WANI RABON........

CHAPTER 18 (MEETINGS)

by @deejasmah

WANI RABON.........🦋🦋🦋


Elegant Online Writers ( E.O.W)


Khadeejah Bint Ismail ( deejasmah)


In dedication to all single ladies out there........

 

Arewabooks @ deejasmah


WhatsApp @***

N.B WhatsApp only not call😁


CHAPTER 18 ( MEETINGS)



There are people who support you in many decisions you make and in every steps you take in life,those are the realest people you need they never turn their backs on you no matter how tough the situation might be.......I'm so lucky to be surrounded by those set of people....among them are Ummu Ajmal my own soul sister Allah ya bar zumunci da soyayya ya raya su Jiddah da Ajmal wannan chaptern gabad'aya tukuici ne gareki I know that it ain't that enough for the love you've got for me but I want you to know that your love in my heart has no bounds.........Enjoy this chapter and proudly call it yours😌😍

 Arshad ma yana gaisheki😁


Grill🔐🌹


Demonstrate love by giving it, unconditionally, to yourself. And as you do, you will attract others into your life who will love you without conditions.😍❤



3rd person's POV



Ringing d'in da wayarta takeyi ne ya tashe ta daga baccin a kacalce ta d'akko wayar tana zuba ma screen d'in ido b'aro-b'aro sunan da tai saving ya bayyana "Sir A.B" bud'e idanuwanta tayi cikeda mamaki kafin tace " lafiya kuwa ?" don yau dai Saturday kuma ba wani aiki suke dashi ba wani kiran ne ya sake shigowa a hankali tai picking " Hello sir,Good morning" ta furta cikin muryar bacci 



"Morning Miss Sadauki, how are you.....sorry na katse miki bacci " ya furta a hankali " No sir Issokay I'm good sir " shiru sukayi su duka kafin a hankali yace " uhmmmm....Miss Sadauki there's a business confrence today....at SEVENTEEN HOTEL and we were invited I don't know if you can make it......."



Ajiyar zuciya tayi a hankali tace " what time is it,Sir?" Murmushi yayi har ana iya jiyo sautin murmushin nashi yace "10am " waigawa tayi ta kalli agogo 7:36 lumshe ido tayi ta bud'e " okay sir Allah ya kaimu " Ameen yace kafin ya kashe wayar 



Hamma ta sake yi kafin ta zuro k'afar ta k'asa ba yanda ta iya amma taso ace yau ta morewa baccinta yanda ya dace gefenta ta kalla Areepha bata wurin hakan yasa ta fara gyara gadon kafin ta nufi toilet wanko shi tayi tareda wanka armless free gown ta sanya kafin ta nufi parlour 



Gyaran gidan ta fara komai ta maidashi muhallinsa duk da dai gidan nasu ba wani datti yaiba turare ta baza kan ta koma kitchen breakfast ta shirya musu dai-dai da timetable d'in yau kafin ta koma d'aki 9 har ta d'an gota kad'an shiryawa tayi cikin Turkey wear lilac color riga ce tsayinta ya wuce gwuiwa sai wandonta mai fad'i sosai 



Kasancewar rigar bata zuwa da veil yasa ta d'auko wani turkey veil black ta yane kanta sai k'aramar jaka ta kamfanin LV takalminta lilac sneakers ta sanya looking so cute and simple ko powder babu a face d'inta kwalli ta sa kawai sai lip balm black smart watch ta sawa hannunta d'akin Mamie ta shiga a gaban mirror ta sameta tana shiryawa " Maa good morning " ta fad'a tana zama a gefen gadon " morning bitti.....ina kuma zaki je da safiyar nan haka? ba kince sai yamma zakuje gidan Noosrahn ba?" 


Murmushi tayi tana kallon Areepha da ta farka yanzu kafin ta maida kallonta kan Mamien " wallahi Mamie wai wani conference zaayi yau a seventeen d'azu boss ya kirani yake sanar min " kallonta Mamie tayi tace " su matsalar aikin company kenan aiki bai k'arewa ki kula dai Allah ya taimaka" ameen ta furta cikeda jin d'adi Mamie tace " yanzu gashi bamu shirya breakfast ba kije ki samu tea ne kar ki fita haka nan " dariya tayi tace " Maaa ai na had'a tun d'azu " 



Kallon jin d'adi da alfahari tace " that's very good my love Allah yai miki Albarka " Ameen tace itama cikin farincikin Adduar da tai mata Areepha ce tace " Addah inzo muje mana " kallonta tayi kacokan kafin tace " kije inaaa?" dariya Mamie tayi tace " kina kula wannan lazy bones d'in sai kinyi latti " da sauri ta tashi " aikuwa dai Maaa, sai na dawo daga can zan biya gidan bestie " tare suka fito da Areepha dake sanye da pyjamas ash color magana suke k'asa-k'asa breakfast tayi tai mush m sallama gabad'aya 



Da yake gidan babu nisa da titi yasa ta taka a k'afa har zuwa titin, kuma bata jima a titin ba tana zuwa babu dad'ewa ta samu keke sanar mai inda zata tayi ya fad'a mata kud'inta babu b'ata lokaci tace mai " muje toh " shigewa tayi tana adduar Allah yasa kar tai latti cikin ikon Allah kuwa 9:58 a bakin hotel d'in tayi mata sallamar mai keken tayi tana nufar hotel d'in ba tareda ta san inda zata nufa ba hon taji a bayanta hakan yasa ta juya da sauri daga ganin motar da tai hon d'in basai an fad'a ba tasan shine dukda bata tab'a ganinshi da motar ba but ta sanshi da son hawa motar izza and undoubtedly this Silver colored Cadillac is surely his hakan yasa ta k'arasa shiga ciki kusa da parking lot ta d'an tsaya a lokacin da yake shirin yin parking 



Shi d'inne kuwa ya fito daga motar sanye da wata Black six pieces High Arm hole suit ya had'ata da sky blue shirt da plain black trouser yayi matuk'ar yin kyau ainun lumshe ido tayi tana sake kallonshi a zahirin gaskiya Sir A.B ya iya wanka daidai zamanin shi da kuma matsayin shi don in har yai wanka ya fito ko ba'a fad'a maka ba kasan cewa Naira ta koka a jikinshi ko takalmin k'afarshi k'irar Black giliard studded leather loafers kad'ai ya ishi deejasmah jari😅😩🤲 

 Balle agogon hannunshi na kamfanin vacheron constantin cikin tafiyar nan tashi ta zaratan maza ya k'araso gaban ta ( daga kallonshi na raina kaina aradu....yoh anya za'a bani damar shiga ciki har in d'auko muku tsegumi kuwa 🤔 yoh ai korata zasuyi duk gayun da naci na biyo Faheemah a baya raina kaina nayi 😌 bari dai mugani )



K'are mata kallo yayi she really look good and smart in his eyes abunda yake k'yara birge shi da ita is her love for simplicity and uniqueness ko kad'an bata shigar wai don burge wani ko janyo attention d'in wasu kanta komai tana yinshi ne da nutsuwa da kamun kai and her modesty is next bai tab'a ganinta da shigan banza ba the fact that she's wearing suit baisa ta tab'a exposing jikinta ba tama fi sa blazer kuma trousers d'inta free ne 



Murmushi yayi tare da cewa " Miss Sadauki is always there at the right time.....duk sauri na kin fini" ya k'are da tsokana tura baki tayi tace " thank God you came at the right time too....I would have not know where to go...." Hanya ya nuna mata yana cewa " since I'm here then let's go in" wucewa yayi ita kuma tana gefenshi conference room suka nufa sun tarar wurin ya fara cika inda aka tanada dan Matawalle Global suka zauna 10:30 aka fara gabatar da abunda ya kawo su wurin wanda ya d'auke su har zuwa 2:30 kafin aka gama tare suka fito dashi kamar yadda suka shiga tare 



Taheer Ammani ne mai Ammani investments ne ya tsayar dasu suna gaisawa da kuma maganar business saidai hankalinshi duka yana kan Faheemah haushi ta fara ji balle ma mutumin naku sai wurin uku suka nufi motar kallonshi tayi a hankali tace " ni bari in nemi keke " kallo ya watso mata yana cewa " ai da yake yau na fara saukeki.....will you get in the car ko zaki tsaya ne ki zuba min ido " tana tura baki ta shiga ta zauna shima shiga yayi ya zauna ya ja motar 



A hankali tace " Ung dosa zanje " yi yai kamar baiji ba saida ya hau titi da kyau kafin yace " what for......?" 'au ashe yana jina' a zuciyar ta ta furta tana hararar gefenshi sarai yaga hararar da tai masa saidai bai tankawa hakan ba instead maimaita tambayar shi yayi da cewa " uhmmm " turo baki tayi tace " gidan k'awata zanje "



Gyad'a kai yayi can kuma yace " uhmmm....nice ta wurin ina a ung dosar?" Harga Allah ta gaji da tambayoyin shi tunda can Faheemah ba maison damuwa bane balle yanzu can ciki tace " Ishaku road " da mamaki ya kalleta saboda shi d'in bai san relationship d'inta da Noosrah ko Sahal ba don sanda akai bikinsu bai k'asa shima daga baya yaje gidan sau d'aya ne ma daga wannan kuma bai sake ba hakan yasa ya tak'aita mamakinshi maybe ba gidan bane 



A hankali tana mai kwatance har ya kawo bakin gate d'in gidan yayi kafin yace " dama kinsan Sahal ne ?" Murmushi tayi tace " yeah......." Wata tambayar ya jeho mata " what's the relationship between you two?" Da badan tana son ta bar motan da kam bazata amsa ba don ta gaji da tambayoyinshi ba cikin gajiya tace " matarshi is my better half " tana fad'in hakan ta bud'e motar tana cewa " thanks for the ride sir " shigewa tayi ta bar shi yana binta da ido yanzu ya gane wato ita d'in k'awar matar Sahal ce " oops I should have know that since....kusancin su da Sahal says that all..." Jan motarshi yayi shima yai gaba 



A gidan ta k'arashe yininta don sai Magrib ta bar gidan bayan sunsha firar da suka dad'e basuyi irinshi ba saidai ta tausayawa Bestien nata sosai saboda tabbas cikinta ba k'aramin bata wuya yakeyi ba sannan ta sauya sosai tayi bak'i haka kuma dukta kumbure kamar wacce tasha yeast k'afarta kam kamar ba nata ba don BPn ta ya hau ainun koda ta koma gidan ma maganar da ta dunga yi dasu Mamie kenan a gida dukansu fatan sauka lafiya sukaiwa Noosrahn muma dai addu'an muke mata da ma sauran mata masu tsohon ciki a duk inda suke Allah ya rabasu lafiya Ameen ya rabb 



A cikin watan kuwa kusan kullum cikin meeting suke har weekends ma hakan tun bata complain har ta fara don fitar ta fara yawa saidai Mamie ta nuna Mata cewa tai hak'uri don a hakan ma aikin nata da sauk'i compared to sauran wasu companies kuma akwai biya mai kyau kuma bata fita kowani state kuma aikin nata akwai kiyaye dokoki da tsarin addini hakan yasa ta hak'ura ta cigaba da aikin nata 



Ta b'angaren shi kuwa wata dama ne tazo mai na had'uwa da ita hakan yasa wani lokacin ko an nemi ganawa dashi ya kan kaishi zuwa weekend don hakan ne zaisa ya ganta da weekend d'in har ma ya samu damar kaita gida wata rana da Mukhtar suke zuwa meeting d'in wasu lokutan kuma su biyu ne kad'ai suke tafiya ko sun had'u yanzu kam bai binta da kallo sosai dukda dai da idanuwa kawai yake binta shima ba sosai ba saidai har k'asan ranshi yana jin soyayyarta saidai bai manta da kashedin Arshad ba hakan yasa yake kawar da maganan shi akanshi 



Yau Saturday tun jiya ya sanar da ita cewa gobe akwai meeting da Ammani investment a Bugatti dake Kaduna da k'arfe hud'u na yamma hakan yasa ta shirya cikin wata blue black d'in Arabian gown ta zura veil d'in kawai ta yana akanta sai jakarta data rik'e sallama tayi dasu kana ta nufi wajen yau kam bolt tai ordering har NNDC mall d'in 



A VIP lounge ta tarar dashi a zaune a lokacin mutanen Ammani Investment d'in basu k'arasoba ba k'aramin kyau yai mata ba kasancewar yau ba suit yasa ba ba kuma kaftan ba but sanye yake da Shirt Black da black Velvet trouser sai black palms a k'afarshi black kayan da ya sanya ba k'aramin fitowa yai da golden skin d'inshi ba he looks so simple yet handsome as always kallonta yayi yana mata nuni data k'araso 



Zama tayi a side d'inshi tana gaishe shi amsawa yai da kulawa yana kallonta da kyau don shima tayi mai kyau ainun especially yanda kayan ya haska flawless skin d'inta kana ganin ta kasan bata da damuwa ko wata matsala a duniyarta sai wanda ba'a rasa ba wayarta ta ciro tana duba abu don haka nan taji ta uncomfortable around him kuma hakan bai tab'a faruwa da ita ba Shi ko idon shi k'irrr a kanta kaman ya samu abun kallo shi har mamaki yake yanda baya gajiya da kallon ta 



A haka mutanen Ammani Investment suka zo suka tarar dasu a wurin tattaunawa suka fara yi taci sa'a meeting d'in bai wani dad'e ba suka k'are ta bayan sun samu matsaya bayan sun kammala ne Taheer Ammani ya buk'aci ganawa da Arshad d'in amma su biyu kawai don haka suka nemi wani seat suka zauna wayarta ta sake cirowa 



Bayan kamar 20 minutes ne ya taso bai ko kalleta ba yace " let's go " tashi tayi ta biyo shi a baya tana jinjina masifar shi Allah ma yaso an kawo mata shawarman da tai ordering kuma har ta biya ko da suka shiga motar ma sai tsaki yake yi kamar wanda akaiwa wani abu kawar da fuskar ta tayi daga kan shi don bata san mai tayi ba don haka bata maida hankali kan hakan ba har ya sauketa fuskar shi babu rahama sallama tayi mai ta nufi cikin gida as usual bin ta yai da kallo har ta shige cikin gida kafin yaja motar 



Ya na tafe ya na mai jin zafin kalaman Taheer Ammani wai Faheemah yake so k'wata yayi sannan ya ce " zanga ta inda zaka sake ganin ta ma balle ka ce kana sonta " lumshe idanun shi yana sak'a cewa ya gama zuwa meeting da ita tunda su mazan basu jin kunya ko kad'an ( ahhh kaji min bawa dai 😂 dama ai ita bata son zuwa don ba yanda ta iya ne kuma in mazan basu da kunya ai jinsin ku d'aya ko dan dai ya zama cewa shi wanzami bai son jarfa ne 🙄 sannan Faheemahr mu a kasuwa take ko yanzu muka samu wani Aradu gud'a zaka ji anayi 😏 Ehee)



2days later 

Faheemah's POV 

Zaune nake a office d'ina wasu files nake had'awa wanda aka kawo daga bursary department boss ne ya bani aikin in fitar da wasu reports na wasu months daga cikin duka files d'in a dai-dai lokacin ne wasu 'yan mata suka bud'e k'ofar suka shigo office d'in cike da mamaki nake kallon su don na tabbatar da cewa ba suyi knocking ba hard'e hannu nayi a k'irji ina k'are musu kallo a tsanake 



Su biyu ne d'ayar fara ce irin mai yellow-yellow d'innan kuma tafi tsawo d'ayar kuma nata farin mai sirkin ja ne kuma tafi d'ayar k'wari kallon farko na gane cewa su d'in 'ya'yan hutu ne wainda basu san babu a rayuwar su ba tsaf na k'are musu kallo sai na d'auke kai ina mai cigaba da aikin gaba na don na lura ba wani kunya suke da ita ba sai da suka gama k'arewa office d'in kallo kafin suka k'araso ciki 




Doguwar cikin su ne ta doso inda nake tana cewa " Ammm,we are here to see the president " ban d'ago na kalleta ba sai aikin gaba na da keyi maimaita maganar ta sakeyi hakan yasa na gyara zaman glass d'ina sannan na kalleta na ce " uhmm, do you have an appointment?," kallo na sukayi a tare suka fashe da dariya can tace " who's talking about appointment here ?, well munfi k'arfin hakan a nan,so tell him that yayi bak'i " 



Dariya maganar tasu ta bani don haka ban b'oye ba nayi abi na can kuma na d'aure na ce " well,you can do that yourself " kallona sukayi alamu basu gane mai nake nufi ba kallon raini suka bini dashi yanzu d'ayar ce ta tanka " mun miki kalar 'yan aike ne ?, ke muke son ki sanar dashi hakan " k'are musu kallo nayi tsaff kafin na maida kaina ga system d'in gaba na ganin tanka su ma b'ata lokaci ne hakan yasa suka fara surfa min rashin kunya ko kallonsu banyi ba don nasan cewa a girme na tsere musu and yin irin wannan hayaniyar a wurin da nake aiki tamkar zubarda mutunci na nayi hakan yasa nai gum da bakina tamkar bana wurin amma k'ok'arin neman securities nake su zo su fidda min su daga office



 " Zeezah what the h**k are you doing here?!!" A matuk'ar tsora ce muka juya don jin muryan da kuma mai muryan dake tsaye a bakin k'ofa nan da nan jikin su ya fara tsuma niko kallo d'aya nai musu na kawar da kaina don na fahimci sun fi kusa da juna..............



I'm so sorry kun jini shiru 2 days banda lafiya ne amma na fara warwarewa Alhamdulillah naga messages d'inku na gode k'warai da kulawa deejasmah taku ce 😍❤

#vote

#comment

#share

#add

Love y'all😍


Deejasmah🦋🔐❤