CHAPTER FOURTEEN
by @ummubasheer
Washegari da safe*
Kasancewar ranar weekend ne, DEEJA da yake tana son yin girki Kuma ta dage sai ta koya, kitchen ta Shiga inda ta tarar da gwogwo wace take musu girki, gaishe ta tayi, cikin fara'a ta amsa Nan DEEJA ta fara taya ta aiki tana kallon yanda take komai, bayan sun gama ne DEEJA ta shirya komai a dinning table, Dan duk mutanen gidan na barci, bedroom ta nufa, ta Shiga toilet tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin Swiss lace peach colour, tayi kyau sosai lipstick pink tasa sannan ta sa wani Necklace and earrings na fashion designer, sai shining take like star, sai k'amshi takeyi, ASHRAF dake barci yaji k'amshin turaren ta, bud'e ido yayi yace"Baby zo kiji"ya mik'a mata hannun shi.
Turo baki tayi cikin shagwab'a ta rik'e hannun shi,jawo ta yayi ta fad'a kan k'irjin shi, rufe su yayi da blanket Yana kissing d'in ko'ina a jikin ta, kukan shagwab'a ta sa mai, da sauri ya had'e bakin su Yana tsosa, ture shi ta fara cikin Wasa tana cewa"ni dai ka Bari"
Da k'yar ya iya barin ta yace"baby ke d'in ce akwai sweet"
Rufe ido tayi da sauri ta tashi tace"kaje kayi wanka muyi breakfast"
Mik'ewa tsaye yayi Yana rik'e da ita Wai sai dai suyi wankan tare, da k'yar tayi Mai wayau ta gudu.
Bayan ya shirya ne ya sauko downstairs inda ya tarar da duk sun tashi za'ayi breakfast, gaishe su yayi da k'yar Aunty MEERAH ta amsa Cox Bata son Mommy ta fahimci akwai wani abu.
Bayan sun gama breakfast ne ASHRAF da DEEJA suna zaune a kan kujera dake cikin bedroom d'in su, sai kitso take Mai da gashi, Wai yak'i yin aski ai gara tayi mai kitso kawai, murmushi kawai yake Mata Cox Yana son ta shirmen ta da k'uruciyar ta na bashi sha'awa, rik'e hannun ta yayi ta tsaya, bakin shi ya Kai kan lips d'in ta yayi kissing d'in ta, cike da shagwab'a tace"ka Fara ko?"๐
Hannun shi yasa cikin rigar ta Yana Wasa da breast d'in ta, lumshe ido tayi da alama tana Jin dad'i, can dai ta mik'e da sauri zata gudu. Rik'o ta yayi yace"ki shirya za muje gidan su INNA"
Habawa ai tsale tayi ta rungume shi cikin farin ciki sosai take Mai godiya, k'ara shiryawa tayi Kuma tayi kyau, sannan suka nufa parlour inda suka tarar da Mommy sukayi mata sallama, har HANA tana cewa zata bi su, wani mugun kallo Mommy tayi Mata da yasa tasha jinin jikin ta, Bata bi su ba.
Da missalin k'arfe 1:00 pm suka isa k'auyen, ba k'aramin farin ciki INNA tayi ba ganin jikan ta, YAYA BILAL ma yaji dad'i sosai ganin K'ANWAR shi tana cikin kwanciyar hankali, Haka dai suka dinga hira, DEEJA har gidan Hansai taje inda ta tarar da ita da tsohon ciki sai tausayin ta take ji, tana cewa ita gaskiya bata son ciki indai Haka ake wahala, K'arfe 5:00 pm suka bar k'auyen, DEEJA sai kuka take Wai Bata son bin shi, ni ko nace ai auren kenan.
Bayan sati biyu
DEEJA ce sanye da Arabian gown black tayi rolling d'in veil d'in a kanta sai ta fito Sak balarabiya, ASHRAF da ya ganta sai da yayi ta Mata pictures a wayan shi cox she's looking pretty.
Gidan Abokin shi SALIM ya Kai ta, hannu biyu matar ta tarbe su, Mai suna Ummie, tana da kirki ga son mutane, bayan sun gaisa ne taja DEEJA bedroom d'in ta inda suka fara hira, duk da cewan Ummie ta lura DEEJA akwai yarinta Amma Haka ta dage sukayi hira har ta Bata wasu magungunan Mata, tare da fad'a mata yanda zatayi, da kanta ma ta fara shirya ta inda suka shiga kitchen ta had'a kankana da ruwan zogale tare da peak milk na ruwa(Mata ku dinga gwada wannan sosai fa yake aiki), kasancewar su ASHRAF sun d'an fita, shine suka samu damar abin da suke so, ranar dai sai dare yazo ya d'auke ta, sosai taji tana k'aunar Ummie Cox tana da kirki sosai.
A wannan Daren DEEJA tasha azaba Dan mutumin naku k'in barin ta yayi, sai da ta fara kukan shagwab'a sannan ya hak'ura ba Dan yaso ba, ni ko nace aikin ki Ummie yayi kyau.๐
A Haka rayuwa yaci gaba da tafiya, tsakanin DEEJA da ASHRAF soyayya suke gudanarwa mai k'arfin gaske, sannan Kuma tana zuwa makaranta da islamiyya yanzu ta fara natsuwa, sai dai d'an tsokana Wanda a jikin ta yake a hankali k'ila zata Bari, Haka take faman tsokanan HANA Mommy tayi ta fama da su tana fad'a.
B'angaren Mommy da Aunty MEERAH kuwa sun takura ma DEEJA ko da yaushe cikin yin mata fad'a suke Dan suna ganin ai YAYAN TA ne sanadiyar kashe ALHAJI BILYAMIN mahaifin su ASHRAF, a gaskiya DEEJA Sosai take hak'uri da su tana musu biyayya Kuma bata fad'a ma kowa har ASHRAF bata fad'a mai, in tak'aice muku DEEJA na Shan wahala gurin Mommy.
Aunty MEERAH tana matuk'ar k'aunar MALIK Amma tak'i yarda ta gane cewa bashi bane ya kashe mata mahaifin ta dan har yanzu tana zargin shi.
Wata rana kwatsam sai ga MUSA Wanda ya kasance abokin ALHAJI BILYAMIN, ziyara ya kawo musu, sosai sukayi mamaki, Nan aka sauke shi a guest room, bayan ya huta ne suka k'ara gaisawa sannan ya bayyana musu abin da ya faru tsakanin su ALHAJI BILYAMIN da ALHAJI NASIR,! Sunyi matuk'ar girgiza da Jin ainihin abin da ya faru! Duk da Haka Mommy ba tace komai ba Amma a ranta ba Wai ta yarda bane tace dai su MALIK ne sanadi!
MEERAH kuka sosai ta dingayi Ashe MALIK bai kashe mata mahaifin ta ba, ashe mahaifin ta shine Wanda ya yaudare iyayen MALIK, sannan Malam MUSA ya gyara zama inda ya fara basu labarin abin da ya faru cikin shekaru goman Nan da suka shud'e kamar Haka.
Yace"Bayan mutuwar ALHAJI BILYAMIN nayi bincike sosai Dan gano ainihin k'auyen da ILIYASU yake, lokacin da na gano da kaina naje k'auyen, Dan insa a kama shi, sai dai na tarar da bai ma San inda kanshi yake ba Yana fama da kaf'ar shi Wanda na harbe shi a gurin, k'afan duk ya rub'e, ga ba kud'in magani, ganin irin azaban da yake Sha sai na k'yale shi domin ya d'and'dani azaba yasan cewa kashe mutum ba Wasa ba bare har mutane biyu, sai na k'yale shi, Bayan shekaru biyar naje wani hospital sai Naga wani gurgu ba shi da kaf'a d'aya da alama ya rub'e ne an yanke, naji tsoro lokacin da ya rik'e ni Yana Kiran suna na Yana neman gafara na, sai daga baya na tuno fuskar nashi Ashe ILIYASU ne, kamanin shi duk sun canza, yayi ta rok'o na Akan in yafe Mai Kuma in zo in neman mai gafarar ku, sai dai nayi k'okarin zuwa sai Kuma Allah bai nufa ba sai yanzu, shekarun baya da suka wuce naji labarin rasuwan shi, yayi Kuma mutuwar wulak'anci" ya numfasa sannan yace"Ina baku hak'uri sosai Allah Kuma ya jik'an ALHAJI BILYAMIN da ALHAJI NASIR, Allah ya raba mu da sharin mutane da mahassada, Wannan shine ainihin abin da ya faru"
"Ameen ya Allah" su kace a tare. Mommy cikin share hawaye cikin tunanin mijin ta sannan ta bar gurin yayin da MEERAH ke ta rusa kuka da nadama da tir da halin da mahaifin ta yayi a lokacin kafin mutuwar shi.
Har gurin gate ASHRAF ya rako shi lokacin da zai tafi Yana Mai godiyan ziyaran da ya kawo musu. Nan suka yi sallama ya tafi Yana musu fatan alkhairi a rayuwar su.
Jikin ASHRAF yayi sanyi domin shima ya tuno da rasuwan mahaifin su, straight bedroom d'in su ya nufa, DEEJA dake zaune da sauri ta tashi tsaye cikin mamakin meye ne ya samu mijin ta lokaci d'aya ya canza Dan Bata tab'a ganin shi a cikin irin wannan yanayin ba, da sauri ta rik'o hannun shi tana tambayar meke faruwa.
Zama sukayi kan bed inda ya rungume ta, idanun shi jajazur, rungume shi tayi tana shafa Bayan shi tare da bashi hak'uri duk da bata san meke faruwa ba, k'ara rungume ta yayi da d'an k'arfi Yana sauke ajiyar zuciya, a tare suka kwanta kan bed d'in, kissing d'in shi ta fara, Cox ya d'aga Mata hankali da yanayin shi, k'ara rungume ta yayi suna kissing d'in juna kamar zasu cinye lips d'in su, da k'yar ya sake ta ya rungume ta suna sauke ajiyar zuciya a tare.
Cikin satin Nan gidan ya Zama wani iri, domin tuno da rasuwan ALHAJI BILYAMIN.
Bayan wata d'aya
MEERAH na cikin damuwa k'aunar MALIK take ba k'adan ba, gaba d'aya ta canza burin ta d'aya shine taga sun dawo da soyayyar su sunyi aure, duk da tasan Mommy ba zata yarda ba Kuma tana tunanin anya MALIK zai aure ta kuwa? Ganin yaudaran da mahaifin ta yayi ma na shi.
Ranar Friday ta shirya cikin wani Arabian gown light blue tayi rolling d'in veil a kan ta, wow tayi kyau sosai black handbag and shoe tasa sai dai bata yi make up ba Dan yanzu burin ta shine taga Masoyin ta, d'aukar key d'in mota tayi ta nufa parlour tayi ma Mommy sallama akan za taje gidan wata friend d'in ta.
Lokacin da ta Isa k'auyen parking tayi a k'ofar gidan su DEEJA, tare da fitowa ta Shiga ciki, INNA na zaune tana sauraren Radio taji anyi sallama tare da shigowa.
Ba k'aramin mamaki tayi ba ganin MEERAH, Tace"Lale barka da zuwa ga guri ki zauna" ta nuna mata kujera dake gefe.
Zama MEERAH tayi ta gaishe ta amsawa INNA tayi cikin fara'a tana tambayar mutanen gidan da jikar ta DEEJA, Ruwa INNA ta kawo Mata tasha sannan gurin ya d'auki shiru tsawon 10 minutes sannan MEERAH tayi magana inda tace"INNA nazo neman gafara ku ne bisa abin da mahaifina yayi Wanda Sam ban sani ba"
Cikin mamaki INNA ta tambaye ta meke faruwa, ba tare da b'ata lokaci ba MEERAH ta sanar da INNA komai da Malam MUSA ya fad'a musu, sosai INNA tayi kuka tana tsine ma ILIYASU, Nan take ta tuno da d'an ta ALHAJI NASIR, hak'uri MEERAH tayi ta Bata sannan tayi shiru.
MEERAH tace"INNA MALIK baya Nan ne? Ina son neman gafarar shi in fad'a mai gaskiya"
INNA tace"eh baya Nan Bayan ya dawo masalacin juma'a shine ya wuce gareji"
Da mamaki tace"INNA gareji Kuma?"
Tace"eh ai tun bayan rasuwan iyayen ku ya dawo Nan yake aiki a garejin domin yace baya buk'atar rayuwar Jin dad'i gara yayi rayuwa a k'auye Kuma duk saboda A KAN K'ANWAR SHI yayi hakan"
Cike da mamaki tace" A KAN K'ANWAR SHI?"
INNA tace"eh, Bari in Kira wani yaro ya raka ki can garejin" mik'ewa tsaye tayi ta nufa k'ofar gida ta samu yaro ya raka ta.
MEERAH ko ba k'aramin mamaki tayi ba, Ashe dai Yana k'aunar k'anwar shi sosai tunda gashi Yana rayuwa a k'auye Bayan yanda tasan shi d'an gayu ne ga kud'i ga kyau ga halaye masu kyau but ji yanda yake rayuwa a k'auyen Nan.
Lokacin da ta Isa garejin yaron ya Shiga ya Kira MALIK (sorry Zan dinga Mai amfani da ainihin sunan shi maimakon BILAL), MALIK yayi mamaki da yaron yace Wai wata y'ar gayu Mai mota na Kiran shi, sai ya fara tunanin ko yarinyan Yayan Mahaifiyar shi ne shiyasa ya fita.
Ganin MEERAH ya bala'in d'aga mai hankali ga tsananin mamaki, ita ko tana ganin shi ta fashe da kuka sosai.
K'arasawa gurin ta yayi yace"zubar hawayen ki tamkar ruwan dalma ne a cikin zuciya na, Zan so ki taimake ni kiyi shiru ko Zan samu natsuwa"
Jin kalaman shi yasa ta k'ara kukan wato har yanzu shima yana k'aunar ta kenan? Mik'a mata handkerchief yayi Mai k'amshi yace ta share hawayen, karb'a tayi ta goge tana cewa"Tabbas nayi kuskure da na guje maka Wanda hakan ya faru ne akan rashin sani, Amma nayi *ALK'AWARI* bazan sake barin ka ba duk da mahaifina yayi *YAUDARA DA CIN AMANA* gare ku, zanyi burin mu zama *ZURI'A D'AYA* domin Kyakyawan halayen ka" ta k'are cikin hawaye.
Murmushi yayi yace" nayi matuk'ar farin cikin yanda Kika ce haka, Zan rayu dake kamar yanda *ASEEM* ya rayu da *NAJWA* (RAYUWAR NAJWA litafi na) "
Nan MEERAH ta fad'a mai duk abin da Malam MUSA ya fad'a musu, shi kanshi sai da hankalin shi ya tashi sosai, Nan dai sukayi hira da yin ma iyayen su addu'a, sannan suka yi exchanging d'in number'n su, har gurin motar ta ya raka ta sai da taga tafiyar ta sannan ya Shiga gurin INNA suna jimamin abin da ya faru.
*LOVE*๐
Wani irin soyayya ne Mai zafin gaske a tsakanin su domin yanzu kullum cikin yin waya suke, Haka Kuma sun shirya yin aure a tsakanin su duk da suna tunanin Mommy ce matsalan su, Mommy bata tab'a lura akwai wani soyayya a tsakanin MEERAH da MALIK ba Dan ta cire shi a lissafi ma, sai dai tana matuk'ar ba DEEJA wahala, yanzu MEERAH idan Mommy nama DEEJA fad'a sai ta dinga kare ta Wanda Mommy takan yi mamakin hakan. Yanzu MEERAH na matuk'ar son DEEJA domin soyayyar dake tsakanin ta da yayan DEEJA d'in.
*Ashdee one love*๐
*Masu karatu shin Kuna ganin DEEJA zata yarda YAYAN TA ya aura MEERAH kuwa? Shin YAYAN nata zai iya yin abin da K'ANWAR SHI take so Dan kar ku manta yace A KAN K'ANWA TA Zan iya komai, to ya kenan? Ku biyo ni Dan Jin yanda zata kasance.*