100-101
by @nuceeyluv
ยฎ *OMAR* *KO* *FAROOQ* โ
100_101
๐ก๐๐ป *GAREKA* *ADMIN* *AMIR* *TAFIDA* *INA* *GARGADIN* *KA* *DA* *BABBAR* *MURYA* *KA* *DAINA* *MIN* *EDITING* *KANA* *MAKA* *SUNAN* *KA* *A* *MATSAYIN* *KAI* *KAYI* *TYPING* *idan* *sunan* *naka* *kake* *son* *sawa* *sai* *ka* *kirkiri* taka basirar ka rubuta naka novel din dan kaji dadin sa sunan ka. _bawai_ _nayi_ _typing_ *Wani* *KATON* *YA* CIRE SUNANA YASA NASHI BA HOPE KA FAHIMCE *NI*????
"Omar saida ya gama yangar sa sannan ya ajiye cup din batare d yace wa imaan komai ba. "Imaan kam tana ganin ya aje tayi saurin jawo cup ta hada nata tea din, ahaka tayi ta tura abincin da sauri dan wani irin azababben yunwa takeji, saida taji ta damm sannan ta kwashe kayan ta bar side din omar. "Sai dare sannan sukabar gidan kafin subar gidan kuwa saida mummy ta durawa imaan tsumi da turarukan kamshi, sannan tayi mata fada akan ta dinga cin abinci ta daina wahalar da kanta sosai itadai imaan saidai tace toh dan ita kadai tasan wahalar da take sha wajen ya omar.
*****
Gidan jiya ma'ana tunda suka koma gida imaan ta koma bakin aiki kr2n ma sai dare take samu tayi, yanzuma duk idanunta sun kankance sbd rashin bcci.
"Bangaren omar kam sha'anin sa yake hankali kwance, idan mummy ta kirashi ya dinga takurawa imaan sai yace yana iya bakin kokarin sa. "Saukowa yake hankali kwance, harya zo falo ya zauna abunda ya saba ya kunna yana kallon 'yan kwallo. "Imaan na waje ta gama shara tana bayin flower duk ta bude da kurar shara tayi butu2, taji anyi sallama, lkcn data dago ido ta kalli wacce tayi sallamar harta yi hanayar falo, imaan tayi mgn da dan qarfi tace baiwar Allah.... Bata qarasa mgnr ba ganin wacce ta juyo ce yasa ta washe baki tana dariya batare datace komai ba. "Matar ta tako tana kallon imaan kallo na mamaki da al'ajabi... Imaan ta katse mata tunanin da fadin lale marhaban Anty ameera INA ya farooq din? Wacce aka kira da Anty ameera tasa hannu tana goge ido dan tabbatar wa kanta gsky dan da farko tayi zaton 'Yar aiki CE., imaan ta ajiye abin bayin fulawar ta karaso wajen ta tace kiyi mgn mana Anty ameera duk Wanda ya lura da yanayin imaan tabbas zai tabbatar tana mgnr ne cike da farincikin ganin ta. "Anty ameera dakyar ta iya furta imaan anya ba mafarki nake ba? Imaan cike da rashin fahimta tace mekika gani? Anty ameera tace kalleki fa imaan kamar ba imaan 'Yar mummy me kwalliyar nan Dana sani ba, INA ma'aikatan gidan naga kina bayi da kanki? Sai yanxu imaan ta shiga duba jikin ta duk yyi kura kasancewa jiya anyi hiska gidan yyi kura, cike da tausayin kanta ta dago tana kallon Anty ameera saidai ta kasa cewa komai. "Anty ameera tace tunda na ga kinyi shiru lalle akwai mgn a kasa, nan ta fara karewa imaan kallo sai yanxu ta hango uban ramar data zabga ga baki da tayi. "Kafin tace wani Abu sai ganin imaan tayi ta kece da kuka. "Anty ameera ta shiga rudani tace ke lpy? Imaan cikin kuka tace dan Allah anty imaan Ku kawo min agaji wlhy INA cikin wani hali. "Yah salam anty ameera ta furta tace kinga share hawayenki mu shiga daga ciki sai kimin mgn a tsanake.
"Imaan ta share hawayen ta da murmushi tace muje. "Haka suka shiga falon hade da sallama, "omar yanaji dake imaan CE tayi sallamar ko kallon kofar beyi bare asa ran amsa warsa. "Anty ameera ta saki baki tana ganin ikon Allah, tasan sarai omar yaji sallamar Amman ga mamakin ta taga ko juyowa ma baiyi ba, imaan kuwa daman batasa ran amsawar saba, dan haka taja hannun anty ameera da niyyar su haura sama, keeeee taji ankira imaan tayi saurin sakin hannun anty imaan har tana hada kafa ta nufi wajen omar ko be ambaci sunan ba tasan da ita yake. "Anty ameera tsananin mamaki ne kawai ke mata yawo a ido. "Kafin omar yace wani Abu, anty ameera ta karasa wajen tana fadin a'a twin bro hala baka lura da zuwa na bane. "A razane omar ya juyo yana kallon ameera dake tahowa wajen, baki na rawa na rashin gsky yace am..a..sannu fan Matar bro.. Tun yaushe kika zo? Ameera tace tun dazu mana..tare da imaan muka shigo ai bayan ta gama bayin flower, omar yahau Sosa kai hankalin sa a tashe ga wata irin kunya data lullube shi domin Allah kadai yasan karyar da yake sharara2 musu ita d farooq idan yaje gidan idan suka tambayi imaan sai yace tana bcci ko tana kallo, wata rana anty ameera tace anya ma tana muku abinci? Sai yace haba ai saidai na girka mata dan banason ta da wahala.....ganin ya shiga tunani anan ameera tasa ayar tmby? Katse masa tunanin tayi da fadin toya Hutu, omar yace am..lpy.. Toh ..INA farooq din? Ameera tace ya tafi sauri yake ai da tare zamu shigo. "Omar yace OK..OK..OK.. Ameera tace bari dai na Baku waje dan naga dazu ka kirata. "Omar ya tashi yana hada wayoyin sa yace a.a shikenan kawai, bari dai ni nabar muku gidan. Ameera tace haba dai dan Nazo saika fita? Omar yyi murmushi yace No prob.. Yana fadin haka yabar falon da sauri.
********
"Fitar omar,anan anty ameera ta kalli imaan da tayi zuru tana kallon ta. Anty ameera tace imaan rashin lpy kikayi haka? Imaan ta girgiza kai. Tace toh meya saki wannan ramar lpyr? Ga wani irin baqi da kikayi? "Imaan tayi murmushin takaici sannan tace Anty ameera lbrina me tsawo ne bari na kawo miki abin sha. "Nan ta mike taje fridge ta dauko mata lemo sannan taje kitchen ta dauko cup, sannan ta kawo gaban anty ameera. Ameera bayan tasha lemon ta kalli imaan tace na kosa ki bani lbrinki kamar yanda kikace. "Hawayen dake makale a idon imaan shiya ida zurarowa kan kumatun ta, sannan tace anty ameera.............nan ta kwashe komai ta fada mata na irin wulaqancin da omar yake mata har zuwa yanzu.
"Tsananin firgici haka anty ameera ta shiga cike da tsantsar tausayin imaan daya dirar mata a zuciya, ko Kadan bata ta6a kawo omar zai aikata abinda yyiwa imaan ba koda rabinsa ne. "Cike da tausayi ta kalli imaan, sannan tace Abu na farko dazan CE maki shine kiyi hakuri da halin da kika tsinci kanki a wannan gidan, sannan inaso ki cire tsanar omar da kikayi a ranki na tabbata koda a hospital dinnan ya kula daku tabbas idan lkcn mutuwar ummanki tayi ba makawa saita yishi, ya kamata ace kin rungumi kaddara. "Kodan rikon da mahaifiyar su ta miki tsakani da Allah yaci ace kin cire tsanar shi a ranki, shikuma duk abinda yyi maki da sannu zaizo ya nemi yafiyar ki. "Sannan ki cire wannan tsoron da kike masa dan ba Aljani bane. Haba imaan kamar ba mace ba? Ai duk taurin kan da namiji mace kadai CE zata iya tankwasa shi, haddai da omar yake kiranki jaririya kinga kenan ya raina halittar ki kenan ko? Toh bakiyi abinda zai jawo hankalin sa bane. Dan duk wannan girman kan nasa tuni zai ajiye shi a gefe.
"Imaan taja numfashi sannan tace naji duk abinda kikace anty ameera but banji zan iya cire tsanar shi a raina ba..ameera tace haba imaan kamar ba musulma ba? Kinsan sairai babu kyau musulmi ya kullaci dan uwansa ko? Ai basai kin kullace shi ba a hanakli zaki zazzage abin bacin ran da yyi maki cikin sauki, bayan haka zakice bazaki yafewa Wanda ya baki jinin da kike rayuwa dashi ba? Imaan ta zaro ido tace wanne jini? Ameera tace zakice min bakisan da jinin omar kike rayuwa ba? Imaan ta girgiza kai alamar bata sani ba..ameera ta sanar mata komai kamar yanda taji daga bakin farooq saidai ta boye da yanda omar din ya bada jinin dan so take ta gyara musu zamantakewar su. "Jikin imaan yyi sanyi jin da jinin omar take rayuwa sai tace insha Allah zan cire tsanar shi a zuciya ta. "Anty ameera tayi murmushin jin dadi yauwa koke fa yanzu kika fara hawowa layi, Abu na gaba inaso ki shirya muje na siyo maki kayan da zakiyi yakin kwato 'yancin ki a matsayin ki na Matar aure. Imaan tace wanne kaya kuma? Ameera tace kedai shirya bari na kira mazajen namu na sanar musu. Imaan ta tashi ta haura sama tana tunanin wanne kaya anty ameera zata saya mata na yakin kwato 'yanci.
Nuceey luv๐