatan nata sheki, buɗe wadrop nasu tayi ta dauko wani dogon riga pink da gylen sa tasaka ya mike har kasa ta dauko flat takalmi tasa,fita tayi tasame su a parlour tamusu sallama ta wuce suma sunga yanda take sauri basu tsaya yi mata tambaye tambaye ba fatan su de Allah yasa a dace...
Noor fara ce,doguwa,wanda jikin ta ya tafi da tsayin ta,tana da round face da dogon hancin ta, wanda ba sosai bane duk da haka hasken tan yakara fito da kyawun nata bata da kan-kanta koh girman baki,kyawun surar ta har yaso yafi fuskan tan kyau...
Jan motan take da gudu har ta isa gurin,office in lawyoyi ne duk gurin daga gani kasan masu zaman kansu ne,tafito a motan ta wuce tarasa wani beni ne office nasan yake domin beni biyu ne kuma duk na facing juna bismillah tayi tasa kai tace bari na fara duba dama tabi offices in na karshen kenan taga barrister Anwar M.A, a manne a jikin office in knocking tayi chan taji kamar anyi magana tashigo, buɗe wa tayi ta shiga da sallaman ta,ta gaishe shi ya amsa mata, kafin tace...
Dan Allah Barrister Anwar na nan?
Eh yana nan sai de ya sauka kasa amma bari na kai ki.taga alamun secretary sane kar yace yabar masa office a buɗe koh wani abu kwanda taje da kanta...
No, A'a bakomai ka nuna min gurin kawai zanje na same sa....
Idan kin sauka ta backyard akwai resting area zaki gansa a gurin maybe yana zaune a gefe Shi kadai...
To shikenan na gode tace masa...
Ahankali take takun ta har ta isa gurin ga warin sigari da take ji, taga wani na tsaye shi kaɗai bayan sa a juye isa tayi kusa dashi amma da alamun bai ji motsin mutum ba,hannu tasa zata taɓa kafadan sa,sai ta fasa kuma tasaya alamun shi ke shan sigarin tagani,kafin ta ankara babu ya juyo ya buso mata hayakin sigarin ( Smoking is very harmful to your health)da ya zuka yayi,tari yaji ta fara sosai saboda yanda take tarin alamun bata son warin, gashi kuma ta sheka...
Ruwa ruwa alamun haka yaji take faɗa a muryan tarin nata...
cikin hanzari ya mika mata ruwan san dake ajiye.
karba tayi da sauri tasha ta sake meda wa tasha sai kuma ta tuna cewan ba ita tafara shan ruwan ba,me hakan ke nufi kenan?
raguwan ruwan sa ya bata subahanallahi aikuwa take ta watsar da rakuwan na bakin ta ji take kamar ta amayar da wanda tasha tawani zura masa ido tana kallon sa, what kind of a person is he? Take tambayan kanta takeyi...
Who are you? Tambayan daya jefo mata kenan...
Batayi magana ba.wacece ke? ya sake tambayan ta shiru...
Me kike so shiru.kurma ce?
To idan kurma ce ai batayi magana ba tsaki yaja yafara tafiya zai bar gurin.
Sai lokacin ta dawo hayyacin ta,taga alamun tafiya zaiyi ya barta a gurin.
Excuse me Please,Malam kaji, kaji, Tsayawa yayi kawai batare da ya juya ya ganta ba.
Sunana "Noor Muhammad Abdul Majeed",nazo... duba "Anwar" ne I mean "Barrister...... Anwar" maybe you would know him...... koh zaka iya faɗa min inda yake?
Yana gama jin ta tafiyan san yayi batare da bata amsa ba,jiki ne ya bata koh shine sai kuma tace bari tabi bayan sa,binsan da tayi taga office me dauke da sunan Barrister Anwar in ya shiga itama zuwa tayi ta shiga,ji tayi yana cemasa.
ka nuna mata gurin ta,kuma next time kar ka sake tura min wani koh wata idan na fita.
Noor ce ta ari bakin sa tace ni nace masa zanje ba turani yayi ba amma.........
ina buɗe dayan kofan cikin office in yayi ya shiga da alamu wannan na secretary ne.
cikin ne office nasa,mutumin ne ya dawo da ita daga kallon kofan da ya buɗe da take yi.
Hajjiya ga guri nan ki zauna.
Alright, Thank You, I am "Noor" and you?...