SAKACINA KO HALIN MAZA

Page 16

by @jamilalawalzangojamcy

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*   




 *RUBUTAWA:-*

 *JAMILA LAWAL ZANGO*


          *SADAUKARWA GA:-*


 *SUMMY M NA'IGE*

       _(Aminiya)_       


    

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*


             *Page 16*


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! 

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I'm

 selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* 

Whatsapp OR

Call ***




BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM



Jikin Baba Sani ya na rawa ya dawo gida don murnar kuɗin da Daddy ya biya a matsayin sadakin Juwairiya,da ga gurin ɗaurin auren ɗakinsa ya wuce sai da ya yi fasalin kuɗin ya cire kuɗi kaɗan da nufin zai bawa Juwairiya sadakinta,wan da sauran ya saka su a aljihunsa murna cike a zuciyarsa, ganin irin yadda rayuwarsa ta canza lokaci guda kuma duk a saboda Juwairiya.


Ya yi kiran Juwairiya da take girki duk da damuwar da yake ranta amma ta na jin daɗin yadda Mama ta samu sauƙi jikinta ya yi sauki,ga kuma Ibrahim da shi ma an yi masa aikin a ƙafar sa ya samu sauƙi sai wani daɗi ya mamaye mata zuciya har take girkin da kula ta na son Mama ta ci abincin sosai.


Kiran da Baba Sani ya ƙwala mata ya sa ta ji gabanta ya faɗi ras!Don ta san yanzu in dai zai kira ta to akan maganar auren ne.Cikin saiɓin jiki ta amsa tare da saurin zuwa gurin sa.


" Amaryar shekara ɗaya yaufa an ɗaura auren ki da A.m ɗazu."Ya faɗa tare da miƙa mata kuɗi.

Wani irin zufa ya keto mata da sauri ta dafe ƙirjinta." Na shiga uku."A bin da ta ce kenan sai hawaye suka fara turereniya a ƙuncinta.


Miƙa mata kuɗin ya yi amma sai ta ƙi amsa tare da shigewa cikin gida hankalinta ya tashi sosai ganin da ga yau ta zama matar A.m.

Tun da ya gaya mata maganar ɗaurin aurenta ta shiga cikin wani hali na rashin natsuwa gabaki ɗaya ta ruɗe,ta na cikin waswasin tunani sai ga kiran sa ya shigo da ta tuna yau a matsayin mijinta ya kira ta kuma ba ta san me zai ce mata ba sai ta ƙara ruɗewa.

Daga bisani kashe wayar ta yi gabaki ɗayan ta ta kai ta ɗakin ta in da take ɓoyewa kar Mama ta gani.Ta koma gurin girkin ta da take tunanin kar ya ƙone.

Sam ta manta ta saka gishiri a girkin ba tare da ta tuna ba kawai ta ɗauki gishirin da nufin ta zuba ba,ta sai ta gishirin a tukunya wanda hannunta ya zame ta juye shi duka sannan kuma a lokacin ta tuna ta riga ta saka gishiri.


Kawai sai ta fashe da kukan da ta kasa gane saboda juye gishirin ne take kuka,ko kuma a kan maganar da Baba Sani ya gaya mata ne oho.



Mama da ke falo ta na shan magungunan ta sai ta ji kukan Juwairiya da ƙarfi ta na rera shi kamar wata ƙaramar yarinya duk da jikinta ba ƙarfi, amma hakan nan ta daure ta fito ta na dafe bango a ranta ta na mamakin mai ya saka ta kuka haka.


     "Lafiyar ki kuwa?"

Ta ce a lokacin da ta ƙaraso gurin sai ta yi turus! Don ita hankalinta ya tashi ta ɗauka ƙone wa ta yi,amma ganin lafiyarta ƙalau sai hankalinta ya kwanta 

Ganin ba ta amsa mata tambayar da ta yi mata ba.

Kama ta ta yi ta riƙe tare da shigar da ita cikin ɗaki saboda kukan da take yi ya tsorata ta." Ki yi shiru don Allah ki dai na kuka kin san abin da likita ya gaya min,yanzu haka dalilin kukan ki ba ki ji yadda zuciyata take bugawa ba."Ta faɗa tare da dafe ƙirjinta da yake harbawa da ƙarfin gaske.


Ganin haka hankalinta ya tashi da sauri ta share fuskarta duk duk yadda ta so ta ƙaƙaro murmushi a fuskarta,amma hakan ya faskara wasu sabbin hawayen da suka ƙara yin matsuguni a fuskarta.


" Mama don Allah kar ki saka damuwa a ran ki.Girkin ne ya bani haushi saboda na manta na zuba gishiri kuma na zo na ƙara shi ne hannuna ya goce na juye duka."


Dariya Mama ta yi ta ce." Juwairiya wacce ta iya girki komai auna wa ake shi ne yau ta yi juye lailai yau hannu ya ƙwace kenan.To ai ni ban ga abin kuka ba sai dai in a kwai abin da kike ɓoyewa."


Gaban Juwairiya ya faɗi jin Mama ta na so ta ɗago ta sai ta yi sauri ta tsaida hawayen ba shiri."Iya kan abin da ke damuna Mama kenan haba dole na yi kuka bayan tsawon jinya da kika sha a ƙasar waje,yau za ki ci girkina ga shi hannu ya ƙwace min."


Mama ta koma ta zauna ta ce " To ba sai ki ɗora wani ba."Ai da sauri ta miƙe tare da faɗin."To." ganin yadda Mama ta kafe ta da ido haka kawai sai wani irin kunya ya lulluɓeta har ta ji ta kasa haɗa ido da ita.


  " Ok bara na je na ɗora na san yunwa kuke ji."Ta faɗa ta na shafa kan Ibrahim da ke zaune ba ya tafiya saboda likita ya ba shi lokacin da zai fara tafiya.


"Juwairiya dawo magana zan yi dake."Mama ta faɗa tare da lumshe idanunta da su kai mata nauyi.

"Mama don Allah bari na gama girkin kar yunwa ta dame ku ga Ibrahim har ya fara yaushi."

Ta ce cikin in ina ta na son ta kauce ma idanun Mama." Kar ki damu da dawo kawai akan mutumim nan bawon Allah da ya ke taimakonmu,na ke son mu yi magana ni fa kullum tunanin sa nake yi ga shi ya ƙi bayyana kan shi,bare mu yi masa godiya an ya saboda Allah yake mana ni fa na fara shakku a raina.".

Juwairiya ta firgita da maganar da Mama ta yi mata ta san da ma dole ta yi mata waɗannan tarin tambayoyin game da kuɗin da A.m yake kashe musu ya wuce misali.


Ganin Mama ta fara zargi a zuciyarta sai ta daure ta kauda duk wani tsoro da shakku a ranta,ta kalli Mama da natsuwa ta koma ta zauna ta ce." Mama ki yi masa kyakykyawar fahimta kin san irin tarin kuɗin da suke da shi,sannan da zai cuce mu kuɗin ba zai biyo ta hannun Baba Sani ba.Don Allah ki kauda komai a ranki kuma in ma sabon gidan da ya gidan da ya siya mana ne ba kya so sai a mayar masa."

Da ƙwarin gwiyarta take magana saboda ta yi tunanin yanzu ita ace za ta din ga buga ƙwallon a raga kuma in ba ta jajirce ba Mama za ta ɗago ta wanda hakan zai ɓata shirin su.



"Lamarin duniya a kwai tsoro ke yarinya ce amma ba zaki gane ba kuma da kike maganar Baba Sani ai duk kanwar ja ce,ke sheda ce akan halin sa kin san irin halaccin da mahaifin ku ya yi mishi amma ya manta ya kasa tallafar rayuwarmu,shirun da kika ga na yi hakan ya samo asali ne saboda alƙawarin da na yi ma mahaifin ki wanda ya tilasta min na yi masa daga baya na zo ina dana sani,amma wallahi kin ji na rantse da ban yi ma mahaifin ki alƙawari ba da na ɗauki mataki akan yadda ya hana rayuwarmu saƙat."


Ta ce ta na kallon Juwairiya da ta firfito da idanunta ganin yadda Mama take magana, saboda tsawon rayuwarta fa ita ba ta taɓa jin ta ɗaga harshe ba,sai yau lamarin ya matuƙar razana ta har ta fara dana sanin amincewarta don da wuya shirin su ya tafi ga shi A.m ya kashe kuɗin sa.

Mama ce taci gaba da magana ganin ta yi shiru ta na zare ido sai ta ce." Wa ya sani ko kuɗin kammu muke ci."

Yayin da tsoro ya ƙara kamata tuna yanzu duniya ba gaskiya.


" Da ma Baba Sani zai yi miki bayani Mama ni ne na ce ya bari ki ƙara samun sauƙi Wato shi mutumim da yake taimaka mana ya auri matarsa wacce ƴar majalisa ce. To gabaki ɗaya rayuwarta ƙasar waje ta yi karatu,ta samu gata sosai wanda hakan yake saka suna samun saɓani ga shi ba ta iya girki ba komai ba ta yi."


Ta yi shiru ta na son ta ji ko me Mama za ta ce amma sai ta ga ta tsaya ta harɗe hannunta a ƙirjinta ta na sauraren wannan tatsuniyar ita tunanin ta to meye haɗin ta da wannan dogon labarin wanda take ganin ina ruwan ta da labarin sa.


Juwairiya ta rasa in da za ta kama ta ci gaba da zancen a wannan lokacin ji take kamar ta ɗora hannu ta yi ta kuka ganin yadda Mama ta kafe ta da ido.


" To saboda wannan ne ya na son a koya mata abubuwa da girki yake son ya s..."Juwairiya da ta ci gaba da magana sai kuma ta tsaya tare da sakin kuka wanda hakan ya ta da hankalin Mama, amma sai ta yi shiru ta na kallonta yadda take kuka mai sauti.


" Shi ne yake son mace wacce za ta zauna a gidan shi na shekara ɗaya ta koya ma matarsa girki da yadda ake kula da gida,na tsawon shekara ɗaya kuma duk wacce ta amince za ta yi zai tallafa ma rayuwar su,ban san tsinannen da ya gaya masa halin da kuke ciki ba har ya zaɓi Juwairiya a matsayin wacce za ta yi,don wallahi da na sani ba zan bari ba ai gara na saka ƴata."Muryar Baba Sani suka ji ya na magana a bakin ƙofa.


Mama ta ji wani irin juwa ya kamata murna za ta yi ko farin ciki amma kuma Juwairiya ta din ga yawon aikatau kenan?Juwairiya a yanzu ya kama ta ace ta na ɗakinta,sai dai kuma mutumim ya yi hidima ga rayuwar su wanda wani ɗan'uwan ka ba zai iya haka ba.



Ta buɗe baki da nufin ta nuna rashin amincewarta amma sai ta kasa saboda ya yi musu halacci haka kawai sai ta ji ba za ta iya musawa ba,amma ranta ta saka dole in Juwairiya ta gama aikin ta za ta yi aure da irin mijin da take so ko da hakan zai saka ta karya alƙawarin da ta yi ma marigayin mijinta ne don za su raba abin faɗi ƙila kutu za ta raba su,saboda haƙurin abin da yake mata wanda sakamakon hakan ya sa zuciyarta ta buga.


Juwairiya ta shiga tsananin mamaki gani Mama ba ta ƙara ce mata komai ba ta takure gefe zuciyarta cike da tashin hankali,wani irin zazzaɓi ya rufe ta sai makyarkyata take hawaye ya na zuba a ƙuncin ta.


Mama ta yi jim da kofi a hannunta bayan ta ba ta magani tasha." Ni fa hankalina ya tashi Juwairiya ke ma kin yi gangancin karɓar wannan kwangilar duk da hakan ya tseratar da ke da ga auren wannan tsohon,amma kin manta irin wulaƙancin da dukan da kika sha a dalilin aikatau."


Juwairiya ba ta ce komai ba sai hawaye da suke shatata fuskarta.

Mama tace ta rasa wani irin tunani za ta yi akan maganar aikin Juwairiyar da za ta yi,kuma da ta nemi sanin waye hatta ita Juwairiyar ba ta gaya mata ba sai wani lulluɓin biri suke yi wa kare an ya? Akwa lauje cikin naɗi!Ta faɗi a zuciyarta cike da shakku.

Ta zauna a gefen gadon da take kwance tare da janyo mata bargo." Allah ya baki lafiya."Ta ce tare da zabga tagumi.


Wa su irin zafafan hawaye suka wanke mata fuska sai ta canza kwanciyarta saboda ta juya ma Mama baya." Ki yafe min Mama na san ban yi miki adalci ba,amma na yi hakan ne saboda na ceci rayuwar ku duk da hakan ni zai kai ni kushewata saboda ƙara kusanci da na yi da shi,shi zai jagoranci ruhina zuwa mutuwa.Allah na roƙe ka ka cire min son sa a cikin zuciyata."


*****



A.m zaune a tanƙamemen falon sa da remote a hannun sa gefe kuma Zainab ce take aiki da computa da ta ɗora a cinyarta,saboda gwanancewa da aiki da ita da ta yi ba tare da ta kalle abin da take daddannawa ba take aikin ta,yayin da hankalinta ya na kan A.m da yake ta jan tsaki ya na juyi a kujerar.


Talatu mai aiki wacce take sabuwar ƴar aikin da Mominta ta kawo mata saboda halinta sam ba ta daɗewa da me aiki.Ita ce ta yi sallama ta shigo idanunta akan A.m saura ƙiris ta yi ɓari amma sai ta ije ta ci gaba da kallon shi.


A.m wanda da ma hanya yake jira miƙewa ya yi ya kwasa mata mari ya ce." Wai ke wace irin mayyar yarinya ce ba na hanaki kallona ba!Banza ƙatuwa da ke maza fice min daga falo! Kuma yau zaki bar gidan nan."


Da sauri ta ruga ta na shafa gurin da ya mare ta don ta ji zafi sosai jikinta har rawa yake saboda ita duk ta gan shi,sai ta ji ta na son ya kula ta duk da ta san shi ba san ta bane amma ya na da kyan da duk mace za ta yi mafarkin samun shi.

Zainab kuwa tsaki ta yi a ranta ta ce." Haka kawai duk ka tsani ƴan aiki kullum cikin canza masu aiki muke wannan karan sai dai ka yi haƙuri amma ba zan canza ba."

Juya wa ya yi ya kalli Zey da ta daina aikin da take yi ta na kallon shi ya ce." Allah na tsani yarinyar nan ke duk masu aikin ki dangin mayu kike ɗauko wa,gaskiya ki sallame ta ni sam ma abincin ta ba ya min daɗi."


"To ni ya kake son na yi ko ni kake son na dun ga yi maka girkin?"Ta ɗan saki dariya ta ci gaba da magana ta na ce wa." In haka kake tunani gara ma ka cire har na yi aure ban taɓa shiga kicin da nufin na yi girki kai ko ruwan zafi ban iya dafawa ba,ka ga ya zama dole ka ci na ta in ba so kake ka ɗauko kuku namiji ba wanda da ma kafiyarka na tsiya da baƙin kishi ya hana ka,amma ni ban ga dalilin da ya sa ka za ka ƙi ɗaukar kuku namiji ba a gidammu su suke girki ni kai na na gaji da cin abincin masu aiki."



Wani kallo ya watsa mata ya ce." Zainab ki kiyaye ni da maganar kuku a haka yadda kike zama kusan naked ne zan ɗauko kuku,matan ma da suke kallon ki ni na san baƙin cikin halin da nake shiga sai dai na lura shashasha ce ke kin ɗauki rayuwar yahudu da nasara ba ki san darajar kan ki ba."


"To aiko ka na ruwa wallahi tunna duk yawon duniya da ka yi baka waye ba ni ban ga dalilin da zai saka kasa na din ga ɓoye kai na ba kamar wata ƙonannniya."

Ta ba shi amsa cike da gatsali ta na girgiza ƙafa.


" Ƙaryar iskanci kike tunna kin nuna ba za ki canza ta ba sai dai ki zaɓa ko aikin ko ki zauna ki rinƙa dafa min abincin da kanki,tun da na tashi na ga iyayena suna girki a gidammu amma ke saboda sakarci ki ce ba ki iya ba.Ki na ganin ƙannina duk sun iya girki ke na rasa wani irin tarbiya kika samu. "

Ta katse ta hanyar ɗaga masa hannu ta ce."Ka dakata kar abin ya zama cin fuska kuma da kake wannan maganar ai ka san wacce kake aure da matsayin ubana."


"Dallah rufe min baki ke ma kin san sai dai ki yi min gori na mahaifin ki ya riƙe muƙami,amma ba wai ko kun fi mu kuɗi ba iya tarbiya ne kawai da muka hora su da shi, saboda arzikin da muke da shi bai saka ya sa mun yi watsi da al'adarmu ta yi ma miji girki."


Tsaki ta saki ta ci gaba da aikinta ta na faɗin." Ai sai ka yi ba ka da aiki ne ni ina da abin yi kamar yadda ka gani."Ta ɗan ƙara sakin ƙaramin tsaƙi a hankali ta ce." Jarababbe kawai."


Ya kalle ta ya na baƙin cikin halin ta don shi bai yi tunanin halinta haka yake ba."Mu zuba da ni dake tunna baki da mutunci kuma da ga yau in kika ƙara zuwa wani guri bayan akin ki Allah y...."


Da sauri ta tashi ta waurgar da ƴar mini system ɗin dake hannunta tare da faɗawa jikin shi ta rufe bakin shi jin zai kafa mata dokar fita,in ta bari hakan ya faru ita kuwa ya za ta yi da zuwa pati da yawaon da suke da ƙawayen ta.


" Haba mai sanyina don Allah ka yi haƙuri karka faɗi haka kai ma ka san wallahi ban saba zaman gida ba,in ka hanani fita ya zan yi kuma ka san kai ma zaka saka Allah ya yi fushi da ni ne,amma na riga na saba da yawo ba zan iya zama guri ɗaya ba ko da ka rantse."


Ya kalleta da mamakin abin da ta ce ba yan Allah ya jarabce shi da sonta ya riga ya rufe mishi ido da sai ya ce bai yi dacen macen ƙwarai ba,amma so makoho har zuciyarsa ta sauko ya kalleta da shauki ya haɗa hannunta duka ya na murxawa da hannunsa don ya na ganin damar sa ne yanzu ya ce.


" Na lura don kin ga ina son ki shi ya sa kike wahalar da zuciyata Zey amma ba komai ina fatan Allah ya saka miki irin son, da nake miki a zuciyarki nawa zaki gane halin da na ke ciki."Ya faɗa ga mamakin ta sai ta ga yana hawaye.

Hankalinta ya tashi ta ƙara maƙalƙalewa a jikinsa ta na share masa hawaye saboda jikinta ya mutu murus da son sa.



" Ni ma fa ina sonka hubby kai ɗin ne ka cika faɗa ba ka min uzuri duk da ƙoƙorina da nake kuma ka san yanayin aikina.


Janye hannunta ya yi akan fuskarsa aran sa ya na faɗin." Na sani amma kuma hakan bai hana ki fita ba."


A fili kuwa sai ya saki ɗan murmushi kamar ba shi ya gama hawayen baƙin cikin Juwairiya za ta shigo duniyar auren su ba wanda ya ɗora laifin duk akan Zainab amma sai ya ce.

" To ki canza me aiki ni bana son wancan yarinyar k..."


Ta ƙatse shi ta na faɗin ."Na ji zan canza amma kuma Momi ta ce in dai muka kori wannan ba za ta ƙara ne mo mana mai aiki ba tunna ba ni da haƙuri."


" Kar ki damu dama tuntuni nake son na tambaye ki na yi ma Atine mai aikin gidammu ta kawo mana macce matashiya wacce ta iya girki sosai,in kin bani dama sai na gaya mata ta nemo mana kuma ba za'a daɗe ba, za ki ga ta kawo mana tunnna ita ma ta na irin kawo su kusan family mu ita take kawo musu masu aiki."


Ya ce tare da rungumeta ya na goga fuskar shi a na ta."Ok ba komai sai ta kawo mana amma ba za mu kore ta ba sai an kawo mana wata."


A.m hamkalinsa ya kwanta ganin bai sha wahalar samun haɗin kanta ba miƙewa ya yi ya shige ɗakin sa,ya gallah wanka ya fice kai tsaye gidan su ya wuce ya sami Atine mai aiki ya ce." Ina son in kika tashi zamu fita da ke zuwa wata unguwa amma ya zama sirri a tsakanimmu in kika yi min hakan zaki samu alkhairi."


"Ka faɗi ko mene ne in sha Allahu zan yi maka."


Ta ce cikin mamakin in da za su kuɗi ya zaro masu yawa ya ba ta.Atine jikinta na rawa ta karɓa ta na kallon shi." Wata yarinya nake son na nuna miki ki kaiwa Zainab a matsayin ƴar aiki.Shikenan buƙata ta kuma ba na son kowa ya sani kawai ki bar shi a matsayin ke kika kawota."


Duk da mamakin maganar da ta yi amma tunanin ta bai kai ko ina ba,ta amince masa akan sai ya zo daga ƙarshe watsar da tunanin ta yi don ta san ya wuce ƙarfin ya kula ƴar aiki ,kasancewar yadda ta ga ya na hantarar su bare ma ta yi tunanin wani abin.



********


A ranar da Juwairiya za ta tafi hankalinta ya tashi matuƙa wanda da Mama ta so taƙi kan ta din ga kwana duk da a kwai nisa sosai ta so Juwairiyar ta din ga zuwa ta na kwana har shekara ɗayan ta yi,amma sai Baba Sani ya kafe dole sai dai ta din ga kwana tunna kuɗi ya biya.


TO MASU KARATU GA DAI AMARYA JUWAIRIYA ZA TA TAFI GIDAN ANGONTA KO YA ZAMAN SU ZAI KAYA ?SAI KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN SAKACI KO HALIN MAZA.


             TAKU


       JAMILA LAWAL ZANGO



ƊUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ƊIN KU YA NA SAKA NI NISHAƊI.


MAMAN SUDAIS 

AISHATU MINNA

FATIMA ZARA JOS

SAHURA NURA RABIN RAINA

NABILA MAMAN SAFWAN 

HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM




 Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha shidda.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba ***_.



Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.

Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.







COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.