ZANEN ZABUWA

Chapter 6

by @nanahaleema11

*ZANEN ZABUWA*

       ©️ *Nana Haleema.*

*Page 6*

   Washe gari Jannat ta tashi babu laifi ta d'an samu kwari amma ba wani sosai ba kasancewar bata da lecture a ranar ya saka bata wani yi yunk'urin shiryawa ba tayi kwanciyar ta a d'aki.

Gwaggo ce tayi komai na gidan tun kafin ta tashi daga bacci tana tashi ta tarar har abinci ta dafa ta ajjiye mata, jikin ta a mace sosai ta mik'e ta fito tsakar gida ta kalli Gwaggo da take zaune tana gyara shinkafa tace, "Gwaggo sannu da aiki."

Kallon ta tayi tace, "Yauwa Jannat, ya jikin naki?." Jingina tayi da bango tace, "Da sauk'i Gwaggo, maimakon ki tashe ni nayi aikin gidan." Gwaggo tace, "keda baki da lafiya ina ke ina aiki, kije ki wanke bakin ki kizo kice abinci."

A hankali take takawa zuwa inda taga tukunya akan murhun gawayi dake tsakar gidan ta bud'e ganin ruwan zafi ne ya saka ta jawo bokiti ta juye ta sirka sannan ta d'auka ta kai band'akin dake tsakar gidan, d'aki ta koma ta cire kayan ta ta yafo mayafi madaidaici ta fito ta wuce Gwaggo ta shiga band'akin.

   Bata wani jima sosai ba ta bud'e k'ofar band'akin ta fito ba tare da ta yafa mayafin ba tayi d'aurin k'irji zanin iya guiwa, d'ago idon da zatayi suka had'a ido da Imran da yayi sallama a lokacin ya shigo gidan idon sa ya kai inda take.

Saurin d'auke kai yayi itama tayi saurin sukuyar da kai tace, "ina kwana Yaya." "Lafiya lau" abinda yace kenan ya wuce zuwa inda Gwaggo take ita kuma kamar munafuka ta wuce su ta shiga d'aki. 

Kamar munafuka haka take zare ido a d'aki hannun ta dafe da k'irjin ta sabida bugun da zuciyar ta take mata dan ba k'arami kyau yayi mata a idon ta ba, ya shirya cikin ash d'in yadi mai kauri d'inkin riga da wando rigar mai k'aramin hannu kansa babu hula gashin kansa ya kwanta sosai sai d'aukar ido yake. hawaye taji sun cika mata ido bata hana kanta ba ta barsu suna zubowa tana shiryawa a hankali tana jiyo hirar su da Gwaggo sama-sama.

  Tsaf ta shirya cikin doguwar riga ta yadi mai santsi ta saka hula ta fito tsakar gidan, zama tayi kusa da Gwaggo ta jingina da kafad'ar Gwaggo idon ta a lumshe tana jin yadda idon sa yake yawo a kanta hakan ya saka ta kin bud'e dan tasan tabbas sai sun had'a ido dashi, "Jannat ya jikin naki?." Ya fad'a cikin murya can k'asa yana kallon ta.

  Bud'e idon ta tayi ta kalle shi tace, "Da sauk'i Yaya."

"Kin sha magani?."

"A'a yanzu zanci abinci nasha maganin."

"Ina abincin nata Gwaggo?" Ya fad'a yana kallon Gwaggo. Gwaggo ta nuna masa inda yake da hannu ya mik'e tsaye ya d'auko mata ya ajjiye a gaban ta kafin ya sake komawa kitchen d'in ya had'o mata black tea mai zafi shima ajjiye mata yace, "gashi nan d'auki kici sai kisha magani."

Numfashi ta sauke kafin ta bud'e plate d'in da ya ajjiye mata taga kosai ne kamar yadda take son sa ya wuce babu zafi sai yaji a gefe, d'auka tayi a hankali tana ci tana had'awa da tea d'in kafin ta ture kosan ta shanye iya tea d'in.

    Da kansa ya kuma mik'ewa ya shiga falon Gwaggo ya d'auko maganin ya dawo ya b'allo mata ko wanne ya bata tasha sannan yace, "To Gwaggo zan tafi in akwai wani abun a kira ni a waya." Gwaggon ta d'aga kai tace, "To Imran Allah ya kikaye ya kuma bada sa'a." Da amin ya amsa ya juya ya fita.

Gwaggo ta dawo da kallon ta ga Jannat da idon ta yake a kulle tace, "Jannat!." Jin yadda Gwaggo ta kira ta d'in ya saka ta bud'e ido ta kalle ta tace, "Na'am Gwaggo."

"Wani abun zan tambaye ki ina fatan kuma zaki bani amsar gaskiya ba k'arya ba."

"Insha Allahu Gwaggo."

"Kina son Imran so na aure ne?."

Darammm gaban ta ya fad'i ta d'ago da sauri ta sake kallon Gwaggo suka had'a ido tayi saurin d'auke idon ta lokaci d'aya fuskar ta da yanayin ta bayyana abinda yake zuciyar ta, jikin ta ya soma rawa haka harshen ta so take ta furta wani abu amma ta kasa sai hawaye da ya taru a idon ta.

   Tsafff Gwaggo ta karanci yanayin ta amma sai bata nuna mata ba tace, "Ina tambayar ki kinyi min shiru." Bakin ta na rawa maganar na fita dak'yar kamar ana fizgo ta daga bakin ta tace, "A'a Gwaggo matsayin Yaya kawai nake kallo sa."

Hawaye sharrrrr suka zubo mata wanda tayi k'okarin rik'e su amma ta kasa sai da suka sakko. "Ikon Allah sai kallo, Jannatu meye na kukan kuma? Dan na tambaye ki shine kike kuka?." Gwaggo ta fad'a da mamaki tana kallon ta.

Girgiza kai tayi alamun a'a kafin tace, "Ba haka bane ba." Gwaggo tace, "shikenan ai Allah ya zab'a miki mafi alkhairi, sannan ina so na sanar dake a cikin masu zuwa neman ki da aure ki daure ki saurari koda guda biyu ne cikin su sai a samu na aure kiyi auren ki ki huta kema."

Share hawayen ta tayi ta d'ago ta kalli Gwaggo tace, "Yaya Imran ya hana ni kula kowa." Gwaggo tayi y'ar dariya tace, "To in baki kula kowa ba ta yaya zaki ki samu mijin aure ko shine zai aure ki?". Shiru tayi bata amsa ba dan tambayar tayi mata nauyi a zuciyar ta.

  "Ya hana ki kula kowa ne sabida karatun ki yana tsoron kar soyayya ta d'auke miki hankali ki daina karatu shine dalilin sa ba wani abun ba, Jannat yanzu lokaci yayi da ya kamata ace kema kinyi aure kin tare a gidan mijin ki dan haka ki fad'a masa shi Imran d'in nace zaki saurari masu zuwa neman auren ki sabida lokacin da ya kamata ace kinyi aure yayi kinji ko?."

D'aga mata kai kawai ta iya domin wata irin azaba take ji a k'irjin ta in Gwaggo ta ambaci aure da wani ba Imran ba. "Yauwa Allah yayi miki albarka, tashi kije ki huta" Gwaggo ta fad'a sannan ta d'auki farancin shinkafar ta ta cigaba da gyarawa.

A sanyaye ta mik'e ta shiga d'aki ta kwanta a kan gado tana kallon rufin d'akin, _yaushe ne Yaya zai fahimci ina son sa, yaushe zai gane cewa shine a raina? Yaushe zai fahimci cewa bazan iya rayuwa da wani in bashi ba, ina son shi ina kuma qaunar shi haka ina bala'in kishin sa meyasa ya kasa fahimta yake min kallon k'anwar sa? Ya Allah na rok'e ka ka kawo min mafita a wannan yanayin da nake ciki._

Lumshe ido tayi hawaye suka kuma sakko mata ta share idon ta bayan ta gama zancen zucin ta mik'e tsaye ta d'auki hijjabi ta saka, k'arar wayar ta ya hana ta fitar da tayi niya ta dawo da baya ta d'auki wayar ganin sunan Nafisa ya saka ta d'auka. Daga can b'angaren Nafisa tace, "Jannat ya jikin?".

"Da sauk'i Nafisa ya gajiya?."

"Alhamdulillah, ina fatan dai kin samu lafiya?."

"Na samu sauk'i sosai."

"Ma sha Allah, Mama ce akayi musu rasuwa ta tafi ta barni a gidan amma da zuwa nayi niyar yi."

"Allah sarki, Allah ya jik'an rai ki kuma ce ina mata gaisuwa."

"Amin, zataji insha Allah zuwa gobe kuma zan shigo."

"To Allah ya kawo ki, nagode sosai Allah ya bar zumunci." Ta amsa da amin sukayi sallama ta kashe wayar.

Da wayar ta fito a hannun ta ta kalli Gwaggo tace, "Gwaggo bara na shiga wajan Umma na dawo." Da to ta amsa mata ta cigaba da aikin ta ita kuma ta fita zuwa gidan su Imran.

B'angaren Imran kuwa tunda ya bar gidan su Jannat Company ya nufa, yana zaune a inda suke zama suna aikin sarrafa kwalin da ake zuba lemon a ciki kasancewar sa masanin computer shi aikin sane wannan yana zaune yana yi cikin nutsuwa duk da ba'a cikin nutsuwar tasa yake ba hankalin sa gabad'aya yana kan Jannat da kuma tunanin abinda yake damun ta har ya kaita ga rashin lafiya.

Mufeedah na zaune a office d'inta tana kallon sa ta camera tayi zooming fuskar sa tana k'are masa kallon tana lumshe idon ta, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta d'auki wayar dake kusa da ita ta danna kira ba jimawa aka d'auka sannan tace, "Assistant ka turo min computer man d'in nan yanzu." Tana fad'ar hakan ta yanke wayar tana cigaba da kallon sa har lokacin da taga wanda ta kira yaje inda yake ya fad'a masa shi kuma ya amsa, sai da ya gama abinda yake yi sannan ya mik'e ya tawo zuwa office d'in nata.

Sauri tayi ta canja inda yake kalla ta gyara zaman d'ankwalin kanta ta tabbatar komai dai-dai yake kafin ta fara danna computer kamar gaske, da sallama ya bud'e office d'in ya shigo fuskar sa ba yabo babu fallasa ya tsaya daga can baya yace, "Madam ance kina nema na."

Da murmushi ta d'ago kai tace, "haka ne Imran, k'araso mana." Bai musu ba ya k'araso ta nuna masa wajan zama ya zauna kafin ta gyara zama itama tace, "ya mai jiki?". "Ta samu sauk'i." Ya bata amsa a tak'aice. "Ma sha Allah, Allah ya k'ara lafiya." "Amin mun gode."

Shiru ne ya biyo baya a ranta tana so ta tambaya wacece wacce bata da lafiya amma tana tunanin kar ta wuce makid'i da rawa hakan ya saka taja bakin ta ta tsuke ta rasa abinda zata ce, jin shirun yayi yawa ya saka shi ya kalli agogo yace, "Yau Friday lokacin bari na company ya kusa" ya fad'a yana kallon ta.

Diriricewa tayi sabida yadda yayi bala'in tafiya da imanin musamman sanyayyiyar maganar sa mai kama da wanda yasha ruwan sanyi ta tace, "Haka ne daman na kira ne na tambayi ya jikin madam d'in taka." Mik'ewa tsaye yayi tare da fad'in, "oh nagode sosai da kulawar ki, zan iya tafiya?."

D'aga masa kai tayi tana murmushi shi kuma yayi gaba abinsa ya barta a wajan a zaune tana k'are masa kallo kamar ta samun tv.

Yana fita ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe ido qaunar sa na sake shiga ko wanne b'angare na jikin ta, tun a kallon farko ta fahimci ta afka tarkon soyayyar sa. K'arar wayar ta ta dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi ta sauke numfashi ta bud'e ido ta d'auki wayar tana duba mai kiran, amsa kiran tayi jikin ta duk a mace bata jima tana wayar ba ta mik'e tare da d'aukar jakar tayi ta fita daga office d'in.

A inda aka tanada dan ajjiye abin hawa ta hango Imran a tsaye ya juya baya suna magana da d'aya daga cikin ma'aikatan company yana dariya, duk da ya juya hakan bai hana taga yadda fuskar sa ta washe ba dan yana yi yana d'an juyowa kad'an yana kuma dariya cikin nutsuwa wushiryar sa a bayyane.

Kamar wawuya haka ta saki baki da hanci tana kallon sa har assistant d'in ta yazo wajan yana yi mata magana bata sani ba sai da ya d'an tafa hannun sa sannan ta firgita ta kalle shi, "Madam ina miki magana baki jini ba" ya fad'a yana kallon ta da mamakin abinda ya d'auke mata hankali haka.

Numfashi ta d'an fitar kafin tace, "ban jika ba, wani abun ne?." Yace, "daman wannan file d'in da na kawo miki nake so naji kin saka hannu a kai?." D'an dafe kai tayi tare da yatsine fuska tana satar kallon inda Imran yake tace, "I forgot sai zuwa Monday" ta fad'a tana niyar barin wajan.

"But madam...." kafin ya k'arasa tayi saurin d'aga masa hannu ta bar wajan dole yayi shiru yabi bayan ta. Imran da ya juyo a lokacin ya hangi tana isa inda motar ta take ya d'auke kansa suka cigaba da magana da Samir har ta shiga motar ta bar cikin company tana kallon sa ta mirror.

Samir da yabi motar tata da kallo ya dawo da kallon sa ga Imran yace, "Imran kaga wani irin kallo da madam take maka kuwa?."

D'ago nasa idon tayi ya kalli Samir ya d'an tab'e baki yace, "ban gani ba kai da idon ka ya kai kanta ka gani ai."

Y'ar dariya shima yayi kafin yace, "wallahi da gaske nake ta zuba maka ido fa sosai." Baice komai ba sai murmushi kawai da yayi kafin daga baya yace, "lokacin masallaci ya kusa ni zan wuce" ya fad'a yana barin wajan ba tare da ya jira mai Samir zaice ba.

    Jannat kuwa har bayan juma'a tana gidan Umma a kwance a falo Umma na gefen ta suna hira kad'an-kad'an. Jannat dai daurewa kawai take tana bawa Umma amsa amma ita kad'ai tasan abinda take ji a jikin ta da kuma zuciyar ta.

Gab da sallar magariba ta koma gida har lokacin Imran bai dawo gida ba sai dai ya kira Umma a waya ya sanar da ita yaje wani waje, tana shiga gida alwala tayi ba jimawa akayi sallah tayi sallah kafin ta koma d'aki ta zauna tana jin zazza6i na neman rufe ta.

Gwaggo da kanta ta mik'a mata abinci amma bata kalli abincin ba tana kwance sallar i'sha kawai ta saka ta mik'e itama tana idarwa ta koma ta kwanta.

Tayi nisa a cikin tunani hawaye na zuba a idon ta har bata san lokacin da aka shigo d'akin ba sai jan babban d'an yatsan k'afar ta da taji anyi hakan ya saka ta firgita ta mik'e zaune tana k'okarin neman wayar ta ta kunna kasancewar d'akin babu haske, wayar ta lalubo ta kunna fitila ta haska d'akin ta ganshi a tsaye ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon ta fuskar sa babu alamun fara'a ko kad'an.

Duk sai ta diririce tama manta da hawaye a kan fuskar ta ta rasa abinda zatayi, "d'auko abincin da maganin ki kizo falo" abinda ya fad'a kenan cikin bada umarni ya juya ya fita.

Jiki a sanyaye ta mik'e ta d'auki abinda yace ta fito falon kasancewar shima akwai fitila mai haske ya saka bata haska ba, a zaune ta ganshi ya tankwashe k'afar sa Gwaggo kuma na tsakar gida a zaune amma kana hango ta kasancewar lalulen falon a d'age yake.

Zama tayi a d'an nesa dashi ta sunkuyar da kai tana jiran taji abinda zaice, cikin kakkausar muryar da take saka ta ta shiga cikin nutsuwar ta yace, "sai nace kici abincin zaki ci?." Jikin ta har rawa yake ta jawo kwanon ta fara cin abincin a hankali duk da ba dad'in sa take ji ba amma haka ta daure taci da d'an dama kafin ta ture tasha ruwa, dan duk da sabon da sukayi hakan bai hana ta sakkar sa ba.

"jeki ki wanke hannun ki ki dawo" ya fad'a yana kallon ta. Dole ta mik'e taje ta wanko hannun ta ta dawo ta zauna a inda take taja ledar maganin ta sha ta zauna zaman jiran me zaice mata.

   "Jannat!." Ya ambata cikin murya.

mai sanyi mai cike da dad'i da kuma taushi had'i da kwantar da hankali da sanya nutsuwa ga wanda yake sauraron ta.

Gaban ta ya fad'i ta runtse ido ta bud'e zuciyar ta ta fara mata wani irin zillo da dole sai da tayi saurin dafe ta sabida yadda take jin tana yi mata barazanar fasa k'irjin ta ta fito domin yadda ya kira sunan ta ba k'aramin ratsa ta yayi ba. "Jannat!." Ya sake furtawa yana kallon ta ganin kamar bata ji kiran farko ba.

A hankali ta d'ago ido ta kalle shi tace, "Na'am."

"Zan tambaye ki wani abu amma ki tabbatar kin bani amsa kar kuma kiyi min k'arya." D'aga masa kai tayi alamun to gaban ta na fad'uwa kafin yace, "Me yake damun ki?."

Runtse ido ta sake yi tana jin wani abu kamar tafiyar kiyashi na zaga jikin ta ta cize baki zuciyar ta na bata umarnin furta masa gaskiyar abinda yake ranta amma bakin ta yayi nauyi ta kasa sarrafa maganar balle har ta kai ga furta ta. Dak'yar ta samu bakin ta ya bud'e ta d'ago idanun ta da suke koma ja sabida bala'in bugun zuciya da kuma tashin hankalin da take ciki tace, "Babu abinda yake damu na."

Ido ya kafa mata duk da kanta na k'asa amma hakan bai hana taji tasirin idanun sa a jikin ta ba dalilin da ya sanya ta saukar da kanta k'asa. Numfashi ya fesar kafin yace, "k'arya kike." D'ago ido tayi jin abinda yace suka had'a ido ya d'age girar sa sama tare da ware mata idanu yace, "kinji me nace ai." K'asa ta sake mayar da kanta kafin tace, "da gaske nake." D'an murmushi yayi mai kama da murmushin takaici ya cize bakin sa kafin yace, "Jannat yaushe kika fara yi min karya ne? Yanzu ni zaki kalla ki cewa babu abinda yake damun ki?."

Kanta take girgizawa idon ta a rufe daman tasan bata da abinda zata kare kanta a wajan sa domin kuwa babu wata halayya tata wacce bai sani ba ya kuma karance ta kaf ba ko motsi tayi yasan me yake nufi, "Jannat yaushe kika canja ni matsayin Yayan ki? Yaushe kika canja ni daga matsayin wanda kike fad'awa damuwar ki? Ko na gaza ne ta fannin baki shawara a duk lokacin da hakan ta faru."

Girgiza kai tayi idanun ta suka ciko da kwallah tana so ta masa magana amma ta kasa ya cigaba da fad'in, "gashi kuwa kina nuna min hakan, Jannat in baki fad'a min abinda yake damun ki ba wa zaki fad'awa? Sanadin damuwar da kika saka a ranki har kwanciya kikayi a asibiti na wasu awanni amma kice min babu komai?." Ya k'arasa fad'a cikin sanyi da sigar lallashi.

Kanta take girgizawa zuwa lokacin hawaye sun fara sakkowa daga idon ta amma har lokacin ta kasa ce masa komai, runtse ido yayi ya bud'e su a kanta yana kallon yadda take hawaye duk da kanta a k'asa yake yace, "shikenan Jannat kiyi hak'uri in na shiga abinda bai shafe ni ba tunda gashi naga kina kuka, ki daina kuka kinji kinga baki da lafiya tunda kin canja ni daga matsayin da nake bazan takura ki ba amma in Abba ya dawo zan sanar dashi duk abinda ya faru shi sai ya tambaye ki." Kukan ta ya fara fitowa fili a hankali ta d'ago kai ta kalle shi tace, "kayi hak'uri Yaya ba haka nake nufi ba."

"To ya kike nufi Jannat? Na tambaye ki kinyi min k'arya na kuma tambayar ki kika fara kuka me kike so na d'auka kenan?."

"Kayi hak'uri dan Allah."

"Ke zan bawa hak'uri dana takura ki."

"Kayi hak'uri zan fad'a maka."

"To ina jin ki."

Rasa abinda zata ce masa tayi domin tayiwa kanta alqawarin koda son sa zai zama ajalin ta baza ta furta masa tana son sa ba, "Kwana biyun nan sai na dinga jin fad'uwar gaba ina ji kamar wani abu mara kyau zai faru dani ga kuma makaranta ina tsoron kar hakan ya saka na fad'i exams shiyasa" ta fad'a bakin ta na rawa sosai.

Shiru yayi bai amsa ba sai kallon ta kawai da yake yi jin hakan ya saka ta d'ago ido suka had'a ido yace, "Wannan ba shine abinda yake ranki ba". Bata janye idon ta daga kansa ba tace, "shine Yaya." Sake d'aure fuska taga yayi kafin yace, "Another k'arya."

    Sauke idon ta k'asa tayi kafin tace wani abu ya sake cewa, "idon ki kad'ai ya tabbatar min da abinda kika fad'a ba shine a ranki ba. Jannat kawar ki ma ta fad'a min kwana biyu bakya mayar da hankali akan karatu kullum cikin tunani kike nima kuma na tabbatar da hakan dan haka ki fad'a min abinda yake damun ki ko kuma ki had'u da fushi na wanda baki tab'a gani ba wallahi."

Ajiyar zuciya take yi a hankali tana sauraron abinda yake fad'a bugun zuciyar ta na sake gudu tace, "To ai baka jira na gama fad'a maka ba." "Okay, ina jin ki, wacce k'aryar ce a gaba kuma?." "Gwaggo ce tace wai na lokaci yayi da zanyi aure ni kuma bana son had'a aure da karatu" ta fad'a a shagwa6ar da ta zame mata jiki ga hawaye a kwance a kan fuskar ta.

   D'an jimmm yayi kafin yace, "Auren ne bakya so ko kuma had'a aure da karatun ne bakya so?." "Ni duka ma bana so" ta fad'a cikin murya mai nuna tsantsar raunin da take ciki. "Meyasa hakan to? Ko kuma akwai wanda kike so ne?."

Gaban ta ya fad'i ta had'd'iye wani abu mai daci ta d'ago ido ta kalle shi tace, "ni babu wanda nake so" ta fad'a tana fashewa da kuka mai sauti. Tsayawa yayi yana kallon ikon Allah kafin yace, "to meye na kuka kuma? Ki daina wannan kukan kin san bana so ko?."

Tsayar da kukan tayi tana share hawaye ya kuma cewa, "kar ki damu babu wanda zai aurar dake yanzu indai ina da rai sai lokacin da kika kawo min wanda kike so ki aura da kanki kinji ko?."

Sak tayi tana kallon sa jin abinda yace ya saka zuciyar ta ta sake karyewa hawaye suka cigaba da zuba, dafe kai yayi yace, "Jannat wai ya kike so nayi ne? Ina jin zafin ganin hawayen ki a raina dan Allah ki daina."

Share hawayen tayi ta mayar da kanta k'asa zuwa lokacin ta fara jin kamar jiri na d'aukar ta duk da a zaune take, "Bayan wannan sai kuma meye a ranki?" Ya sake tambaya yana kallon ta.

Girgiza kai tayi alamun babu komai ya girgiza kai shima dan duk abinda ta fad'a bai yadda ba akwai abinda yake damun ta jikin sa yana bashi hakan, "waye wannan d'an school d'in naku?." A hankali tace, "nima ban san shi ba kawai ina zaune yazo yana fad'a min magana."

"In kika samu lafiya zamu je school d'in naku ayi miki iyaka dashi ko a hanya kar ya kuma yi miki wata maganar banza balle ya kai ga kai hannun sa jikin ki" ya k'arasa fad'i cikin muryar da take nuna ransa ya sosu a kan hakan.

  Ita dai bata ce komai ba domin ta kanta take ita kad'ai tasan a yanayin da take a lokacin ya kuma cewa, "Ban hana ki fitowa daga wanka baki saka hijjab ba?." D'aga kai tayi tace, "ka hana ni."

"Meyasa kika yi d'azu?".

Tace, "babu komai."

"Meyasa yanzu bakya jin magana ne wai? Yanzu da nida wani muka shigo gidan fa?" Ya fad'a cikin fad'a har ya manta rarrashin ta yake yi.

D'ago ido tayi ta kalle shi taga yanayin fuskar sa ya canja akan d'azu ta lumshe ido a ranta tana mamakin yadda yake nuna kishin ta akan komai amma kuma babu soyayyar ta a ransa abin yana d'aure mata kai yana kuka bata mamaki sosai, "kayi hak'uri bazan sake ba". Ajiyar zuciya yayi yace, "yanzu kije ki kwanta naga bakya jin dad'i amma ina so ki sani, duk abinda kika fad'a ban amince shine a ranki ba ki tanadi amsar da zaki bani in kika samu lafiya in kuma ba haka ba zanyi fushi dake wanda ban tab'a yi ba tunda muke kin gane?." D'aga kai tayi alamun ta amince zaiyi magana wayar sa tayi k'ara ya d'auka yana kallon screen d'in wayar ganin bai san number ba.

   Katsewa kiran yayi bai d'auka ba wani ya sake shigowa dole ya d'auka ya saka ta a speaker yace, "Assalamu alaikum." Daga can b'angaren akace tace, "wa'alaika salam, Imran ya gida?."

D'an jimmm yayi jin muryar mace har kuma ta ambaci sunan sa ya saka shi yace, "lafiya, da wa nake magana please." Y'ar dariya tayi tace, "kana magana da Mufeedah manager a company da kake aiki."

D'an tab'e baki yayi kad'an kafin yace, "ohhh."

Mufeedah tace, "ya mai jikin?." Ya amsa da fad'in, "da sauk'i, ina wani abu yanzu zan kashe".

Bai jira mai zata ce ba ya yanke wayar tare da kallon inda Jannat take. Kamar ya sani kuwa ta kafa masa ido tunda ya fara wayar k'irjin ta yake wani irin bugu kamar ana doka ganga haka take ji tashin hankali da kishi ya bayyana k'arara a kan fuskar ta. "Wacece ta kira ka?" Ta tsinci muryar ta tana furta hakan ba tare da ta sani ba. baiyi mamakin tambayar ta ba dan bai d'auke shi a wani abu ba yace, "Manager company da nake aiki ce." Sai da ya bata amsa sannan ta fahimci abinda ta aikata ta mayar da kanta k'asa k'irjin na bugawa da sauri hankalin ta yayi bala'in tashi.

   "Dare yayi Jannaty muje ki kwanta" ya fad'a yana mik'ewa tsaye tare da kallon ta, dole ta mik'e tayi baya kamar zata fad'i yayi saurin taro ta yana fad'in, "Sannu kiyi a hankali."

Had'uwar jikin su waje d'aya ya haifar mata da sabon yanayi bayan wanda take ciki, "sannu, muje ki kwanta" ya fad'a yana rik'e hannun ta har cikin d'akin bayan ya kunna fitilar wayar sa yana haskawa, sai da ta kwanta sannan ya kalle ta yace, "Sai da safe Jannaty" yana fad'ar hakan ya fito daga d'akin ya barta a kwance tana kallon sa.

     Mayar da idon ta tayi ta lumshe bayan ya b'ace daga idon ta ta fashe da sabon kuka mara sauti, sai da tayi mai isar ta har ta kasa bud'e idon ta sabida ciwon da kanta yake mata ga bala'in zafi da take ji a k'irjin ta, runtse ido tayi tayi k'okarin mik'ewa zaune dan tana so ta fita tayi alwala sai ta kwanta amma ta gagara hakan, dak'yar ta iya mik'ewa zaune hannayen ta duka suna kanta ta dafe ta mik'e tsaye jiri ya kwashe ta tayi baya ta fad'a kan katifa idanun ta ya rufe ruf tunanin ta da hankalin ta suka tsaya cak bata sake sanin inda kanta yake ba.

Free page😁


_Wannan labarin na kud'i ne ki biya naira 300 kacal ki karanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, domin biya tuntub'i wannan number but only WhatsApp. ***_

Wattpad @ Nana_haleema

Arewabooks @nanahaleema11.