Page 5
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 56*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call ***
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Cikin tashin hankali Zainab take kallon shi tana jin wani irin hajijiya na iban ta, amma ta dake tana masa mugun kallo ji take kamar ta saka, bindiga ta harbe shi ko ta buɗe idanunta ta ga ba shi a cikin duniyar.
" A.m ni ka saki saboda wata banza ba tare da ka damu da halin da zan shiga ba, saboda na duki ƴarka za ka sakeni? Bayan ka tabbatar mini da ban da matsayin da zan yi hukunci a kansu!" Sai kawai ta saka kuka sosai tare da kukan kura ta shaƙe shi, zuciyarta na gaya mata ta yi ajalin su duka, kafin ta bar cikin gidan.
Juwairiya da ta kifa kanta cikin tashin hankali tana jin wani irin takaici na A.m da ya yi sakin ba tare da ya yi tunani ba.
A lokacin da ya buɗe baki zai faɗi sakin, ta yi maza da azama ta matso za ta rufe masa baki, amma sai Zainab ta ture ta tare da shaƙe shi, don haka sai ta matsa ta yi shiru kawai, in da ta ji daɗi ba saki uku ya yi ba, sai dai kuma abin da take yi tabbas zai saka shi ya yi duka.
" Matsa ki ba ni guri munafuka masu bin boka Allah sai ya wulaƙanta rayuwarki! Na raba ni da mijina da kika yi ba zan taɓa yafe miki ba." Zainab ta ce da ita tana mugun kuka mai ban tausayi, amma sai dai fuskarta ko kaɗan ba ta nuna alamun karaya ba.
Juwairiya ta saka kuka sosai tana kallon tashin hankalin da ke faruwa, domin Zainab ta shaƙe shi akan dole dambe take son su yi, duk da ta san cewa babu abin da za ta tsinta a kansa, musamman da yake cikin fushi.
" Don Allah A.m ka bari kaifa namiji ne bai kamata ka yi saurin furta saki ba, kuma tana da iko akan yaran ita ma yaranta ne."Ta ce cikin rashin jin daɗin abin da ke faruwa.
"Rufe mini baki munafuka karki ƙara saka mini baki banza mara zuciya, duk wani abin da ke faruwa sanadinki ki ne! Babu ruwana da waɗannan yaran domin a sanadinsu nake wulaƙanta, ji nake a halin yanzu kamar na saka bindiga na kashe su na tsane su."
Sai A.m ya rinƙa kallonta cikin tsananin mamaki yana jin wani mugun haushin ta." Tabbas ba ki da imani a cikin zuciyarki tun da kika nuna bakya ƙaunar yarana haka , bana sonki kuma ba zan taɓa zama da wacce ta tsani yarana ba, domin ina son su fiye da kowa! Ke bari in gaya miki ko da ace mahaifiyarsu ta yi musu haka ba tare da laifi ba, saina hukunta ta balle ke da ko ɓatan wata ba ki taɓa yi ba."
Ƙara jin wani tashin hankali ta yi jin abin da ya faɗa ta ƙara kai masa cakuma tare da fasa ihu." Kamar yadda ka tsane ni haka nake fatan na tsane ka A.m ka yaudareni ka ci amanar son da na yi maka! Da bakinka kake mini gorin haihuwa!"
Sai ta fara matsawa tana kallon yaran tana kallonsa ta kuma kai idanunta ga uwar yaran ta juya da gudu za ta fita, sai kuma ta dawo ta ce." Ba zan bar gidan nan ba sai na yi muku taɓo wanda ba zai taɓa gogewa a cikin rayuwarku ba, tun da ba ka duba halin da nake ciki ba, na Jonh ka sake ni so kake zuciyata ta buga."
Juwairiya ta firgita ganin yadda ta koma ta san cewa saki babu daɗi domin ta san dafin da yake da shi, amma yanayin da ta koma sai yi mugun tsorata ta, ta fara ja da baya saboda ba ta manta da halinta ba, in har tana cikin fushi, sai dai kafin ta yi wani yunƙuri ta ruga zuwa kicin ta buɗe tukunyar gas yana ta fita, tare da ɗauko ashana tana dariya kamar wacce ta zare.
" Zainab kar ki aikata haka wallahi in kika kashe mini yara sai na illata rayuwarki! Na san halinki sam zuciyarki babu ɗigon imani da tausayi, saboda iyayenki ba su ba ki ilmin addini ba, amma in kika bari wani abu ya samu yarana zan kashe ki fa." Ya faɗa da tsananin tashin hankali yana zare ido yayin da warin gas ya dame shi.
"Ba sai in ina raye za ka ɗauki hukunci ba! Kashe ku zan yi mu yi mutuwar kasko."
" Don Allah ka maida auren ku kar ta kashe mu ko ta illan ta mu." Juwairiya ta ce cikin kuka tare da kama yaranta ta rungume da suka yi cirko-cirko.
Cikin dubara A.m ya zagaya ta bayanta ya fisge ashanar tare da murɗe hannunta har sai da ta yi ƙasa, mari guda biyar ya yi mata ya saka ƙafa ya haure ta, saboda ji yake kamar ya yi ajalinta sam Zainab ba ta da hankali.
"Banza shashasha kawai mara tunani uban wani ya hana ki haihu ke kika illanta kanki da mugun son duniyarki, ga in da ya kaiki ya baro."
Zainab ta yi kuka sosai ji take tabbas A.m baya ƙaunarta duba ga irin cin mutuncin da ya yi mata, da ya ga tana mi shi hauka daga ƙarshe dukan ta ya shiga wanda ya ɗaga hankalin Juwairiya ta ɗora hannun ta aka tana janyo shi da yake dukanta kamar ya samu jaka.
" Ka bar dukan ba ka da imani A.m haka kake dukan mace kamar ka samu gardi? Ko da yake ba zan yi mamaki ba duba ga irin shaƙar da ka yi mini a lokacin.
A.m da idanunsa sun rufe baya ji kuma baya gani dukanta yake ba tare da tunani ba, har sai da masu gadi suka shigo cikin falon suka ƙwace ta.
" Ba ki da hali Zainab kin azabtar da rayuwata ba na sonki na tsane ki Zainab! Don haka ba zan ƙara zama da na..."
" Karka ƙara sakin ta domin na rantse maka in har baka zauna da ita ba, ba zan zauna da kai ba A.m, so kake duniya ta zage ni na raba aurenku." Ta faɗa cikin kuka tare da yin sufa ta toshe bakinsa.
Da ƙyar suka fitar da ita daga cikin gidan tana mai da numfashi da kyar.
Juwairiya ta duƙa cikin tashin hankali tare da rufe yaranta da hannunta ta saka kuka, tunanin ta duk ranar da A.m ya samu wata macen da yake so bayan ita zai iya mata abin da ya fi na Zainab duba ga irin rayuwar da suka yi, duk da cewar sun yi rayuwa tare da faɗa da rashin yi wa juna uzuri, amma ba ta manta kalar soyayyar da suka yi da ita, wanda suka kusa saka mata ciwon zuciya in ta gan su a tare .
Sai ta rikice ta kasa kallon sa wani irin mugun tsoronsa da ya cika mata zuciya.
Zama ya yi ba tare da ya kalli kowa a cikin su ba
Ɗaukar ruwan sanyi ya yi ya shiga kwarara wa cikinsa daga bisani ya dawo ya zauna, sai kuma ya kalli yaransa da suka yi tsuru-tsuru suna kallonsa, musamman Binaifa da ta ga ya canza mata.
Hannu ya miƙa musu amma sai suka saka kuka sosai Hasan ya ruga da gudu yana kiran."Momi."
Tun lokacin da ga fara dukanta yaran suke kuka suna kiran sunanta amma a lokacin ya yi nisa baya jin kira.
Tashi ya ya rike su Hasan ya kasa rarrashin su jin kukan yake kamar suna mi shi waƙa, saboda ya baya ƙaunar son ƙara zama da ita.
Kama yaran ya yi ya nufi inda take zaune ta haɗa kai da gwiya cikin jimamin abin da ya faru.
"Juwairaah ki kwantar da hankalinki babu abin da ta isa ta yi zan saka matakan tsaro ta yadda ba za ta iya cutar da ku ba."
" Ka yi shiru don Allah! Mene ne amfanin sakin da ka yi mata? Da wani irin ido zan iya kallon mutane na raba ka da ita, bayan duniya ta san cewa kun so junanku? In har kana son zama da ni to ka dawo da matarka! Karka manta har kyautar yaranka ka ba ta saboda soyayya ya kake son na yi da yaran da suka saba da ita."
Dafe kansa ya yi cikin zafi ya zauna sai kuma ya miƙe da nufin ya bi ta, amma ko da ya murɗa ƙofar ɗakinta sai ya ji ƙofar a rufe, ya yi bugun duniya ta ƙi buɗe masa, daga ƙarshe ransa ya ɓace kwasan yaran ya yi da suke ta kuka ya yi gidan Momi da su.
Juwairiya ba ta fito daga cikin ɗakin ba har lokacin kuka take yi tana tausayin Zainab akan abin da ya faru, sai da ta ji tashin motarsa sannan ta fito ta ɗaura girki duk a tsorace take gani take kamar za ta dawo gidan ta cutar da ita, da ta ga tsoron ya ƙi barinta sai ta rinƙa faɗin addu'a har ta ji ya ragu, ta kammala girki ta koma cikin ɗakinta tare da rufe ƙofa, burinta bai wuce A.m ya sauko ya dawo da Zainab ba shi ya sa take son ta yi fushi da shi, don ya haƙura.
Koda ya sanar a gida Abba kamar zai mare shi ya rinƙa kallon shi cikin takaici yana kallon su duka, da ɗa da uban sam ba su da hankali kan su kawai suka sani.
" Ban san ranar da za ka yi hankali ba!Na tabbata duk yadda kake son Juwairiya watarana za ka iya dukanta. Haba A.m da an yi maka abu sai duka kanka aka fara haihuwa so kake ka ɓata yaran, in har za ka ci gaba da dukan makusantanka don sun duki yaranka tabbas za ka iya ɓata tarbiyarsu." Ya ce da mugun takaici yana jin kamar ya kai mi shi duka sai ya koma kan Daddy da ya goyi bayan ɗansa, saboda ya ce ba zai so ɗan wani ya ƙi na shi ba.
" Karfa ka manta yarinyar nan ƴar amininka ce da wani ido kake son ka kalle shi? Ka san Allah ba zan ƙara saka bakina akan lamarinka ba, sai kuje can ku ƙarata."
A.m shiru kawai ya yi amma ba ya jin zai so ta dawo Allah ya haɗa ta da rabon ta kawai domin ya yarda ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda.
Ya daɗe sosai a gidan har sai da yaran suka sake ya kuma tabbata ta saki ranta zuwa yanzu ya kwashi yaran suka koma gida.
Zainab da take cikin tashin hankali ta fita daga gidan yayin da take ta kuka na ban tausayi, damuwa ta yi mata yawa ji take kamar za ta harbe kanta ta mutu.
" A.m ya sake ni Hannatu na rantse A.m sai ya gane kuransa sakina ya yi fa a gaban ƴar matsiyata! Ta ci nasara ta raba ni da mijina na shiga uku rayuwa ta juya mini baya." Ta ce tare da faɗa kan jikin hannu da tsabar tashin hankali ta saki wayarta ta faɗi ƙasa.
" A.m ya iya sakin ki saboda wata kai maza ba su da amana bayan duk tozarcin da ya yi miki ya haɗa ki da wata kishi, shi ne yanzu sai ya rabu dake." Sai ta ƙara sakin kuka dama mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashin awaki.
" Ina sonsa ya guje ni! Anya ya yi mini adalci kenan? A halin yanzu ina cikin tashin hankali bayan ƙare sauraren shari'a da John Daddy ya kirani zai tafi Dubai ya ɗauko lauyar da zai kare ni, in aji ina gani wani banza zai ƙwace mini asibiti, bayan yaudara ta ya yi ya turo wani ya yi mini tallar zuba hannun jari sai da na kwashe dukkan kuɗina zai bijiro mini da wannan maganar, tun ranar da Juwairiya ta dawo gidan nan A.m bai damu da halin da nake ci ba." Sosai take kuka kamar numfashinta zai ɗauke.
Hannatu ta yi shiru jikinta ya yi sanyi tsananin tausayinta ya kamata.
Da ƙyar take rarrashinta amma ta ƙi yin shiru sai kuka da take yi sosai kamar za ta mutu.
" Don Allah ki ki saka direbanki ya tuƙa ni a halin da nake ciki ba zan iya ƙara minti ɗaya a gidanki ba."
" Da kin bari ƙin ɗan ci wani abu duka yaushe muka rabu kuma bai kamata ki ɗau hanya a haka ba." Ta faɗa ganin halin da take ci.
" No don Allah ki barni na tafi." Duk yadda ta so ta tsaya ko abinci ta ci amma ta kafe kan dole ta haɗata da direba ya kaita gida.
Faɗawa jikin Momi ta yi ta saki ƙara amma babu ko ɗigon hawaye a fuskarsa, saboda kukan da ta ke ta yi a mota hawayen sun ƙafe.
" A.m ya sakeni baya sona ya fifita Juwairiya a kaina na shiga uku!" Momi ta miƙe a zabure cikin tashin hankali tana jin kamar za ta yi hauka.
" Kan uba! A.m ɗin ya sakeki akan wata banza can? Ai ko ba shi da mutunci lallai ya cika ɗan iska." Ta faɗa cikin jimami tana jin mugun tsanar Juwairiya, sai kuma ta saki tsaƙi tare da ture ta daga jikinta da jin haushin ta ta ce.
" Bacin son dake tsakanin ƴa da uwa ko kallon ki ba zan yi ba, shashasha kawai saboda sam ba ki san mai ƙaunarki ba, babu irin lallaɓarki da ban yi ba akan mu koma gurin Malam, amma kika ƙi saboda mugun kafiyarki Zainab ai ga irin ta nan, tsawon shekaru kina masa ɗawainiya da yaransa don mahaifiyarsu ta dawo ya wulaƙanta ki."
Sai kukanta ya ƙaru sosai ta janye jikinta daga gareta kamar yadda ta buƙata, amma sai ta koma ƙasa ta sa ihu tana birgima a ƙasa.
" Wayyo Allah kowa ya tsane ni mene laifina duniya ta daina rawa da ni? Ba zan ƙara bin boka ba don ba Malam ba ne wanda kike magana, kuma ban ga abin da ya yi mini ba sai ƙara matsala da ya yi, na tuba Momi ina roƙon Allah ya kawar da ni da bin Malamannan, don haka ki yi gaggawar tuba."
Momi takaici ya isheta sai ta yi maza ta shige cikin ɗakinta tare da janyo hannun Zainab da ta zama tamkar mahaukaciya, ganin da masu aikinta take wannan maganar.
" Na yadda ba ki da hankali tuni kika zare saboda son wannan mahaukacin, a gaban masu aiki kike wannan maganar so kike ki tona mini asiri?"
Zainab ta so ta yi wa Momi wa'a zi sai dai halin da take ciki ba zai ba ta dama ba hannun Momi ta haɗa duka ta ce.
"Ki gafarce ni Momi na san A.m ya yi mini butulci amma ki sani ba.."
" Rufe mini baki! In wa'azi kike buƙata maza ki je masallaci banza wacce ta kasa gane in da gabas ya dosa ba ta san ciwon kanta ba, ke har kina da bakin wa'azi bayan kin kasa yi wa kanki kika kashe ƙwayoyin haihuwarki, saboda tunanin ki na banza ga shi ko ƙwan kaza kin kasa haihuwa ballantana ɗan mutum." Sai ta rinƙa kallonta tana ja da baya cikin tsananin mamaki ta ce.
" Momiii."
Ta ja sunan tare da wasali har da yi mishi gunna idanunta ta rintse ta ce." Momi har dake a cikin masu yi mini gorin haihuwa, akan abin da na aikata kuma na yi kuskure na ke roƙon Allah ya yafe mini? Domin duk wanda ya yi mini baƙin ciki barin na ne, ni kaɗai na san halin da nake ciki dawowar Juwairiya don na gwammace na mutu da baƙin cikin da nake gani a gidan "
Ta ce tana kallon Momi da babu ko ɗigon nadama a fuskarta saboda tana jin haushin abin da ta yi, wanda take ganin kamar Zainab ita ta ƙirƙiri matsalarta da kanta.
" Na gode Momi daga yau duk wanda ya yi mini gori ba zan damu ba! Saboda mahaifiyata wacce ta tafi kowa sanin zafina take faɗin haka, amma ki sani duk abin da za ki ce ba zan ƙara bin bokaye ba, ina miki fatan ki gane domin in kika mutu a haka makomarki Momi ba za ta yi kyau ba."
Tsaki ta yi ta miƙe za ta fice daga ɗakin." Sai ki ta zama baƙin cikin ɗa namiji da na kishiya ya kashe ki,! Kuma ina mai gargaɗinki da karki sake kira mahaifinki ki gaya masa, saboda karki kashe mini mijina ina son shi, ki yi mini asara bayan ke kin yi sake wata ta ƙwace miki miji, mahaifinki na cikin tashin hankali na maganar Jonh a lokacin ba irin kashedin da ba mu yi miki ba kika na ce sai kin haɗa hannun jari da shi, ki bar shi ya ji da abu ɗaya in ya dawo sai ki gaya masa, tun da ke kullum ba kya rabuwa da matsala, kuma ba zan zama maigadinki a gidan nan ba, gobe zan wuce China daga nan sai mu dawo da mahaifinki."
Garam ta rufe ƙofa ta bar ta tsaye kamar an dasa shuka tana cikin mamakin canzawar Momi don kawai ta ƙi yarda ta bi bokaye.
" Allah ya shirya Momi da masu hali irin na ta wan can da na yi ina neman Allah ya yafe mini."
Faɗawa ta yi kan gado tana kuka mai sauti tamkar wacce ta ta shiga gasar kuka kuma ta dage sai ta ci.
" Ba zan zauna a gidan ba da zarar kin tafi zan tafi Abuja gidan Anty Batula." Ta ce tana jin ɗacin rabuwa da ita da A.m ya yi zafin har cikin ƙoƙon ranta, wanda yake haɗa zazzafan zafi mai kama da zai ƙona fatar jikinta, nan take jikinta ya gashe har shuci mai fitar da tiriri take yi.
Duk halin da take ciki Momi ba ta damu da ita ba ta yi kuka sosai kamar idanunta za su faɗo, kullum tunaninta yanzu shikenan ta bar mata A.m kenan? Mijin da tafi so fiye da kowa a rayuwa, in ta tuna haka tan ji kamar za ta kashe kanta.
Sati ɗaya da dawowarta gida Momi ta shirya ta tafi Ƙasar china wanda daga can za su dawo da Daddy.
Gidan sai ya rage daga ita sai tarin ɓasu aiki ganin haka kwana biyu da tafiyar Momi ta shirya ta wuce garin Abuja gidan Batula, kamar yadda suka tsara.
Batula na ƙoƙarin kwantar mata da hankalin sosai tana nun mata in har ta gama inda za ta samu duk irin mijin da take so.
" Dubi yadda Allah ya yi miki kyau Zainab babu ɗa namijin da ya isa ya raina ki mahaifinki na da kuɗi ga ilmi da iya kwalliya sai kin sha mamakin namijin da zai aure ki." Ta ce mata tana share mata hawaye.
Irin waɗannan kalamai yake ɗan kwantar mata da hankali ta ɗan fara sakin jikinta, burinta Daddy ya dawo ta sanar mi shi.
Zainab ta fara gajiya da zama a gidan Anty Batula saboda mijinta irin mafaɗacin nan ne ko cokali aka ije zai ce ba a ije daidai ba, duk da ta san halin shi sai dai ba za ta iya zama a gidan da yake kullum cikin ihu yake mata har da zagi kuma haka nan take daurewa tana nuna ba ta damu ba.
Ta saka a ranta in har cikin satin nan basu dawo ba, za ta koma gida ta jira dawowarsu.
Tana zaune a falo ta rafka tagume tana kallon tashar zeeyworld suna shirin fim na soyayya ba tare da ta sani ba, hawaye yake bin ƙuncinta tuna wa da A.m da ta yi.
Wayar Anty Batula da yake ta ringing ta miƙe don ta kai mata da take cikin kicin tana ba masu aiki umurnin abin da za a dafa.
Ganin numbar Momi da sauri ta ɗauka burinta bai wauce ace sun dawo ba.
Ɗagawa ta yi ta ƙi magana jin haushin Momi ba ta kirata a wayarta ba.
" Hello muna magana da yar'uwar mai wayar nan ne? In ita ce don Allah ta zo asibitin Murtala dake Garin Kano sun yi hatsari a jirgi ita da mijinta Allah ya yi musu rasuwa."
Wani irin ƙara Zainab ta saki kawai sai ji ta yi
ta yanke jiki ta faɗi ƙasa babu numfashi.
Jin faɗuwar ya saka Anty Batula ta rugo da gudu ta ɗauki wayar jin har yanzu ana magana a wayar ba tare da an yanke ba, sai dai ba ta gama jin maganar ba ta yanke jiki ta bi jerin Zainab da take ƙasa babu alamun numfashi.
ALLAH SARKI ZAINAB WALLAHI SAI DA NA YI HAWAYE MUTUWAR IYAYE BA ABU BA NE MAI SAUƘI BALLE A HALIN DA KIKE CIKI.
KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.
BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU
JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY
TALLAH!TALLAH!!TALLAH!!!
INA ƳAN MATA DA MATAN AUREN DA SUKA SHAYAR SUKE SON MARTAR ƘIRJIN SU YA DAWO?
INA MATAN DA SUKE FAMA DA RASHIN ƘIBA KO INA A ƘAME?
MAZA GARZAYO KI SIYA INGANTACCEN MAGANIN GYARAN NONO DA ƘIBA,MAGANIN AN RIGA AN GWADA KUMA YA NA DA AKYAU ƘWARAI.BARI IN GAYA MIKI YAR'UWA DUK WADDA TA CE MIKI MARTABAR ƘIRJINKI,ZAI DAWO MATUƘAR JIKINKI BAI MURJE BA,TO GASKIYA KUƊIN KI KAWAI ZA TA CI.
IN HAR KINA SON MAGANIN YA YI AIKI A JIKIN KI SAI KIN DAURE,KIN SHA SAFE DA YAMMA.SANNAN MUNA AIKAWA KO INA SIYAN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA.
MAGANIN AKAN FARASHI MAI TSAUƘI IN KINA SO MAZA GARZAYO KI KIRA WANAN NUMBAR ( ***) KO (***)
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba ***_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
COMMENT,READ FOLLOW READ AND SHARE.