P-2
Page🟩2
------Baby ta leƙo ɗakinsu Ummita ta ce"hey guys ku fito Momcy na kiranku??kun san yau Dady na zai dawo kunga sai ku taya mu sauran aikin ko".?
Ummita ta ɗan ɓata rai kaɗan, don i'ta arayuwarta ta tsani aiki wannan aikin ma don babu yadda za tayi ne da babu abinda zaisa tayi.Ta turo baki gaba suka fito tare falon Khairat kuwa ko kallonta bata yi ba, don mugun haushinta take ji saboda mugun burin da take dashi arayuwarta, kana ɗan talaka?amman ka dinga ɗorawa kanka rayuwar da ba taka ba?.
Suna i'sowa falon Kyakkyawar matar na zaune tana waya, hankalinta ƙwance Ummita ta kalli ƙafarta yadda aka rangaɗa mata lalle me matuƙar kyau, daman gata fara sol kamar balarabiya sai lallen yayi kamar don ita aka yishi.
Tuni Ummita taji wani irin mugun mashin baƙin ciki ya tsarga mata, sai taji dama ita ce Wannan matar Yadda take rayuwarta ita kaɗai agidanta, ka mijinta kyakkyawan ƙarshe, wanda take ji dama ace mijinta ne, to da daga ranar ta hanashi fita saboda sa idon ƴan mata.
Bayan Halima ta gama wayar ne ta ce"Ummita Khairat ku tashi mu shiga kitchen, dafatan dai kun iya girki ko"???.
Ɗaga kai sukayi dukansu, Ummita kuwa sai kallonta take har sai da Khairat ta ɗam dungure ta sannan ta juyo suka shiga kitchen ɗin, sosai Take kallon kitchen ɗin tana yaba irin mugun kyaun da ya yi, kitchen ne me mugun girma gashi an tsarashi sosai, komai na kitchen ɗin ja ne da fari harda wata ƙatuwar Tv a kitchen ɗin, Ummita fa ta samu abin kallo don har Halima ta fito musu da kayan aikin bata san ma an fito dasu ba, ita dai hankalinta yana kan kayan kitchen ɗin wani abin ma idan ta ganshi tsoro yake bata.
Khairat ta ɗan taɓata kaɗan sannan ta dawo hayyacinta, Halima ta fara koya musu komai yadda ya zasuyi amfani da kayan kitchen ɗin, nan da nan suka fara aikinsu cikin ƙwarewa, Ummita ta ƙware a girki sosai, don aƙwai wata me siyarda abinci da tayi aiki awajenta to ananne ta zama star awajen girki.
Halima tayi mamaki sosai, don wani abin ma itace ke koya mata yadda za tayi, don haka sai ta saki jikinta ta barsu suka cigaba da gabatar da komai yadda ya kamata.
Halima ta wuce kai tsaye ɗakinta ta shirya cikin wasu haɗaɗɗan leshi wanda ya amsa sunansa, tayi kyau sosai sai walƙiya take gwanin sha'awa, kai ka ce yau take sallah Ummita ta saki baki da hanci tana kallon Halima, alokacin da take shigowa cikin madafar,ta nuna musu yadda zasu jera kayan abincin,shi kanshi dining ɗin abin kallo ne, ƙato ne sosai zai iya cin kujeru sha huɗu,an ƙawatashi sosai bayan sun gama aikinne Halima ta basu kaya tace su sanya,Kaya ne masu kyau sosai kana ganinsu kuma kasan masu tsada ne sosai.
Ummita ta ajje kayan ta shiga banɗaki wanka, sosai take kallon banɗakin yadda akayi matuƙar ƙayatashi,komai na banɗakin kalar sararin samaniya ne, Ummita kam bata iya amfani da komai ba, don haka ta fito kai tsaye,Khairat ta kalleta ta ce"lafiya dai Ummita?ke fa nake jira inyi wanka?".
Ummita ta ɓata rai sosai sannan ta cuno ɗan ƙaramin bakinta ta ce"Anty Khairat Allah na rasa yadda zanyi anfani da komai na banɗakin nan".?
Khairat ta ce"to ba sai mu tambayi Baby ba?a'i ina ganin zai fi sauƙi ko"?.
Ummita ta ɓata rai sannan ta ce"Hmm Gaskiya Khairat kina son jaza mana raini wallahi,yanzu idan banda haka a'i ba sai mun tambaye ta ba?muje kawai muyi ta gwadawa har mu samu mu iya komai".?
Khairat ta kalli ƙanwarta sosai sannan ta ce"kash!gaskiya Ummita girman kanki yana bani mamaki?idan banda haka wai har kike faɗar zan jaza mana raini wajen Baby?ke idan kina da nutsuwa da hankali,a'i mu awajensu musakai ne mu?amman basu ɗauke mu haka ba?don me mu baza mu yi musu biyayya ba?yanzu idan muka shiga banɗakin muka ɓata wani abin fa?ke kina ganin zamu iya gyarawa?kuma sai muje muce musu me"?.
Ummita ta taɓe baki sannan ta ce"To sai dai ke kije ki tambaya amman ni dai bazanje ba?wannan ma a'i salon jazawa kai raini ne."
Ita dai Khairat bata kulata ba ta wuce wajen Baby,A falo ta same ta tana waya,sai da ta ɗan tsaya ta kamalla sanna ta juyo da murmushi ta ce"Anty Khairat ya naga bakiyi wankan ba"?.
Khairat ta ɗan murmusa sannan ta ce"daman wallahi banɗakin ne muka kasa amfani dashi,to shine nace bari mu tambayi Baby".
Baby ta ce"to muje Anty Khairat,don yanzu saura minti sha biyar jirginsu Dady ya sauka,kuma kunga tare zamuje daku don taro Dady na".
Khairat dai bata ce komai ba,don ita sam ba tada magana,idan kaji tayi magana to sai dai abu ne me muhimmaci,ita a ganinta a'i bai kamata a tafi dasu taro wannan hamshaƙin kyakkyawan ba,gashi kuma su da suke masu aiki?a'i gwara a barsu agida su ƙarasa wasu ayyukan,kuma sai take gani kamar dai matar gidan tasa an kawo sune don su ɗauke musu kewa,don masu aiki maza da mata sunfi Goma agidan,duk kuma suna sanye ne da uniform ɗinsu gwanin sha'awa.
Ummita na ganin shigowarsu ta miƙe ta tashi,tana ɗan sosa ƙeya don ita aganinta a'i abin kunya ne wannan.
Baby kuwa kai tsaye ta shige banɗakin,ta koya wa Khairat komai ita kuwa ƴar girman kan tana ɗaki ta kasa zuwa taga komai.
Baby ta fito abinta,tana tsokanar Ummita ta fita waje,Ummita na ganin ta fita ta matso kusa da Khairat ta ce"ni wallahi Kunyar Babyn nan nake ji wallahi,musamman ma yanzu da kika sa ta gane mu ƴan ƙauye ne".Khairat dai bata ce mata komai ba ta fara cire kayanta tana ɗaura wani tawul alamar zata shiga wanka.
Ganin hakan yasa Ummita ta wuce banɗakin da gudu tana cewa"tunda an kunna fanfon a'i ba komai,bari inyi wanka na wankan da ban taɓayi ba,don taro kyakkyawa Baban Baby".
Ita dai Khairat kasa magana tayi,saboda yadda take nuna abu afili babu wani ɓoye ɓoye,Baban Baby shi kuwa wata irin macece bai taɓa gani ba?tunda yanzu ma wataƙil daga garin turawa xai dawo?."
Wani irin mugun ihu Ummita tayi,da gudu ta fito tana ihu tana cewa"wayyo Allah na fuskata,na ƙone Wallahi fuskata ta ƙone don Allah Khairat ki duba min"?.
Abinka da ɗan uwa da sauri Khairat ta fara duba mata fuskar,da yake Ummita fara ce sai ga wajen har ya ɗashe yayi jawur..sai kuma lokacinne Khairat ta tuno Baby ta ce mata fanfan na ruwan zafi ne,ga bokiti nan idan tana son ta haɗa ga fanfan sanyi nan gana Zafi,idan kuma da shower zasuyi gashinan,duk ta koyawa Khairat komai ita kuma ƴar girman kai bata tsaya ta koyi komai ba,ita dai abinda ta sani girman kai da kuma Buri.
Sosai Ummita ke kuka,Khairat tayi rarrashin har ta gaji sannan ta miƙe ta ce"Kizo muje in nuna miki yadda ake amfani da komai,don naga ke har yanzu baki san komai ba amman kuma girman kai ya hanaki ki koya".
Babu yadda Ummita za tayi,dolenta ta shige gaba suka shiga banɗakin don itama tana son koya,ko don gaba tunda sunzo gidan ne bada niyyar yini ba.
Khairat ta nuna mata komai sannan ta fito daga banɗakin,Sosai Ummita tayi wanka kamar zata canja fatar jikinta,tana yi tana santin ruwan da kuma sabulun,saboda ruwan wani irin mugun daɗin wanka ne dashi,ga sabulun da mugun ƙamshi gami da kumfa kamar kamfanin sabulu.
Ta ɗauki mintina da dama tana wannan wankan,har Khairat ta gaji taje bakin banɗakin tana bugawa,amman Ummita ko ajikinta sai da ta gama tsaf sannan ta fito,alokacin har Baby ta iso kuma lokacin bai fi mintina ya sauka ba.
Baby ta ce"kash!har yanzu baku gama ba?Momy na ta jiranku?to bari mu tafi saboda wallahi sun kusa sauka,gwara muje kuyi haƙuri yanzu zamu dawo".
Ummita ta kasa magana saboda tsabar baƙin ciki,ji take kamar ta kamo Baby ra daka taso ace yau ɗaya sunje filin jirgi amman Baby ta hana faruwar hakan,a cewarta wannan a'i baƙin ciki ne don kada aga Babanta.
Ita kuwa Baby taba fitowa ta samu Halima har ta shiga danƙareriyar motarta tana jiransu,Securities suna tsai tsai suna jiran su shiga su rufe.
Baby na shiga kuwa suka rufe,Halima ta ce"Baby lafiya kika taho ke kaɗai?ko basu shirya bane"?.
Baby ta ce"eh Momy basu shirya ba,kuma kinga Dadyna ya kusa sauka."
Halima ta ce"haka ne gaskiya don yanzun ma sai dai muyi sauri".
Halima na bada uder ɗin su tafi,motocin suka biyo bayansu wasu agabansu wasu a bayansu haka suka tafi Filin jirgin Baby sai murna take ita dai za taga Dadynta.
Halima kuwa duk bayan mintina sai tayi murmushi,yau wata biyu kenan rabonta da ta saka gwarzon mijinta a idonta,tana masifar son mijinta da kuma ƙaunarsa,bata son duk wani abunda zai shiga tsakaninta da mijinta,tana addu'ar Allah ubangiji ya barta da mijinta har abada.
********
. . .kai tsaye Indo gidansu ta wuce,tana shigowa gidan ta iske Innarta na tankaɗe,Indo ta zumbuɗo baki gaba sanan ta ce"gettere ! Yauma tuwon zakiyi Inna?gaskiya ni bazanci ba".?
Ko kallonta Innar bata yi ba,ta cigaba da tankaɗenta,Yayar Indo Aminatu nata wanke wanke,ta ce"don Allah Indo zo ki ƙarasamin zanje Makarantar Allo in bada hadda"?.
Indo ta ce"oh ni sai akace miki gantali nake ko?to zauna ki ƙarasa kayanki,kije kuma kisha bulalar malam Modibbo".
Aminatu tayi rau rau da idanuwa sannan ta ce"Inna kice mata ta tayani Allah za'a dake ni,ita kuma kinga ba zuwa take ba yanzu".
Inna ta kalli Indo sannan ta ce"ke yanzu Indo sai ance miki ki taya yayarki aiki?ke kullum babu abinda kika iya sai shegen yawo?babu arabi babu boko"?.
Indo ta zumɓuro baki sannan ta ce"Allah don Inna ta saka bakine da babu abinda zanyi,tunda ke kin iya haɗa mutum da iyayensa."
murmushi Amina tayi kawai ba tare da tace komai ba,don Idan Indo na da kunya baza ta ce mata wai tana haɗa ta da iyayenta ba,don mahaifinsu yana masifar son Indo akaf cikin ƴaƴansa,yana son Indo sosai son da shi kansa baya yiwa kansa,bai ƙi yarasa komai ba indai zai buɗe idanuwansa ya gansa gashi ga Indo.
Aminatu ta wuce kawai ta sanya hijabinta,sannan ta ɗauki allonta ta wuce abinta,Indo kuwa sai harararta take ita kuwa Inna sai kallonta take sannan ta ce"idan kin gama hararar ƴar uwar taki sai ki wuce kiyi wanke wanken".
Indo ta zauna ta ƙarasa wanke wanken,tana roƙar ubangiji Allah yasa wani ya shiga gonarta yaji jiki,ai kuwa akayi sa'a sai ga Matar Babanta ta fito daga ɗaki,wacce ake cewa Inna Harira ta ce"Indo yau kuma ke ce da wanke wanke?duk rashin kunyarki?duk yadda akayi wani rashin mutuncin kike so ki ƙulla".
Indo bata kulata ba ta cigaba da wanke wankenta,Innar Indo kuwa Murna take Indonta ta fara hankali,tunda gashi an kulata don ayi rigima kuma taƙi kulawa.
Daman matan Mahaifin Indo Huɗu ne,Kuma mahaifiyarta ce uwar gida ammanfa mahaifin Indo mutun ne me auri sake,ya auri mata yafi sai a irga,wasunsu akan Indo ake sakinsu wasu kuma wani dalilinne,su Indo suna da yawa a ƙalla zasu kai Su ashirin da biyar wasu yaran suna gidan wasu kuma suna wajen iyayensu,Indo ƴar gata ce sosai awajen mahaifinta,ko da mahaifiyarta ne kuwa zai iya yin kacaca don yana masifar sonta kamar ruhi.
Indo ta kammala wanke wankenta ta kai ɗaki ta ajje,Allah ya taimaketa Inna ta gama Tuwonta da wuri.
Inna Harira ta kalli Mahaifiyar Indo a wani wulaƙance sannan ta ce"yauwa Idan kin sauke zan ɗora ruwan zafi".Innar Indo ta ce"la babu komai zo ki ɗora Harira".
Inna Harira ta ce"saka Indo ta ɗoramin saboda kaina ke ciwo".Innar Indo tasan babu wani ciwon kai amman saboda kada dai ta bada ita awajen Indo ta ce"Indo zo ki ɗorawa Innarki ruwan zafi".
Nan ma Indo bata ce komai ba ta wuce abinta wuce ta ɗora mata ruwan zafin,Tazo zata shiga ɗakinsu kenan Inna Harira ta watso mata ruwa,sai tayi sauri ta ce"yi haƙuri fa ban sani ba".
Tana faɗar hakan ta tintsire da dariya sannan ta wuce ɗakinta,Innar Indo tana jinta tasan babu wani tana sane tayi hakan,Indo ta shigo ɗakin ko ajikinta ta cire kayanta,agaban Innarta babu ruwanta don ita kullum ganin kanta take ƙaramar yarinya.
Innar ta ce"Indo wai ke haryanzu baki girma bane?a yanzu fa kina da kusan shekara sha huɗu amman baza ki daina wannan haukar taki ba"?.ki kiyaye ni akan kina cire kaya agabana."
Indo ta turo baki sannan ta ce"ba Inna Harira ce take son ta kaini ƙarshe ba?Allah ina tsoron muguntar da zan mata,don wallahi har ta mutu baza ta manta dani ba ehe".
Indo ta faɗi hakan tana cire wasu kaya riga da wando kamar na pakistan,cikin kayan da Baffanta ke siyo mata.tana saka kayan tana murguɗa baki tare da mita.
Innar Indo ta girgiza kanta don tasan Indo baza ta daina abinda take ba,sai kuwa taji Indo ta kyalkyale da dariya sannan ta ce"hhhhhh ho ni Indo magani Hegi da Hegiya maganin ƴar banza da ɗan banza,a taɓoni a taɓo masifa ka barni ka zauna baki alekum".
Innar ta kalleta sosai,ita wani lokacin ma idan Indo tayi wani abun gani take kamar ba ita kaɗai ce tayi ba saboda yadda ta iya zaro maganganu.. . . . .✍🏾