Page 19
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 19*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call ***
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
A.m ya shiga cikin tsananin tashin hankali ya juya ya kalli Juwairiya da take jin duk abin da yake faruwa,ga jikinta sai kyarma take yi har ta fara haɗa haƙori kaf!kaf!!
Sai tashin hankalin sa ya nunku ya kuma rasa tunanin da zai yi.Hannunsa ya sa ya tallabe kansa can kuma ya shiga shafa sumar kansa ya na tunanin mafita,don shi babban tashin hankalin shi da Zainab ba ita kaɗan za ta dawo ba ya san ce wa ta ce su zo ne su lallashe shi.
Wayar sa ya zaro ya yi kiranta ringing ɗaya ta ɗauka ta na kashe murya ta ce." Hello Habibina ai mun kusa ƙarasowa gidan..."
Wata uwar tsawa ya daka mata da ya firgita ta ya ce." Ni ko Zainab wallahi in kika shigo gidana na da waɗan nan dabbobin sai na yi miki mugun rashin mutunci,don haka ki ce musu ko wace banza ta kama gabanta tunna su mahaukata ne.Kuma zaki dawo zaki ga abin da zai faru! Allah ya sa su yi gigin shigowa gidan."
Da fushi yake magana tamkar ta na gaban shi don iya abin da zai yi kenan ya hana su shigowa cikin gidan.
Zainab ta yi shiru da waya sororo a hannunta, ta rasa ya za ta yi ga shi ta gama koɗa kanta ta isa da shi,don sun nuna ƙin zuwa saboda sun san halinsa ba kamar mazajen su yake ba.
" Kai direba tsaya wallahi Zauji yau rashin mutunci yake ji kun ji abin da ya ce."
Ta faɗa a kunya ce ta na kallon su.
"Mai ya ce ɗan rashin mutuncin?"
Anty Fati ta tamabaya don ta san za'a rina sanin hali."Gaskiya ko wace mace ta tafi gidan ta ku sauke ni anan kawai ina ga ƴan iskan ƴan uwansa sun zuga shi ne,amma da amincewar sa na tafi Dubai yanzu ya na faɗa min kar ku zo mishi gida ."
Ta faɗa a kunyace don ya ba ta kunya ga shi ta gama zuga musu ƙarya." Kar ki yadda Zey ya haɗa ki fita kin ga dai irin ribar da muka samu,ki nuna mishi turjewar ki."
Anty Fati ta faɗi cikin maganar zuga ta na son ta ƙara zuga ta don ta shirya duk abin da yake ji.
" Ke ma kin san halina kawai ba na son ya wulaƙanta ku ne ku je kawai ni wallahi akan sana'ta zan iya haƙura da aikin gwannati bare kuma ya ce zai kawo min cikas."
Anty Maryam da ba ta ce komai ba ita ma ta na tunanin abin da za ta tarar,in ta koma sai yanzu ta yi magana ta ce." To ki rabu da shi mana yadda kike da kyan nan ai kin san ki na fita za'a wawushe."
Wani mugun kallo ta yi mata tamkar za ta kai mata duka ta ce." Ka ji Anty Maryam da maganar banza ni da Hubbi ai mutu ka raba takalmin kaza! So kike na kashe aurena na je na auri mai mata ko wanda zai yi min kishiya nan gaba,hakan ma ba zai yiwu ba don ni da kishiya ko a lahira ba na fata kuma zan iya yin komai a kanta ni da ita yaƙi ne tsakaninmu."
"To ki tafi mana ga shi har yanzu ana yayyafi kuma kin buɗe mota kin tsaya ki na zuba,don kawai an miki maganar kishiya duk da family ɗin mu ba'a mana kishiya, amma Zey ki rage kishin ki to ke da mijinki ba ya haihuwa wace mace za ta zauna da shi ai sai ke ƴar wahala."
Dariya ta yi ta na ɗaga musu hannu ta ce da ƙarfi ta yadda za su ji ta don motar su ta fara tafiya." A huta gajiya a haka nake son abina kuma sai mutuwa za ta raba mu.Kayana zan shigo na karɓa."
Sannan ta juya da nufin ta shiga gida yayin da gabanta yake dukan tara!Tara!! Don ta san ba za su kwase da sauƙi ba.
A.m ya juya da nufin ya yi ma Juwairiya magana amma sai ya ga ba ta a cikin ɗakin har ya fara taku zai bita sai kuma ya dawo,jikinsa na rawa da shi kan sa ya kasa gane kansa ya na jin wani canji a jikinsa.
Sai kawai ya nufi cikin bayi don ya tsarkake kan shi ya yi salla amma sa ya fasa jin ana buɗe gida da alamun Zainab ce ta shigo,da sauri ya ƴarasa gurin windo ya buɗe ilai kuwa ita ce ta shigo da gudu saboda ruwa da yake dukanta.
Girgiza kan shi ya wuce cikin bayi da sauri don ya san in Zainab ta same shi a haka za ta fahimci wani abu,kuma rashin mutunci yake son ya yi mata sai dai yanayin da yake ciki na rashin ƙarfi ba zai ba shi damar yin hakan ba.
Ya jima a cikin bayi duk da kiran da Zainab take kwaɗa masa bayan ta shigo ganin ba ta gan shi ba,amma hakan bai sa ya ko ɗaga kan sa ba ya na ta tunanin da shi kansa in aka tsare shi ba zai ce ga dalilin tunanin ba.
Ikon Allah dama Baba Sani ƙarya yake yi wa Juwairiya mace ce mai nagarta da kamun kai?Haka kawai sai ya ji tsanar mutumim ya kama shi har ya na jin zai iya komai don ya taimaki rayuwarta.
Ko da ya fito faga ɗakin bai ga Zainab ba wacce ya tabbata ta ga ji da zaman jiran shi ƙila ita ma ta na bayi ta yi wanka.
Sallah ya yi da sauri don yau ne karon farko da ya rasa jam'i shi lokacin ne ya wuce gani yake yau gari ya yi saurin wayewa.
" Hubbyna oyoyo zuciya ta yi kewar ka da gangar jiki."
Ta faɗa lokacin da ta buɗe ƙofa duk da cikin tsoro take amma sai ta daure ta kauda tsoronta ta furta hakan,don ita a shirye take koma mai zai faru ya faru in dai akan fita ne saboda ta ji daɗin fitan sosai.
Wani irin mummunan kallo ya watsa mata wanda ya sa ta firgita ta tsaya tare da fasa rungume shi da ta yi ninya.
A.m da yake a zucciye da ita ya miƙe tare da fasa shafa addu'ar ya gaura mata mari ji kake kau!
" Banza mara mutunci ni zaki maida ɗan tasha ki tafi wata ƙasa ba tare da sanina ba ki dawo ki na min ilinbo ko.To wallahi sai dai ki zaɓa ko ni ko fita zuwa waje."
Zainab ta saka kuka iya ƙarfinta kamar yadda ta san ya tsani kuka tare da watsi da kayan shafar shi da suke jere a madubi ta ce.
" Ai wallahi ka mari auren ka ba sai na zaɓa ba dama na sha gaya maka duk ranar da ka ƙara marina sai na bar maka gidan ka!Don kawai na fita zuwa waje saboda ba ka wayewa ba za ka mare ni,da ka zo nai man aurena da ka yi bincike ba'a gaya maka Momina ta na fita zuwa waje saro kaya ba,ai kai ma ka san dole na yi sana'ar ta kuma in baka manta ba har jari Daddy ya ba ni lokacin da za'a kawo ni gidanka."
Da takaici ya kalleta ganin ɓarnar da tayi mishi ya matsa kusa da ita daidai lokacin da ta ruga za ta fita don ganin yanayin sa ta san dukan ta zai yi,amma sai ya yi nasarar kamota ya riƙeta kamar zai ɓallata.
" Zainab ba cin son ki da nake yi da rabuwa zan yi dake saboda baki da tarbiya ni kaina na yi kuskure da ban yi bincike ba,saboda mun ga Daddyna na tare da mahaifin ki ashe ƴar mace na aura.To bari kiji wallahi ba zan zauna dake a haka ba maza ki fice min daga gida mara mutunci kawai."Ya ce zuciyar sa na tafasa kamar za ta fito.
Ya saketa cikin rashin tsoro ta tsaya ta kuma kauda duk tsoron da take ji na sa tuna huɗubar da Yayyinta,suka yi mata cewar su ma duk sai da suka sha artabu da mazajen su sannan suka haƙura suka bar su.
" Na gode da cin mutuncin da kake yi ma uwata amma ka sani yadda ba ka daraja mahaifiyata ba ni ba babu wani da banza da zan daraja, kuma Daddyna zan kira na gaya mishi dukana kake yi mugu azzalimi mai dukan mace."Ta ce ta na kuka da ƙarfinta.
Wani marin ya kawo mata ya na faɗin ." Ok haka kika ce to bari na ƙara miki sai kiji daɗin faɗin kashe ki na yi,kuma yanzu zaki bar min gidana ba sai an jima ba ki je can ki sami shashasha irin ki ki aura,amma ni ba zan bar mace mafi soyuwa a gare ni ta na cuɗanya da wasu mazan ba ke ko kishin kan ki ba ƙya yi ...."
Katse shi ta yi ta na faɗin."Babu in da za ni wallahi ai nasan ɓaɓatun banza kake yi,amma ba zaka iya rabuwa da ni ba."
A.m ya zaro bell ɗin shi ya na kallonta ya ce " Tunna haka kika ce zan nuna miki halina baki san wane ne ni ba,amma sai kin tafi gidan ku in ya so in iyayenki suna son ki yi zaman auren sa hana ki tunna ni kin raina ni."
Zainab ta yi mamaki sosai ganin duk abin da za ta yi mishi ta yi amma ya kafe kan dole ta tafi,hankalinta ya tashi sosai domin in har ta tafi ƴan'uwanta za su din ga mata dariyar a she dama ba ta fi ƙarfin mijinta ba.
Sai dabara ta faɗo mata lokacin da ya janyo mata akwatinta ya tura mata ta ɗauki waya za ta kira Daddynta, sai ta canza shawara ta kira Daddyn A.m ta fashe da kuka ta ce.
" Daddy A.m zai kashe ni da duka mun samu saɓani na kuma bashi haƙuri,amma kuma yaƙi dukana yake sosai.Don Allah Daddy ka zo ka taimake ni!Ga shi nan da bell ya nifo ni."Ta ce tare da saka sabon kuka ta saki ƙara ganin A.m ya yo kanta don ko kaɗan bai yi tunanin Daddy za ta kira ba."
" Baki da hankali ko mahaifina zaki kira uban me ya sa baki kira naki ba?"Ya ce tare da doka wayar a ƙasa.
Hakalin Daddy ya tashi matuƙar gaske jin wayar ta mutu wanda ya zargi A.m ya karɓe wayar,sai ya shiga safa da marwa don ya san halin ɗan na sa ba shi da haƙuri sam!
Har ya danna numbar ainihin mahaifinsa da nufin ya kira sa sai kuma ya fasa ya kira numbar A.m,wace ta yi ta ringing bai ɗaga ba duk da ya na kallon wayar.
A karo na ba adadi A.m ya ɗauki wayar tare da kanga ta a kunninsa cikin fushi ya ce.
" Hello Daddy."
"Abdurrahman ba da hankali ko! Ƴar mutane kake duka wa ya ce maka ana dukar mace in ka saba mata da haka,kafiya za ta din ga mata ita mace ai ƴar lallashi ne.Ka taɓa ganin wani ya duka matarsa a cikinmu irin tarbiyar da na baja kenan?"
Daddy ya tambaye sa cikin zafi ba tare da ya tsaya jin mai zai ce ba." Wallahi Zainab ta rai na ni nina san halin da take min!Daddy wata ƙasa ta sallake ta tafi saro kaya har zuwa Dubai bayan na hana ta.Shin Daddy na gaza ɗaukar ɗawainiyar ta ne?"
Shi ma ya furta cikin ɓacin rai da kuma murya mai sauti don ya manta da Daddy yake magana.
Daddy ya ji maganar wani iri tabbas ya ji ba ta kyauta ba,amma shi A.m har yau ya kasa gane wace irin mace yake aure kuma ƴar waye.
Jin Daddy bai ce komai ba sai ya yi ƙuta ya ce." Na rantse dole ta bar min gidana tunna ba ta da tarbiya ni ba zan yadda ta mai da ni namijin tace ba."
Ya ce ya na huci don Zainab ta ba shi haushi matuƙar gaske shi ya sa dama ya ɗauki alƙwarin in ta dawo ba za su kwashe ta daɗi ba,sai ta gane shi baya ɗaukar raini shi ya sa ya ɓoye sonta a wani guri na zuciyarsa don kar ya han shi ɗaukar mataki.
" Abdurrahman dama ka auri ƴar abokina ne saboda ka tozarta ni, ka nuna ban isa dakai ba saboda ba ni na haife ka ba ko?Ka na son ka tada min da taɓon ba na haihuwa ko?"
Daddy ya faɗa a raunane wanda hankalin A.m ya tashi da jin abin da ya faɗa don ji ya yi kamar kuka yake yi.
" No Daddy don Allah kar ka ce haka wallahi kai ɗin kafi mahaifina don zan iya bijire masa,amma ban da maganarka ka yafe min."
Ya ce hankalinsa a tashe ya na ma mata mugun kallo saboda yau ne rana ta farko da Daddy ya yi mishi irin wannan maganar.
"To ina baka haƙuri tabbas ba ta kyauta ba karka ƙara dukan matarka ta sunna yanzu gani nan zuwa gidan,zan yi mata faɗa kuma dole ta daina tunna baka so ai kai kake da iko da ita."
Daddy ya ce masa cikin muryar taushi da lallashi ya na son ya kwantar da hankalinsa,ya san zai iya yin ɓatatta.
" To sai ka zo."
Ya kashe wayar ya na huci kamar mesa daga ƙarshe ficewa ya yi a ɗakin ya bar ta ya koma farfajiyar gidan ya na jiran Daddy,don har yanzu bai huce ba dole Zainab ta zaɓi ɗaya duk da ya san barazana kawai yake mata amma ba zai iya rabuwa da ita ba.
Zainab kuwa ba yan fitarsa ta yi tsaki tare da saka makulli a ɗakin ta na shafa ƙuncinta da ya sha mari ta ɗauki wayarta da ya fasa ta ce.Wahalalle kawai ka gama jarabarka sai ka siyar min wata wayar kuma ba zan fasa sana'a ta ba ƙarshen da zarar na samu lokaci wata ƙasar zan koma.Sai dai in hauka za ka yi ka yi."
Ya na tsaye a farfajiyar gidan ya ji hon wanda ya tabbata Daddy ne ya zo,mai gadi ya buɗe masa get ya shigo.
Da sauri A.m ya ruga kamar wani ƙaramin yaro ya faɗa jikin Daddy ya na magana kamar zai yi kuka.Dariya ya yi ya shafa bayan shi suka shiga ciki.
Faɗa sosai Daddy ya yi ma Zainab wacce ta ɗauke shi a matsayin son kai kuma ya tursasa mata ta ba A.m haƙuri,sannan ƙar ya ƙara jin ta fita ko unguwa ba wata ƙasa ba in dai ba da izinin sa ba.
Ya kuma ƙara da ce wa." Tunna A.m ba ya so ta dai na zuwa in ya so ko shi zai iya yi mata oder.
A kasale ta miƙe ta na ganin kamar son kai Daddy ya yi mata,amma ta rantse ko sama da ƙasa za ta haɗe ba wanda ya isa ya hana ta fita waje,don har ta fara saka kanta a cikin matan da za'a fara irgawa suna da kuɗi a cikin Nigeriya, so ba wani ƙwaro da zai hana ta fita.
Amma a fili sai ta ƙara sakin kuka ta ce " Na yi nadaama kuma na ba shi haƙuri Amma ya ƙi haƙura."
" Shikenan Daddy ya wuce amma kar ta ƙara."
Ya faɗa cikin ɓacin rai sannan ya miƙe ganin Daddy ya miƙe." Ok Allah ya kyauta ku yi haƙuri dama aure ɗan haƙuri ne ni zan tafi."
A.m ya shafa kan shi ya na murmushi ya ce." Daddy ya zo gidan son amma ko ruwa ba'a kawo mishi ba,ka yi haƙuri Daddy ni kaina haƙuri nake da ƴar taku komai ba ta iya ba sai shegen yawon tsiya da rai na miji,Allah Daddy ko ruwan zafi ban taɓa sha ba wanda Zainab ta dafa,asalima ce wa ta yi ba ta iya ba.Shi ya sa nake tunanin ta rako mata ne kawai.
Daddy ya saki dariya ya na faɗin daidai lokacin da ya nufi ƙofa." Ah ah wanan to magana ake yada min ba haƙuri ake ba ni ba,amma kuma a haka ka ga ƴar tamu ka kace in ba ita ba sai rijiya."
Ttsaki ya yi ya na hararar ta ya ce " Shigo shigo ciki akai min ban san halin ta ba na ba ta amanar zuciyata."
Zainab kuwa mai da mishi da harar da yake mata ta yi ta ce." Ba wani nan wahala ce na ce ba zan yi ba ai ko addini bai ce dole sai na yi ba,kuma yanzu ai baka da matsalar abinci tunna ga Juwairiya nan mai aiki."
A.m ya watsa mata wani kallo wanda shi ya sa ma'anar sa jin ta ambaci Juwariya.
Ganin Daddy zai fice sai Zainab ta ce." Daddy bari na yi kiran Juwairiya ta kawo maka abinci,na san yanzu haka ta na kicin kuma zaka yaba don ta na da zaƙinn hannu."
Wani irin tashin hankali A.m ya ji ganin ta nufi kicin ɗin har ya na dana sanin maganar da ya yi gashi ƙilu zai jawo mishi bau!
Ya buɗe baki da nufin ya yi maganar da bai san me bakinsa zai ce ba sai ya ji Daddy ya ce.
" Karki damu ƴata kin san bana karyawa sai sha ɗaya bari na tafi Allah ya yi muku albarka,kuma don Allah ku din ga haƙuri da junan ku."Sai ta dawo ta fasa ta na murmushi.
Wani irin wawan ajiyar zuciya ya saki wanda ya sa har sai da Zainab ta juyo ta kalle shi,ya watsa mata harara,ya shige sama da sauri ya nufi ɗakinsa ya kwashi zanin gadon da ya saka a warshing mashine ya kunna da sauri har ya na sheƙa ruwa a ƙasa garin ya zuba a ciki.
Zainab ce ta shigo ta zauna a kan gadon ta na ƙare ma ɗakin kallo ganin ya na bayi sai kwanta ta na jiran sa,amma sai yaƙi fitowa ya tsaya kamar me tunanin wa ni abu da ya manta.
A hankali Zainab ta taso ta tsaya ta bayansa ta huging ɗinsa da sauri ya ture hannunta ya koma gado ya kwanta tare da rufe idanunsa ya janyo bargo ya lulluɓa da shi.
Ganin haka ita ma ta hau ta ɗaga bargon ta shige tare da rungume shi,ya sa ka hannunsa ya ture ta ta faɗi ƙasa don har yanzu haushinta yake ji,haka kawai ta ba ma wata mace damar shigowa rayuwarsa ga shi ya na jin wani abu da ba zai iya ce wa ga shi ba,don har yanzu jikinsa babu ƙarfi.
Da takaici ya isheta sai kawai ta fashe da kuka don ta bugu sosai ta miƙe ta na share hawaye ta ce." Bari na fita tunna baka buƙatar son ganina! Haba ko Allah muna yi mishi laifi ya yafe mana."
Ta saka takalmi ta kuma ce wa." Dama yunwa nake ji bari naje na ci abinci."
Haba da sauri ya diro a kan gadon da ya ƙudundune kansa da bargo ya janyo ta da ƙarfi ta faɗa kan gadon ya na zare ido.
" Ke ce kika ban haushi matuƙa amma na haƙura tunna kin ce ba zaki ƙara ba."
Ya ce da ita ya na murmushin dole ya saka hannun shi ya tallabeta ganin ta na murmushi ya ci gaba da ce wa." Baki san tashin hankalin da na shiga ba da baki nan kin san duk yawon ki ba ki taɓa bari mun raba shinfiɗa ba.Tun lokacin da na ce miki mun iso kika kashe waya na tsargu."
Ya ƙura mata ido ya na kallonta ya kai bakinsa kusa da kunninta ya na mamakin abin da zai ce mata." Ko dafa da na dawo na ga baƙya nan sai wancan wa take da suna ta bani abinci wurgi da shi na yi,a hotel na zauna saboda gidan ya yi min baƙi na kasa bacci ni kaɗai gabaki ɗaya kewanki ya dame ni,gaskiya ina son ki matuƙa."
Ya numfasa ya na mata wani tsadadden kallo da murmushi ya ci gaba da ce wa." Ina masallaci na ga kiranki duk da fushi nake dake har na fito cikin hotel ɗin da nufin na ɗauki mota na ɗauko ki,sai ga shi kin kira ni in bar shi mijin Fati ya turo muku direba shi ya sa na karyo mota na dawo gidan tunna matar gidan ta dawo."
Ya faɗa ya na kaida kansa gefe shi kansa ya na mamakin kansa.
Zainab murmushinta ya ƙaru ta na jin wani irin girman kai da alfahari da mijinta da take yi,sai ta kama shi ta rungume ta na faɗin."Ina sonka Habibina ni na san ba za ka iya rabuwa da ni ba,ko ce wa da ka yi na bar maka gidan ka kana faɗi ne kawai amma ni da kai mutu ka raba."
" Tabbas Zainab maganarki dutse da sai dai ki taho asibiti jinya."Ya faɗa
Dariya suka yi duka ya rufe su da bargo ya kasheta da soyaryar shi sannan ya sa ta baccin dole,saboda ya sakin mata nauyin shi wai dole sai ta kwanta sun yi bacci,duk da ba shi take ji ba.
Kallonsa take yi yadda yake saukar da numfashinsa a hankali,daga gani baccin na kai mishi karo ita kuwa ta kasa baccin saboda wani irin yunwa dake ƙwaƙwularta,saboda rabonta da abinci tun daren jiya ta kasa ci ta na fargabar yadda za su kwashe da shi.
Shafa fuskarsa ta yi da yake ta sheƙi da kyau ta na mamakin mai ya hana shi bacci,sai kuma ta danganta hakan da ce mata da ya yi ba'a gida yake kwana ba ƙila ya kasa bacci ne.
A.m da fari baccin ƙarya yake yi ya saka mata nauyin jikinsa don kar ta ce za ta buƙaci abinci, ta je gurin Juwairiya don ya san a halin da take ciki ba yadda za'a yi ta iya wani aiki a gidan,amma kuma daga ba ya saboda rashin baccin da bai yi ma wannan mai kukan tsiyar da ta hana shi bacci sai bacci ya kwashe shi.
Da Zaina b ta gaji da juyi a gado ta bubbuga shi ya ɗan buɗe ido ya na kallonta.
" Gaskiya ka tashi ni fa na gaji da baccin nan yunwa na son ta yi min lahani."
Ta faɗa ta na jan shi ya sauko shahada ya yi ya sauka tare da miƙa da salati,ya shige bayi ganin haka ita ma ta sai ta wuce ɗakinta ta shiga bayi wanka ta yi ta zira duguwar riga,suka fito falo suna taku a jere sai kace ba su suke ta faɗa ba.
************
Juwairiya kuwa bayan ta gama jin wayar da A.m yake yi da Zainab ta shiga tashin hankali matuƙa! A wannan lokaci ji take kamar ta buɗe ido ta ga ba ta a doron ƙasa kuka take yi sosai na rashin abu mafi girma a rayuwarta,wanda Baba Sani ya so ya yi galabar raba ta da shi dama mutane da dama amma ta yi yaƙi tukuru,ta ada na abin ta sai ga shi yau ta siyar da shi saboda kuɗi ta na shan wulaƙanci ba tare da an daraja ta ba.
Ta rintse idanunta ta na jin wani irin ciwo mai raɗaɗi a zuciyarta yayin da wasu tarin hawaye suka ci gaba da turereniya a fuskarta.
Cije bakinta ta yi lokacin da ta miƙe ta na jin wani irin azabar raɗaɗi ya na zagaye duk ilahirin jikinta.
A hankali ta fice daga ɗakin ba tare da ya sani ba jin matar so ta dawo yayin da hankalinta ya tashi,amma ta wani gefen ta na jin ina ma ace Zainab ta riske su a wannan yanayi koma mai zai faru ya faru,don ta gaji da tarin raɗaɗin azabar da take kurɓar ruwan baƙin cikinsa a cikin rayuwarta.
Ta na shiga ɗaki sai ta fashe da kuka sosai har ta yi mai isar ta sannan ta rarrafa ta shiga bayi ta gana ma kanta,azaba da ruwan zafi don ta rage ma kanta ciwo da nauyin da jikinta ya yi.
Bayan ta yi wanka ta fito ta yi sallah a zaune sai bacci mai haɗe da zazzaɓi ya kama ta wanda faɗan su ya tashe ta,ba wai don ta gaji da baccon ba tunna duka yaushe ta kwanta sai dai ta ji daɗin baccin don ya ɗan rage mata wani ƙunci daga cikin damuwarta.
Ta din ga jin hayaniyar su da kukan Zainab har da saukar marin da ya yi mata.
Ta saka hannunta ta toshe kunnin ta amma sai ta ji sun sauko ƙasa suna ta faɗa sosai,ya faɗa ta faɗa sam babu tsari a rayuwar auren su don ba sa daraja juna.
Gabaki ɗaya sai ta ɗauki laifin ta ɗora akan A.m wanda yanzu take jin haushin sa fiye da komai a rayuwarta,ga wani irin kishinsa da ya ƙara ninkuwa a ranta mai girma wanda take jin kamar ta illata duk wadda ta raɓe shi.
Ta na jin suna faɗa daga bisani ta ji shiru sai muryar namiji ta ji ya na sasanci,wanda daga baya ta game mahaifin A.m ne.
Sasancin da aka yi a tsakanin su suka koma ciki shi ya ba ta damar yin baccin wahala,duk da ta san ya kamata ta shirya ma mutanen gidan abinci,sai dai ba za ta iya ba saboda jikinta da ko ina yake mata ciwo.
A tare suka sauko ƙasar sun ci gayu sosai an sha kyau.
Zainab ta tsaya ta na kallon dinning cike da mamaki ganin ba komai wayam.
Ta kalli A.m ta na faɗin." Ina wannan wawiyar take ba ta shirya min abinci ba duk da na kira ta ba ɗauka ba na tura mata da text."
A.m ya da gaban sa ya faɗi amma sai ya taɓe bakin sa ya ce.
" Ina zan sani ko kin bani ajiyar ta ne?Ni da ba'a gida nake kwana ba."
Ya faɗa ya na wani cin magani har da ɗan harara yake sakin mata.
Ƙwala mata kira ta yi sau uku sai ga Juwairiya ta fito a wani yanayi ta na jan ƙafarta.
Da masifa Juwairiya ta kalle ta ta fara magana da ce wa." Ina abinci na kuma gidan uban wa kika shiga na kira wayar ki na gaya miki zan dawo amma baki ɗauka ba."
Ta faɗa tare da tsare Juwairiya da ido kamar ta na son ta gano dalilin ƙin ɗaga wayar da ta yi.
Juwairiya ta saci kallon A.m da yake zaune a ɗaya daga cikin kujerun dinning ya na danna waya,kamar bai san da mutane a gurin ba amma kuma a zahirin gaskiya hankalin sa na gurin su ya na son ya ji mai za ta ce,yayin da gaban sa yake faɗi duk a tsorace yake sai dai ya yi ta maza ya dake.
Juwairiya ta mai da kanta ƙasa hawaye na bin fuskarta jikinta har kyarma yake yi,saboda har yanzu zazzaɓi take ji,ita kanta ba za ta ce ga in da wayarta take ba don rabon ta ita tun jiya da ya ce ta gyara masa ɗakinsa.
" Ki yi haƙuri wayata ba caji na gaya ma maigadi ya kunna jannareto don ba wuta,amma ya ƙi tashi sannan na so na kunna sola sai dai ban iya ba ina gudun kar na ɓata na haƙura k....."
" Rufe min baki nɓbanza daƙiƙiya jahila solar ce kika kasa kunnawa abu a rubuce ba na tunanin kin yi firamari,ni tsoro nake karki din ga ƙona min kayan wuta ko ki ta da gobara ai dai yi asarar kuɗin tara wallahi.To uban me ya hana ki yin abinci."
Zainab ta ce ta na hararar ta don ranta ya ɓace ta so ta samu abincinta da ta yi rashin sa na kwana biyu mai daɗi da,shi ya sa taƙi sakin jikinta ta ci abinci da za ta taho.
Wannan karon A.m ya yi tsubbul da bakinsa ya ce." Wa za ta dafa ma abincin ni da na gaya miki a hotel na ke kwana ita da masu aiki ne kawai ƙila sun yi sun ci,tunna ba ta san za ki dawo ba."
Ya ce cikin sauri ya na tsoron kar ta yi katoɓara don ganin ta fara kuka.
Juwairiya kuwa gwalalo idanunta ta yi ta na kallon sa jin ƙaryar da ya shirya mata.
Karab! Kuwa suka haɗa ido kowa ya yi saurin ɗauke kansa.
A.m sai da ya sakin mata harara sannan ya ɗauke kansa,Juwairiya kuwa wani irin kunyarsa ya kama ta ta rintse idanunta da sauri.
" Ke."
Ta daka mata tsawar da ya firgita ta." To uban wa kike ma kuka daga tambayarki?Maza ki je ki ɗora min abinci yunwa nake ji kuma ki kawo min abun da zan iya ci kafin ki ɗora girkin."
Sai hawayen Juwairiya ya ƙara zarya a fuskarata ta kalli Zainab ta ce " Don Allah ki yi haƙuri bani da lafiya zazzaɓi nake ji,ba zan iya girki ba."
Ta faɗa cikin muryar da ta bayyana irin kukan da ta sha tun daren jiya.
Zainab ta harare ta ta ce." Allah ya sa mutuwa za ki yi amma sai kin yi min abinci kin san yunwar da nake ji maza wuce.Kuma ki kawo min abin da zamu taɓa ni da zauji."
Ta zauna tare da ɗaukar remote ta kunna kallo ta na karkaɗa ƙafa ta na jan A.m da hira wanda ya kasa ko da tari ne ya na ta kallon fuskar wayarsa,da ya kasa ɗauke idanunsa a kanta bayan babu abin da yake yi.
Juwairiya na shiga ta haɗa kanta da bangon kicin ɗin ta na kuka sosai take jin jikinta ba daɗi.
Ta daɗe a haka sannan ta soya dankalin turawa da ƙwai ta kuma haɗa musu da tea mai kauri ta kai musu,ta na tafiya tamkar wacce ƙwai ya fashe mawa a cikin ta.
" Ok maza ki je ki haɗa mai nauyi don wannan ba zai ƙosar da ni ba."
Ta ce mata ba yan ta ije mata ba tare da ta kalle ta ba.
"Anty Zainab ki yi haƙuri ba ni da lafiya don Allah sa..."
Mari ta wanka mata a fuskarta da take jiƙe da hawaye ta ce.
" Ban san lokacin da kika raina ni ba har kike musayan yawu da ni banza dangin matsiyata!Maza wuce ki yi abin da na saki."
A.m ya tashi da sauri ya na faɗin " Haba Zainab ta ce miki ba ta da lafiya ba ki da tausayi ne.."
Katse shi ta yi ta ce." Ba da kai nake yi ba ba ta da lafiya ta sha magani,uban wa take son ya yi mana girkin meye amfanin ta a gidan?Ko ubanta yake neman ma na kuɗin da za mu biya ta?"
SAUKAR MARIN YA SA NA FIRGITA AMMA NA CI GABA DA RUBUTU SAI DAI KUMA TAUSAYIN JUWAIRIYA YA HANANI ƘARASAWA,DON NA KASA GANE MAI NAKE RUBUTA AN YA ZAINAB KIN KYAUTA KUWA.
KUCI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN BARI NA ƘARA TUNA MUKU DA SUNAN LINTAFIN
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU
JAMILA LAWAL ZANGO
TUNATARWA
DON ALLAH ƳAN'UWANA MATA KADA KARATUN LINTAFI YA ƊAUKE HANKULANMU MU MANTA DA BAUTAR UBANGIJI,KU TUNA ALLAH YA HALICCE MU DON MU BAUTA MASA NE.
GOBE JUMA'A KAR A MANTA KARATUN SURATUL KAHAFI ALLAH YA BA MU ALKAIRUN DA KE CIKINTA AMIN
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha shidda.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba ***_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.