P-4
Page🟪4
---------Babu yadda za tayi haka tabi Baby suka shiga sashen Hajiya gabanta sai faɗuwa yake,suna shigowa ɓangaren Allah ya taimakesu Hajiya bata falon,Sosai hakan ya faranta ran Halima ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da suke a danƙareren falon Hajiya.
Ta cewa Baby"bana son in shiga ɗakin Hajiya don ina tunanin ko ba ita kaɗai bace,in kin shiga Baby sai kice tare muke don wataƙil ko Baba yana nan don naga sashensa abuɗe".
Baby ta ce"to Momy bari in shiga sai in gaya mata,amman ni wallahi da nayi zamana anan,don bana son masifar wannan jarababbiyar tsohuwar".Baby ta faɗi hakan tana chono baki gaba don ta tsani duk wanda baya son mahaifiyarta,don ita fa haryanzu gani take Halima ce mahaifiyarta,don bata taɓa nuna mata wani abu da zaisa ta san ita ba mahaifiyarta bace,kuma ko gorin da akewa Halimar ma cewa take'wai su Momy basu san sanda kika haifeni bane?ko don sunga har yanzu baki sake haihuwa bane'?.
Sosai maganar ke dukan zuciyar Halima,sai dai babu yadda za tayi don tasan ba itace ta haifi Baby ba,amman har aranta tana jin kamar itace ta tsugunna ta haifi Baby,tunda yayarta ce ta haife ta.
Baby na shiga ta iske Hajiyar Maska na waya,tana ganinta ta kashe wayar tana cewa"sai da Safe Hajiya Talatu".
Baby ta ce"Hajiya Ina wuni".?
Hajiyar ta kalleta sannan ta ce"lafiya klau Taƙwarata,ya gidan?yau uwar baƙin halin ta barki kizo inda muke?saboda kada mu cinye ki?amman a'i kina zuwa gidan Hajiya Xulaiha ko?tunda ita wannan kakarki ce ta wajen uwa ko"?.
Baby ta zumɓuro baki gaba tamkar zatayi kuka ta kalli Hajiya da Lulu Eyes ɗinta ta ce"Hajiya ni fa Momy bata hanani zuwa nan gidan,nima makaranta ce ke hanani zuwa wajenku".
Hajiya ta ce"ni zaki faɗawa makaranta?babu weekend ne?ke dai kawai kice uwar riƙonki ta koya miki baƙin hali?to a'i kuwa idan kika ce halin wannan zakiyi zakisha wahala sosai".
I'ta dai Baby bata ƙara magana ba,don Allah Allah take ta fita daga ɗakin,sam bata san taji wani ko wata yana zagar mata mahaifiya,kuma ta tsani kalmar nan da mutane ke faɗa mata a kullum wai Mimynta ba mahaifiyarta ba ce.
Tana cikin wannan halinne taji Hajiya na cewa"kinzo kin tsaya min aka kamar wata sandar ba'are,ke idan an faɗi laifin uwar riƙonki sai ki hau cika kina batsewa kamar zakiyi duka ko?".
Baby ta fara magana a ƙage ta ce"Hajiya don Allah abar wannan maganar,ni da Momyna ce ita tana falo,kuma mun rako Dadyna yau ya dawo daga tafiyar da yayi".
Hajiyar Maska ta fara magana cikin faɗa.
"Oh aiko ki tayi kizo ki jawo ni ki kai ni?bata san ɗakina ba?ko kuwa yau ma ranin tazo ta gwadamin?to wallahi Halima ta kiyaye ni,idan ba haka ba zata san tayi da ƴar garin Maska".
Baby kuwa tsabar fushi kasa tsayawa tayi,ta fice fuuu cikin fushi sai taji sam bata san ganin matar,saboda yadda ta tsani mahaifiyarta dama ta hana kowa zaman lafiya,Alhali ita ta zauna lafiya da mijinta,don Hajiya kaka ba mutum ce me tsaurarawa ba,duk da dai tana da faɗa amman faɗanta sai an taɓa ta sannan takeyi ba haka kawai irinna Hajiyar Maska ba.
Baby na fita Hajiyar Maska ta ce"Ni wallahi al'amarin Baby yana bani mamaki?Yarinya kamar wacce aka yiwa asiri?kullum ana gaya miki ga hanyar da zakibi don ki cusgunawa wannan mayyar data liƙewa ubanki,ammanke kullum kare ta kike?to ni nasan abinda zanyi don yau ɗinna ba sai gobe ba,zan nunawa Halima cewar ita bata isa ta dinga haɗani da ɗana ba."
Itw kaɗai dai take ta faɗanta.
MD yana shigowa ya ce"a'ah Ya kuma kika zauna anan Halima"?.
A hankali ta ɗago don kanta ne yake sara mata,haka take ita bata iya saka abu aranta ba,yanzun nan sai kaga ta rame ta zama abar tausayi.
"Hajiyar na ciki ne shiyasa ban shiga ba,ba jira ta fito amman Baby ma tace ita kaɗai ce,yanzu ma shiga zanyi mu gaisa".
Bai ce mata ƙala ba ya wuce abinsa,don shi ba mutunne me magana ba,shiyasa wasu suke ganin kamar yana da girman kai,kuma shi haka Allah yayi sa aƙwaishi da miskilanci,wannan kuma halin mahaifinsa ne,don shima ba ruwansa ba komai ya kewa magana ba,sai dai yana da zuciya sosai,don ko su Hajiyar Maska suna shayinsa sosai.
Yana shiga Hajiya tayi masa banza kamar bata san Allah yayi ruwansa ba,yana ganin hakan yasan lallai aƙwai abinda ya faru,sai dai bai kawo komai ba ya tsugunna har ƙasa,sannan ya fara gaida mahaifiyar tashi cikin girmamawa.
Hajiyar Maska ta kalleshi sannan ta ce"yanzu Muhammad har nayi lalavewar da za'a rainani haka?matar ka ta zauna min a falo sannan ta ce wai inzo mu gaisa?tasan kuwa ni wacece awajen ta?Muhammad kana neman aljanna kuwa?kana son ka gama da duniya lafiya kuwa?".
Da sauri ya kalli Hajiyar tasa sannan ya ce"Hajiya wallahi ban san abinda ke faruwa ba?na tambayeta yanzu tace abinda yasa bata shigo ba ta ɗauka ba ke kaɗai bace,shiyasa bata shigo ba amman kiyi haƙuri Hajiya".
Da sauri Hajiyar Maska ta ce"inyi haƙuri Muhammad?saboda an cuce ni?sai ka zuba ido yanzu matarka tana wulaƙantani?ta inda Salis ya fika kenan?matansa guda biyun nan bai yarda kowaccensu ta nemi rai nani ba,amman kai sai ka tsaya mace na juya ka kamar sitiyarin mota".
Kasa magana yayi,amman kana ganinsa kasan ransa a matuƙar ɓace yake amman ya daure ya sunkuyar da kansa.
MD mutunne me mugun haƙuri,sai dai yana da zuciya sosai saboda haka bai fiya son zaman garin ba,saboda Tashin hankalin daya ke ciki,tsakanin matarsa da mahaifiyarsa,yasha zama yayi tunani akan abinda yake haɗa mahaifiyarsa da matarsa amman bai taɓa gano komai ba,kawai dai abinda ya gane abune guda ɗaya shine matuƙar Halima zata zo inda Hajiya take,to dole sai an samu matsala idan kuma bata zo ba shima matsalar ne,tunda matan ƴan uwansa duk suna zuwa gidan,bai kamata ace matarsa ce kawai bata zuwa ba,saboda wani dalilin ɓatawarta da Mahaifiyarsa,shi kuma ya rasa yadda zaiyi a samu maslaha.
A hankali ya tashi tsaye duk karsashin daya zo dashi sai yaji yanzu duk babu shi saboda ɓacin rai,haka ya fito zuciyarsa na masa wani irin zafi.
Ko daya ke yanzu dai idan akayi duba na tsanaki,za'a ga tabbas Halima ce da laifi saboda a'i ita ya kamata taje har inda Hajiya take,ba Hajiyar ce zata zo inda take ba.
Halima na ganin fuskarsa tasan lallai Hajiya ta haɗa ta da mijinta,sai dai koma menene ta shirya ƙarɓarsa tunda yau tazo inda Hajiya take,kuma tasan dole sai wani abin ya faru.
"Halima me yasa bakya son zaman lafiya ne?me yasa kullum kike son haɗani da Hajiyata ne?ne yasa bakya son in zauna lafiya da mahaifiyata?kina son in shiga aljanna kuwa?Halima bana son inyi miki abinda zakizo kina dana sani ne,shiyasa nake kyale ki kullum ina ɗorawa mahaifiyata laifi,akan wannan matsalar da muke ciki,amman ke bakya ganin duk wani ƙoƙarina?zan amshi raganar duka al'umma yanzu,kina son in shiga tashin hankalin da zan kasa biyawa mutane buƙatarsu,waɗanda suka ɗauramin nauyi?Halima ina son ki shiga har ɗakin Hajiya yanzu ki bata haƙuri,haƙiƙa abinda kika yimin yau ya ɓata min rai sosai."
Halima kuwa tunda ya fara magana ta sunkuyar da kanta,ta kasa ɗagowa ma ta haɗa idanu dashi duk da daman idan Mijinta na mata magana ko haɗa idanu bata yi dashi,don dai ta bashi girmansa na mijinta tare dayi masa biyayya.
Wasu hawaye ne masu zafi suka fara zubo mata,ita da Mijinta zata iya irga sau nawa suka taɓa yin faɗa,tasan mijinta ba shida matsala zasu iya shekara ba tare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba,kullum cikin zaman lafiya suke gwanin sha'awa.
Hajiya na tsaye duk tana kallon diramar dake faruwa,duk da haka bata ji daɗin yadda Muhammad ya yiwa Halima ba,taso ace yaci mata mutunci sosai idan ma har da dama ya haɗa mata da takaddar saki,don ita ayanzu babu abinda take farin cikin gani irin taga an saki Halima,amman shiru duk abinda take haɗa mata bata ji sakamako ba.
Hajiya ta ce"Muhammad a'i ni har yanzu baka burgeni ba,saboda daman irin wannan faɗan da kake mata kamar wani lusari shiyasa take rai na ka,amman babu komai ni nasan matakin da zan ɗauka.
Wata irin tsawa ya yiwa Halima yana cewa"Halima!ba cewa nayi kije ki bawa Hajiya haƙuri ba?me yasa kike son ɗoramin magana ne?me yasa bakya son zaman lafiya ne"?.
Halima ta tashi a hankali,jikinta har kakkarwa yake saboda tsawar da MD yayi mata,ta je har gaban Hajiya ta tsugunna sannan ta ce.
"Hajiya don Allah kiyi haƙuri,in sha Allah bazan sake miki makamancin haka ba,ki yafe min don Allah"?.
Hajiyar Maska ta kalle ta sannan ta ce"sai anyi magana ki dinga sunkuyar da kai,daman irinku haka kuke Ni dai Allah ya haɗa ɗana da masifa ta aurenki,aure kusan shekara goma sha amman babu ɓatan wata har yau."
*****---*****
. . .Inna Harira ta miƙe tana masifa tana ce wa"Wallahi bazan yarda ba,wannan shaiɗaniyar yarinyar ce ta sanya min yaji acikin ruwa,wallahi bazan yarda ba hegiyar yarinya mara kunya,wacce bata aan mutuncin mutane ba Allah ya isana wallahi".
Ta faɗi hakan tana kuka kamar ƴar ƙaramar yarinya.
Ita kanta Innar Indo ta gane ƴar tata ce tayi,amman tasan ta inda zata biyowa Indon,don daman mahaifinta ke ɗaure mata gaba don ta raina kowa.
Inna Harira dai ranar masifa ta dinga yi,matan gidan kuwa ko kallon arziƙi bata ishe su ba don daman tuni sun daɗe da yin faɗa da ita,don bayan Innar Indo itace me fawa agidan,don su ƴan kallo ne agidan,don ko Innar Indo darajar ƴarta take ciki ne gidan yake ɗaga mata ƙafa,amman Inna Harira ita ce me gidan sai yadda ta dama haka ake sha,sai dai fa Indo ƙadangaren kan tulu ce,bata fito ba sai da ta shirya don babu inda bata je ba,akan a haɗa Indo da mahaifinta amman sai suce mata su baza su iya ba,don sun gano wani babban al'amari a tsakanin Baban Indo da ƴar tasa.. . . .✍🏾