Chapter 15
*ZANEN ZABUWA*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 15*
Kallon inda ta nuna yayi yace, "kar ki damu Jannat zanyi masa bayani ya fahimta." Ita dai ba jin sa take ba hannun ta har rawa yake ta bud'e murfin motar ta fito kanta a k'asa.
A hankali take takawa zuwa inda yake yana kallon ta har ta k'araso ta wuce gida bai kalle ta ba sai kallon Muhsin da yake yi da yake k'arasowa inda yake. Kusa dashi ya k'arasa ya d'urkusa har k'asa yace, "Abba barka da dare." D'aure fuska Abba yayi yace, "barkan ka."
"Sunana Muhsin ni d'an makarantar su Jannat ne." Kallon sa Abba yayi sosai yana nazarin sa kafin yace, "dan kana d'an makarantar su shine kake d'auko ta a mota a daren nan?." Gigiza kai yayi yace, "A'a Abba, sun jima yau basu fito daga jarabawa ba shiyasa da ta fito ta jima bata samu abin hawa ba shine nace tazo na sauke ta dak'yar ta amince ta biyo ni."
Abba ya sauke numfashi yace, "to madallah an gode."
"Abba kuma daman nace zan zo na same ka akan matsalar da Jannat take ciki, tunda muka samu labarin ta rasa yayan ta shikenan ta koma kamar ba ita ba ko karatu bata mayar da hankali a kansa koda yaushe cikin tunani take ta keb'ance kanta, shiyasa nace daman zan zo na same ka domin karatun ta ba irin wanda zata dinga saka damuwa bane yana buk'atar nutsuwa da kuma maida hankali." Abba dai yayi shiru yana jin sa har ya kai k'arshe sannan yace,
"Shikenan an gode in sha Allah kuma za'a yiwa tubkar hanci." Murmushi Muhsin yayi yace, "babu komai Abba, a tashi lafiya." Ya fad'a yana mik'ewa daga tsugunon da yayi ya nufi motar sa Abba yana kallon sa har ya shiga mota ya b'acewa ganin sa kana ya mik'e ya shiga gida.
Sallah ya tarar Jannat d'in nayi ya samu waje ya zauna har ta idar sannan yace, "Khadijah yaushe kika koma haka ban sani ba? Yaushe kika fara shiga motar samari ban sani ba?." Jikin ta ya fara rawa ta kasa magana sai kanta da tayi k'asa dashi tana tunanin abinda zata ce masa.
Gwaggo ya kalla yace, "wato yarinyar nan tunda Imran ya b'ace ta canja halayyar ta gabad'aya ashe daman dalilin ganin idon sane ya saka take a nutse, yanzu kuma da baya nan sai ta samu damar yin abinda ta ga dama, wai Jannat ce ta shigo gaban motar wani saurayi wanda bata sani ba ya kawo ta gida a daren nan." Gwaggo da take sauraren sa tace, "waye shi yaron?."
"Ina zan san waye nima, yaro zubin yaran manya ne da basa jin magana sun raina kowa musamman talaka wai Jannat ta biyo shi a mota ya kawo ta gida."
Shiru Gwaggo tayi tana kallon Jannat da ta kasa cewa komai sai raba ido da take yi jikin ta na rawa kana kallon ta kaga mara gaskiya, "Jannat ya haka?" Gwaggo ta fad'a tana kallon ta.
Shiru tayi ta kasa cewa komai sai k'asa da ta kuma yi da kanta tana fara sharar kwallah.
K'wafa Abba yayi kafin yace, "daga yau sai yau in na sake ganin ki a motar wani saurayi ya kawo ki wallahi sai na sab'a miki kuma daga ranar kin daina zuwa makarantar kenan daman ba so nake na, ke ni a yanzu ma sai na hana ki zuwa dan banga abinda kike tsinanawa ba." Gwaggo tace, "ayi hak'uri ka sake bata dama in ta sake sai a hana ta d'in."
Baice komai ba ya mik'e ya fita daga gidan don ransa a b'ace yake sosai.
Gwaggo ta kalli Jannat tace, "Jannat da hankalin ki da tunanin ki ina ke ina shigowar motar saurayi ya kawo ki gida? Kin san fa yadda duniyar nan ta lalace ba kowa ne na kirki ba inda ya cutar dake fa?."
Jannat da take kuka tace, "Allah Gwaggo sai da nace bazan shiga ba ya dinga had'a ni da Allah shiyasa ma na shiga kuma shine wanda ya taimake ni jiya yau ma in badan shi ba da yanzu ban samu jarabawar farko ba dan lokacin da naje na makara".
"Shikenan naji kidai kiyaye gaba kin san halin mahaifin ki tsaf zai hana ki karatun nan." D'aga kai tayi alamun to Gwaggo ta mik'e ta shiga d'aki ita kuma ta tayar da sallar i'sha.
Da wuri ta shiga gidan Umma ta kwanta ta d'auki wayar ta ta shiga inda take adana hotuna tana kallon hotunan Imran d'in ta, murmushi take tana hawaye tana cigaba da gani.
Kira ne ya shigo wayar ta ta kalli number taga bata san ta hakan ya saka tak'i d'auka ta cigaba da kallon ta. Wani kiran ne ya kuma shigo ta kalli inda Umma take kwance taga tayi bacci gudun kar ta tashe ta ya saka ta mik'ewa ta koma falon Umma kafin ta d'auki wayar da sallama.
"Wa'alaiki salam, Jaana ya kika koma gida?." Jin muryar wanda batayi tunani ba ya saka ta cikin mamaki tace, "Muhsin daman kana da number ta?."
"Woww! woww!! dan Allah sake maimaita suna na naji."
"Muhsin."
"Oh god, tunda nake a duniya ban tab'a jin wanda ya iya fad'ar sunana kamar ki ba, dan Allah ki cigaba da fad'a har sai nace ki bari."
D'an murmushi tayi tace, "Baka amsa min ba." "I'm sorry wallahi sweet voice d'in kine ya saka na manta da komai, but ke ya akayi kika gane nine?."
"Your voice." Ta bashi amsa a tak'aice.
Murmushi yayi mata har taji sautin sa yace, "Yau ni kaina ina da tabbacin zanyi bacci da na jima banyi irin saba Jaana, yanzu har matsayin da nake dashi a wajan ki ya kai ki rik'e murya ta?."
"Inda zaka bani amsar tambaya ta da nafi jin dad'i."
"Okay sorry, na jima ina da number ki tun lokacin da na saka a nemin komai naki har da number ki aka kawo min."
Shiru tayi bata ce komai ba jin hakan ya saka shi yace, "kiyi hak'uri d'azu nasan Abba yayi miki fad'a nasan kuma nine silar hakan badan na d'auko ki ba da yanzu hakan bata faru ba." Ajiyar zuciya tayi tace, "ya wuce."
"Nagode."
Shiru tayi nan ma bata ce komai ba yace, "na baki labari?." Tace, "uhum."
"Wata rana wani saurayi da budurwa suna tafiya sai ga wani mahaukaci yazo wucewa sai saurayin yaga budurwar nan ta kalli wannan mahaukacin tace, "Wane daman baka mutu ba?." Sai saurayin nan wanda suke tare yace, "daman kin san shi ne?." Tace, "eh na san shi tsohon saurayi nane da ya yaudare ni shine na haukata shi." Sai kawai saurayin nata ya fara kuka yace, "wallahi ni bazan yaudare ki ba."
Dariya sosai Jannat take yi bayan ya kai k'arshe labarin ta manta dare ne ba rana ba take kyakyata dariya abin ta, "amma dai anyi matsoraci, koda yake banga laifin sa ba data haukata ci gwara yayi mata kuka" ta k'arasa fad'a tana sake sakin wata dariyar.
Shiru yayi yana jin yadda take dariya ko ba'a fad'a ba yasan ya gefa ta cikin nishad'i a daren hakan ya saka shi jin dad'i shima, sai da ta gama dariyar sannan tace, "nagode sosai Muhsin ka sani farin ciki a wannan lokacin."
"Fata na kenan daman Jaana na saka ki farin ciki shine abinda nake so."
"Ai kuwa ka saka ni nagode sosai."
"Kinfi k'arfin hakan a waje na, dare yana yi kije ki kwanta kar ki makara gobe kina da exams."
"Haka ne, sai da safe."
"Allah ya tashe mu lafiya kyakykyawa ta." Daga haka suka yanke kiran Jannat ta mik'e ta shiga ciki har lokacin da murmushi a fuskar ta a haka ta kwanta bacci ya d'auke ta cikin nishad'i.
B'angaren Muhsin tana kashe wayar yayi murmushi shima ya kwanta akan gadon sa idon sa lumshe yana jin sabon nishad'i yana shiga jikin sa, numfashi ya fesar kafin yace, "i love you Jaana, buri na na saka ki farin ciki fiye da wanda Imran ya saka ki, Allah ya mallaka min ke matsayin mata ta." Da wannan tunane-tunanen shima bacci ya kwashe shi.
Tun daga ranar shaquwa ta fara kawo ziyara a tsakanin Jannat da Muhsin, koda yaushe cikin waya suke inda bata je makaranta ba zai kira ta suyi waya ko suyi video call har lokacin bai tab'a furta yana son ta ba duk da ya bayyana mata alamomi da dama amma bai furta ba.
B'angaren Jannat d'in itama zuciyar ta ta fad'a tarkon Muhsin domin kuwa soyayyar sa tayi mata mugun kamu har ta kai ta kawo takan iya d'aukar k'afa taje makaranta kawai dan su had'u koda bata da lecture dan tun daga ranar da Abba yayi mata fad'a bata kuma yadda Muhsin ya kawo ta gida ba.
Soyayya suke a b'oye duk da babu wanda ya furta a cikin su amma kwayar idon su da kuma gangar jikin su zata tabbatar maka da k'aunar da suke yiwa junan su.
Yau ta kama ranar talata da wuri Jannat ta tafi makaranta domin lecture k'arfe takwas ce da ita, bayan sun fito daga lecture farko malamin da zai musu ta biyun ya sanar da class captain bazai samu damar shiga class d'in nasu ba sai next week hakan ya saka kowa ya fara watsewa dan lecture biyu dasu a ranar.
Jannat na zaune a inda take jiran Muhsin koda yaushe tana aukin kalle-kalle tana so ta ga ta inda zai b'ullo, daga can nesa ta hango motar sa yana yi mata fitila alamun ta k'araso tayi murmushi ta d'auki jakar ta ta k'arasa inda motar take.
Gaban motar ta bud'e mata yace, "shigo mana Jaana." Yadda taji maganar sa ya saka ta shiga ta kalle shi tace, "lafiya kake kuwa?." Idanun sa ya d'ago ya kalle ta yace, "me kika gani?." Bata daina kallon sa ba har lokacin tace, "yanayin ka ya nuna baka da lafiya kalli idon ka ma duk ya canja."
Ajiyar zuciya yayi yace, "Jaana!." Jin yadda ya ambaci sunan ta ya saka ta kalle shi tace, "Na'am." Gyara zama yayi ya fuskance ta sosai yace, "i love you Jaana, i love you more infact ban san iya adadin son da nake miki ba, tun ranar dana fara ganin ki na kasa mantawa dake har kawo yanzu, i want to marry u Jaana."
Wani irin zirrrrrrrr Jannat take ji yana zaga ko ina na jikin ta har tafin k'afar ta dana hannun ta, jin wannan shocking d'in take yi a ko ina na jikin ta gashi ta kasa d'auke idon ta daga kansa shima kuma ita yake kallo, abubuwa da dama take gani a cikin idon sa shima kuma hakan take a b'angaren sa, ta kasa tantance abinda take ji a zuciyar ta kamar farin ciki kamar akasin sa ta kasa gane yanayin ta a lokacin, lumshe ido tayi ta bud'e a kan fuskar sa har lokacin shima ita yake kallo.
"Ina son ki Jannat, ina qaunar ki, ina burin ki zama uwar y'ay'a na, Jannat zaki aure ni?." Ya katse mata tunani da fad'in haka yana kallon ta kamar zai mata kuka sabida soyayyar ta da yake ji a jikin sa na zagayawa ko wanne b'angare.
Kwantar da kanta tayi a jikin kujerar motar tana jin sabon yanayin da bata tab'a ji ba yana bin ko ina na jikin ta, hannun ta d'aya ya rik'e ya sake cewa, "shirun ki na haifar min azaba a cikin zuciya ta, zuciya ta tana cike da fargabar abinda shirun nan naki yake nufi, dan Allah kar kice A'a wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Da gaske ina son ki kuma auren ki zanyi, kar kiyi tunanin nafi k'arfin ki sabida matsayin mahaifi na nida ke duka d'aya muke."
Jin yadda yake jijjiga mata hannu cikin wani irin salo ya sake kashe mata jiki ta kasa furta masa komai sai idon ta da ta sake runtsewa tana sauke numfashi a hankali.
"Jaanaaaaaa!." Ya fad'a cikin wata murya mara sauti wacce take can k'asa kamar baya son maganar.
Dogon numfashi taja jin yadda sunan ya shiga har cikin kafofin gashin jikin ta ta sauke numfashi tana jin wani irin yanayi a tare da ita.
"Do u love me jaanaaaaa!?." Ya sake maimaitawa yana murza yatsun hannun ta fuskar sa na gab da tata. Numfashin sa da yake fita da dumi yana shiga kafofin hancin ta ya gauraye da khamshin jikin sa ga khamshin motar ga sanyin a.c da yake tashi sai hakan ya so ya jefa ta cikin sabon yanayi ta rasa nutsuwar ta sai lumshe ido ta dake sake yi.
D'aga masa kai tayi alamun eh ba tare da tasan tayi hakan ba, da sauri ya kalle ta ya sake cewa, "kina sona Jaana?." Sake d'aga masa kai tayi alamun ehh kafin ta sauke kanta zuwa kan cinyoyin ta ta saka hannu d'aya ta rufe fuskar ta.
"Wayyo na Allah." Shine abinda ya furta ya koma jikin kujera ya jingina yaja hannun ta zuwa saitin zuciyar sa ya d'ora tana jin yadda zuciyar sa take bugawa da sauri. Sai da suka sami mintina sama da biyar a haka kafin ya dawo nutsuwar sa ya bud'e ido ya sauke su a kanta har lokacin kanta na kife a cinyoyin ta yace, "dan Allah Jaana ki d'ago ki kalli cikin ido na kice ina son ka Muhsin."
Tana jin sa amma bata tunanin zata iya d'agowa tayi abinda yace hakan ya saka ta sake nutsa kanta a jikin ta tana jin wani irin nauyi a lokaci d'aya.
"Jaaanaaa please." Jin yanayin muryar sa kamar zai mata kuka ya saka ta d'ago ta kalle shi tace, "Ina son ka Muhsi....." Ai kafin ta kai k'arshe yayi mata wata kyakykyawar runguma kamar zai b'alla mata k'ashin bayan ta.
"Thanks you Jaana, Allah ya saka miki da alkhairi, Allah ya biya ki Jaana, nayi miki alqawarin baki dukkan farin cikin da kike nema a duniya, zan kula dake fiye da ko wanne d'a namiji a duniya, zan so ki fiye da yadda zan so kaina, zan kula dake fiye da yadda zan kula da kaina Jaana, i love you soooo much Jaanaaaaaa". Sharrrrr hawaye ya zubo daga idon sa domin yanayin da yake jin zuciyar sa in baiyi kuka zata iya tarwatsewa gwara ya fitar yaji dad'i.
Tsintar kanta da tayi akan k'irjin sa sai yaso ya mantar da ita a duniyar da take ciki domin wata irin nutsuwa da soyayyar sa taji tana fitowa daga k'irjin sa yana shiga nata k'irjin, khamshin turaren sa da take shak'a ya hana ta katab'us tana jin abu mai d'umi yana sauka a wuyan ta zuwa bayan ta.
Sun d'auki lokaci mai tsaho a haka suna sauk'i soyayya ya hana su komai sai sauraron bugun zuciyar juna da suke yi.
D'ago ta yayi daga jikin sa ya rik'e fuskar ta yace, "nagode sosai Jaaana zan cigaba da son ki daga nan har a tashi duniya, zan cigaba da qaunar ki daga nan har Allah ya zare min rai, ina son ki Jannat."
K'asa tayi da idon ta tana murmushi ganin hawaye a idon sa ba k'aramin farin ciki taji ba ganin a akan son ta yake kuka sai take ji kamar tafi ko wacce mace sa'a a duniya.
Zoben dake karamin tsayan hannun sa ya zaro ya ja hannun ta na haggu ya zira mata tsayan kusa da karamin yace, "wannan shine zoben alqawari Jaaana, nayi miki alqawari bazan tab'a rabuwa dake ba duk tsanani duk farin ciki muna tare, zan kula dake fiye da komai a duniya, zan soki fiye da yadda nake son kaina."
Murmushi tayi tana kallon hannun nata ta koma wajan ta ta zauna tace, "nima nayi maka alqawarin duk tsanani duk dad'i ina tare da kai babu abinda zai raba mu." Murmushi yayi kana ya mik'o mata hannun sa alamun ta saka masa zobe kamar yadda yayi mata.
Kallon hannun nasa tayi tace, "Bani da zobe da zai maka ni ai amma zan samo nima." Kallon hannun ta yayi na dama yace, "ga wani nan ina gani." Kallon wanda yake magana akai tayi gaban ta ya fad'i ganin wanda Imran ya bata ne domin alqawarin wata magana baza ta sake had'a su da Muhsin ba, haka kawai ta ji fad'uwar gaban ba tare da tasan dalilin hakan ba.
Kallon sa tayi tace, "Yaya na ne ya bani wannan bana son rabuwa dashi." D'age gira yayi yace, "Zoben yayan ki ya fini kenan?."
"Haba ni na isa nace haka? Yayi maka kad'an kuma ai."
"Ni a haka nake so indai bai fini mahimmaci ba ki bani."
Numfashi ta sauke ba musu ta fara zaro zoben daga hannun ta kalaman Imran suna yi mata yawo a cikin kanta, _duk ranar da kika cire zoben nan kin karya alqawari kenan._ maganar sa ta fad'o mata ta runtse ido ta zare ta sakawa Muhsin a yatsan sa k'arami.
Kallon azurfar yayi yace, "yayan ki ya iya zab'e tayi kyau sosai." Shauk'in soyayyar sa da take ciki ya saka tace, "kuma kasan dalilin bani zoben nan akan meye?." Girgiza mata kai yayi yace, "A'a matata sai kin fad'a."
"Lokacin da kuka yi fad'an nan yace kar na kuma kula ka wannan zoben na alqawarin bazan sake kula ka bane, amma kasan meyasa na baka?."
Y'ar dariya yayi kad'an yace, "Sabida cewa yayi kar na kuskura wani fad'a ya sake shiga tsakanin mu dakai kuma naga wannan ai ba fad'a muke ba na tabbata koda yana nan zaiyi farin ciki da hakan ko?."
"Sosai ma kuwa Jaanaa, ai yayan naki yana kula dake sosai amma duk da bazai kai ni kula dake ba insha Allah."
Murmushi tayi mai kyau bata ce masa komai ba ya kunna motar suka fara tafiya yace, "gobe in Allah ya kaimu zan zo na samu Abba na gabatar masa da kaina a matsayin mai neman auren ki dan bana so a d'auki lokaci nafi do nan da 3 months mun shiga daga ciki."
"Da wuri haka?."
"A bari ya wuce ai shine ya kawo rabon wani, haka kawai na tsaya sanya wani yazo ya kwace min ke?."
"Bana tunanin akwai irin wannan mazan."
"Wow! Ashe dai na gina babbar fada zuciyar Khadijaty."
Bata ce komai ba sai murmushi yace, "zaki raka ni wani waje?." Ta kalle shi tace, "ina kenan?."
"Gidan gona Daddy ya aike ni abu zan karb'o kawai mu fito." D'an jimmm tayi kafin tace, "muje."
"Thanks you."
Tafiya suke suna hira irin ta masoya ko wanne yana jin d'an uwan sa a jikin sa har suka k'arasa gidan gonar ya shiga ciki yayi parking yace, "Ki jira ni yanzu zan dawo." D'aga masa kai tayi yayi murmushi yace, "i love you" ya bud'e motar ya fita ta bishi da kallo har ya shige ciki.
Masu tsaron k'ofar da Imran suna ganin sa suka k'arasa suka kwashi gaisuwa shi kuma ya shiga ciki.
Yana zaune kamar koda yaushe idon sa a rufe sai bakin sa da yake motsawa alamun karatu yake ko magana yake yi, murmushi Muhsin yayi yana kallon sa yace, "Malam Imran yau nazo maka da wani babban albishir wanda zai sanya ka farin ciki."
Bud'e ido Imran yayi ya kalle shi baice masa komai ba ya d'auke kansa ya mayar gefe. Waya Muhsin ya d'auko ya shiga cikin hotunan sa ya lalubo hoton da ya saka ayi musu da Jannat suna tsaka da hira a makaranta ba tare da ta sani ba, nuna masa yayi yace, "nasan baka manta wannan ba ko?." Kallon wayar imran yayi ai bai san lokacin da ya samu kuzarin kwace wayar a hannun sa yana zooming fuskar Jannat.
"Tabarakallah haka Jannty ta koma? Ashe ina da rabon sake ganin fuskar ki Jannty?." A rud'e yake maganar muryar sa har rawa take gata a dashe ba'a ji sosai, kana jin yadda yake maganar kasan zuciyar sa cike take da kewa da kuma begen sake ganin fuskar Jannat.
Ganin kamar ma bai k'unsa masa bak'in cikin da yake so ya sake shi ba ya kwace wayar yace, "Ka daina kallon fuskar matata malam."
"Na fad'a maka Jannat baza ta tab'a zama matar ka ba."
"Haka kake tunani dai, amma bara na saka maka wani abu kaji."
Danne-danne yake a wayar kafin ya kunna sai ga muryar Jannat inda take yiwa Mushin alqawarin babu abinda sai raba su.
Kallon Muhsin Imran yayi duk da jikin sa yayi sanyi da jin muryar tata dan ko a wanne yanayi yaji maganar ta zai gane ta, ganin ya d'an shiga rud'ani ya saka Muhsin yin murmushi ya nuna masa azurfar hannun sa yace, "wannan fa? Kaine ka bata akan alqawarin kar ta sake kula ni ko? To gashi ta bani ita kuma a kan alqawarin baza ta tab'a rabuwa dani ba duk tsanani, koda kana tantama akan itace ta bani d'in zaka tabbatar ta hanyar ya akayi nasan cewa kunyi wannan alqawarin da ita,? Imran na fad'a maka ba'a ja dani a zauna lafiya kana zaune a nan zan kawo mata iv na bikin mu da Jannat dan yanzu haka tare muke da ita tana zaune a mota."
Ganin Imran din yayi shiru ya kasa cewa komai ya saka Muhsin murmushin nasara yace, "na barka lafiya siriki na daman zuwa nayi na shaida maka k'aunar dake tsakani na da k'anwar ka dan Allah Yayan mu ka saka mana albarka." Ya k'arasa fad'a yana wani mayaudarin murmushi yana kallon Imran din yana tafiya da baya kafin ya juya ya fice ya barshi a zaune yana saqa da warwara.
_Oh ready an fara payment na book2 naira 300 ne har ynzu, domin biya tuntub'i wannan number 2347045242700 but only WhatsApp._
Wattpad@ Nana_haleema
Arewabooks @nanahaleema11.