CHAPTER FIFTEEN
by @ummubasheer
Sister Xainab da sis Maimounath, ku ne dai kuka koya min Dan ba ruwana๐, K'awas Badeeyerh Ina Bayan ki muna tare*๐
*Soyayya* tsakanin MALIK da MEERAH ya wuce yanda Kuke tunani domin yanzu har had'uwa suke yi ba tare da sanin kowa ba, Rana d'aya MEERAH ta rasa yanda zatayi Cox tana buk'atar shawara Dan yanzu aure suke son yi ita da MALIK, ASHRAF ta samu da maganar Dan babu wani kunya da zata ji tunda tana k'aunar MALIK, ASHRAF baiyi mamaki ba Cox already yasan tana k'aunar shi till now, shawaran da ta Bata taji dad'i sosai Dan cewa yayi taje ta samu Daddy da maganar yasan Daddy zai amince idan yaso yaje ya samu Mommy yanda akayi nashi.
Haka kuwa tayi Dan taje ta same shi Kuma yaji dad'i Dan gaskiya Yana son yaga tayi aure ita ma Nan yace kar ta damu zasuyi magana da Mommy, cikin farin ciki ta Kira MALIK ta fad'a mai shima yaji dad'i, addu'an su dai shine Allah yasa ta yarda.
Daddy da kanshi ya same ta da maganar ai ko ta girgiza sosai Dan Bata tab'a tunanin hakan ba, nan ta nuna ita fa Sam bata yarda ba da k'yar Daddy ya shawo kanta yayi mata nasiha sosai inda jikin ta yayi sanyi, ba'a son ranta ba dai.
Wani gida Mai shegen kyau MALIK ya gina ya tare shi da INNA, lokacin da ASHRAF ya Kai DEEJA ai kamar ta zauna a gidan tsabar farin ciki, INNA ce ke bata labarin auren da MALIK zaiyi da MEERAH, hankalin ta ya tashi, wato MEERAH da Bata da kirki tana mugunta mata shine yanzu YAYAN TA zai aura, kuka ta fashe da shi sosai ai ba shiri MALIK da yaji kukan ta ya shigo Yana tambayar lafiya?
Cikin kuka tace" gaskiya ni YAYA NA bana son ta, muguwa ce, ka aura wata kawai Amma Banda Aunty MEERAH"๐ญ
Hankalin shi a tashe yace" yi shiru K'ANWA TA, Amma tana da kirki fa, nasan tana son ki"
Tace" ni dai wallahi bana son ta"๐ซ
Cikin rarrashin ta yace"ya Isa Haka K'ANWA TA, abin da kike so shi za'ayi"
Sannan ta hak'ura, ASHRAF yazo suka tafi gida, shi dai ya lura ranta a b'ace Amma baiyi tunanin wani abu ba, a tunanin shi kewar su INNA take yi.
Wannan shine ana wata ga wata, domin DEEJA tace Sam bata yarda da auren ba yayin da MALIK ya Shiga tashin hankali Dan Yana son farin cikin K'ANWAR SHI Amma Kuma Yana matuk'ar k'aunar MEERAH Haka dai su KABIR sukayi ta bashi hak'uri suka ce yayi auren Dan yarinta ke damun DEEJA, shi dai baya son b'ata Mata rai.
B'angaren MEERAH ta Shiga tashin hankali, Haka tasa DEEJA a gaba tana Bata hak'uri da nuna mata cewa tayi nadama kuma tana son ta, ita dai DEEJA ta dage Bata so, Haka ma da ASHRAF yaji yace ta fad'a ma YAYAN TA cewa ta yarda da auren, kuka ta sa mai da yace Haka, ita gaskiya tak'i yarda Nan yace sai ta fad'a mai dalilin da yasa tak'i yarda, Nan ta fad'a mai komai Akan abin da MEERAH tayi mata, ya tausaya mata sosai, Kuma ya bata hak'uri tare da nuna mata tayi hak'uri komai ya wuce tunda yanzu MEERAH na bata hak'uri, tsananin k'aunar da take ma mijin ta ASHRAF sai ta amince domin ta tuna lokacin da ita ma YAYAN TA yak'i amincewa but in the end Kuma ya amince Dan Haka Kiran shi tayi a waya tace ta yarda da auren komai ai ya wuce, sosai yaji dad'i Nan take ya Kira MEERAH a waya, da k'yar ta d'auka Dan haushi take ji, Wai meyasa zai ce sai k'anwar shi ta amince za'ayi auren Bayan suna son junan su Kuma manyan su sun amince, Nan ya sanar da ita ai ko tayi murna sosai.
Ansa ranar d'aurin auren MALIK da MEERAH Nan da sati uku masu zuwa, inda zasu tare a Nan gidan da ya Gina, Nan aka Fara shirye-shiryen biki.
Bayan sati biyu
Biki saura sati d'aya kenan inda DEEJA tayi ta ma ASHRAF kuka Wai sai ya barta taje gidan su domin a Fara shirye-shiryen biki da ita. Ba Dan ya so ba ya barta, shi da kanshi ya Kai ta.
Sai ana gobe d'aurin aure ta dawo gidan ta, inda akayi Arabian night, ranar ba k'aramin kyau tayi ba kamar ita ce Amaryan, ASHRAF ko sai mak'ale Mata yake, Dan ma gurin babu maza da bazai barta ba.
Washegari da missalin k'arfe 2:00 pm aka d'aura auren ABDUL-MALIK (Bilal) NASIR tare da AMEERAH BILYAMIN, akan sadaki mafi daraja Naira dubu hamsin dubamin mutane sun shaida d'aurin auren Mai cike da tarin Albarka, ni ko nace wannan shine tsananin rabo, tunda gashi ko Bayan iyayen sun rasu Kuma anyi auren Allah ya Sanya alkhairi.
Around 8:00 pm aka d'auki amarya zuwa gidan ta, gaskiya gida yayi kyau sosai domin Side d'in INNA da ban nasu da ban, guri yayi kyau Masha Allah, Nan aka watse aka bar Amarya da Angon ta, ni ko nace Sai da safe.
Bayan mutane sun watse, DEEJA tayi wanka tasa wani irin nighties masu shegen kyau ga wani irin k'amshi Mai sanyi da dad'i dake tashi a jikin ta, tana zaune gaban dressing mirror tana shafa lotion, ASHRAF ne ya shigo hannun shi rik'e da leda.
K'arasawa yayi ya rungume ta Yana shak'ar k'amshin ta, cikin wani irin yanayi yace"baby I love you and I missed you"
Mik'ewa tsaye tayi tare da nufan bed tana cewa"I'm feeling sleepy"๐
Da sauri ya nufe ta yace"no baby don't said that, nayi kewar ki and you know nayi k'okari tun last week fa"๐คฆ๐ปโโ
Cikin shagwab'a tace"yo ai kasan fa......"โน
Katse mata magana yayi ta hanyar had'e lips d'in su ya fara kissing d'in ta in a passionate way, ni ko fita nayi waje tare da rufe musu k'ofa.
Bayan wata d'aya
Mommy na takura ma DEEJA sosai, komai na gidan ita takeyi har girki wani lokacin ita keyi, ASHRAF bai tab'a sanin haka ba saboda cikin watan baya Zama kullum Yana gurin aiki, sai dare idan ya dawo, Sam baya samun time sai weekend Wanda Yana d'an lura da hakan sai dai da yayi magana Mommy zata haushi da bala'i.
Mommy ce zaune da matar Daddy suna hira inda Mommy ke fad'a ma matar Daddy wacce ake Kiran ta da Ummie cewa gaskiya ita ba ta son DEEJA bare yanzu da taji shiru ko ciki Bata da shi gaskiya ita tana son ASHRAF yayi wani auren, murmushin mugunta Ummie tayi a ranta cewa take ai fad'uwa yazo dai-dai da Zama, Dama ga 'yar ta MUFEEDA sai kawai ta aure ASHRAF domin dama Ummie irin matan Nan ne masu son abin duniya, bare tasan irin dukiyar da su ASHRAF ke da shi, Haka Kuma tana k'okarin SAIF yaron ta ya aura HANA Nan gaba.
Gyara zama tayi tace..................
*Ashdee one love*๐
*TAKU CE ๐๐ผUMMU BASHEER*
[06/02 3:41 pm] Ummu Basheer: ๐น *A KAN K'ANWA TA* ๐น
๐น
{ *TRUE LOVE STORY* }
*NA*
*UMMU BASHEER*
ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
(We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐)_
#***
*#IG PML WRITERS*
#***
#***
*PAGE* *33~34*
*Kuyi hak'uri kunji ni shiru kwana biyu, I'm very sorry, bana samun times ne kuyi managing wannan, Thanks for the love and, care love you all*
*Gyara* Zama tayi tace"Mai zai hana mu had'a MUFEEDA da ASHRAF?"
Cikin sauri ta kalle ta tace"kina ganin zasu so junan su?"
Dariyan samun nasara Ummie tayi tace"ko ma basa son junan su zasu so daga baya, tunda yanzu muna da iko dasu Dan Haka ni Ina ganin ba matsala in dai MUFEEDA ce"
Mommy tace"to shikenan hakan ma yayi Kinga sai ayi auren zumunci kenan"
Nan sukayi ta hira tare da shirya yanda bikin zai kasance.
Lokacin da Ummie ta koma gida ta samu MUFEEDA da maganar, da sauri MUFEEDA ta mik'e tsaye Jin abin da Ummie'n ta fad'a, Tace"Ummie yanzu fa an daina irin wannan auren ya kamata ku waye mana"
Cikin haushi Ummie tace"wato kenan mu ne bamu waye ba ko? Fool kawai ana neman Miki gidan hutu kina kaucewa to ba zai yuwu ba dole ki aure ASHRAF" ta bar gurin.
Tsaki MUFEEDA tayi a ranta tace wannan Ummie'n Sam bata waye ba sai kace old school, Wai auren dole, ni wallahi yanda nake Jin dad'in harka da Mata ba abin da zai sa na aura namiji (Wa'izzubila Allah kayi Mana tsari), Nan tayi ta Jin haushin Ummie Dan ita ko k'adan Bata son ASHRAF Kai ita maza ne ma bata so, ita DEEJA ce ke bata sha'awa tana son yarinyan, Dan Haka ta Kira wata K'awar ta a waya ta fad'a Mata abin da Ummie tace Nan K'awar tayi ta zuga ta Wai Kar ta yarda ta amince da auren.
Mommy ce zaune a parlour tana jiran dawowan ASHRAF daga aiki, shigowa gidan yayi da alamar gajiya a tare da shi, rigar doctor d'in shi na rik'e a hannun shi, da k'yar ya rik'e briefcase d'in shi tsabar gajiya, k'arasawa yayi ya gaishe da Mommy sannan ya mik'e tsaye ya nufa hanyar upstairs. Dakatar da shi tayi tare da umartan shi ya dawo ya zauna za suyi magana.
Zama yayi Yana sauraren ta, inda ta sanar mai da maganar had'a auren shi da MUFEEDA!
A razane ya mik'e cikin matuk'ar tashin hankali yace"Mommy Dan Allah Kar kice haka Ina son Mata ta, Kuma ni bani da sha'awan auren Mata biyu, please Mommy Kar kiyi min Haka"
A fusace tace"shut up bana son Jin komai Dan ba shawaran ka nake nema ba wannan umurni ne"
Kamar zaiyi kuka yace"No Mommy please don't say that, I really loved her"
Daka mai tsawa tayi tace"get out of here nonsense, yanzu Kai Dan baka da kunya har zaka kalle ni kace Wai kana son matar ka, idan ba rashin kunya ba"
Ranshi a b'ace ya nufa upstairs. DEEJA na kwance Dan har ta fara barci sai gashi ya shigo, da sauri taje ta rungume shi tare da sakar mai kiss a kumatu, daurewa kawai yayi baya son ta gano wani Abu, sai da yayi wanka yasa pyjamas sannan ta kawo mai abinci, da k'yar ya iya cin abincin, sannan suka kwanta barci.
DEEJA jikin ta yayi sanyi domin ta lura akwai abin da ke damun shi, Zama tayi cikin shagwab'a tace" nifa na lura akwai abin da ke damun ka, kawai you don't want to tell me ne"
Zama shima yayi tare da hugging d'in ta yace"no baby babu komai, kawai aiki ne yayi min yawa a office, that's why"
Tace"are you sure?"
Kiss d'in forehead d'in ta yayi yace"very sure my baby"
Nan suka shiga duniyar ma'aurata, Bayan sunyi wanka har DEEJA tayi barci Nan ya zauna Yana ta tunani Cox shi gaskiya baya son MUFEEDA yarinyan Bata da tarbiyya ko k'adan Kuma sannan Yana tunani Dan yasan DEEJA baza ta yarda ba, gashi idan tak'i yarda YAYAN TA zai k'i yarda shima, dole yasan yanda zaiyi Kar auren ya yuwu.a Haka ya kwana cikin tunani da bak'in ciki.
An d'auki tsawon sati biyu, Amma Sam ASHRAF da MUFEEDA sunk'i yarda, gashi baya son DEEJA ta sani.
Matar SAIF ta haihu, ASHRAF da kanshi ya Kai DEEJA, ai ko tunda taga baby'n taji tana son haihuwa ita ma, yaron kyakyawa, Bayan sun dawo gida Haka tasa ASHRAF a gaba da kuka sosai fa.
Yace"baby Wai mene ne?"
Cikin kuka tace"ni wallahi baby nake so, Gaskiya kayi min ciki Nima in samu baby irin nasu SAIF"๐ซ
Habawa ai bai san lokacin da ya fara dariya ba, maganar ta ya bashi dariya yace"I'm sorry baby, Allah shine mai bayarwa, Dan Haka muyi addu'a Allah ya ba mu"
Tace"to tashi mu Fara salla Dan gaskiya Ina son baby, inyi ta Mata wanka da kwaliyya"๐
Nan dai sukayi ta addu'a.
Washegari da Rana
Mommy ce ka fad'a ma Aunty MEERAH auren da zasu had'a na ASHRAF da MUFEEDA, sosai tayi mamaki Kuma gaskiya bata son auren domin tasan MUFEEDA Bata da tarbiyya, Ashe DEEJA na jinsu Wanda shigowan ta parlour'n kenan, ai wani iri ihu ta tayi, da sauri su Mommy suka kalle ta, inda Mommy tace"ke Baki da hankali ne? Zaki zo kina Mana ihu?"
Da sauri DEEJA ta rik'e k'afar Mommy tana kuka tace"Dan Allah Mommy Kar kiyi ma ASHRAF aure, wallahi Ina son shi, Dan Allah kar kisa ayi min kishiya"
Ture ta Mommy tayi tace"you are very stupid, dole sai yayi aure Dan na tsane ki"
Idanun DEEJA jajazur ta kalle Mommy tace.................