NAZLAH

17 - 18

by @autarmama

Shafa kanta tayi, tare da girgiza kanta alamar ta daina mata godiya haka.



   sosai Nazlah tasha kyattutuka na ban mamaki, dan daga ko wane sashe kawo mata kyauta ake har mutananta sai da suka minmiko mata, su kansu su Adda Nabila Yarinyar ta burgesu, haka aka tashi kowa da mamakin Nazlah da burgeshi a cikin ranshi.




    Su Nazlah kuwa haka suka dauki niƙi-niƙin kayyayakin kyauttutu kansu , suka tafi gida, sai dai Abun Mamaki bayan sun shiga gida suna shiga Ɗaki suka ci karo da kyauttutuka na ban mamaki ajiye tulugu guda, da kallo Ummu take bin kayan kafin ta kalli Yah Haleem tace "Haleem abun nan ya fara tsorata ni da yawa, mutanan nan so suke su kashe ni da tsoro, ɗiɓe kayan nan ka fice dasu", ta fada tana zama kan Yangwananniyar Katifar da take gefe.




    Yah Haleem na kai hannu zai dauka, Nazlah ta rike hannunshi, ta re da cewa "Bandirawo dai na,,wannan kyauta ce ba'a mayar da hannun kyauta baya ,shaidan ne kawai yake mayar da kyauta in an mishi", ta fada kanta *ƘAASA*.




   Cikin Hasala Ummu tace "zaki bari a fita da su ko sai na saɓa miki?", ta fada cikin bada umarni, kallon Ummu tayi kafin tace "Ummu kar a fitar da kayan nan kyauta ce aka kawo mata, in kuma aka fitar dasu to duk abun da ya biyo baya ba ruwana , domin wannan ba daga ni bane daga Sarki ne", ta fada tana komawa gefe ta zauna, kallon Ummu Yah Haleem ya yi, itama ta kalleshi , sai kuma suka kalli Nazlah da ta duƙar da kanta ƙasa tana kallon Kyauttutukan da suka shigo da su.




    "A fita da su?", Yah Haleem ya fada yana kallon Ummu, girgiza kanta tayi, tare da cewa "ka barsu", kallon Ummun Nazlah tayi kafin ta mike ta fice daga ɗakin , tana fita tsakar gida ta cire dan kwalinta da hijab ta fada banɗaki,bayan Nazlah ta fita Ummu tace "Haleem ya za muuyi da kayan nan, kasan Mahaifinku da ya shigo zai tattarasu ya tafi da su chan ya salwantar dasu , mai shawara?", ta fada tana kallomshi.




      jinjina kanshi ya yi, tare da cewa "to ko mu kai gidan Iya sai a ajiye ?, kin ga ba zai bi kayan chan ba", ya fada yana kallon uwayen kayan da suka kusan cika dakin, dan ɗakin ba wani mai girma bane sosai, jijjiga kai tayi tare da cewa "hakan kawai za'a y.....!!", bata ƙarasa ba suka ji Nazlah ta kwala ƙara.



    da sauri jikimsu har mazari yake suka fito suna rige², turus Ummu tayi tana kallon Hijab da Dan kwallin Nazlah da yake yashe a gurin, Yah Haleem kuwa toiler din ya nufa dan daga ciki yake jiyo ihun ta.




     yana shiga ya tarar da ita ƙasa yashe tana burgima da ihu, dakyar ta iya cicciɓarta ya fito da ita sa boda wani nauyi da tayi, ɗakin Ummu ya shiga da ita, tare da shimfiɗeta a ƙasa, "mai haka!", Yah Haleem ya fada cikin ɓacin rai, ganin yarda ya haɗe ranshi ya yi kicin²,yasa Nazlah cewa "Murna muka zo..!" , ta fada tana ci gaba da burgima.




     tsawa ya daka mata tare da cewa " haka ake murnan?, kuma tun ɗazun mai yasa baku zo ba, lokacin da kowa yake taya murnar sai yanzu?, shin kunzo ne domin ku dagula mata lissafi ko kuwa kunzo ne domin ɓata mata ranar farin cikinta?", ya fada cikin ɓacin rai.



    girgiza kai tayi tare da ce wa"bamu da ikon zuwa a wannan lokacin domin Sarkin Musulamai ne a gurin, ba muzo dan dagula mata lissafi ba, hasali ma murna muka zo tayata akan wata murnan, amma zamu tafi ", ta fada tana daga kai zata yi Atishawa, saurin dakatar da ita ya yi , ta hanyar daka mata tsawa, da sauri ta natsu, cikin kaushin murya yace "mai yasa kuka fara bayyana kan ku  tun yanzu?,ko kuna son nakasa mata rayuwa ne?", ya ƙarasa fada cikin rauni.




     shiru tayi kafin ta ce "lokacin bayyanar mu ne baiyi ba sai yanzu, da ya yi da tuntuni mum bayyana, ko da yake dama muna a laɓe gane mune kawai ba'ayi ba sai yanzu, kuma mu dan Allah kayi haƙuri kun tafu", tana kai wa nan tayi atishawa da karfi ba tare da ta bari ya ƙarayin wata magana ba.




      shimfiɗeta ya yi, tare da fitowa, ajiyar Zuciya Ummu ta sauke tare da raɓawa gefe daya ta zauna, abun duniya ya mata yawa, kallonta Yah Haleem ya yu, tare da ce wa "kar ki sanya damuwa a ranki, ni bari na fita, na samu mana abun da zamu ci",ya fada yana yin gaba, da fatan Alkhairi ta bishi , yana fita Abba ya shigo yana washe baki, kallonta ya yi, tare da ce wa "Ummun su sannu da hutawa", dagowa tayi baki bude tana kallonshi, zama ya yi a gefenta tare da ce wa "ina chan ina buga caca naji wani abun Alkhairi da ya sauka, ni ban ma san zatayi sauka ba, wai waya ma sanyata makarantar, ina kayan suke", dan tsananin takaici da mamaki kasa magana tayi, sai ta tyna lokacin da ta fada mishi za'a sanya Yarinyar Makaranta ya je ya kaita, sai cewa ya yi "na kai wa? wannan shegiya?, ni fa bana kaunarta, in ma kika kaita kukayi Amfani da sunana Ban yafe ba", har ƙasa ta zuƙunna rana rokonshi yaƙi, sai dai Haleem ya kaita aka yi mata register da sunansa, amma yanzu sai gashi wai yazo a bashi abun da ta samu.




     "bakya ji ina miki magana kika yi shiru?",,Abba ya daka mata tsawa, Iya da take shigowa tace "To Ubanka zata ce maka in baya yi shiru ba Wallahi Lawan ka kiyayeni , na ce ka fita a idona na rufe", ta fada tana shigowa cikin hasala, da ɓacin rai.





    "to wai Iya mai yasa kike so ki shiga tsakanina da Iyalina ne, ba fa na son haka", ya fada cikin daga murya shima, "Eyyi dama in baka yi haka ba ai baka cika da Mu'azu ba, to bari na fada,maka sisi ba zaka samu ba a cikin abun da Yarinyar nan ta samu, dan bakasan komai na,karatunta ba", ta fada tana shigewa ciki.




       kayan ta tattara cikin buhu ta dauka ta fice dasu waje , Yara ta dinga ɗiba tana ba mawa suna kai mata gida, har ta jide tsaf , Lawan kuwa yana zaune cike da baƙin ciki, dan wata caca zasu buga da wani Alhaji da ya sa 50k , shbe yazo ya kwashi abun da suka samo ya kai, dan ya zauna ayi c'ac'ar dashi.




     ```BAYAN KWANA BIYU```





       Kullum Adda Zainab da Nazlah take kwana, take tashi da ita a cikin ranta, ga kuma abun Hameed kullum gani take yana ƙara ta'azzara.



    kamar kullum suna zaune cikin palo, suna fira, Haleesa ce tace "Wai ni kam Adda , ya batun nemawa Auta Mata yar 10years kin fasa ne ko ya?, gaba baki ƙara maganar ba!,"numfashi ta sauke kafin ta ce "bawai na fasa ba har yanzu ina kan bakana" , da sauri Adda Nabila tace ",Ni kam Adda mu gwada sa'ar mu akan Yarinyar nan mana", duk kallonta suka yi kafin Adda Nafisa tace "wace Yarinya..!?", dan murmushi tayi kafin tace "Hafizar nan mana Nazlah", tsalle Haleesa ta buga tare da ce wa "Wallahi kuwa nima tunani nake a kanta, dan Allah Adda",,ta fada tana dan yi fuskar tausayi.




     Jinjina kanta tayi, tare da cewa "nima ita nake tunani, amma bari na fadawa Hajiya in ta aminta da ita gobe ba sai muje ba", ta fada tana mikewa, duk bin bayanta sukayi, dan zuwa ɗakin mahaifiyarsu, zaune suka sameta tana karatun Al-qur'ani, zama sukayi a gefenta, suna saurarob Daddadar muryar Mahaifiyar tasu da ta ƙara dadi da tana karatun, sai da ta kai karshen page din da take, kafin ta tsaya tana kallonsu, ta cikin Eyesglass dinta, ganin yarda suka natsu yasa ta zare glass din , ta tattara gaba daya hankalinta garesu.




     Adda Zainab ce ta matsa tare da riƙeta, Alamar magana mai muhimmanci zata fada mata, dan murmushi tayi kafin tace "ina sauraronki daga gani akwai magana mai muhimmamci a bakin ki", ta fada tana kallon sauran, duk murmushi sukayi , gyaran murya tayi tare da cewa "Hajiya akan Maganar Auran Autanki, mu mun ga dacewa da natsuwar Yarinyar nan Nazlah, kuma munyi sha'awar zamanta a cikin Ahalinmu, shine muka zo mu fada miki", tun da Adda Zainab ta fara magana Hajiya ta zuba mata idanunta, sai da ta kai karshen bayaninta ta sauke numfashi tare da cewa "Uhmm Zainab, lallai kam nima sai da na ayyana hakan a cikin raina, sai dai wannan Yarinyar tawa Auta Ƙanƙanta, ba zata iya dauke buƙatunshi ba, za'a iya cutar da ita, ke kanki kinsan Auta yana da buƙatuwa sosai, bakya ganin za'a tauyeta ,"shiru ta dan yi, kafin tace "Hajiya ina ji a raina Yarinyar nan ba zata cutu ba har an ta aureshi, sannan ina da yaƙin cewa zai kula da ita, kuma dama ai Miji shi yake koyawa Matarshi komai, in ma ragwanci ko Jarumta, dan haka ina ganin babu wata matsala, domin Yarinyar nan tana da ilimin Addini, ina da yaƙinin ba zata taɓa kauce hanya ba, kuma zata,kula dashi, dan tasan haƙƙin miji akan matarshi, idan kin Amince gobe muje gidansu", ta fada tana kara damke hannunta.




    Numfashi ta sauke kafin tace "toshi kenan", fa fada tana ci gaba da karatunta, da murnarsu suka fito, bayan sun fito kuma Adda Zainab ta cewa Haleesa "An somin Wayar Hajiya na kira Malaminsu ", ta fada tana daukar wayarta.




      da sauri Haleesa ta mike, ta karɓo mata, kiran Malam Arabi tayi akan gove zasu zo, cikin rawar jiki ya amsa musu, dan yasan suka zo zai kwashi damje gidanshi, dan basa zuwa su tafi basu dan lafa mishi wani abu ba, su kuwa firar Nazlah suka ci gaba da yi.





      Washe gari guraren  

4pm sukawa gidansu Nazlah Dirar mikiya da taimakon Malam Arabi da ya rakosu har gidan, bayan sun zo gidan ya tsaya a waje su kuma suka shiga ciki.




     da Sallama suka shiga , suna shiga suka tarar da Nazlah na shara, Ummu na gefe tana duba Azkar, Sallamar su ce tasa Nazlah  dago kanta tana dubansu,washe baki tayi tare da cewa "Ah'ah sannun ku da zuwa, maraba lalle, ku shigo", ta fada tana nuna musu hanya.




      taburma ta shimfiɗa musu suka zauna, kafin ta gaishesucikin mutunci suka gaggaisa, Adda Zainab ce ta ce "Uhmm dama gaisuwa muka zo da rokon iri", cikin rashi fahimta Ummu tace "too gaisuwa da roƙon Iri kuma Hajiya?, ban gane mai kike nufi ba", ta fada tana gyara zamanta.




     dan gutun murmushi tayi tare da cewa, "Ƴa muke so ki bamu",shiru Ummu tayi tare da cewa "anya kuwa nan gidan?, dan nan gidan babu wata Babbar Ƴa mace sai Nazlah, sai dai ko gidan gaba va nan ba", Yar dariya tayi tare da cewa "ita din nake nufi", rike baki Ummu tayi tare da cewa.



    "to a gaskiya wannan ba magana ta bace, amma bari na aika a kira muku Iya sai kuyi magana da ita, ta fada tana kwalawa Nazlah da ta shige ɗaki da Ƴar Adda Zainab karama kira.




     Amsa mata tayi kafin ta fito, goye da Yarinyar a bayanta, dan murmushi Ummu tayi, dan tasan Nazlah da mugun son Yara, ga son ta daukesu, sai dai fa har in ta miƙawa Yaro hannu ya mata ƙuya tofa ba,zata ji kunya ba, gsban uwar ɗa zata makeshi, in kuwa yazo ta ringa lelenshi kenan tana goyashi, da bashi abubuwan wasa da na ciye-ciye hakan yasa Ummu tai hamdalah lokacin da Ƴar Adda Zainab ta miƙawa Nazlah hannu bayan ta miko mata.




     gaban Ummu ta zauna, tare da cewa "Ummu ga ni..!", kallonta tayi tare da ce wa "Iya zaki kira min, kice tazo Anyi Baƙi, suna son Magana da ita", kallon Ummu Adda Nabila tayi, kafin tace "to ki bari kawai sai muje chan din, kar a ƙatse mata wani aiki da take yi ", ta fada tana mikewa.



     murmushi Ummu ta mata, dan dama ta rasa yarda zata ce su tafi chan din ne yasa tace a kirata, da tasan yanzu gab Abba yaje da dawowa daga gurin Cacarshi, mikewa sukayi Nazlah ta sanya Yan takalmanta Sino suka fice daga gidan.




    tafiya suka fara yi zuwa gidan Iya, suna tafiya tana musu Yar fira da yake Nazlah ba dai labari ba, suna cikin tafiya suka haɗu da Hasina, harararta Nazlah tayi , kallonta Adda Zainab tayi tare da cewa "mai ta miki kika harareta ?", yar dariya tayi kafin tace "Bata jin Magana ne to ina dai-daita mata zama ne," ta fada dai-dai lokacin da suka shigo gidan Iya.




    Da Sallama Nazlah ta fara kutsa kai cikin gidan, Iya da take zaune tana cin gujiya ta amsa musu, tare da cewa "Ƴar Halak kinki Ambato tun safe sai yanzu?", lokacin da ta kai karshen maganarta ne kuma ta hango su Adda zainab.




  Washe baki tayu tare da cewa !Ah'ah Ashe da baƙi kuke tafe, Maraba lalle sannunku da zuwa", ta fada tana wangale musu taburmar da take zaune kai, zama sukayi suna gaisheta, da fara'a sosai a kan fuskarta ta amsa musu, Gujiyar gabanta ta mika musu tare da cewa "Bissimillan ku", Adda zainab ce tace "Aaaaaah Gujiya ai kam zamu ci, dan ni ha dade banci gujiya ba"ta fada tana daukar daya.




         kara mika kwanon gujiyar tayi sosai gabanta, tare da cewa "ku ci dan Allah, ai gujiya abar marmari ce, nima na fita naganta shine na siyo na dafa " ,ta fads tana washe baki dan sam bata da rowar abun ta.




      ci suka fara yi, Adda zainab ce ta kalleta tare da cewa "kar kuma mu cinyewa Yar tsohuwa abin ta", ta fada tana yar dariya, dan akwai ta da raha, "Ke..! Nazlatu dauki ki ƙaro musu ma cikin tukunya", ta fada tana kallonta, dauka tayi ta ƙaro , tare da dibo musu ita da Haleesa, kallonta tayi ta washe Yan ƙananan fararen haƙoranta masu kyau tace "Zo muci anan ki bar manya su ci nasu", ta fada tana ajiye musu.




       matsawa tayi suka fara ci a tare, Su Adda kuwa suna ci suna yiwa Iya fira ana dariya, a lokacin in ka gansu sai kayi zaton sunyi irin 20years dinnan a tare , sa boda dukkansu, suna da fara'a, ga saurin sabo.




     sai da suka gama ci tas, kafin nazlah ta jaa Haleesa da Yaran su Adda Nabila suka nufi ɗakin Iya, wasa suka fara yi Haleesa na biyesu duk da ta girme musu tana shan dariya.





    Gyara zama Adda Zainab tayi, kafin ta kwashe duk abin da ya kawosu ta fadawa Iya, shiru Iya tayi tana sauraronsu, har suka kai ƙarshe , numfashi ta sauke tare da cewa "Uhmmmm Banƙi ta taki ba, amma dai Nazlatu Yarinya ce sosai, dan wallahi wannan kayan shiririta ne cike da kanta", ta fada tana kallonsu.




     dan murmushi duk suka yi kafin tace "hakan nakeso domin nafi son wadda zai raina bawai ta raineshi ba , wadda zai dauka tun tana Yarinyarta ita de wadda ko mai za'a daurata akai ba zata ƙi ba kuma zata saba dashi ta tashi dashi, mu dai muna roƙo da ku bamu, sai dai in va muku ba kuma hankalinku bai kwanta da mu ba, kuma kuna jin bazaku iya haɗa zuri'a damu ba", ta fada tana dan kallon Iya.




      "Iyeeeee kaji yar butar uwa, mu suwa ye da zamu ƙi haɗa zuri'a daku, ai babu wanda ba zai iya haɗa zuri'a daku ba, tunda kun dage na baku sai dai har sai kun gaji da shiriritarta , Allah ya sawa tarayyar albarka, amma kuma ni ba zan munafurce ku ba, Baban Yarinyar nan bashi da hali mai kyau , dan nasan ko ban faɗa muku ba za'a tareku a fada muku, domin wannan Alaqar Aure ce nasan dole a samu yan baƙin ciki da zasu shiga su fita, in kuwa na fada muku na fita ko ba sabulu", kallon juna suka yi .




Adda Nabila ce ta ce "to Iya zamu iya sanin Halin dan kar muji wai-wai a waje", dan murmushin takaici Iya tayi kafin tace "uhmmm halin yan zamani ya sawa kanshi, caca yake da shan sugari, sai dai na tabbata wata rana zai daina dan ba halinshi bane, daga bayan nan abun ya sameshi", ta fada tana kallonsu, da tsoron kar su fasa.




     "Laaaaah Iya ai wannan ba komai bane, kaddara ce muna mishi fatan Allah ya shiryeshi, kuma hakan ba zaisa mu fasa Aure ba", Adda Nafisa ta fada tana dan murmushi.




    jinjina kai Iya tayi kafin tace "to shi kenan mun gode da karamcinku garemu, yanzu yaushe kukeson Auren ya kai?, dan ina son na nuna muku na baku Ƴar kamar yarda kuka nuna kaunarku garemu", ta fada tana rike hannun Adda Zainab.




     "Iya in ba damuwa nan da sati daya, domin zai tafi da ita ne chan gurin aikinshi da yake Soja ne to baya zama gida sai in yazo hutu, kuma bamu buƙatar komai naku domin komai da akwai shi kama daga kan, kayan ɗaki, kayan kitchen da sauransu", Adda Zainab ta fada tana murmushi, jijina kai Iya tayi kai Iya tayi tare da ce wa "to shi kenan mun gode sosai", Fira suka ci gaba da yi, cikin raha tana tsokanarsu suna tsokanarta, har guraren magrib kafin su wuce gida, cike da jin dadin karamcin Iyayen Nazlah gare su.





     Bayan kwana biyu, suka ririɓo kayan sa biki suka kawo kama daga kan goro,biscuits , sweet , chew gum, da kuɗi na sa rana da sauransu, ranar da aka aiko ranar Abba ya sani, sai dai ya yi ko in kula da maganar da Ummu ta kara tuntuɓarshi ma sai cewa ya yi "ke..! ki ƙyale ni da maganar auren nan, ina ruwa na da wani auren ta, ku da kuka ruruɓo abun ku ku zakuyi, dan wallahi tsinke ba zan bayar ba", ys fada yana ficewarshi, haka Ummu ta zauna Cikin damuwa, da tunanin anya Abba zai chanja halinshi kuwa, tun da ta aureshi take fama dashi bata taɓa jin dadin aure ba a rayuwarta, kuma haka taƙe haƙuri da dauke kai, dan tasan abun da Iya ta mata A rayuwa har abada ba zata iya biyanta ba, shi yasa take yada kai bata taba daga kai ta kalleshi ba, in yana mata abu, kawai ta dauka ita ibada take, kuma mai ibada baya taɓa sarewa, domin Aljanna yake nema.




      Yah Haleem kuwa da aka fads mishi, sai da ya nuna ƙin amincewarshi dan Yasan Nazlah Yarinya ce sosai , sai dai da Iya ta fatattakeshi ta nuna mishi da Yarda ake Aure sai ya haƙura badan ya so ba, haka akayi ta shirye-shirye, Oganninyar kuwa ita bata wani sani ba tadai ga ana ta ɗura mata abubuwa masu zaƙi ana mata shirye - shirye, amms kwaɗayi da wauta yasa ita duk abun da aka bata ba tambaya take shanyewa sa boda duk masu zaƙi ne.




     maganin Infection kuwa shine akan gaba wanda ake bata(uhmmm Yan uwa, in har Yarki budurwa ce zatayi Aure, maganin Infection ya kamata ki fara bata, dan shine akan gaba, Maganin Mata babu abun da yake sai tatso ni'imarta ta tattaru guri daya, sannan yana kara dankarar da infection a jiki, in zaki siya maganin mata na dubu 5k to ki siya maganin Sanyi na 15k , domin yanzu ba babba ba Yaro, ba mai kuɗi na talaka, kowa yana fama da wannan ciwon sai dai na wani yafi na wani,infection babban matsala ne,domin yana hana jin dadin Auren, yana sakar da wasu ciwuwukan da dama, sai kiga anyi Aure wata daya, biyu, ukku, an fara samun matsala, Yarinya bata jin dadin aure, ko Mijin baya jin dadin Mu'amulla da matar, sai kiga kwana kaɗan da aure an fara kawo kiki ƙorafe-ƙorafe, shin mai yake kawo wannan matsalar ?, amsan infection, idan mai ba zaki mata maganinshi ba, to karki dura mata kayan mata, dan har gwara ki barta ba ki mata komai ba, dan zai kara yawan infection din a jikinta, sannan zai dakushe mata ni'imarta , kinga kuwa gwara a ki barta haka , Allah dai yasa mu dace, a kula maganin Sanyi shine gaba da na Mata).





     Ana sauran kwana biyu biki da daddare, Hameed yazo gidan Hajiya, bayan sun gama gaggaisawa Adda Zainab ta jaashi bedroom dinta, kallonshi tayi tare da cewa "Auta...!", kallonta ya yi,yana son yaji mai zata ce.




     gyara zamanta tayi da kyau tare da cewa "ni na maka katsalandan kuma ina fatan ba zaka bani kunya ba zaka rike zaɓina da hannu bibiyu?", kallonta ya yi cikin rashin fahimta, tare da cewa "katsallandan din mai Adda? ai babu wani katsalandan da zaki a cikin rayuwata, nasan komai zakiyi ba zaki taɓa yi dan ki cutar da ni ba",,murmushi tayi tare da cewa "to naji dadi da ka fahimci haka,kasan ba zan taɓa cutar da kai ba, " jinjina kanshi ya yi.



    "toh Aure na nema maka, kuma an bamu , jibi daurin aure, sai dai kayi hkr nayi lattin gaya maka", idanunshi ya tsura mata cikin fargaba yace "Adda Aure fa?, duka yaushe nayi wanchan da zaki ce kuma wani aure yanzu?, " wani kallo ta mishi tare da cewa.




   "ni na nemo kuma an bani ,bani da damuwa da yaushe kayi wanchan, kaje ka ci gaba da shirye-shirye ka dan bama buƙatar komai naka , in kuma ban isa da na zaɓa maka mata ba sai ka faɗa min", ta fada tana tsura mishi idanunta, masu matuƙar kaifi da kwarjini.





     girgiza kanshi ya yi, tare da cewa "ni bana da sha'awar aure yanzu, hasali ma ni yanzu tsoron mata nake, duba da abubuwan da naga Sadiyya nayi, sai nake ganin kamar duk daya suke", dafa kafadarshi tayi tare da cewa.




    "na tabbatar wannan ba zata maka abun da Sadiyya take yi ba , ya bawa da tarbiyarta da kamala tare da kwarjini yasa na nema maka ita, kuma kowa ya yi na'am da ita, sannan Yarinya ce danya shataf wadda kai zaka koya mata komai na rayuwa, ka zaka koya mata yarda zata yi kuma duk abun da ka koyar da ita tashi zata tashi", tura baki ya yi gaba tare da cewa "Yar raino zaku bani dai, wadda duk zan koyawa wannan ai sai yar 10 to 12,"ya fada yana kallonta.




    Yar dariya tayi tare da cewa "to ka kaddara ma mai kamar wannan shekarun ce Yarinyar, " bude baki ya yi yana kallonta kafin yace "Adda 10 to 12 years, to a tatsi mage ko a kashe?,k





***



```DAGA TASKAR ƳAR LELEN ROYAL STAR```